Sashe 55
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Islaha tunda ta tashi wajen daga aiki ta kiran Barr amma bai ɗauka ba, bata jin daɗin jikinta saboda yanayin da take ciki. Ta yi ƙaramin tsaki, ta hau napep ta nufi inda suka yi da Saheer zasu haɗu. Gab da ƙofar gidansu Saheer ta ga motar Sadik, ta sauka ta nufi motar ta buɗe kawai ta shiga tana jan numfashi dan jinta take a takure.
Saheer ya kalle ta sai ya ga yi haske kuma ta yi kyau sosai, Islaha ta buɗe ido suka haɗa ido da shi, Saheer ya ce, "kwana a cikin ac, da ruwa mai roba ya karɓe ki, kin ƙara kyau Islaha. Allah ya bani kuɗin da zan sa ka mana ac a gidanmu."
Islaha bata ba shi amsa ba, ta kawar da kanta sannan ta ce, "Hamma ina yini."
Ya ce, "Ya jikin ki?."
"Lafiya lau."
"Yau sai na ganki a napep, ina driver na ki?."
Islaha ta yi tsaki tana tunawa da rainin wayon da Rehaan ya yi mata ta ce, "ban neme sa ba."
"Meyasa?."
"raina min hankali aka yi akan motar, shiyasa ni kuma ce na daina hawa motar, sai na ga abinda aka isa ayi min a cikin gidan."
Kafin ya tambaye ta ta abinda aka yi mata ta riga shi magana ta ce, "Baffa yana nan? Ina so na shiga mu gaisa."
Ya ɗaga kai ya ce, "Yana nan" ya faɗa yana ɗauko leda a back seat ya miƙa ya ce, "Ga lays ɗin na ki nan."
Islaha ta karɓa ta ce, "Na gode Hamma, ashe ba la ka manta ba." Ya yi murmushi kawai bai ce komai ba.
Islaha ta ce, "ka ce kana so mu haÉ—u, kuma ka yi shiru."
Ya juyo ya kalle ta ya ce, "Ina Rehaan É—in?."
Islaha ta buÉ—e idanunta waje ta ce, "Yawo nake yi da shi a jaka?."
Yadda ta yi maganar ya ba shi dariya, ya yi dariya ya ce, "Ina tambayar ki ne kawai."
"To ai kaine Hamma, kamar wata wacce ta ke yawo da shi a jakar ta ka ce min ina Rehaan?. Ba ya ƙasar nan, an ce yana Engaland." Saheer ya girgiza kai bai ce komai ba.
Islaha ta sake kallonsa ta ce, "Meyasa ka tambaye ni inda yake?."
Ya É—age kafaÉ—a ya ce, "kawai."
Bata ce komai ba sai wayarta da take ƙara, ta ɗauko ta daga jaka ta duba ta ga abokiyar aikinta ce, ta ɗauka tana faɗa mata inda ta ajjiye abinda ta ke nema. Bayan ta kashe ta kalle shi ganin har lokacin ita yake kallo, cikin gajiya da kallon ta ce, "Hamma na canja maka ne? Sai kallona ka ke yi."
"Kin canja magana, ba ki ji nace kin ƙara kyau ba?."
"Ina kyaun a nan?."
"Ga shi nan na gani, skin É—inki ta koma kamar zuma."
Islaha ta yi murmushi dan ta kawar da maganar ta ce, "ya aikin gidanka, ana yi?."
Ya É—aga kai ya ce, "ana yi sosai ma, kuÉ—i ne babu a hannuna, kin ga ban koma aiki ba har yanzu. Tsoron hanyar nake ji wallahi, ni kaÉ—ai na san wahalar da na sha a hannun mutanen nan."
Islaha ta ce, "wai a daidai ina suka kama ka?."
"A Bauchi ne. Kin san in zan je Nijar daga Adamawa hanya mafi tsaro da sauƙi, amma tafi nisa itace na hau motar Bauchi, daga Bauchi na shiga Kano, daga Kano na shiga Katsina, daga nan na hau hanyar Nijar. Na bi hanyar da ake tunanin tana da tsaron ma ban tsira ba."
"Allah ya kiyaye gaba, in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba."
"Allah ya sa. Akwai abinda nake tunawa a can, ina ji kamar na bar wani gurbi mai mahimmaci a rayuwata, wani lokacin sai na ji kamar na koma."
Islaha da mamaki ta ce, "ban taɓa jin wanda ya baro dajin yake cewa yana ji a ransa kamar ya koma ba sai kai, meye abinda ka ke tunawa?."
Ya waiwayo ya kalle ta yana ajiyarzuciya ya ce, "amana aka bani, kuma na taho na bar ta a can, amma akwai Allah."
"Amanar me?."
"Zan faÉ—a miki, ba yanzu ba."
"To shikenan. Amma sai na ga meyasa baza ka cigaba da neman kuÉ—in ka a nan ba, ba sai ka canja wani wajen ba."
Ya lumshe ido ya ce, "an fi samun alkhairi, kuma kin san ance mutum ya mayar da hankali akan ƙwarewarsa." Ta ɗaga kai tana kallon agogo jin ana kiran sallar la'asar.
Ta ce, "har lokacin sallah ya yi, zan je mu gaisa da Baffa." Ya É—aga mata kai ta fita daga motar.
Ya bita da kallo yana bitar komai daki-daki a ransa, yana jin tsoro a zuciyarsa, yana ganin kamar ya rasa ta har abada, wani lokacin sai ya ga kamar Islaha ta fi ƙarfinsa gabaɗaya, amma alƙawarin da ta yi masa yana ba shi ƙarfin guiwa matuƙa.
Islaha bata shiga gidan ba sai da ta tabbatar an idar da sallah, tana tsaye a harabar gidan ta harɗe hannu a ƙirji tana kallon gidan Baffa ya shigo suka haɗa ido, yana ganinta ya yi murmushi ya ce, "Islaha, ke ce tafe?."
Islaha ta yi murmushi ta ce, "Ni ce Baffa."
Baffa ya cs, "Sannun ki da zuwa, ya ba ki shiga ciki ba?."
"Daman kai nake jira ka shigo."
Baffa ya murmusa ta ce, "mu je to." Tare suka shiga har ɓangarensa ya zauna sannan ya ce, "Maraba da Islaha, jiya nake zancen ki a raina."
Ta yi murmushi ta ce, "Ina yini Baffa."
Ya amsa da fara'a ya ce, "Ina fatan komai lafiya."
"Lafiya lau Baffa."
"Ma sha Allah, Allah ya cigaba da shiga lamarin ki. Na ji daɗi da na ganki haka, na ji daɗi da ki ka karɓi ƙaddara ki ka saka a ranki Allah ne ya zaɓa miki mijin da ki ka aura, Allah ya yi miki albarka."
"Amin Baffa."
"Kamar kin san ina neman ki."
Islaha ta ji gabanta ya faÉ—i duk da bata san akan me zai yi mata magana ba, amma sai ta ji kamar akan auren yarjejeniyar da ta yi ne.
Baffa ya ce, "lokacin da aka ɗaura auren ki, akwai kuɗi masu yawa da aka tura min, akace mim kuɗi me irin wanda ake yiwa yarinya na hidimar aure. Kuɗin aure, lefe, da sauran hidimar da ba a yi miki a lokaci aurenki ba saboda ƙurewar lokaci. Kuɗi ne masu yawa Islaha, dan sai da aka kulle min banki da kuɗin suka shiga, ban jima da gama gyaran bank ɗin ba. Abinda ya saka ban yi miki magana ba saboda yadda ki ka bar gidan nan, da yadda Hamman ki ya dawo, shiyasa na jinkirta. Amma tunda kin nutsu, zan tura miki kuɗin ki."
Islaha ta ce, "Baffa ka bar su a hannunka kawai, ni ba sai na karɓa ba."
Ya yi murmushi ya ce, "A'a Islaha, bazan ajjiye a wajena ba, in na mutu ban ba ki ba fa? Faɗa min lambar akawun ɗin ki na saka miki kuɗin ki. Bazan ci abinda ba nawa ba, haƙƙinki ne, ke za ki ci kayan ki."
"Amma Baffa ai ni na ce ka bari, ni wallahi ban san me zan yi da kuÉ—in ba."
"Za ki sani in na ba ki, ba ni na sa ka miki."
"Don Allah Baffa."
"A'a Islaha, bana so muna ja in ja da ke, kawo kawai." Babu yadda ta iya haka ta ba da account details É—in ta.
Sai kuma ya ce, "rarraba su ma na yi a akawun mabanbanta saboda na tura miki lokaci É—aya, Da na je banki akwai wanda muka yi magana da shi, ya ce in zan tura miki na faÉ—a masa, zai kwashe duka ya tura miki."
Ita dai bata ce komai ba, kanta yana ƙasa tana ganin Baffa yana ta danna waya alamun kuɗin zai tura mata. Ya ɗan jima a haka kafin ya ce, "Ma sha Allah, na sauke nauyi. Kuɗin ki sun bar hannuna."
Bata ji alert a lokacin ba amma ta san zasu shigo. Ta É—ago kanta ta ce, "To Baffa na gode, Allah ya saka da alkhairi."
"Amin Islaha. Ki shiga ku gaisa da mutanen gidan."
Bata yi masa musu ba ba ta miƙe ta fita daga falon a a daidai lokacin alert ɗin ga faɗo wayar ta. Ta kalli kuɗin ta notification sai ta buɗe ido, ta shiga bank application ɗin ta ga uban kuɗin da su ke ciki. Da hanzai ta shiga calculator a tunanin ko bata gane lissafin ba, ta rubuta kuɗin da ta gani, ta tabbatar da gaske kuɗin ta gani a cikin wayar ta.
Islaha cikin firgici ta ce, "Na shiga uku! wannan kuɗin na yi me dasu?" Ta haɗa harda dafe ƙirji bayan ta zaro idanu.
Da hanzari ta koma wajan Baffa, ta same sa a zaune inda ta bar sa ta ce, "Baffa kuɗin sun zo, ya zan yi da kuɗin nan? Wallahi ban san me zan yi daau ba. Kuma nima na san sai an yi frezzing account ɗina, bai taɓa ɗaukar kuɗi mai yawa haka ba. Baffa don Allah na dawo ma ka dasu ka ajjiye a hannunka."
Baffa ya yi murmushi ya ce, "Haƙƙin ki ne, ki yi yadda ki ke so."
Babu yadda ta isa haka ta fito tana sake kallon kuÉ—in ta shiga wajan Mama.
A zaune ta same ta ita da Karima aminiyarta, suna ta waya da Labiba cikin nishaɗi ana saka mata albarka. Islaha ta shiga da sallama ta zauna daidai lokacin da Labiba ta ce, "Islaha ai yawonta ta gama yi a jedda, babu gidan balaraben da ba a santa ba, ba san adadin mazan da ta sani ba wallahi, ƙarshe har zubar da ciki ta yi."
Mama ta kalli Islaha da take jin abinda Labiba ta cd sannan ta ce, "zata aikata, wannan yarinyar me baza ta iya ba?. Ke dai ki cigaba da kama kanki a duk inda ki ke.
Allah ya yi miki albarka, Allah ya kare ki, ki cigaba da turo mana kuÉ—i muna harkokin gaban mu."
"Amin Mama. Ai Makka ya fi Jedda daÉ—i, tunda nan da hausawa sosai, can kuwa babu."
"ki yi zaman ki a nan, Allah ya kawo miji na gari ki yi auren ki."
"Amin Mama, ina zuwa" ta faÉ—a tana kashe wayar ta.