← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 110

Sashe 41

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari friday da wuri ta tashi ta yi wanka ta shirya, ta buɗe window tana ganin yadda mutane suka cika a gidan ana karɓar sadakar abinci da kuɗi, ta bar wajen ta saka kaya gama shiryawa ta fito da niyar tafiya office. Bata same shi a falo ba kamar yadda ta yi zato, ta sauka ta fita suka wuce wajan aiki.

Motar Lawal tana sauke ta suka haÉ—a ido da Ummi, Islaha ta É—an yi tsaki ta É—auke kai daga kallonta ta nufi ciki bata sake kalon ta ba. Daman ta san Safeera bata cika zuwa ranar friday ba, bata same ta ba ta wuce inda zata je.

Ummi tana shiga ta nufi wajan Muslim ta rufe office É—in sannan ta kalle shi ta ce, "Muslim ka ga abinda na gani."

Ya waiwayo ya kalle ta ya ce, "me ya faru?."

Ummi ta yi ƙwafa ta ce, "Islaha na gani a wata zundumemiyar range rover baƙa mai shegen kyau, kuma abinda ya bani mamaki tana baya a zaune, irin madam da driver ta ɗin nan."

Muslim ya ce, "an zo wajan, tabbas zargina ya zama gaskiya, in Islaha ba ta yi aure ba to zaman dadiro take yi da wani. GabaÉ—aya ta canja, ko gidansu aka je ba a cika samunta a can ba, abin yana É—aure min kai."

"Ba sai mu tambayi ƙawarta ba."

"na yi tambayar duniya ta ƙi cewa komai, shima Saleem ɗin yaƙi ya ce komai.

"

Ummi ta riƙe baki ta ce, "Lamarin ya ɗaure min kai nima, ta ƙaro wani class. Ka ga girman motar da aka ajjiye ta kuwa?."

Muslim ya ce, "ya zama dole mu san abinda zamu yi, da wannan damar zamu yi anfani wajen ganin ƙarshenta. Ko aure ta yi mu a wajan mu ba aure bane, zamu lalata mata suna mu zubar mata da mutunci a kafafen yaɗa labarai."

Ummi ta ce, "Kar mu yi wannan gangancin, dan ba mu san waye a bayanta ba."

"in ke baza ki yi ba ni zan yi, bazan zuba ido tauraruwarta tana cigaba da É—aukaka ba. Wallahi sai na yi maganinta."

"Ni sai nake gani me zai hana baza mu bi abin ta ƙasa ba, mu je wajan malamai a yi mana aiki a kanta."

"Sai dai wannan ya biyo baya, amma wannan da na faÉ—a shi za a fara yi Ummi."

Ummi ta ce, "Shikenan ayi hakan, in ba haka ba zata cigaba da wuce tunanin." Ya yi ƙwafa yana girgiza kansa cikin mugunta.

Islaha bata jima a wajen aikin ba ta bar wajan, bata tsaya kiran driver ba ta hau napep zuwa gidansu Saheer. Sai da ta tsaya sannan ta kira Saheer yana É—auka ya ce, "Islaha tun jiya nake jiran ki."

Islaha ta ce, "gani nazo, ina fatan Mama bata nan."

"Nima bana gida, amma gani nan ina hanya ki jira ni."

Islaha ta yanke wayar ta cigaba da tsayuwa a wajan, ba jimawa Saheer ya ƙaraso da motar Sadik ya tsaya a gabanta, ya sauke glass ya kalle ta ya ce, "shigo."

Islaha bata ce komai ba ta buÉ—e gaban motar ta shiga da sallama. Saheer ya amsa sallamar ya bita da kallon da ya yi mata yawa, har sai da ta ce, "Hamma ya dai?."

Bai daina kallon ta ba ya ce, "Cikin kwana biyar na ga kin yi kyau abin ki, kamar kina gidana."

Ta rufe ido ta buÉ—e cikin son kawar da maganar ta ce, "ina wani kyau a nan, kawai dan jiya ban fita bane shiyasa."

"me ya hana ki fita jiyan?."

"Kaina ne ya dinga ciwo, ka san na samu attack a shekaran jiya da abin ya faru."

Saheer sai ya haÉ—e rai ya ce, "ni tambayar da nake so na yi miki, me ya kai ki fita dashi a mota daga ke sai shi?."

"Hamma na faÉ—a maka komai fa, tsoro zama ni kaÉ—ai nake ji shiyasa kawai na shiga muka tafi."

"Islaha zama a gida ke kaɗai bai taɓa ba ki tsoro ba, meyasa yanzu ki ka fara jin tsoron zama ke kaɗai?."

"Hamma dare ne a lokacin, ƙarfe ɗaya da wani abun na dare, ba dole na ji tsoro ba."

Saheer ya girgiza kai ya ce, "Ni na fara jin tsoro, anya ban rasa ki ba?."

Nana Haleema.

RDB3P33
Nana Haleema.

Islaha ta yi shiru taƙi ba shi amsa, dan bata cika son ya dinga kawo mata wannan maganar ba, tunda Safeera ta tunasar da ita take tsoron aikatawa, bata so Allah ya kamata da laifi mai girman wannan. Sai kuma ta kalle shi ta ga yana kallonta, gudun kar ya gasgata ya rasata ɗin kamar yadda su Mama suke faɗa sai ta ce, "Ba ka rasa ni ba Hamma, ina nan dawowa, ka bari lokacin ya yi kawai.”

Ta dakata da maganar ta yi tsaki ta ce, "Ni ko babu kai me zai kai ni zama da wannan mutumin? Mtsww! Kayan takaici."

Ya bita da kallon mamaki ganin bilhaƙƙi ta ke maganar ta, shi mamaki ta ke ba shi sosai, the most richies man in Adamawa amma ta dinga wani taɓe baki in tana maganarsa tana tsaki. Kuma magana ake yi akan ita matarsa ce, amma ita ko kaɗan bata nuna hakan yana yi mata daɗi, sai kushewa da take yi kullum.

Saheer ya ce, "Yanzu ya jikin ki?."

Ta kalle sa ta ce, "na ji sauƙi."

"kin je aiki?."

"daga can ma nake."

"Daga nan sai ina?."

"Zan shiga cikin jimeta."

"Ki yi me?."

"Wani aiki zan yi kaÉ—an."

Bai tambaye ta wanne aiki bane ya ja bakinsa ya yi shiru, dan ya ga kwana biyu bata cika son faÉ—a masa abinda ya shafe ta ba. Jin ya yi shiru sai ta kalle shi ta ga ba ita yake kallo ba glass É—in gaban motar yake kallo ta ce, "Hamma ba ka bani labarin zama a wajen masu garkuwa da mutane ba."

Ya juyo ya kalle ta, kafin ya yi magana Sudaisa ce ta fara zuwa ransa sannan ya ce, "A ina nake ganin ki balle na ba ki labari?."

"Yanzu ba ga ni ba, kuma ko a chat ai za ka iya faÉ—a min."

"Hmmmm" abinda ya furta kenan bai ce komai ba.

Islaha ta ce, "Har yanzu yanayin ka bai yi normal ba, kana nan da ramar da ka yi kuma hasken ka bai dawo gabaɗaya ba. Sannan ga ƙananun ƙurajen nan da suka ɓata maka hannu, har yanzu basu gama ɓacewa ba."

Ya lumshe ido yana tuna Sudaisa zuciyarsa tana bugawa sosai, yana tunanin ko ta kuɓuta ko tana hannunsu bai sani ba.

A bayyane sai ya ce, "Islaha kenan, dan ba ki san ya wajen yake ba."

"To ka faÉ—a min."

Ya yi shiru bai ce komai ba, ta É—an kalle sa ta ga titi yake kallo ba ita ba ta ce, "Hamma."

Ya juyo ya kalle ta ya ce, "Islaha gani nake kamar kin tafi kenan.”

Islaha ta ce, "ka daina kokwanto a kaina, ka daina kokwanto akan zan dawo ko bazan dawo ba, mu ajjiye maganar zuwa lokacin ka gani. Yadda na yi auren nan saboda rayuwarka, yadda na sadaukar da kaina saboda ranka, haka zan iya yin komai dan ganin na dawo cikin rayuwar ka. Auren watan biyar ne kawai, da ya ƙare shikenan kowa zai kama gabansa."

"Ke ki ke ganin wata biyar a kawai, amma a gare ni mai yawa ne.

"Me zai hana baza ka koma ƙasar Nijar ba, in kana zaune a can za ka fi ganin komai yana gudu fiye da zaman ka a nan."

"Na tafi na bar ki a gidan wani, ni na zauna a can ko?."

Islaha ta ji kamar ta yi tsaki saboda haushin da maganarsa ta bata, sai kuma ta tuna da waye shi a gare ta sai ta ce, "ba ka yarda dani ba?."

Ya yi É—an murmushi ya ce, "Na yarda da ke, amma shi ban yarda da shi ba."

"Kar ya dame ka, ni ko magana ba ta haÉ—a ni shi sai ya zama dole."

"Hmmm, ke ba ki san waye namiji akan mace bane, shiyasa ki ke faɗar haka. Lokaci ɗaya zai canja, ya juya sama ta dawo ƙasa, daga nan sai labari canja, na fara ji ana batun Islaha ta kusa haihuwa."

Saboda haushin maganar sai da ta sarƙe tana tari ta dakata bata kalle shi ba. Ta ta ɗaga hannu sama ta ce, "Allah ya tsare ni, Allah ya kiyaye ni, mugun ji da mugun gani Allah ya kare....." a zuciyarta take addu’ar bata san ta fito waje ba.

Ta kalle shi ta ga ita yake kallo ta ce, "Hamma ka daina yi min irin wannan maganar, irin wannan tunanin ya daina zuwa ranka. Na ce ka zuwa lokacin ya ƙare ka gani, ka jira ka ga abinda zai faru a wata biyar masu zuwa…”

Ƙasa-ƙasa ta ce, “Waye wani Rehaan Yola da za ka dinga saka irin wanann banzan tunanin a ranka? Da na ga wannan ranar ba gwara na ga ranar mutuwa ta ba?. Mtsww!" Ta faɗa tana yin dogon tsaki mai nuni da takaicin da yake damun zuciyar ta.

Saheer dai kallon ta yake yi yana mamakin wannan haƙiƙicewar da take yi, ya san gaskiyarta take faɗa har zuciyarta, amma ya kasa amincewa dan ya san namiji ba abin yarda bane akan mace.

Saheer ya riƙe hannunta, a karo na farko da ta ji gabanta ya faɗi, ta zame hannunta daga cikin nasa, bai hanata ba sai kallonta da yake yo sannan ya ce, "ni dai don Allah ki dawo gare ni, ki riƙe min kanki, ki adana min kanki kar ki yi min wasa da kanki. Ke kin san ina da kishi ba sai na faɗa miki ba, bazan iya jure ganin wani namiji a matsayin mijiki na farko kafin ni ba, don Allah matar Hamma kar ki ba ni kunya."

Islaha sai jikinta yi sanyi lokaci ɗaya, ba maganarsa ce ta saka take jin hakan ba, riƙe mata hannun da ya yi ya ne ya saka take ji zuciyarta tana bugawa, zuciyarta tana faɗa mata bata kyautawa auren da yake kanta ba. Amma ya zata yi? Bata so ta yi wani motsin da zai nunawa Hamma ta zaɓi Rehaan a kansa. Cikin sanyin jiki ta ce, "To Hamma.”
Chapter 41 · 0% Book details