Sashe 12
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abba ya yi murmushi da son faranta mata rai ya ce, "sun dace kam, in zamansu ya fara daÉ—i da wuri zasu manta da yadda auren ya zo."
Sai Abba ya sake faranta mata rai ta sake yin dariya ta ce, "ina ji a jikina hakan zai kasance, hakan ne ma zai faru in Allah ya yarda."
Abba ya amsa kawai yana murmushi, tunda tana so dole ya biye mata, tunda abinda take so kenan haka zai biye mata ko da shi ba ya so. Dan Allah ya sani tunda Rehaan ba ya son auren shi kansa ba wani so ɗin yake yi ba, kawai dai yana biye mata ne, kuma sannan ya yaba da hankali da nutsuwar yarinyar. Burinsa ɗaya, kar a haɗa kai da ita a cutar da Rehaan, dan maƙiyansa ta ko ina zasu iya kawo masa farmaki.
   Islaha bin bayansa take yi tana kallon gashinsa da ya sauka har wuyansa, duk da a ɗaure yake amma yana taɓa wuyansa, hannunsa riƙe da waya yana tafiya yana dubawa. Sai kuma ta ga ya tsaya yana duba wayar kafin ya cigaba da tafiya a hankali kamar ba shi da jini.
Islaha bata san ta yi tsaki ba ta harari bayansa ta ce, "sai É—an banzan iyayi kamar mace, kalle sa don Allah yana tafiya kamar wanda ba shi da jini. Abin takaici, na cuci kaina da na amince da wannan abin."
Nana Haleema.
RDB3P09
Nana Haleema.
A lokacin Islaha ta ga yara ƙananu sun zo da gudu sun riƙe sa, su huɗu ne mata biyu. Sai ta ga ya mayar da wayar aljihu ya riƙe su duka yana maganar da bata jin me yake faɗa ba, yadda yake harkar gabansa kamar ya manta da ita, ya riƙe hannun yaran sun nufi ɓangaren Mama kai tsaye.
ÆŠaya daga cikin yaran ne ta juya ta kalli Islaha, sai ta yi murmushi ta ce, "Uncle she is your wife?."
Islaha ta buɗe ido cikin mamakin ganin yarinya yar ƙarama har ta iya magana da ingilishi.
Ray ya É—an waiwayo ya kalli islaha, ya É—auke kai kalli yarinyar ya ce, "who told you?."
Yarinya ta ce, "Daada." Ya sauke numfashi bai ce komai ba suka cigaba da tafiya.
Sai da zai ya yi pushing glass door ɗin falon Mama sannan ya kalle ta, ya ga tana tahowa kamar bata son ƙarasowa, ga wani kallo da take jifansa dashi kamar zata rufe sa da duka. A haka ta ƙaraso, ya yi pushing ƙofar suka shiga da sallama.
Mama dawowar ta kenan daga event ko mayafi bata ajjiye ba. Ganin Rehaan da jikokin gidan ga kuma Islaha a baya sai ta saki fara'a ta ce, "amarya da ango ne da kansu? Ahh lallai ina da manya-manyan baƙi, sannun ku da zuwa."
Islaha ta ƙarasa kusa da ita ta zauna Mama ta ce, "Islaha ya zaman baƙon waje?."
Islaha ta yi murmushi kawai bata ce komai ba, Mama ta kalli Rehaan ta ce, "Yarinyar nan akwai tarbiyya ga kunya."
Ya É—auke kai kamar bai ji ba, ya cigaba da kallon yaran dan ba shi da lokacin kallon Islaha.
Mama ta ce, "kamar yadda na faÉ—a miki, ni ake kira da Mama, ni ce babba a gidan nan. Ga shi kin zo Æ´an uwan Rehaan É—in duk suna wajan biki, balle ku gaisa."
Islaha bata ce komai ba sai murmushi a zahiri, amma a baɗini takaici ne ya mamaye mata rai, dan zama waje ɗaya da Rehaan ma ɓacin rai ne.
Rehaan ya miƙe ya ce, "zamu je wajan Umma."
Mama ta ce, "ya kamata kam, sai kun fito." Bai amsa ba ya fita, Islaha ta bi bayansa tana ji kamar ta jawo sa ta dinga duka har sai ya daina numfashi saboda haushinsa da take ji.
Mama ta bisu da harara ta ce, "shashashan banza, ai ba a banza na bari aka yi bikin nan ba, ina da ƙudurina a kan hakan. Yarinya sai iya bariki, bayan ta gama yawon banzan ta, ta san maza, maza sun santa, shine zata dinga wani sunkuyar da kai in ana magana? Mtsw Zan yi maganin ku wallahi, da kai da ita duk a hannuna ku ke."
  Wajan Umma suka shiga, suka same ta a zaune ita da Salman yana cin abinci. Salman yana ganinsu ya miƙe tsaye, Rehaan ya yi murmushi ya ƙarasa kusa da shi ya ce, "Ina nawa abincin?."
Salman ya miƙa masa nasa da ake ba shi, Rehaan ya yi murnushi ya zauna kusa da shi.
Ya kalli Umma da ta wani haÉ—e rai ta kawar da kanta gefe, suka gaisa da Rehaan tana amsawa kamar an yi mata dole, sannan Islaha ma ta gaishe ta ta amsa a fizge.
Salman ya nuna Islaha ya ce, "wace wannan?."
Rehaan ya kalli Islaha suka haÉ—a ido, ya É—auke kai ya kalli Salman kafin ya yi magana Salman ya ce, "É—azu da na je ban ganka ba amma na ganta, in na je zan dinga ganinta? Ta yi kama da Dora ta cikin cartoon...." Ya faÉ—a da sigar da Rehaan zai gane wacce yake nufi.
Rehaan ya É—aga masa kai yana kallonsa, shi kuma ya ce, "Ni dai ina sonta."
Rehaan ya yi murmushi cikin ko in kula da kalaman Salman ya ce, "kana sonta?."
Salman ya É—aga kai ya ce, "ina sonta."Â
Rehaan ya kalle ta ya ga ta zubawa Salman ido tana kallonsa, ya sake kallon Salma ya ce, "itama ta ce tana sonka, kuma za ka iya zuwa ko yaushe ku gaisa, daman ƴar uwarka ce, kai da ita babu banbanci...." ya ƙarasa faɗa a hankali yadda ita kaɗai zata ji, yana kallon ta dan da biyu ya faɗi maganar.
Salman ya yi dariya yana juye abincin a jikinsa saboda dariya, Rehaan ya karɓi bowl ɗin yana ya saka spoon yana kwashe wacce ta zube a jikinsa.
Salman da yake kallon Islaha ya riƙe hannun Rehaan ya ce, "zan zo wajan ta kullum......"
Sai ya sake kallon Islaha ya ce, "da gaske kina sona?." Islaha ta kawar da kai gefe bata ce komai ba, tana jin haushin Rehaan jin a fakaice ya ce mata mahaukaciya.
A lokacin Umma ta dawo wajan babu kunya ta kalle su ta ce, "To sai da safen ku, mun gode."
Rehaan ya shafa kan Yayansa cikin tausayawa, ya miƙe Islaha ma ta miƙe ta yi hanyar da suka biyo bata sake kallon kowa ba.
Salman ya miƙe zai bi bayanta Umma ta riƙosa ta ce, "ina za ka je?."
Salman ya ce, "zan bita, ni a wajan ta zan kwana yau."
Umma ta zare masa ido ta ce, "dallah zauna, wajan ubanwa za ka kwana?."
Salman ya riƙe Rehaan kamar zai yi masa kuka ya ce, "ka tafi dani wajanta, ni a wajanta zan kwana."
Umma ta ce, "sai na mare ka wallahi, dallah wuce ka bani waje, ko na kira kifayen Amir su cinye ka." Salman sai ya nufi É—aki jin an kira abinda yake jin tsoro.
Rehaan ya fita yana murmushi, zuciyarsa cike da tausayin Yayan nasa, jin ana tsorata shi da abinda yara ƙananu ne suke tsoron abun, Allah ya gani, yana son nemo masa lafiya amma babarsa ta hana.
A tsaye ya samu Islaha ta haɗe rai, ya ɗan kalle ta ya ga ta sha mur tana kallon gefe ƙiris take kira ta fara masifa. Bai ce komai ba ya wuce ɓangaren amarya Abba, ganin ya tafi dole ta bi bayansa. A nan ma basu jima ba, sun gaisa sama-sama sannan ya fito suka tafi ɓangaren Mamy.
Islaha suna shiga wajan Mamy gabanta ya faɗi, domin ita ba ita kaɗai bace, suna da yawa kuma duk irinta ne masu fararen fata, sai matar nan da suka samu saɓani da ita.
Suna shiga Rehaan ya yi murmushi ya ce, "ba ku yi bacci ba?."
Sanah itace take iya mayar da magana da hausa kaÉ—an-kaÉ—an ta ce, "yanzu muka dawo, ina mu ina bacci? Sannun ku da zuwa." Ya É—aga kai alamun yauwa, Islaha tana daga tsaye ta kasa motsawa balle ta shigo.
Sanah ta kalle ta ta ce, "shigo mana" ta faÉ—a cikin hausarta da bata wani fita sosai.
Ammi ta yi caraf ta ce, "ta ya zata shigo, bayan rashin kunyar da ta yiwa uwar mijinta ɗazu? Har da ƙoƙarin marina."
Islaha ta lumshe ido ta buɗe takaici yana mamaye mata zuciya, Allah ya sani zata iya yin aljanun ƙarya ta zane matar nan, bata son rashin jan mutumin da jan girma daga wajen wanda ya dace.
Mamy ta kalli Islaha da take tsaye ta É—auke kanta ta kalli Rehaan ta ce, "ka ci abinci?."
Rehaan ya ce, "na ci."
Sanah ganin Mamy ba ta Islaha take yi ba sai ta ce, "shigo mana Islaha, ko ba haka sunan yake ba?." Islaha ta yi murmushi tana jin daɗin yadda matar take yi mata, ta ƙarasa a hankali ta zauna a kan carpet.
Ammi ta ce, "Rehaan yarinyar nan ɗazu ka ga abinda ta yi mana ni da mahaifiyar ka? Ni daman na santa, lokacin da ba ka da lafiya har ka kwanta a asibiti a nan muka haɗu, yarinyar nan ta tare mu ta dinga yi mana rashin kunya bayan ta ɗaukarwa Mamy atm card. Ban taɓa ganin yarinya mara tarbiyya da rashin sanin darajar na gaba kamar ta ba."
Rehaan hankalinsa ba ya kanta, game ya ke taya yaran gidan da suka biyosa wajen Mamy, sai daga baya ya kalli Ammi bai ce komai ba ya kalli Islaha da ya ga tana kallon Ammi irij kallo na takaici.
Sanah ta ce, "ya isa don Allah, ba abinda ya kawo ta kenan ba, zuwa ta yi mu gaisa."
Mamy dai bata ce komai ba, kamar bata san dasu a wajan ba, waya ta É—auka tana dannawa kamar babu wanda ya zo wajanta dan ya gaishe ta.
Sanah ta ce, "a ina ki ke aiki?."
Islaha ta ce, "Toron guiwa tv."
"Ma sha Allah, Ashe tv presenter ce."
Islaha ta yi murmushi bata ce komai ba, duk ta takura saboda yadda aka karɓe ta a wajan. Ba haushin tarbarsu take ji ba, wanzuwar Ammi a wajen shine takaicinta, ji take zata yi aljanun ƙarya ta karya ta wallahi.