Sashe 26
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suka fita suka shiga gidansu Safeera, suka yi alwala tare da yin sallar azahar, Islaha ta jingina da gadon Safeera tana sauke numfashi a hankali.
Safeera ta ce, "wai akan saƙon da Zainab ta bawa Yafindo ne?."
Ta É—aga kai ta ce, "Tunda ki ka ji haka, tabbas akwai lauje a cikin naÉ—i, sune suka hana ta magana dani, kuma wallahi bazan dakata ba."
Safeera ta ce, "ki yi a hankali, ko dan saboda ita, kar a cutar da tsohuwar Allah."
Islaha bata ce komai ba ta ɗaga kai kawai, sai kuma ta yamutsa fuska ta buɗe jaka ta ɗauko cincin a ƙaramar pack tana ci.
Safeera ta saka hannu suna ci tare, kafin ta zame ta kwanta a wajen bacci ya É—auke ta. Safeefa ma bacci take ji amma an kusa sallah bazata yi ba, sai ta tashi ta fita tana aiki.
Bayan sallar la'asar Islaha ta ce, "Ina kayana Safeera?."
"Gasu nan."
"Zan É—an É—auki wasu" ta faÉ—a tana buÉ—ewa tana É—auka wanda zata yi amfani dasu.
Ta ajjiye a gefe ta ce, "zan je wajan Hamma yanzu, ya ce yana so zamu yi magana."
Safeera kai tsaye ta ce, "sai kin dawo."
"Ki zo mu je don Allah."
Safeera bata ce komai ba ta saka hijjab suka bar ƙannenta a gidan suka shiga gidan.
A harabar gidan Islaha ta tsaya ta kira shi a waya ta ce, "Ga ni na zo."
A lokacin aka yiwa Safeera waya ta duba ganin Baba ne yake yi mata waya sai ta ɗauka, tana kashewa ta ce, "Baba ya aiko daga kasuwa na ba da saƙo a kai masa, bara na je na bayar na dawo." Islaha ta ɗaga kai Safeera ta fita da sauri.
Basu jima da wayar ba ya fito daga É—akinsa yana nufo inda take tsaye, ya zuba mata ido yama kallo ganin fuskar ta babu walwala ko kaÉ—an.
Saheer ya ce, "mu je Falon Mama, bata nan." Tare suka shiga suka zauna akan kujera daban daban, Islaha ta jingina da kujera bata ce komai ba.
Saheer zuba mata ido na wani lokaci, ganin ita ba shi take kallo ba wani wajen take kallo daban. Ya ce, "Ba ki shirya magana dani bane?."
Ta É—ago ido ta kalle sa ta ce, "sau nawa ina so nayi magana da kai kana share ni?."
Ya É—an girgiza kai ya ce, "kin san kishi kuwa?." Bata amsa ba sai kawar da kanta da ta yi bata amsa masa ba, dan bata da amsar tambayarsa.
Saheer ya ce, "Ina jin ki.
Ta sake kallonsa ta ce, "in na faɗa maka zaka iya cewa ƙarya nake yi, ni kuma bazan jure wannan kalmar ba."
Ya zuba mata ido bai amsa ba, sai kuma ya É—an É—aga kai ya ce, "ina jin ki."
Ta buÉ—e handbag É—inta ta É—auko takarda guda biyu ta ce, "auren contract ne, an bani kuÉ—in fansarka na bada kaina zan zauna a matsayin mata na wata biyar, yau an ci kwana uku, saura kwana É—ari da arba'in da bakwai. Ban sani ba ko baza ka yarda ba, Amma Allah ya san meye a zuciyata, na yi ne saboda kar su kashe ka" ta faÉ—a muryarta tana fara cracking.
Ta yi ƙoƙarin daidaita kanta kar ta yi kuka ta ce, "Amma wai kaine ka ce min na zaɓi kuɗi akan halacci ko Hamma?."
Saheer ya ce, "Islaha Allah ne kaÉ—ai ya san abinda nake ji a raina, aure ki ka yi, ki ke zaune da wani namijin a mtsayin mijinki, ya ki ke so na yi?."
"amma kai ka san babu wani mai kuÉ—i da isa ya ruÉ—e ni na aure sa na bar ka ko? Kasan babu wani wanda zai zo ya É—auki hankalina saboda kuÉ—i. Wallahi babu shi a duniya, har yanzu ba a yi wanda kuÉ—insa ko wani nasa zai yaudare nii ba, ka fi kowa sannin kuÉ—i basa É—aukar hankalina kuma basa tayar min da hankali. In na ce ina so kawai ina so ne, ko da kuÉ—i ko babu na yarda zan zauna a inda Allah ya ajjiye ni."
Saheer "Ina jin ki, ya saka hannu a takardar jarjejeniya sannan ya ba ki miliyan hamsin saboda ki zauna da shi? Waye shi a garin Yola?."
Islaha ta kalle shi ta ce, "shima ba son auren yake yi ba kamar yadda bana so nima.
Daga taimako abin ya zamar min alaƙaƙai, kakarsa na taimakawa na kaita gida, daga nan take cewa sai na auri jikinta. Da farko na yi tunanin wasa take yi ko kuma rikicin girma ne, ashe ni ce ban fahimta daidai ba. Shine suka zo da maganar wajan Baffa, ni kuma daman na san shi, ya nuna ba ya son auren har ya kawo zancen auren wata biyar, dan da ace bai kawo batun contract ba ko kaɗan ban ji a raina shi ya kamata na yi ba. A wannan lokacin aka turo video ka ana dukan ka, sai na kasa jurewa na je na amince da auren wata biyar amma da sharaɗin zai bani kuɗi. Kuma ya bani kuɗin, tunda ga si har ka kuɓuta, ka ga dole na zauna da sji har lokaci ya ƙare."
Saheer da yake kallon ta ya ce, "ba ki faÉ—a min waye shi ba."
Ta É—an sauke numfashi ta lumshe ido ta buÉ—e sannan ta É—ago ido ta kalle sa ta ce, "Rehaan yola."
Saheer ya tsayar da idonsa ƙyam a kanta, ya buɗe su yana kallonta cikin tsananin mamaki da bugawar zuciya da firgici mai yawa.......
Nana Haleema.
RDB2P22
Nana Haleema.
Ganin yadda ya zuba mata idanu sai ta É—auke kai daga kallonsa, ta kawar da kai gefe ta yi shiru bata ce komai ba.
Shiru ya ratsa tsakaninsu kafin ya tashi zaune sosai yana kallonta ya ce, "Ranar da aka sace ki, da ki ka dawo daga ba ya kin ce shine. Sannan da ki ka je Jeddah, nan ma da ki ka dawo kin ce kin haÉ—u dashi a can, yanzu kuma kin yi auren yarjejeniya da shi."
Ya ja numfashi kafin ya lumshe ido ya ce, "Islaha!."
Bata kalle shi ba ta ce, "Hamma!."
Ya ce, "meyasa baza ki faÉ—a min gaskiya ba, meyasa baza ki faÉ—a min duk wannan abubuwan plan É—in ki ne?. Anya garkuwa dani baya cikin plan É—inku ke da Rehaan?."
Islaha ta waiwayo ta kalle shi jin abinda yake faɗa, ta girgiza kai tana harararsa ta ce, "Hamma na gaji, na gaji da yi maka rantsuwa kana ƙaryata ni...."
"Ina so ka san in ina da niyar auren Rehaan bazan ƙulla auren wata biyar da shi ba, zan aure sa ne kai tsaye kamar yadda iyayensa suka nema. Meyasa ba ka yarda dani ba, meyasa zuciyarka ta ke rawa a kaina ko yaushe?. Kawai dan na burge ka ko dan na ɓoye gaskiya sai na rantse akan ƙarya? Hamma bazan zubar da hawayena a kan ƙarya ba, bazan rantse akan ƙarya ba, bazan zo na zauna a gaban ka akan ƙarya ba. In kana ganin plan mu ka haɗa nida shi mu je a hakan ne kawai, Allah yana ji kuma yana gani."
Saheer ya ce, "maganar ta ki ce bata yi making sense ba, ko waye a matsayina dole ya amince akwai wani abu a tsakanin ki da Rehaan. Rehaan yola da yake yiwa mutane wahalar gani, yaro matashi da sunansa ya yi tambari a ƙasar nan gabaɗaya, yaron da ake ƙididdigar ya fi ko wanne matashi kuɗi a ganin nan. Ba iya Yola ba, ana cewa a yanzu a nigeria yana daga cikin matasan da Allah ya yi musu baiwar kuɗi. Islaha ta ya ki ke so na yarda da wannan kitimurmurar?."
"Ba ka yarda Rehaan Yolan bane?."
"Ina shakku a kan hakan, me ya haÉ—a ki dashi da rayuwarki take katantanwa a cikin tasa?."
Ta yi ajiyar ta miƙa masa takardun ta ce, "Ka duba, wataƙila in ka ga sunansa da signing ɗinsa ka yarda shine."
Bai musa ba ya karɓa, ya fara buɗe takardar Rehaan yana karanta rules ɗinsa bit by bit. Ya ninke ta Rehaan, ya buɗe ta Iskaha yana bi a hankali har ya gama, ya ajjiye mata ta kwashe ta saka a jaka.
Ta sake kallonsa ta ce, "In ka amince dani daidai ne, in zuciyarka tana shakku a kaina wannan ma daidai ne Hamma. Abu ɗaya nake so ka sani, Rehaan shine ya shiga rayuwata bani na shiga ta sa ba, shine ya kwanto kura daga cikin kejinta ya sake ta a cikin jama'a. A yanzu ni matarsa ce, shaidu ɗaurin aure sun shaida kuma an ba da sadaki. Amma a wajena da wajensa ni matar yarjejeniya ce, da zarar lokaci ya ƙare kowa zai kama gabansa."
"No intimacy, kuma ya yarda?."
A sama ta ji tambayar tasa, ta É—ago suka haÉ—a
Ido sai ta É—auke kai daga kallonsa ta ce, "ka karanta da kanka ka gani, kuma ka ga inda ya saka hannu, da bai amince ba ka gani ba."
Ya zuba mata ido bai É—auke idanunsa ba yana kallon ta, sai ya gyaÉ—a kai ya ce, "Kuma ke kina ganin zai sake ki?."
"Me zai hana? Da zarar contract ya ƙare zai sake ni na kama gabana. Shima ba ya son auren kamar yadda bana so. Kowa yana rayuwa da ɗan uwansa ne saboda babu yadda zamu yi, ni na zauna dashi saboda kai, shi yana zaune dani saboda kakarsa da mahaifinsa."
Saheer ya sauke numfashi ya ce, "zuciyata tana faɗa min kamar auren nan bazai rabu, ina ganim kamar na rasa ki har abada. Ina ganin kamar kin tafi kenan, duk zaman jiran ki da na dinga yi kamar ya tashi a banza. Inda za ki dawo ɗin zan jira ki daga nan har shekara biyar ba wata biyar ba, amma dawowar ki ce na san baza ta taɓa yuwa ba. Babu yadda za a yi ki auri namiji kamar sa sannan ki bar shi ki dawo wajena ba."