Sashe 80
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rehaan ya kalli Islaha da ta kwanta akan tiles tana kuka, ya sake kallon Safeera ya ce, "me yake damunta?."
Safeera ta ce, "cramps ne."
Ya ɗan yi jim kafin ya sake kallonta ganin da gaske kukan take yi. Safeera ta durƙusa a gabanta ta ce, "Islaha daure na raka ki ɗaki, ki tashi don Allah."
Daƙyar ta iya miƙewa suka tafi ɗakin, sai da ta zuge mata zip ɗin rigarta ta cire mata, ta kwanta akan gadon ta rufe mata jiki da duvet, ta ɗauko magnin da yake ajjiye kan drawer ta bata ta sha, ta kunna mata ac ta ce, "sannu." Bata iya amsawa ba ta ɗaga mata kai kawai.
Safeera ta dawo parlor ta ganshi a inda ta bar shi a tsaye kamar mai tunani. Cikin dauriya ta kalle shi dan kwarjini yake yi mata ta ce, "Sir yau tana jin ciwo fiye da ko yaushe, ko za a baya magani don Allah?."
Rehaan ya É—an É—aga kai sannan ya ce, "tana ina?."
"Tana cikin É—aki."
"Okay" ya faÉ—a yana komawa É—akinsa. Safeera tana tsaye ya fito daga É—akin ya buÉ—e É—akinta ya shiga.
Ɗakin babu haske ko kaɗan, ya ƙarasa inda ta ke kwance yana kallonta. Idanunta a kulle yake amma hawaye ne yake sakkowa daga idanunta, bai mata ce komai ba ya zauna daga gefenta dan ya lura serious ciwo take yi.
Ya zuba mata ido yana kallonta, kafin ya miƙa hannunsa ya taɓa forehead ɗinta ya ji da zafi, ya taɓa wuyanta ya ji nan ya fi ko ina yin zafin. Water bag ce a hannunsa wacce ya ɗauko daga ɗaki, ya dinga juya bag ɗin a hannunsa yana kallonta, ya yi ajiyar zuciya yana tunanin yadda zai ɗora mata bag ɗin a ƙasan cikinta.
A lokacin ya tuna da Safeera, ya miƙe ya fito da niyar ya sakata ta ɗora mata bag ɗin amma bata nan alamun ta tafi. Ya koma da baya yana kallonta, kitson kanta guda biyun kawai yake kallo har ya ƙarasa ya zauna daga gefe.
Kamar mai jin tsoro ya É—an matsa inda ta ke, ya É—auki water bag É—in da ya zuba mata ruwan É—umi, ya janye duvet É—in da aka rufe mata jiki.
Duk da babu haske ɗakin sai da ya mayar ya rufe mata jikinta ganin yanayin da take ciki daga ita sai baƙar bra, bai san babu riga a jikinta ba da bai fara buɗe ta ba, ya kulle ido ya buɗe yana sake kallon ta ya rasa me zai yi mata.
Sai kuma ya ya sake mayar da hannunsa ya riƙe duvet ɗin, ba tare da ya janye shi ba ya saka hannunsa a ciki, ya kai water bag ɗin ƙasanta cikinta a hankali ya ɗora.
Shi kansa sai da runtse ido, dan baya so ya aikata abinda yake niya, kar ta fassara shi da wata manufa. Bag É—in bata hau kan inda ake so ta hau ba, dan a kan mara ake É—orata, dole sai ya É—an janye dogon wandon da yake jikinta sannan zai É—orata a inda ake so.
Kamar mai jin tsoro ya riƙe saman wandon, ya ɗan yi ƙasa da shi kaɗan, hannunsa ya shafi wajen gabansa ya faɗi lokaci ɗaya hannunsa ya fara rawa. Babu shiri ya ɗora mata bag ɗin a saman mararta, ya ɗora hannunsa akan bag ɗin ya ɗan danna kaɗan yadda ɗumin ruwan zai ratsa ta har ya saka jinin ya yi melting.
A lokacin ta firgita ta riƙe hannunsa da yake akan bag ɗin, ta juyo tana kallonsa suka haɗa ido, sai ta yi nufin miƙewa ya riƙe kafaɗarta da ɗaya hannun ya mayar da ita ta kwanta.
Ya kwanto kaÉ—an yana kallon fuskar ta ya ce, "ina taimaka miki ne, relax!."
Sai ta koma ta kwanta a hankali, hannunsa yana kan water bug ɗin da ta ke jikinta, ga ahi jikinta babu riga, fatarsa hannunsa tana taɓa fatar cikinta. Ta yi shiru idanunta a rufe har lokacin hannunsa yana cikin bargon bai cire ba. Sai da ruwan da ya ɗora mata ya yi sanyi sannan ya ɗauko bag ya fito da ita ita ya ajjiye a gefe, ya sake taɓa goshinta ya ji zazzaɓin ya sauka har ta yi bacci.
Ya kalli fuskar ta ya ga bacci take yi, kuma ga gumi a goshinta. Ya ɗora hannunsa a goshinta ya shafa gumin, sai ya ɗauki remote ya ƙara mata ac.
Maimakon ya tashi ya tafi sai zauna ya zuba mata ido yana kallonta, ya kasa ya janye idanunsa daga kanta yana ji zuciyarsa tana bugawa sosai.
Kanta yake kallo da aka yi mata kitson da yake ɗaukar hankalinsa, bai san ya kai hannunsa ya shafa kalbar kanta ba, abinda yake ɗaukar hankalinsa kenan indai zai gani a jikinta, tun a Jeddah take ɗaukar hankalinsa sai yau ya samu damar taɓawa. Allah ya taimaka baccin ta ya yi nisa bata san hidimar da yake yi mata ba, hakan alamu ne na ta ji daɗin abinda ya yi mata.
Ya miƙe zai fita ya ji ta riƙe masa hannu, ya kalli hannunsa ya ga ta saka a ciki nata kuma bacci take yi. Ya yi murmushi yana kallon ta cikin wani irin yanayi, ya ɗan ranƙwafo ya janye hannunsa, ya shafa fuskar ta tare da pecking goshinta ba tare da ya yi nufin yi ba. Ya sake rufe mata jikinta, ya fita daga ɗakin yana waiwayonta.......
Nana Haleema.
RDB3P60
Nana Haleema.
Yana fitowa daga ɗakin Mamy ta shigo falon ya kalle ta kafin ya yi magana ta ce, "Na haɗu da ƙawar Islaha ne tace min bata da lafiya, me yake damunta?."
Ya É—an yi shiru sannan ya ce, "Cramps."
Mamy ta ce, "Ayya, na lura yana bata wahala da ba ka nan. Yanzu ya jikin nata? Ka bata magani?."
Ya ɗaga kai ya ce, "ƙawarta ta bata magani, ta yi bacci."
Mamy ta wuce shi ta shiga É—akin ganin bacci take yi sai ta fito ta ce, "take care of her, ka yi mata duk abinda ya kamata, please."
Ya lumshe ido dan a gajiye yake sosai, amma haka ya buÉ—e ido ya ce,â€Okay Mamy."
Mamy ta ce, "i saw your interview, za mu yi maganar gobe in sha Allah, Good night."
Ya yi mata side hug sannan ya ce, "good night Mamy."
Ta juya ta sauka ya rufe ido yana ajiyar zuciya, ya sake kallon ɗakin sai ya buɗe ƙofar ya ɗan leƙa ta yana hangota a kwance tana bacci.
Shi in akace wani babu lafiya ba ya iya nutsuwa, ba ya so ya ji wanda suke tare ance ba shi da lafiya yanzu duk sai ya damu kansa.
Ya shiga ɗakin yana kallon yadda take bacci peacefully, ya miƙa hannunsa ya taɓa wuyanta ya ji temperature ɗinta normal.
A lokacin Islaha ta buɗe ido suka haɗa ido cikin ƙaramin hasken ɗakin, yanayin yadda idanunta suka koma irin na mai bacci ya saka Rehaan ya lumshe ido ya buɗe yana sake kallon idanunta da suka ɗauki hankalinsa, sai kuma ta mayar da idanunta ta rufe alamun a cikin bacci ta buɗesu.
Ya ɗora hannunsa a kanta ya shafa gashinta da yake ɗaukar hankalinsa sosai, yana kallon fuskar ta yana tuna yadda suka yi da ita kafin su yi interview. Ya janye hannunsa daga kanta, ya fita daga ɗakin ya rufe mata ƙofa.
Islaha sai cikin dare ta farka tana jin yunwa mai yawa, ta tashi zaune tana runtse ido har lokacin tana jin ciwon amma ba sosai ba.
Ta miƙe tsaye ta shiga banɗaki ta yi wanka ta fito ta saka doguwar riga mara nayi ta kalli agogo ta ga ƙarfe uku da rabi na dare, ta buɗe ƙofar falon ta fito tana kallon falon.
Falon shiru babu kowa, amma akwai blue light a kunne, ta ƙaraso tsakiyar falon tana tafiya a hankali dan har lokacin marar ta tana yi mata ciwo kaɗan kaɗan. Daidai lokacin Rehaan ya yi sallamar sallah ya juyo ya side ɗin da take tsaye. Ba su haɗa ido ba dan bata kula dashi ba, sai da ta juyo suka haɗa ido a lokacin har ya miƙe tsaye yana kallonta.
Kallonta yake yi yana mamakin abinda ya fito da ita a daren, ga shi ko É—ankwali babu a kanta, rigar jikinta iyakacinta guiwa, kana kallon fuskarta kasan bata da lafiya.
Islaha ganin yana kallonta sai ta yi nufin komawa ciki, dan bata so suna haɗuwa da ƙaramar riga a jikinta, bata jin daɗi in yana ganinta a haka.
Cikin muryarsa mai É—aukar hankali ya ce, "Are you okay?."
Maimakon ta ƙarasa koma ɗakin kawai sai ta fara kuka, ta koma ɗaki da hanzari ta zauna a kan gado tana kuka.
Rehaan ta dafe goshinsa ganin daga yi magana ta fara kuka, kamar kar ya bita dan bai sani ba ko maganarsa ce ta saka ta kuka, shi kuma ba ya son takura mata tunda bata da lafiya ba neman faɗa yake yi ba. Kasa haƙura ya yi haka ya bi bayanta ya shiga yana kallonta ganin kuka take yi da gaske ba wasa ba. Abin ya ba shi mamaki ya tsaya daga bayanta ya ce, "Are you okay?."
Islaha cikin kuka ta ce, "Yunwa nake ji."
Rehaan sai ya ji daÉ—i da ba wani abun ne yake damunta baya ce, "kawai dan kina jin yunwa sai ki yi kuka?."
Bata ce masa komai ba kuma bata daina kuka ba, ya ce, "okay me ki ke so ki ci?."
Ta lumshe ido tana jin yadda yake yi mata magana a hankali cikin kulawa da, ta ce, "Spicy Noodle."
Ya bi bayanta da kallo dan bayanta kaÉ—ai yake iya gani, shape É—in jikunta ya biyo ta baya sosai, ya bayyana kamar an zana mata shi.
Ya É—an É—auke idanunsa ya ce, "Okay dare ne yanzu, ki je ki dafa da kan ki" ya faÉ—a yana fita daga É—akin.
Islaha bata fito ba ta koma ta kwanta a hankali, gabaɗaya in tana period rasa nutuwarta take yi, ta dinga yin abubuwa kamar ƙaramar yarinya. Ta yi lamo a kan gadon, tana tunanin Hamma da yana nan da duk abinda ta ke so sai ya kawo mata a daren ya bata.
A bayyane ta ce, "Allah ka kawo min mai bani."