← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 110

Sashe 97

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abba ya girgiza kai ya ce, "Rehaan ni ba ƙi nayi ba, amma ina so ka tuna ko da bata aikata ba yadda baki ya yi yawa a kanta rabuwa da ita shine mafita. An yi waje ka ce zaka yi bincike, na cikin gidan ma bincike zaka yi?.”

Rehaan ya kalli Abba yana tuna lokacin da ya same shi ya faɗa masa ba ya son auren, amma ya dinga ba shi haƙuri yana yabonta, yana cewa zai yi alfahari da ita ya yi haƙuri, amma sai ga shi yau kuma shine ya ke kushe ta.

Abba ya ce, "Daada ta matsa wuta akan yarinyar nan, itace tana sonta yanzu kuma ta ce bata so. Ka san Daada sa riƙo da al’ada, ta riƙe al’ada kamar yadda ta riƙe addini, duk abinda zai ɓata sunan Fulani bata ƙaunarsa. Dan haka ka yi gagggawa a san abinda za a yi."

Zai yi magana ya ga É—aya daga cikin masu aiki akan case É—in nan yana kiransa, bai É—auka ba ya kalli Abba ya ce, "Abba zan yi duk abinda ya kamata, yanzu ma akan case É—in nake." Kafin Abba ya yi magana ya ce, "zan je Abba." Ya É—aga masa kai ya fita yana É—aukar wayar.

Daga can ɓangaren aka ce, "Sir mun samu masu main account ɗin, yanzu haka suna hannunmu."

Rehaan ya yi ajiyar zuciya ta jin daÉ—i yana lumshe ido kafin ya buÉ—e ya ce, "A kai su guest house."

"Amma sir za mu barsu a office mu yi bincike."

"Ina so a yi komai ina nan."

"Okay Sir."

Ya kashe wayar ya kira Shams a waya suka hau mota suka tafi gidan.

A can ya same su gabaɗaya harda Jazy, yana shiga ya kallu wacce ta ke durƙushe a ƙasa tana kuka, ya kalli officer alamun ƙarin bayani.

Ya ce, "Ummi LamiÉ—o, itace ta yi creating account É—in, amma ba da wayar ta aka yi posting ba, an yi posting da wata wayar ne."

Ummi ta É—ago ido dan ta ga wanda ake yiwa bayani ta ga Rehaan a zaune yana kallon wanda yake yi masa magana. Cikin firgici "Mr Rehaan!."

Officer ya kalle ta ya ce, "Ummi."

Ta kalle shi ya ce, "dake da wa ku ka haÉ—a kai ku ka yi wannan aikin?."

Ta sunkuyar da kai ƙasa ta ce, "ni ban san komai a kai ba, abinda na sani kawai an buɗe account da wayata, bayan nan ban san komai ba."

"Waye ya buÉ—e account É—in?."

"Muslim ne, abokin aikinmu gabaÉ—aya har Islaha."

Officer ya É—auki waya ya saka a kunne ya ba da umarnin kawo Muslim da ya ke hannu, daman ya tambayeta ne dan ta maimaita Rehaan ya ji.

Babu jimawa aka shigo da shi aka duƙar da shi a wajan, Muslim ganin Rehaan sai da gabansa ya faɗi sosai ba kaɗan, duk da Rehaan ɗin ba shi yake kallo ba amma kwarjininsa ya cika wajan.

Officer ya ce, "Muslim!.”

Muslim ya kalle shi sannan ya ce, “meye dalilin ka na yaɗa hotunan nan?."

Muslim ya kalle sa ya ce, "ni ban aikata komai ba, sharri ta yi min."

Ummi ta ce, "ƙarya yake yi wallahi, shine ya yi komai, har ƙoƙarin zuba mata acid a fuska ya taɓa yi, ranar da aka taɓa sace ta, ya yi ƙoƙarin lalata mata fuska, wallahi shine."

"Kema ba kin ce sai kin ga bayanta ba? Na ga case É—in har yanzu yana gaban yan sanda. Ke ki ka ce sai kin kashe ta, kuma wannna hanyar ma hanyar kisa ce."

Officer ya ce, "Muslim kar ka yi mana wasa da hankali, ka kalli wanda yake gabanka a zaune…” ya faɗa yana nuna masa Rehaan.

Muslim ya sunkuyar da kai Officer ya ce, “ka faɗa mana gaskiya kawai, meye dalilinka na aikata haka?."

Muslim ya yi shiru sannan ya ce, "saboda ta fi mu ɗaukaka ne kawai, mun kasance mune gaba kafin zuwanta, tunda ta zo kowa sunanta ake kira, mu aka manta da mu kamar ba da mu aka yi gwagwarmaya ba.”

"A ina ka samu hotuna da videon da ka yaÉ—a?."

"AI ne ya yi, ba hotunanta bane, Mun yi amfani da AI wajan haɗawa, mun ƙirƙira mun yi ne ba dan mun san ya jikinta yake ba, abu ɗaya mu ka sani a kan surar jikinta, tana da bracelet a hannunta sannan tana da dogon gashi. Fuskar ta kaɗai muka yi amfani da ita, amma bayan fuska komai ba nata bane.”

"Ya aka yi ka san tana da dogon gashi?."

Ya nuna Ummi ya ce, "itace ta ke gani in sun je sallah."

"Kana nufin yanzu AI ne ya haÉ—a wannan video?."

"Wallahi shine, mun samu wanda ya ƙware a fanni shine ya haɗa mana. Amma wallahi duk abinda mu ka ce ƙarya muke yi mata. Har Chairman ɗin mu muka samu aka haɗa ƙarya da gaskiya da muryar Islaha, mu kace tana kai sirrin gidan wani waje, duk ƙarya muke yi.”

Officer ya ce, "ƙoƙarin zuba mata acid fa a wancan lokacin?."

Muslim ya ce, "mun yi niyar lalata mata fuska ne, yadda mutane zasu daina marmarin son ganinta, bayan wannan babu komai."

Officer ya kalli Rehaan ya ce, "that’s all Sir."

Rehaan ya kalli Jazy da ba shi ya ke kallon ba su Muslim yake kallo, kafin Jazy ya ce, "Offier a yi musu video yanzu nan su faɗi laifinsu da bakinsu, sannan a kai su kotu ta yanke musu hukunci daidai da abinda suka aikata.”

Ummi ta ce, "don Allah Mr Jafar, don girman Allah ka taimaka kar a kai ni kotu. Na amsa laifina dan a yafe min, wallahi bazan sake kallon Islaha ba balle na yi mata wani abun, ka yi haƙuri ka yafe mana don Allah."

Babu wnada ya kula takamar da kurame take magana, Officer ya ce, "ke abin ya yi miki yawa ai Ummi, bayan wannan laifin, ga furucin sai kin ga bayanta…..”

Ya kalli waɗanda suke tsaye ya cr, “Ku ɗauke su mu je" a take aka fita dasu suna ta magiya babu wanda ya sauraresu.

Jazy ya ce, "good job Officer! Amma ina so a tabbatar an sun yi video, sannan duk wani blog da ya saka hoton ko video nan a tabbatar da an goge shi, ko da nan gaba in aka kuma ganin wani ya É—ora hoton kawai a kama shi."

Officer ya ce, "an gama Mr jafar. Abin daÉ—in ma da ba ita É—in ba ce computer ce, amma za a yi maganinsu, ko dan masu hali irin nasu." Suka yi sallama suka tafi aka bar Jazy da Rehaan da ya kasa magana.

Jazy ya ce, "Mamy ta faɗa min abinda ya kuma faruwa a jiyan, mutanen gidan ku sun dage sai sun ga bayan yarinyar nan. Rayuwar ta abar tausayi ce gabaɗaya, bata cancanci wannan takurawar da baƙiin cikin da take ƙunsa a gidanku ba.”

Rehaan ya ɗago ido ya kalle sa, bai ce masa komai ba ya miƙe ya shiga ciki.

Nana Haleema.
KRBBK:
RDB3P71
Nana Haleema.

Sunana Ummi, ni abokiyar aikin Islaha ce. Ni da abokin aikina Muslim, muka haɗa kai aka ƙirƙiri AI video da fuskar Islaha, mu ka yaɗa a duniya da sunan itace take fasiƙanci bayan ba ita ba ce, bata san ma mun yi ba. Wallahi ba Islaha bace, mu muka haɗa ba tare da ta sani ba. Mun yi ne saboda son zuciya, muna ganin ta fi mu ɗaukaka, kowa a wajan aikin mu ita yake so bamu ba. Har maganar sirrin gidan da muka ce tana fitarwa ta wajan aiki duk shirin mu ne, wallahi bata san komai ba. Mun yi ne dan mu tozarta ta.

Abinda yake yawo a duniya kenan, kafin magrib labari ya cika ko ina, wasu suna tausayin Islaha, wasu kuma suna ganin kawai an yi ne dan a kare ta.

Islaha Mamy ce ta saka ta ta yi bacci babu wanda ya tashe ta ya faÉ—a mata, sabuwar wayarta tana hannun Safeera, duk wanda ya kira itace take É—auka ta ce bacci take yi.

Sallah ce ta tashe ta, ta miƙe tayi alwala tayi sallah ta fito falon Mamy. Sai da ta zauna sannan Safeera ta nuna mata abinda yake faruwa, ta buɗe baki tana kallon Ummi da Muslim da suka yi wujiga wujiga alamun sun sha baƙar wahala, ta rufe baki da hannunta hawayen farin ciki yana zubo mata.

Ta kalli Safeera tana dariya kuma tana hawaye ta ce, "da gaske bani bace haÉ—awa aka yi?."

"Ba ke bace Islaha, haÉ—awa aka yi, kuma an goge su kaf, ko a tiktok babu."

Islaha ta ce, “Ummi da Muslim ne zuka haɗa min wannan abun?."

"Ga shi Allah ya tona musu asiri."

Mamy da ta ke kallon ta murmusa ta ce, "ba kuka za ki yi ba, murna za ki yi."

Ta kalli Mamy ta ce, "Mamy akan aikin jarida aka yi min wannan sharri? Akan aiki aka so a zuba min acid, akan aiki aka so kashe ni? Mamy me na tare musu?."

"Mutane kenan ai, Allah ya kare ki daga sharrinsu." Islaha ta girgiza kai tana sake kallon videonsu tana mamakin wannan sharrin da suka yi mata.

Safeera ta miƙa mata waya ta ce, "Ga Baffa." Ta karɓa suka gaisa da Baffa yana yi mata murna akan abinda ya faru. Islaha ta kira Saheer bai ɗauka ba sai bata sake kira ba ta ajjiye wayar.

Islaha ta kalli Mamy cikin farin ciki ta ce, "Mamy ta ya aka yi aka gano su ne?."

Mamy ta ce, "an yi nemo main account É—in da suka buÉ—e, ita kuma da gmail É—inta aka buÉ—e shi, ta haka aka gano su."

"Kenan ana iya gano mutum ko da ya karya sim card ko ya goge account É—in?."

"Ga shi kin gani."

"Amma muna da waÉ—anan kayan aikin a nigeria me ya hana a dinga bibiyar masu garkuwa da mutane a kama su? Tunda har aka iya kamo su Ummi da suka buÉ—e account a tiktok a cikin kwana É—ata, za a iya ganosu suma."
Chapter 97 · 0% Book details