← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 110

Sashe 83

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Islaha ta É—auke ido daga kansa, bata saba yi masa magana ba kwata-kwata, ta saba sai dai faÉ—a ya haÉ—a su sannan yake jin bakinta, amma sai ta ji tana so ta yi masa barka da zuwa. Ta buÉ—e baki zata yi magana unexpected ta ji ya ce, "How are you?."

Abin ya bata mamaki, ta É—ago ta kalle sa ta ga ba ita yake kallo ba, wasu kaya da ya ajjiye yake É—auka a kusa da shi. Sai kuma ya saka waya a kunne yana magana, kafin ta ba shi amsa ya shiga É—aki.

Islaha cikin mamaki ta ce, "Ikon Allah, yau kuma ni yake tambaya ya nake?."

Ta bi ɗakinsa da kallo sai kuma ta ƙarasa nata ɗakin ta ajjiye jakar hannunta ta shiga wanka. Bayan ta fito ta shirya ta zauna tana aikin da yake gabanta. Sabuwar number ce ta shigo wayarta ta kalla sai ta ɗauka ta ji ance, "Islaha Mama ce, kina jina?."

Islaha ta ce, "Mama barka da yamma."

"yauwa barka. Na ce akan maganin nan da na ba ki kwanaki, Rehaan ya sha kuwa?."

Islaha ta ce, "Oh wannan na ciwon cikin?."

"Eh ya sha?."

"ya sha amma sau biyu na basa gaskiya."

"Haba Islaha, akan me za ki basa sau biyu? A sati fa na ce miki ya shanye sa."

"to zan basa."

"hakan ne ya kamata. Bana jin daÉ—in wannan ciwon nasa shiyasa na dage har aka samo maganin, ga shi ba a samunsa a kusa sai an yi nisa da garin nan, kar ki wasa dashi don Allah."

Islaha bata ce komai ba ta kashe wayar ta bi wayar da kallo ta ce, "Ikon Allah, matar nan bata da gaskiya akan maganin wannan wallahi, haka kawai ta ɗaga hankalinta akan ban bashi magani ba? Kowa in ya ji yadda ta damu ya san akwai wani abun a ƙasa. Bara ki ga" ta faɗa tana miƙewa ta buɗe drawer ta ɗauki maganin, ta shiga banɗaki ta ƙarasa wajen a sink saka masa ruwa ya tafi, sannan ta wanke hannunta da sabulu ta fito ta cigaba da aikinta.

Bata fito daga ɗaki ba sai bayan sallar magrib, ta fito ta ga Banisha a wajansa suna shan tea, Da Banisha suka gaisa ita kuma ta sauka ƙasa bata ce masa komai ba.

Bata jima ba ta dawo da tea a hannunta, ta shiga ɗaki ta zauna ta cigaba da aikinta. Bayan ta shanye tea ɗin ta sake fitowa tana amsa waya hannunta riƙe da mug ɗin, tana cewa, "Bani da kati ne Safeera shiyasa ban kira ki ba, ina ta so na kira ki ashe katina ya ƙare."

Ganin Jafar sai ta yi murmushi ta tsaya bata cigaba da tafiya ba kuma bata kashe wayar ba ta ce, "Shikenan ki yi haƙuri, zan tura miki yanzu" ta faɗa tana kashe wayar.

Ta kalli Jazy ta ce, "Ina yini Mr Jafar.”

Da murmushi ya c, "Miss Islaha, ya ki ke?."

"lafiya lau."

"Ya aiki? ÆŠazu na ga interview É—in ki, gaskiya ke good presenter ce."

Ta yi murmushi ta ce, "Na gode. Ina Riyya?."

"Riyya tana gidan Mummy.”

Sai kuma ya kalli Rehaan ya ce, "anya ka taɓa kai ta gidan Mummy kuwa?." Bai ce komai ba itama bata ce ba ta sauka daga saman.

Jazy sai bayan ta sauka sannan ya kalli Rehaan ya ce, "ba ka kyauta ba, a matsayin da ka ke da shi ace matar ka ce take cewa bata da katin waya? Wannan wanne irin mugun hali ne wanda ban san ka da shi? Ai ko zaman contarct ku ke yi ya kamata ace kana sauke responsibilities ɗinta, tunda sunanta matar ka. C’mon katin waya ace bata dashi? Haba Rehaan."

Rehaan kalle sa cikin son kare kansw ya ce, "na sani ko an faÉ—a min?."

"Riyya, Janan, Banisha, Ikram da su Nana sai sun faɗa maka ka ke saka musu kati? Duk sati ka ke saka musu katin waya koda na baya bai ƙare ba, har Riyya da ta yi aure ba ka daina ba, har alert remender ka saka a wayar ja saboda kar ka manta, meyasa baka saka ta a layinsu ba?.”

Rehaan ya yi shiru bai ce komai ba dan ya san gaskiya yake faÉ—a masa. Jazy ya ce, "ka saka mata katin Rehaan."

Rehaan bai yi musu ba ya É—auki wayarsa yana dannawa babu jimawa ya ajjiye wayar ya yi shiru bai ce komai.

Jazy cike da tsokana ya ce, "Ashe kana da number ta?."

Ray ya kalle sa ya ce, "ka san babu yadda zan zauna har zuwa yanzu da ita bani da details É—inta, dole akwai, ko da bazai yi min amfani nan gaba. Kawai ban yi saving bane, amma na san inda number ya ke."

"Allah ko? Sannu bature" ya faÉ—a yana yi masa wani kallo.

A lokacin Islaha ta dawo idanunta suna kan waya, sai sake duba amount É—in da aka saka mata katin take yi ganin kuÉ—in kamar ba daidai bane, so take ta banbabce dubu hamsin ce ko dubu biyar amma ta kasa gane katin nawa aka saka mata.

Tsabar ta ruÉ—e bata san a falon ta tsaya ta kira Hamma ba, kuma ta saka a spekar ta ce, "Hamma ka saka min airtime ne yanzu?."

Abin ka da sabuwar iphone 17 take muryar Saheer ta fito raɗau ya ce, "A’a, ban saka miki kati ba, wani abu ne?."

"Ai kuwa wani ya yi kuskuren number ya saka min kati, dan ni dai in ba kai ba bani da wanda yake saka min kati. Kuma na kasa gane amount É—in, kamar dubu biyar kamar kuma dubu hamsin."

"Ayya maybe mistake aka yi, kuma babu number?."

"Daga bank aka saka, amma ina zuwa" ta faÉ—a tana kashewa tare da tunanin wanda zai iya saka mata kati.

Rehaan tunda ta fara waya ya wani nutsu yana jinta kamar mai ɗaukar karatu, ba muryar ta yake saurare na, muryar Saheer yake ji tana shiga ƙwaƙwalwarsa, yana jin wani iri a jikinsa kamar ya san mai irin muryar, ya kasa banbance sanayya ce ko wani yanayin dai bai sani ba. Sannan yadda ta ce ta san bata da mai saka mata kati sai shi sai ya ji maganar har ransa, ya dinga jin wani abu kamar ɓacin rai kamar haushin kansa.

Jazy ganin ta ruÉ—e ya ce "Miss."

Islaha ta É—ago ido ta kalle sa sai ya ce, "ki daina wahalar da kan ki, Rehaan ne ya saka miki airtime."

Islaga mamaki ya saka buÉ—e ido ta ce, "ya saka min kati kuma, ni na ce masa ina so ne?."

Jazy ya ce, "Nima ban sani ba, tambaye sa."

Ai kuwa sai ta kalle sa ta ce, "Ni ban ce ina son airtime ba, zan iya siya da kuÉ—ina ba sai an bani ba."

Rehaan maimkon ya kalle ta sai ya kalli Jazy, kamar zai yi magana sai kuma ya yi shiru ya miƙe tsaye sannan ya ce, "in ka gama ka tura min, ina so na duba kafin na tura musu" bai jira amsarsa ba ya shiga ɗaki.

Jazy ya kalle ta ita kuma ta ce, "ka faɗa masa ni bana buƙatar komai daga wajansa."

"Ke kuwa ki ke buƙata Islaha, c’mon aritime ace ba ki dashi? Kina amsa sunan matar Rehaan ace ba ki dashi? Shine ya sa ka miki."

Ta kalli wayarta sannan ta c, "shine kuma har fifty thosounds?."

Ya yi murmushi ya ce, "duba dakyau ki gani, zero nawa ka ka gani?."

islaha ta sake kallon amount É—in sannan sai ta buÉ—e idanunra ta ce, "kamar dubu É—ari biyar ne fa."

Jazy ya yi dariya ya miƙe ya ce, "good night Miss" ya faɗa tana sauka daga saman.

Islaha ta jima tana kallon kuÉ—in, tana maimaita dubu É—ari biyar a zuciyarta, ta sake duba balance É—in mtn É—inta da dubu É—ari biyar, har da bonus É—in data da aka bata saboda yawan kuÉ—in.

Islaha cikin mamaki ta ce, "dubu ɗari biyar a katin waya kawai?.”

“Ni ya zan yi da wanann kuɗin, wa nake da shi da zan kira shi da wannan uban katin wayar? Sai dai na rabar, na turawa Safeera da abokan arzuƙi, bazan turawa Hamma ba kar ya ga kamar na raina shi.” Ta sake kallon ɗakinsa, tana so ta je ta yi masa magana amma ta kasa.

A lokacin ya fito daga ɗakin ya ƙarasa inda ya tashi ya ɗauki abinda zai ɗauka zai koma.

Islaha ta kalle shi cikin murya kamar tana shagwaɓa ta ce, "ni ban ce ina son kati ba."

Ya juyo ya kalle ta, ya rasa meyasa in ya kalle ta gabansa yake faÉ—uwa, kwana biyu da basa tare baya jin hakan, sai dai in ya tunata ya ji gabansa ya faÉ—i. Bai ce mata komai ba ya koma É—aki dan bai san me zai ce mata ba. Islaha ta shiga É—aki tana sake kallon kuÉ—in dan ita mamaki kuÉ—in yake bata, A haka ta kwamta ta yi bacci tana tunanin kuÉ—im.

Washe gari ya zama date ɗin ya yi daidai da aurensu wata uku kenan, da farin ciki ta tashi, tana jin walwala saura kwana sittin ta rabu da ƙaya. Ko wanka bata yi ta sauka ƙasa, dan haka kawai take jin yunwa sosai.

Bayan ta gama shan tea ɗin sai ta miƙe ta buɗe public bathroom ɗin da yake cikin main parlour ta shiga tana kallonsa. Komai akwai a ciki, hatta body wash sabbabi ne ba a taɓa buɗe su ba, ga soaps da komai sabo ba a taɓa amfani da shi ba. Ganin hakan sai ta shiga dan Chairman yana ta yi mata waya yana cewa ta zo akwai abimda zata yi a can.

A ciki ta yi wankan tsaf, ta gama wankan ta ɗaura towel kenan ta kalli windown da take gefenta ta ga fuskar Salman yana kallonta. Gabanta ya yanke faɗi, suna haɗa ido da ita ya ɗaga mata hannu alamun hello, ta yi ihuu mai ƙarfi ta fito a guje daga banɗakin tana ihu kamar wacce wani abun ya biyo.
Chapter 83 · 0% Book details