← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 110

Sashe 8

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta kunna haske ta tsaya tana kallon ɗakin, sai kuma ta cire mayafin ta ajjiye ta shiga banɗakin. Banɗakin sai ya bata tsoro, dan bata taɓa ganin banɗaki mai girmansa ba, duk yadda ta kai ga ganin girman banɗakin Jeddah, wanda ta buɗe a yanzu ya fi sa girma. Bata tsaya tunani ba, ta gwada kunna shower ta tabbatar komai ya yi, sannan ta yi wanka da alwala. Garin buɗe-buɗe ta buɗe drawer ta ga brush da thoothpaste duk a ledar su, ta yi amfani dashi sannan ta fito.

Kayan da Safeera ta zo mata dasu ta buɗe, ta ɗauki doguwar riga ta saka ta tsaya tana kallon uban kayan da aka bata jiya, ga wata sarƙar gold kamar ta yi magana da bakinta saboda girma.

Ta É—auki waya ta kira Sadik amma bai É—auka ba, tana kiran Safeera ta É—auka, Safeera ta ce, "Amaryar Rehaan, ya aka yi?."

"Ban taɓa zagin ki bane, kar ki yi fatan na fara zagin ki yanzu."

Safeers ta yi dariya jin ƙawar ta a fusace sai ta ce, "me ya yi zafi? Tuba nake ranki ya daɗe.”

"Don Allah ki shiga gida ki duba min Hamma, na rasa ya zan yi, ki duba min shi kafin anjima na fito nazo na gansa"

Da mamaki Safeera ta ce, "ki fito ina?."

"Gidan mana."

"Rufa mana asiri, kar ki fito don Allah.”

"To na rasa ya zanyi, ina so na yi magana da Hamma, bazan iya zama Hamma yana fushi dani ba, yana ganin kamar na zaɓi kuɗi na bar sa. Bazan iya ba wallahi, dole na fito daga gidan nan, bazan iya cigaba da zama ban san halin da yake ciki ba."

"Kwantar da hankalin ki, zan je na gano shi in sha Allah. In ki ka fito yanzu abin bai yi tsari ba, kuma za a fara yawo da ke ana cewa daga kawo ki jiya kin fito daga gidan, daman na ga kamar kakarsa da wannan maman ne kaÉ—ai suke yi miki maraba a gidan."

Islaha cikin rashin damuwa ta ce, "dukkansu basa gabana wallahi, abinda na ga dama shi zan yi, ko wanda ya ajjiye ni bai isa ya dakatar dani ba balle su, dan haka da su so ni, da kar su so ni duk bai damu islaha ba. Ke kin san daidai nake da kowa, ko babar ta sa ce fito na fito zan yi da ita, tunda ban ɗauke ta uwar miji ba.”

Safeera ta sanyaya murya ta ce, "ban da dai babarsa, shi É—in dai."

"Ina faɗa miki ne ai ba wai dan zan yi ɗin ba, itama in ga zata kawo min abinda bazan ɗauka ba wallahi ta kanta zan bi na wuce. Ke Mama kaɗai na ke yiwa biyayyar dole, itama saboda Hamma nake ɗaga mata ƙafa."

"Kwantar da hankalin ki Islaha, In dai Hamma ne yanzu zan je na duba miki shi. Ya za ki yi da aiki gobe?."

"Zan zo."

"Kamar ya?."

"Kamar yadda ki ka ji. Kin ga, ni ba ta aiki nake yi ba, ki je ki duba min Hamma kafin na zo."

Safeera ta ce, "sai na dawo" ta faɗa tana yanke wayar ita kuma ta miƙe jin tana son shan ruwa, kuma a ƙasa ta bar ruwan hakan ya saka.

Tana ƙarasa sakkowa falon aka buɗe ƙofar ba tare da knocking ko an danna door bell ba, hakan ya saka gabanta ya faɗi ta tsaya cak a inda take tana kallon wajan har aka ƙarasa shigowa parlour. Da yake tana tsaye tana kallon wajen ana shigowa suka haɗa ido, gabanta ya faɗi, ta ɗan rufe ido ta buɗe tana sake kallon wajan........

Nana haleema.

RDB3P06
Nana Haleema.

Haɗa ido suka yi da ƙawar Mamy, bayanta kuma Mamy ɗin ce ta shigo tana amsa waya cikin ƙasarta ƙasarta. Islaha ta ɗan yi dumm dan ita bata san da wacce fuska zata karɓe su ba, bata san da me suka zo ba balle ta shirya musu, kuma duk ta gane fuskarsu, ta tuna yadda suka yi dasu a asibiti, da yadda komai ya faru, sannan tana lura da kallon da matar take yi mata, irin kallon raini da ƙasƙanci.

Islaha ta ƙarasa tahowa falon cikin dakiya da son kawar da komai daga ranta, a lokacin Mamy ta sauke wayar ta ɗaga kai tana kallon Islaha.

A daidai lokacin Islaha ta ƙaraso ta kalli Mamy suka haɗa ido, sai ta kawar da kai gefe ta rasa me zata ce musu, ta rasa da wacce kalma zata tarbe su tunda fuskarsu a ɗaure take, ta daure ta ce, “Sannu da zuwa, ina kwana.”

Kafin Mamy ta yi magana ƙawar ta da suke kira sa Ammi ta ce, “in bata kwana ba za ki ganta ne? Ka ji min yarinya da karanbani? Kin manta rashin kunyar da ki ka yi mata a asibiti ko?.” Islaha bata ce komai ba, dan ba ita take kallo ba wani waje take kallo daban.

Ammi ta ce, “Ki ka je ki ka yiwa kakar Rehaan asiri ki ka san yadda ki ka yi aka aura miki Rehaan har ki ka kwana a gidan nan, kina murna ke kin samu dami a kala ko? To ga ki ga gidan nan ai, sai mu gani in za ki samun ribar auren Rehaan ɗin. To in ba dan aikin asiri ba me Rehaan zai yi da le don Allah? Kalli Babar sa” ta faɗa tana nuna Mamy da take tsaye kawai bata ce komai ba.

Ammi ta ce, “kamar ki latsata jini ya fito, saboda kyau da haske. Ki kalli ƙannensa, ke kin san ke ba sa’ar aurensa ba ce. Na rantse da Allah da ace na san ke za a aura masa, da sai na san yadda na yi na ɓarar da faruwar hakan kafin yau, ɓe Rehaan zai yi da ke saboda Allah? Ya zauna dake ya ce ya zauna da wa?.”

“Matarsa!”

islaha ta furta ba tare da ta sani, bata san ta faɗi maganar ba, kawai jin kalmar ta yi ta fito daga bakinta, yadda matar take jawabi tana wani zare idanu ne ya saka ta kasa riƙe magana, shiyasa ta ce mata haka dan ta ji me zata ce.

Ammi ta ji shock na mamaki, ta buɗe baki kallon ta, sai ta kalli Mamy da take kallon Ammi ɗin ba Islaha, ta sake kallon Islaha ta ce, “rashin tarbiyyar ta ki za ki sake nuna min? Ni ki ke kallo ki ke cewa kece matar ɗana Rehaan? Ina matar tasa ta ke? A ina ki ka zama matarsa, ta suna ko ta rubutu?……”

“Ki faɗa min wacce matar kirki ce za a kawo ta gidanta, miji yana wani wajen ko ina ta ke bai sani ba?……”

Ta nuna Islaha da yatsanta ta ce, “ki kiyaye ni, in ki ka ce za ki min rashin kunya sai na saka an ɓatar da ke daga duniyar wallahi, ni ba sa’ar ki ba ce, ni matar former deputy gov of Adamawa state ce.”

Sai a lokacin Mamy ta ce, “Ammi mu bar maganar nan haka.”

Ammi ta juya tana kallom Mamy ta ce, “kina ji tana yi min rashin kunya? Wacece ita a garin nan da zan dinga faɗa ina faɗa kamar wata sa’arta?
Wacece ita?.”

Islaha ta sake zuwa wuya, ranta ya sake ɓaci daman a ɓace yake, ta buɗe baki zata sake yin magana sai ta fasa jin maganar Mamy.

Mamy ta dafa Ammi ta ce, “ya isa haka, mu yi abinda ya kawo mu, kin san ina da baƙin da suke jirana.”

Ammi ta yi ƙwafa tana hararar islaha sannan ta ce, “Daman so nake mu faɗa mata Rehaan ya fi ƙarfin ta, so na ke ta san sai dai ta zo a mai aikinsa ba dai matarsa ba, shiyasa na ce mu zo nan.”

Mamy ta yi tsaki jin daman zuwan ba shi da mahimmaci ta takura mata akan su zo ta ce, “shine silar zuwan? Na yi tunanin wani abun ne ya saka ko ka ce na zo?.”

“Warning nake so mu yi nata, kar ta saki jiki a gidan nan, dan gidan nan ba wajen zamanta bane. Sannan duk abinda ya samu Rehaan itace, kin san yaron nan ya tara maƙiya, tsaf za a haɗa baki da ita a cutar dashi.”

Mamy ta ɗan kalli Islaha ta ga ta zubawa Ammi ido tana kallo, kamar zata yi magan sai ta fasa. A take wayar Mamy ta fara ƙara, tana ɗauka ta fita daga falon tana amsawa.

Ita kanta Islaha da kallo ta bita, domin ba sai ance maka Mamy tana da kyau ba, ba sai ance maka mamy ta haɗa jini da india ba, kai kana gani ka san ita ɗin ƴar ƙasar waje ce.

Ji ta yi an yi snapping fingers a kusa da fuskar ta, sai ta kalle Ammi ta ga tana harararta ta ce, “ba ki isa ba wallahi, yaranmu suna gida a zaune su basu zo wannan matsayin ba sai ke. Ba ki isa ki zo inda suka kasa zuwa ba, ba ki isa ya zama ke ce a nan su suna gida ba, sune suka dace da zama a nan bake ba, su ne suka dace da zama matar Rehaan ba ke ba. Ki rubuta ki ajjiye, sai na zama silar barin ki gidan nan, bana ƙaunar ganin ki ko kaɗan.”

Islaha ta yi wani mayaudarin murmushi da ya tsaya iya fuskar ta, ta yi holding hannunta a ƙirji tana kallon ta ta ce, “ashe shiyasa ki ke ɗaga hankalin ki har ki ke wannan maganar, ashe na ki yaran ki ke so a ta ya a kawo su nan Allah bai yi ba. Ni ɗin da da ki ke ganin ban kai ba, sai gani a matsayin da na ki yaran basu zo ba, kuma babu wanda zai fitar dani sai Allah, ko yanzu na mutu, zan tashi da suna matar Rehaan.”

Ammi ranta ya sake ɓaci ta kalle ta a fusace ta ce, “ni ki ke faɗawa wannan maganar banzar?.”
Chapter 8 · 0% Book details