← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 110

Sashe 14

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Islaha tana daga falo tana jiyo dariyarsu daga sama, shi dai bata jin ko muryarsa, amma tana jin dariyarsu har suka sakko suna cewa, "good night bruh." Bata ɗaga ido ta kalle su ba har suka ƙaraso inda take, dukkansu fuskarsu ɗauke da nishaɗi.

A tare suka haɗa ba ki suka ce, "good night." Ta buɗe ido ta kalle su ta ce, "Allah ya tashe mu lafiya." Daga haka suka fita tare da jan ƙofar, ita kuma ta miƙe ta ɗauki wayarta ta hau saman.

Islaha a falo ta same sa ya ɗora ƙafa kan ɗaya yana amsa video call, yana ta murmushi da alama da mutum mai mahimmaci yake magana.

Daidai lokacin da ta shiga falon ta ji muryar mace cikin ingilishi ta ce, "ina ka bar matar ta ka take?." Rehaan ya É—ago ido ya kalli Islaha da take shigowa falon tana takawa kamar wacce aka yiwa dole sai ta shiga: Ya shafa kansa bai amsa ba ya ce, "yaushe za ki zo?."

"Sai matar ka ta haihu."

"Ashe baza ki zo ba."

Ta yi dayar shaƙiyanci tana tafa hannu sai ya murmusa ya ce, "Bye. Ina da aiki."

"Mr busy, Bye." Bai ce komai ba ya rufe laptop É—in, ya É—auki waya ya fara dannawa cikin nutsuwa.

Islaha bata sake kallonsa ba ta wuce ɗakin da aka ajjiye ta, ta cire mayafinta ta shiga wanka. Bayan ta gama ta fito ta buɗe box ɗin kayanta ta ɗauko ƙaramar riga mara nauyi doguwa mai siririn hannu ta saka.

Ta koma gefen gado ta zauna tana tuna abubuwa kala kala, tunanin Zainab ya danne na Hamma, sai ta firgita kamar wacce aka tsorata ta É—auki waya zata kira Brr Suraj sai ta ga dare ya yi sosai, ta yi ajiyar zuciya tana ayyana ya zama dole gobe ta fita ta je inda ya kamata, dole gobe ta fita daga gidan nan dan samo mafita akan matsalolin da suka same ta.

Rehaan kuwa yana zaune kiran wayar Jazy ya shigo, kamar bazai É—auka ba sai kuma ya É—auka, ya saka a speaker Jazy ya ce, "please Rehaan ka yiwa Riyya magana, sai kuka take yi kamar ba ni ba."

Rehaan ya haÉ—e rai kamar yana ganinsa, sai kuma ya kashe wayar ya kira Jazy video call yana kallon Jazy sanye da pyjamas red colour wanda suka yi masa kyau sosai.

Ray ya ce, "me ka yi mata?."

Jazy ya harare sa ya ce, "me zan yi mata a wannnan lokacin? Dallah in za ka rarrashe ta ka rarrashe ta, ka daina yi min maganar banza."

Riyya ta karɓi wayar tana kallon Rehaan, Ray ya tausasa murya ya ce, "Riyya What wrong?."

"I'm just missing you."

"Ba ga shi kina ganina ba, meyasa ki ke kuka? Ko na zo na tafi dake?."

Ta É—aga kai alamun eh, ya yi murmushi ya ce, "to ki daina kuka, zan zo mu tafi, shikenan?." Ta goge idonta tana murmushi tana bawa Jazy wayar.

Jazy bai yi magana ba sai da ya fito daga É—akin sannan ya kalli wayar ya ce, "Kai gidan ubanwa za ka zo ka É—auke ta? Kana da hankali?."

Ray ya yi dariya sosai sannan ya ce, "billah in na ga dama sai na zo har gidan na tafi da ita."

Jazy ya ce, "kar ka fasa, don Allah ka zo in ka isa."

Ray ya sake yin dariya mai sauti ya ce, "hmmm, kana wasa dani."

Jazy ya ce, "ka je ka ji da matarka, mijin contract."

Ray bai ce komai ba ya yanke wayar yana kallon room ɗin da Islaha ta shiga, a daidai lokacin Islaha ta buɗe ƙofar ta fito sanye da doguwar riga ta bacci, ta yafa mayafi a iya kanta, gashin ta ya sakko har ƙasa, sannan ta gaba ya fito sosai dan mayafin ya zame ta gaba.

Tana fitowa suka haɗa ido, sai ta yi turus taja ta tsaya ta kasa gaba ta kasa baya. Charger ta ta bari a ƙasa, shine take so ta je ta ɗauko ta saka chajin wayar ta, bata san yana zaune da ba da bata yi gangancin fitowa babu mayafi ba.

Nana Haleema.
KRBBK:
RDB3P11
Nana Haleema.

Rehaan tunda suka haÉ—a ido ya É—auke kansa, ya juyar da fuska kamar bai san da ita a wajan ba, nan kuwa yana kallonta ta gefen ido, so yake ya ga tsayuwar me ta ke yi a wajen.

Islaha sai ta koma da baya ta É—auko hijjab ta saka, dan bazata iya wuce shi da rigar jikinta ba, sai da ta saka hijjab sannan ta fito ta sauka downstairs bai ce komai ba itama bata ce ba.

Yana jin takun saukar ta ya waiwayo yana kallon wajen, a lokacin ta dawo tana warware charger da take hannunta. Mamaki ta ba shi ganin har da wani saka hijjab, dan ya san ba a haka ta fito ba, har gashin kanta ya gani a bayyane lokacin da ta buɗe ƙofa, kenan komawa ta yi ta saka hijjab saboda yana zaune ko me take nufi? Dan ya san haka ƴan nigeria suke, da zarar sun ga namiji a waje sai su koma su saka mayafi dan su rufe jikinsu, kuma ya san addini ne ya ba da damar hakan, tunda Mamy ma tana yi.

Haka kawai ya ji bazai iya yin shiru, dole sai ya yi magana ko da baza ta kula shi ba. Gab da zata wuce ta ji muryarsa ya ce, "wait a minute."

Islaha ta ɗan juyo ta kalle sa suka sake haɗa ido, tana mamakin dalilinsa na tsayar da ita. Rehaan ya nuna ta da yatsansa ya ce, "meye na saka hijjab ɗin, Kin manta wacece ke?....Akwai abinda ya yi saura da za ki ɓoye?."

Wani irin ƙunci ya sake mamaye mata zuciya, daman ga shi zuciyarta a wuya take, damuwa ta mamaye mata zuciya ta ko ina, ƙiris take jira ta samu abokin faɗa su yi kaca-kaca.

Islaha ta girgiza ki cikin jin haushin kalamansa, ta cize baki ta kalle sa cikin dauriya ta ce, "babu sauran abinda zan ɓoye kam kamar yadda ka sani, kuma nasan ka tabbatar da babu sauran abin ɓoyewa, to babu ɗin."

Ta nuna shi da yatsa tana buɗe idanunta ta ce, "amma ina so ka san akwai waɗanda basu cancanta su ga ragowar ba, ka san ko a mutanen da suka saba ganin ragowar ma matsayi ne, irin ku ba ku kai matsayin da idanunku zai ga ragowar ba, baza ku jure kallo ba, za ku iya makancewa. Ka kiyaye idanunka daga kallona, in ba haka ba zaka rasa idanun da ka ke gani dasu" tana gama faɗa masa haka ta bar wajan ta shiga cikin ɗakin ta rufe ƙofa.

Rehaan ko kaɗan bai ji haushi ba, ya ɗan yi murmushi yana tuna wacece ita ɗin a Jeddah, yana tuna har ciki ta zubar kuma da idanunsa ya ganta. Ya yi tsaki kaɗan, ya tashi ya shiga ɗakinsa ya rufe ƙofa.

Islaha tana shiga ta cire hijjab É—in ta cillar ta ce, "lallai wannan mutumin da alama bai taki zaman lafiya ba, ni zai kalla ya dinga jifa da waÉ—annan kalaman munana?. Haka É—azu ya faÉ—a min magana a falon waccan babar mahaukacin, wai ai ni mahaukacin É—an uwana ne type É—inmu É—aya, Kenan nima mahaukaciya ce kenan?."

Ta girgiza kai ta ce, "lallai zai ga salon hauka a cikin gidan nan, kafin na bar gidan nan sai na saka ya gangata ni mahaukaciya. Zan nuna masa ni Æ´ar iska ce lamba É—aya, tunda kallon karuwa yake yi min bazan tsaya kare kaina ba, kawai zan nuna masa ita É—ince a aikace, sai na goge masa hadda wallahi."

Ta ƙarasa ta saka chaji ta kwanta a kan makakeken gadon ta, ta ɗauki remote ta kunna ac ta lumshe ido tana ji kamar bata kyautawa rayuwar ta ba gabaɗaya, dan Ray bai dace da ita ba ko kaɗan.

*Jeddah.*

Kuɗi ne masu matuƙar yawa ne a hannunta tana lissafawa Aisha tana ta ya ta har suka lissafa kuɗin saudia masu yawa.

Aisha ta yi dariya ta ce, "kin zama hajiya Labiba."

Ta yi farr da ido cikin jin daÉ—i ta ce, "Ina komawa nigeria mota zan siya."

Aisha ta dara ta ce, "yaushe za ki koma É—in?."

Labiba ta ce, "babu rana balle wata, yadda nake samun kuÉ—in nan me zai mayar dani gida?." Suka yi dariya tare sa tafawa cikin nishaÉ—i.

Labiba ta ce, "Yanzu ina zamu nufa? Tunda kin ga ya ce zamu iya tafiya, zai yi tafiya kuma ƙasar zai bari. Ina zamu nufa yanzu daga nan?."

Aisha ta ce, "kin shirya neman kuÉ—i Hajiya?."

Labiba ta ce, "ki ninka shiri sau dubu, haka na shirya tsaf zan bazama neman arzuƙi."

Aishs ta ce, "in dai kin shirya, ki shirya É—aukar duk wani ganganci da za ki shiga. Ki tattara kayan ki mu wuce garin makka, acan zamu ci kasuwar kuÉ—i yadda muke so."

Labiba ta buÉ—e ido ta ce, "Makka kuma, ba ance suna kama mutane ba?."

Aisha ta ce, "a haka kowa yake zaune, in ba ki da visa ki o igama tabbas ana kama mutane a dawo dasu najeriya, amma mata nawa ne a can suna sana'ar su? Mu ma cikinsu zamu shige."

Labiba ta ce, "ai ni ina da visa ko?."

Ta harare ta ta ce, "visa wata uku suka buga miki, kuma yanzu kin zarce wata uku tuni. Visa ki ta jima da ƙarewa, dani dake duk ɗaya mu ke a nan."

Labiba ta É—an yi shiru kafin ta ce, "Amma cewa aka yi visa shekara É—aya aka yi mana."

"Yaudarar ki aka yi, wallahi ta wata uku aka yi miki ba shekara ba. Da ne ki ke zaune zaman Æ´anci a nan, yanzu za ki fara zaman ganganci, in ta yi ruwa rijiya, in bata yi ba masai."

"kuma a haka zamu shjga makka?."

Ta ce, "a haka zamu je, in kuma baza ki ba sai ki nemi abinda za ki biya wanda suka kawo ki."

Labiba ta ce, "amma ance in visa ta ƙare, wanda aka kawo bai koma ba kamfani suke cin tara ko?."

"Kamfanin na Maman ku ne?."

"Aa, kawai dai...."
Chapter 14 · 0% Book details