Sashe 37
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rehaan ya yi dogon numfashi bai ce mata komai ba, dan shi bai san abinda zai ce mata ba. Abinda yake tunani da ace ta san ya yi kissing É—inta da babu zaman lafiya.
Islaha ta ce, "Ni dai daga yau, in dai ka san za a zo kashe ka kar ka sake jawo ni ciki, ka je can su farfasa ƙwaƙwalarka da bullet bai damu Islaha ba, kai ba Yayana bane balle dan an kashe ka na damu. Duk ranar da za a sake kawo maka attack, ka bari na fita daga gidan nan salin alin, in ya so sai suzo su harbe ka."
Rehaan da ya ga ji da surutunta sai ya miƙe tsaye yana kallonta, sai kuma ya shige ɗaki ya bar ta dan ba shi da lokacin biyewa shirmenta. Sai da ya shiga ɗakin sannan ya yi dariya, yana tuna abinda ta faɗa, wai ya bari ta fita daga gidan sai a kawo masa attack, kamar sai sun nemi izininsa kafin su zo.
Jafar kuwa kai tsaye wajan Mamy ya nufa kamar yadda akace tana nemansa, haka kawai kunyar Mamy ta rufe sa daƙyar ya iya shiga apartment ɗin.A falo suka haɗu da Banisha ya yi murmushi ya bata hannu suka tafa sannan ya ce, "Ina Mamy?."
"tana bedroom."
"Okay Kiddo" ta faɗa yana nufar ɗakin Mamyn, yana jin kansa daban da kullum, yana jinsa kamar baƙo a wajen Mamyn.
Jazy ya kawar da komai ya shiga da sallama ta amsa tana miƙewa zaune daga kwancen da take ta ce, "Yauwa Jafar, kamar ka san kai nake jira."
Gabansa ya faÉ—i dan bai san maganar da Mamy zata yi masa ba, dan tsaf Mamy zata iya yi masa magana akan Riyya.
Ya ƙarasa ya zauna ya ce, "Mamy good morning."
"Morning my son, ya ka ke?."
"Lafiya lau."
Mamy ta ce, "daman tambayarka zan yi...." Sai kuma ta yi shiru, ta nutsu sosai sannan ta ce,
"Wannan yarinyar da ta ke tare da Rehaan, a cikin kwana huÉ—un da ta yi a gidan nan abubuwa masu yawa suna ta faruwa. Daga kan Daada, Salman, yanzu kuma ga attack. Anya ba itace ta ba da masaniyar fitarsa a daren jiya ba?."
Jazy ya yi ajiyar zuciya jin magana bata shafe shi ba, amma duk da haka ya kasa kallon Mamyn ya ce, "Meyasa ki ka ce haka Mamy?."
Mamy ta ce, "Abin ne da mamaki, ya aka yi aka san zai fita har aka yi shiri mai kyau a kansa haka?."
Jazy ya ce, "Mamy da ta san za a yi attacking É—insa da basa ta bi sa ba, da tana da hannu a abinda ya faru da baza ta yarda ta shiga motar ba. Tunda in ta shiga ta san itama mutuwa zata yi, kin ga kenan bata sani ba."
Mamy cikin gamsuwa ta ce, "Haka ne kuma Jafar, amma ni na kasa yarda da hakan."
Ya murmursa ya ce, "Mamy Islaha bata da matsala, na yi bincike a kanta in and out, babu abinda ban sani ba a kanta. Mamy yadda Rehaan baya son auren nan har ta fi sa ƙin auren, bata son Rehaan, haushinsa take ji sosai, ko haɗa ido dashi bata son yi. In kina neman wacce ta auri Rehaan ba dan kuɗinsa ba sai dan rashin mafita to itace."
Mamy ta ce, "kamar ya kenan?."
Jazy ya bawa Mamy labarin komai har auren wata biyar ɗin da suka yi sannan ya ce, "ta aure Rehaan saboda saurayinta, har yanzu akan hakan ta ke, in suka rabu zata je ta auri wanda take so. Ba dan tana son Rehaan ta aure shi ba, sai dan kuɗin fansar saurayinta da ya bata, shi kuma ya aure ta saboda ya yiwa Abba alƙawarin bazai ba shi matsala akan auren ba. Yadda ta ke ƙin auren nan nasu ko shi baya ƙinsa haka wallahi."
Mamy cike da mamaki ta ce, "like seriously?."
"Yess Mamy. Shiyasa na san baza a taɓa haɗa kai da ita a cutar da shi ba, dan bata shigo gidan nan saboda da shi ba sai dan saurayinta. Abu ɗaya na sani akan halinta, Islaha bata da kunya ko kaɗan."
Mamy ta gyaÉ—a kai ta ce, "na san wannan, ni kaina na ga alamun bata da kunya, dan ta yiwa Ammi a gabana....."
"Amma kuma bata rashin kunya akan rashin hujja Mamy, in ka ga ta yi rashin kunya an ɓata mata rai."
Mamy ta ce, "Eh haka ne, dan ko lokacin da ta yiwa Ammi É—in ma itace ta jawo. Amma ka san me Jafar? Sai nake jin na samu peace of mind a kanta, tunda har ba dan kuÉ—i ta aure sa ba, kuma kana da tabbacin baza a bata kuÉ—i dan ta cutar da shi ba."
"Mamy ko Ikram É—in da ki ke zancen za ki aura masa iya abinda zata yi akansa kenan."
Mamy ta ce, "hakan ya yi min Jafar, sai nake ji na aminta da ita sosai, amma zan sake bata lokaci."
Jazy ya ce, "wallahi Mamy baza ki samu wani abun mara kyau akan Islaha ba, bar ta dai da rashin kunya, amma baza ta taɓa cutar da Rehaan ba. Na yi bincike a kanta sosai, abinda bata san na sani ba ma na sani a kan rayuwarta."
Mamy ta yi murmushi ta ce, "Na ji daÉ—in wannan labari."
Ya yi murmushi ya ce, "ina fatan auren nan nasu ya É—ore."
Mamy ta ce, "zan so hakan Jafar, burina ya ssmu macen da zata so shi tsakani da Allah, kuma na ga alama Islaha ce. Amma za mu gani Jafar, za ka iya tafiya, daman dalilin kiran kenan."
Ya yi mata sallama ya miƙe Mamy bata tambaye sa Riyya ba, dan ta lura yana jin kunyarta sosai. Bayan ya fita ta yi shiru tana tunani, tabbas ya kamata ta gwada Islaha akan hakan.......
Nana Haleema.
RDB3P30
Nana Haleema.
*Makkah.*
Tunda suka shiga unguwar take kallon wajan cikin mamaki da al'jabi, yadda ta ga Aisha tana gaisawa da mutane da hausa baza ka ɗauka a ƙasar saudia ka ke ba. Uguwar gabaɗaya hausawa ne a wajen, ga unguwar a tsuke kamar irin layuka nan na cikin getho area. Kuma layin ba shi da space, gabaɗaya mutane sun cika wajen babu hanyar kirki sai ana tafiya ana bin layi. Ba dan ta san da gaske makkah suka shigo ba, da ta ce ƙarya Aisha ta yi mata wani wajen ta kai ta ba makkah ba.
Kallon su take yi kawai ganin yadda suke sana'a hankalinsu a kwance. Wasu sun kwance kayan da suka ƙulle da babban abu kamar kayan gwanjo, wasu suna soya awara, wasu suna dama fura da nono, ga mai alala da mai tsire da duk wani abincin da bahaushe yake ci akwai shi a wajan.
Labiba abin ya bata mamaki dan ba ta taɓa tunanin akwai irin wannan waje a cikin ƙasar saudia kuma a cikin garin makka ba. Ta dinga binsu da ido, maza da mata kowa yana harkokinsa.
Kamar ƙiftwar ido sai ta ga kowa ya miƙe an kwasa a guje ana neman wajan ɓuya, Aisha ta damƙi hannunta suka yi cikin wani gida da gudu ana ture ta tana turewa. Gabaɗaya lokaci ɗaya wajen ya tsaye cak, kowa ya shiga wajan ɓuya saboda masu kame sun zo za su kama su. Duk kuɗin da suka tara a lokacin sun tafi sun bar shi saboda ceton kar a kama su a dawo dashi nigeria.
Labiba bata san ya abin yake ba, shiyasa gabaɗaya take a ruɗe, yadda ta ga ana gudu maza da mata tsoro ya bata, ba dan Aisha ta riƙe hannunta ba da tsayawa zata yi. Sun fi su hamsin a gidan, kowa ya nemi waja ɓuya ya ɓoye.
Labiba ta taɓa Aisha ta ce, "meye hakan?."
Aisha ta ce, "shiii."
Dole ta yi shiru tana kallon yadda kowa ya nutsu ko motsin kirki basa yi. Tana jiyo ihun wasu daga waje, suna ihu suna a taimaka musu amma babu wanda ya fita sai ma sake ɓuya da aka yi. Sun yi mintina asirin a haka, kafin su ji tashin mota alamun askar ɗin tafi, sai kuma lowa ya fito da gudu ya yi wajan sana'arsa ya ɗauke kuɗinsa.
Labiba ta kalli Aisha ta ce, "Meye hakan yake nufi? Ban gane ba."
Aisha ta ce, "jami'an tsaron ƙasar nan ne, sune suke kama mutane su mayar dasu nigeria, ba ki ji ihun wasu ba?."
"Na ji."
"An kama su, zuwa jibi za a kaisu ƙasar su."
"Shine kowa yake guduwa haka?."
"To ke za ki tsaya ne?."
"Amma na ga kowa ya tashi ya bar kuÉ—insa."
"Ana ta ceto kai waye yake ta kuɗi? Tashi mu shiga ciki, ba mu shigo makka da ƙafar dama ba, muna zuwa mutanen sun fara kame."
Wani tsukakken ɗaki suka shiga Labiba ta bi ɗakin da kallo ganin akwai wuta ga ac nan tana aiki, amma baza ka taɓa cewa a makka ka ke ba.
Labiba ta ce, "kuma wai da gaske nan Makka ne? Ni na kasa yarda a makka muke, gani nake kamar a nigeria nake."
Aisha ta kalle ta ta ce, "A makka ki ke."
"Yaushe zan je na ga ka'aba?."
"Ganin ka'aba ne ya kawo ki ko neman kuÉ—i? Ki kiyayi kan ki da shiga haram, wallahi in tsautsayi ya bi ta kanki sai dai ki buÉ—e ido ki gan ki a Yola. Ki tsaya ki nemi kuÉ—in ki, in yaso daga ba ya sai ayi abinda ya kamata."
"Amma na zo har makka ace bazan ga ka'aba ba? Ni ko ban yi niyar umrah ba ina so na je na ga ka'aba."
Aisha ta cire rigar jikinta ta ajjiye ta ce, "Hmmm! Na ki wasa ne, ba ki san ya makka take ba shiyasa" faÉ—a tana shiga wanka ta bar ta a wajan.
Labiba ta nemi waje ta zauna har Aisha ta fito itama ta yi wanka ta canja kaya. Ba jimawa wata babbar mace ta shigo ta bi Labiba da kallo kafin ta kalli Aisha ta ce, "wannan fa?."
Aisha ta ce, "itace wacce na faÉ—a miki zamu zo daga Jedda, sunanta Labiba, bafulatanar Adamawa."
Matar ta kalle ta cikin hausarta da ta fara juyewa zuwa larabci ta ce, "sannun ki."
Labiba ta ce, "Yauwa sannu."