← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 110

Sashe 94

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rehaan ya faɗa a ransa jin kalmar Mama tana ƙoƙarin kayar dashi, in bai ambaci Allah ba zai iya kifawa a wajen, ya rufe idanunsa saboda yadda ya ji maganar tana juyawa masa kamar ana juyawa dashi a sama, bai sani ba ko kunya maganar ta ba shi, ko kuma meye bai gama fahimta ba.

Mamy ta kalli Islaha sannan ta kalle su ta ce, "an samu misunderstanding ne, amma babu yadda za a yi Islaha ta aikata wannan abinda ku ke faɗa. Ni na yarda da ita, kuma na san baza ta taɓa aikata abinda ku ka ce ta yi ba."

"Nazo na gani da idona ki ce ba haka ba? Na kamata tana ƙoƙarin danne min ɗana ki ce baza ta yi ba? Lallai Nadira kina da son zuciya, kina da son kai da nuna naki naki ne a ko yaushe. Kuma ina so ki sani, ko tayi ko ba tayi ba, tunda idona ya gani wallahi sai ta bar gidan nan, ai ba gidan ubanta bane."

Rehaan ya kasa jure wannan cecekucen na su ya ce, "Umma don Allah na ce bar maganar nan."

Ta juyo ta kalle ta ce, "baza a bari ba, sai an faÉ—a!" Ta faÉ—a cikin É—aga murya tana kallonsa.

"Me ya ke faruwa ne haka? Hayaniyar me nake ji daga ɓangaren nan kamar ba dare ba?."

Duk suka juya suna kallon Abba da ya shigo shi da matarsa ta ƙarshe, Abba ƙaraso yana kallon kowa yana nazarin fuskokinsu sannan ya ce, "lafiya dai ko?."

Sai kawai Umma ta fashe da kuka ta ce, "lokacin da na ce maka yarinyar nan tana so ta lalata Salman ba ka yarda ba, sai ake ganin kamar ƙarya nake yi mata, saboda ita matar ɗan gold ce bata laifi. To ka tambayi Saddiƙa, a gabanta komai ya faru, yau mun kama ta da idanunmu a cikin falon nan, ta kwanta a kansa tana ƙoƙarin cire masa kaya. Ni wallahi bazan cigaba da zama da yarinyar nan a gidan nan ba, dole ta bar gidan nan ko ni na bar shi!."

Abba ya kalli Islaha da har lokacin fuskar ta take a rufe, ga gashinta ya sauka har ƙasa ya rufe fuskar gabaɗaya. Ya kalli Rehaan ya ce, "kai me ya faru ne?."

Umma ta buÉ—e baki cikin mamaki ta ce, "shi zaka tambaya ya faÉ—a maka abinda ya faru? Ni bazan faÉ—a ka yarda ba ko?."

Abba bai kulata ba ya sake kallon Rehaan ya ce, "baza ka yi magana ba?."

"Abba ni ban san me ya faru ba, na ga dai kawai sun shigo suna ta faÉ—a. Ban san ya aka yi suka shigo parlour nan ba."

Umma ta sake kallon ta ce, "na faÉ—a maka da idona na ganta, ita tasan na ganta. Wai meyasa baka yi min adalci a gidan nan ne, meyasa a komai sai ka nuna kafi son Rehaan a kan Salman? Dan Rehaan yana da kuÉ—i shikenan sai a dinga nuna mana banbanci a tsakaninsa da sauran yara? Ko dan Salman yana da lalura sai ya zama bashi da amfani? Wallahi ba ka yi mana adalci a gidan nan, ba kai yi mana abinda ya kamata" ta faÉ—a cikin kuka sosai.

A lokacin Mama ta shigo riƙe da hannun Daada da ta je ta taso ta daga bacci dan ta san abinda yake faruwa. Daada ta nemi waje ta zauna ta ce, "Hayaniya ta cika gida, duk girman gidan nan ina jiyo amon muryarsu har ɗakina, Me ya faru?."

Umma ta ƙarasa ta zube a gaban Daada tana kuka ta ce, "dan ɗana yana da taɓin hankali, dan an ga shi kaɗai na mallaka namiji a gidan nan, dan Allah ya ɗora masa lalura shikenan sai kowa ya juya mana baya? Ba a yi min adalci a gidan nan, ana nuna min ba shi da wani amfani tunda Allah ya jarabce shi da matsalar ƙwaƙwalwa. Ko yaushe Rehaan ne akan daidai a gidan, ba ya taɓa yin laifi, ko da ya yi laifin ana ninkewa a nuna kamar ba a gani ba, kawai dan yana da kuɗi?. Ya ake so na yi, da rashin lafiyarsa zan ji ko da rashin adalcin da ake yi min a gidan nan?."

Daada ta ce, "ba ki faÉ—a min abinda na tambaya ba har yanzu."

Umma ta ce, "ni da Saddiƙa, ido da ido muka kama yarinyar nan da Salman a ɗakin nan, fitila a kashe sannan tana kwance a samansa."

Daada ta kalli Umma ta ce, "ke ki ji tsoron Allah Salamatu!."

"Wallahi abinda muka gani kenan Daada, ba ƙarya mu ke yi ba" Mama ta tabbatarwa Daada tana kallonta.

Daada ta kalli Islaha da take yadda take, ta kalli Salman da ya rakuɓe a gefe ɗaya yana kallon su, ta kalli Rehaan da har lokacin yana tsaye hannunsa yana cikin aljihu, ta kalli Mamy da ta jingina da bango bata ce komai ba.

Daada ta ce, "bayan hotuna da video da ya ke yawo a duniya, abin har ya kai ta fara ƙoƙarin lalata mana Salman?."

Umma cikin kuka ta ce, "na faɗi abinda ya faru maimakon Abba ya goya min baya sai yake kallon Rehaan yana tambayarsa me ya faru, kenan ni ga maƙaryaciya?. Da safe zan bar gidan nan, zan ɗauke sa mu bar gidan, zamu bar mata gidan tunda mijinta shine mai faɗa aji. Wallahi tunda ta zo gidan nan nake ganin canji, tunda ta zo gidan ann shikenan ya susuce. In ba nuna masa take yi ba ya za a yi ya sani, in ba buɗe masa ƙofar nan ta yi ba ya za a yi ya iya buɗewa?."

Daada ta kalli Islaha ta ce, "amma wannan yarinya ba ki kyautawa kan ki ba, ban ji daÉ—in wannan abubuwan da suke faruwa ba, duk soyayyar da na nuna miki sakayyata kenan a gare ki?."

Sai a lokacin Islaha ta fashe da kuka mai sauti, har lokacin bata buÉ—e fuska ba sai kukan da ya ke fitowa.

Daada a tausahe take magana ta ce, "ni so nake a raba aure kawai, a yanke duk wata alaƙa da yake tsakaninmu kowa ya huta......"

Ta ɗaga ido ta kalli Rehaan ta ce,"Kai! Ka saki yarinyar nan kowa ya huta, in Allah ya kaimu gobe sai ta tafi. Zamu iya zama da ita a gidan nan ba, mutuncinmu zubewa zai yi. Tunda bata jin kunyar Allah ta gayyato yayanka dan tana taƙamar ba shi da hankali, bata san Allah zai tona mata asiri ba, ai ko dan saboda idanunka sai ta ɗan saurara wani abun. Tunda abin haka ne, ka sake ta bana buƙatar ganinta a gidan nan ko kaɗan, laifina ne da na dage sai da aka auro ta, ban gama fahimtar wacece ita ba, a yanzu ina so ka sake ta."

Rehaan ya ja numfashi mai tsaho ya sauke a hankali, yana jin yadda kukan Islaha yake ratsa ko ina na falon, sautinsa kaÉ—ai ake ji dan kowa ya yi shiru tana jira ya ji me zai ce. Ya kalli Mamy da take kallonsa, sannan ya kalli Daada ya ce, "a bar maganar nan zuwa safiya."

"Baza a bari ba! Saboda ba ka da kishin kanka?yarinya tana neman Yayanka da iskanci amma ka tsaya kana cewa bar maganar zuwa gobe? Matarka ce fa, aurenta ka ke yi tana neman wasu mazan da auren ka!" Umma ta faɗa da ƙarfi tana kallonsa.

Ya kalli Umma ya ce, "kin ce matata ce, tunda kin san tawa ce babu ruwan ki da maganar kishi. Ina sake tabbatar miki da ita ɗince, ni nake da iko da ita ba wani ba, kuma bani da niyar sakinta a yanzu, kuma baza a saka ni na sake ta. Kawai ku bar maganar nan, kowa ya je ya kwanta!" Ya ƙarashe maganar cikin bada umarni.

Umma ta ji kamar ta faɗa cikin wuta saboda takaici da baƙin ciki, ta kasa magana sai kallonsa take yi zuciyarta tana zafi. Mamaki yake bata tana tunanin daman ya iya rashin kunya haka? Dan ita tasan daga ina yini wata magana bata sake haɗa su.

Mama ta ce, "ai kuwa dole ka sake ta, ko dan ƙimar gidan nan. In ka bar ta a gidan nan mutuncin Daada zubewa zai yi a idanun dangi, kaf dangin Abba alfahari ake da jikokin Daada babu ɓata gari, in ka bar wannan ka lalata mata suna."

Daada ta amshe ta ce, "rabu da shi, bazan tashi daga wajen nan ba sai ya saki yarinyar nan, saki uku zai yi mata ba saki É—aya ko biyu ba, so na ke in ta bar gidan nan ta bar shi kenan har abada."

Abba ya kalle Rehaan shima ya kalli Abba kafin Abba ya ce, "Rehaan."

Rehaan ya dakatar da Abba ya ce, "Abba kar ka ce komai don Allah, ka bani dama na yi abinda nake ganin ya dace dani, ko yaushe kaine ka ke saka, a wannan lokacin ka bari na yi komai da kaina. Bani da ra'ayin rabuwa da ita a yanzu, kuma bazan rabu da ita ba. Na ga dai duk kun damu da abinda aka ce ta yi saboda ni ko? Kuna ganim kamar ta ci amanata ne, kuna ganin bata dace ta zauna dani ba ko? To ni na amince zan cigaba da zama da ita a haka, bana buƙatar a sake maimaita min maganar nan, Ina son zama da ita, kuma bazan rabu da ita ba."

Daada ta buÉ—e baki ta ce, "ta shanye shi, wallahi ta shanye mana shi. AbdulAziz kana kallo ko? In ba wanda aka shanye ba ace matarka ta aure tana yawon banza, tana neman Yayanka da mugun abu ka ce kana son zama da ita? Dole mu dage da addu'a."

Rehaan shi Daada mamaki take bashi, kamar ba itace ta dage akan auren ba, ya kalli Islaha da take kuka shi kuma kukan ne baya so, ya sake yin tsaki ya ce, "mu je a hakan, ni dai ku je sai da safe, don Allah!" ya faÉ—a yana nuna musu hanya.

Nana Haleema.

RDB3P69
Nana Haleema.

Saboda yadda suka kaure da hayaniya ba ya jin abinda suke faÉ—a, Daada tana yi, Mama tana yi, Umma tana yi kamar zasu cinye shi. Abba da Mamy da Anty ne kaÉ—ai ba su ce komai ba.
Chapter 94 · 0% Book details