← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 110

Sashe 61

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma cikin faÉ—a da fusata ta ce, "baza ka sha a hannuna ba sai itace zata baka dan ba ka da hankali? Bana ce ka daina yi mata magana ba?."

Salman fara yi Umma kuka ya ce, "ni dai in bata bani magani bazan sha ba."

Mama da ta fi kowa iya bariki sai ta karɓi maganin ta kalle shi ta ce, "Ita kake so ta baka?."

Ya É—aga kai alamun eh Mama ta ce, "goge idanunka."

Salman ya goge ido, ita kuma ta miƙawa Islaha ta ce, "Islaha ba shi maganin."

Islaha ta kalli Mama da take miƙo mata magani, sai ta kalli Mamy da ta ke kallon ta, ta miƙa hannu ta karɓi maganin, ta bashi a hannunsa ya karɓa ba tare da musu ba ya saka a bakin, Islaha ta ba shi ruwa ya sha da kansa.

Umma ta bi shi da kallon takaici, bai taɓa shan magani cikin kwanciyar hankali haka ba, kullum cikin faɗa ake da shi in dai akan sha magani, amma yau shine ya karɓa da kansa ya sha.

Mama ta yi murmushi ta ce, "Ba gashi ya sha É—in ba."

Mamy ta miƙe tsaye ta ce, "Allah ya ƙara sauƙi."

Islaha ganin Mamy ta miƙe sai ta yi nufin barin wajan itama, Salman ya riƙo hijjab ɗinta ya ce, "kar ki tafi ki bar ni."

Islaha ta kalle sa dan yanzu tausayi yake bata ba tsoro ba ta ce, "Zan dawo."

Ya ce, "kin yi alƙawari?." Ta ɗaga kai alamun ta yi.

Salman ya miƙa mata yatsansa ƙarami ya ce, "Mu ƙulla?." Ta ɗan yi murmushi ta kai nata kusa da nasa, bata bari hannunta ya taɓa nasa ba ta ce, "mun ƙulla."

Salman ya yi murmushi mai fitar da kyaunsa ya ce, "Abba ya ce duk wanda aka ƙulla alƙawari bai yi ba Allah zai ƙona sa."

Ta ɗaga kai ta ce, "zan cika in sha Allah." Sai a sannan ya sake ta ya koma ya kwanta yana murmushi. Islaha da Mamy suka fita, Umma ta miƙe ta shiga ɗaki Mama ta bi bayanta.

Mama ta ce, "kamata ya yi ki yi murna mun samu wacce zata dinga ba sa magani ya sha."

Umma ta ce, "shigowar yarinyar nan ba alkhairi bane a rayuwar Salman, tunda ta zo gidan nan ya san ya riƙe mace har ya ce yana sonta. Babban abinda ya bani tsoro, sai bayan shigowar ta gidan nan na tabbatar da Salman yana da lafiya kamar ko wanne namiji, a dah bana ganin abinda na gani a yanzu a tare. Hankali ya tashi, anya yarinyar nan ba neman Salman take yi ba? Daman an ce ta jima tana bin maza, ko an bata aikin da zata yi da irinsu salman ne? Dan ni wallahi na tsorota sosai, jikina yana bani kamar....."

Mama ta katse ta ta ce, "Zata aikata indai wannan yarinyar ce, ba kunya ce da ita ba. Amma zamu tabbatar da hakan, ki cigaba da saka masa ido mu gan iya gudun ruwanta."

Umma ta yi ajiyar zuciya ta ce, "zan cigaba in sha Allah. Ga shi yanzu na ga Nadira ta ja ta a jikinta, ba kamar farkon zuwanta gidan nan ba, yanzu ta riƙe ta hannu biyu alamun ta karɓe ta a matsayin matar Rehaan. Ni sai nake ganin kamar akwai wata manufa akan hakan."

Mama ta ce, "nima na lura yanzu, yarinyar ta daina É—ari É—ari da Nadira, alamun an samu wani daidaito a tsakaninsu, amma ko meye zamu gani."

Umma ta ɗaga kai Mama ta fita daga ɓangaren hankalinta a tashe, bata son alaƙar Mamy da Islaha, bata so a samu wani kusanci da ita ko kaɗan, bata so Islaha ta sake da Mamy ta saki jiki da hira har haka. Da ita kaɗai take so ta saki jiki, ita ta ke so ta ɗauka kamar uwar miji ba Mamy ba, amma ta ga alamar wankin hula zai kai ta dare, ya zama dole ta canja shiri, dan Mamy tana neman ɓarar mata da abinda ta jima tana yi.

Islaha bayan sun koma Mamy ta kalli Islaha ta ce, "Ki dinga yin baya baya, akan Salman babu abinda babarsa bazata yi miki ba. Kina ganin sharrin da ta yi miki farkon zuwan ki gidan nan, zata sake yin wanda ya fi na farko indai akan Salman ne."

Islaha ta ce, "In sha Allah, wallahi Mamy tausayi ya ke bani ne."

"da tausayi Islaha, Salma ya girmi Rehaan, amma kalli yadda rayuwarsa ta koma. Da ace yana da lafiya kamar kowa da yanzu yana nan da matarsa da yaransa. Amma ikon Allah ba a taɓa samun wacce jininsu ya zo ɗaya kamar ki ba."

"Allah sarki."

Islaha ta kalli Mamy ta ce, "zan tafi aiki."

Mamy ta ce, "To sai kin dawo." Islaha ta shiga ta É—auko abinda zata É—auko ta tafi.

Da daddare tana dawowa tun kafin ta shiga ɗaki Mamy ta ce, "Salman zuwansa biyu parlour nan, ya ce baki cika alƙawari ba."

Islaha ta dafe kai ta ce, "na manta."

Mamy ta ce, "tunda kin yi alƙawari ki je ki cika ki dawo."

Islaha ta ce, "To Mamy, bara ba je na dawo" ta faɗa tana fita ta tafi ɓangaren su Salma. Gab da zata shiga ya fito, sai ya juya zai koma alamun ya yi fushi da ita ta ce, "nazo na cika alƙawari."

Salman ya juyo ya ce, "tun É—azu nake jiran ki."

Ta ce, "Na je aiki, sai yanzu na dawo."

Sai ya yi dariya ya ce, "Umma tana ta faÉ—a ta ce wai kar na zo wajan ki, tana shiga wanka na gudo."

Islaha ta yi murmushi ta ce, "to ka koma, zan je na dawo."

"Ni zan bi ki."

"Gidan uwarka za ka bita?" Umma ta faɗa tana jan hannunsa da ƙarfi ta turasa falon.

Umma ta kalli Islaha tana nunta da yatsa ta ce, "Ki kiyaye ni, ɗana ya fi ƙarfin iskancin ki, zan iya sakawa a yi min maganin ki."

Islaha bata ce komai ba ta juya ta koma, dan itama kawai tana daurewa ne dan yana bata tausayi.

Washe gari ma bata dawo ba sai dare, kai tsaye ɓangaren Rehaan ta shiga ta yi wanka ta canja kaya zuwa ƙaramar riga ta bacci, ta saka haijjab da niyar tafiya wajan Mamy sai ta kalli ɗakin Rehaan ta gan shi a buɗe har tana jin magana daga ciki, sai ta ɗan zubawa ɗakin ido cike da mamaki, dan ita ta san kullum a rufe ɗakin ya ke.

Ta É—auke kai zata sauka daga saman sai ta ji ance, "Islaha."

Islaha juyo suka haÉ—a ido da Abba, Islaha ta ce, "Na'am Abba, barka da dare."

"Barkan ki, Shigo mana."

Islaha sai abin ya bata mamaki, amma bata ce komai ba ta shiga ɗakin a hankali kanta a sunkuye. Tana shiga ɗakin ta ji babu sanyi ko kaɗan, temperature ɗakin ya yi normal babu sanyi kuma babu zafi. Islaha ta kalli kan gadon ta ga Mamy a zaune ga Rehaan a kwance a cinyarta, ta ɗaga rigarsa ta ɗora masa towel, goshinsa ma an saka ƙaramin towel sai sauke numfashi ya ke yi a hankali.

Mamy ta kalle Islaha ta ce, "Kin dawo?."

Islaha ta ce, "eh na dawo Mamy."

Mamy ta shafa kan Rehaan da yake cinyarta ta ce, "Rehaan ne ya dawo, sai dai ba shi da lafiya" ta faÉ—a tana shafa gashin kansa.

Saboda idanun Abba da Mamy ya saka ta ce, "Subahanallahi, me ya same sa?."

Abba ya ce, "ciwon ciki ne, wannan ya zamar masa kamar sabo."

"Allah ya ƙara lafiya." Suka amsa da amin.

Abba ya kalli Mamy sai ya ce, "Nadira zo ki ji" ya faÉ—a yana fita daga É—akin.

Mamy ta kalli Rehana da ya ke kwance a jikinta, ta san in yana wannan ciwon cikin ba ya son motsi ko kaɗan, ko ya ya motsa sai ciwon ya dawo baya. Ba ta son motsawa saboda haka, ga shi ya saki jikinsa a jikinta sosai, in ta ce zata miƙa zata fama masa cikinsa. Amma babu yadda zata yi, haka ta zame shi daga jikinta, sai kuma ta kalli Islaha ta ce, "zo islsha."

Islaha bata fahimci me Mamy take shirin sakawa ta yi ba, ta ƙarasa kusa Mamy. Mamy ta ce, "Cire Hijjab ɗin kar ya takura ki, ki zauna ya kwanta a jikinki kafin na dawo."

Islaha ta bi Mamy da kallo tana maimaita ya kwanta a jikinta, ta ga Mamy tana niyar miƙewa alamun ita ta zo ta maye gurbinta ya kwanta akan cinyarta kenan.

Mamy ganin ta tsaya bata ƙaraso ba sai Mamy ta ce, "ƙaraso mana, my dear yana jirana."

Islaha ta ƙarasa a hankali tana magana ƙasa-ƙasa, Mamy ta miƙe a hankali hannunta yana riƙe da kan Rehaan kamar wani mai naƙuda, ta nunawa Islaha inda ta ta shi alamun ta zauna.

Islaha ta zauna a inda Mamy ta tashi, Mamy ta kwanta da Rehaan akan cinyar Islaha, shi kuma ya zagaya da hannunsa ya riƙe bayanta, yana sake nutsa kansa a jikinta yana jan numfashi.........

Nana Haleema.

RDB3P47
Nana Haleema.

Abba ya tsaya yana kallon Mamy har ta ƙarasa sakkowa downstairs sannan ta ce, "gani." Abba ya ce, "ki zo mu tafi ki kwanta, ki bar matarsa ta kula da shi."

Mamy ta buÉ—e idanunta cikin mamaki ta ce, "Kamar ya ta kula da shi, me ta sani akan ciwon cikinsa da zata kula da shi?."

Abba ya ce, "Nadira! Kula da Rehaan yanzu ba naki bane tunda yana da aure, ki bar matarsa ta kula da shi zuwa safiya."

Mamy cikin damuwa ta ce, "ta ya zan bar sa da ita bayan ka san a yadda auren nan ya zo?."

"Ko a ya auren ya zo sunanya matarsa ko?."

Mamy ta yi shiru bata amsa ba Abba ya ce, "ba kin ce min kin amince da ita ba?."

Mamy ta ce, "dan na amince da ita ba hakan yana nufin zan iya barinta da shi ba, in aka cutar da shi fa?.”
Chapter 61 · 0% Book details