Sashe 47
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ban same ta ba, an tabbatar min da bayan fitar ki babu jimawa aka ga wasu sun shiga gidan, daga nan aka ga ta haÉ—o kayanta ta bar gidan."
Islaha ta dafe ƙriji cikin tashin hankali ta ce, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Amma ba su yi mata komai ba ko?."
Ya ce, "Babu abinda su yi mata komai ba, kawai dai an ga ta haÉ—a kayanta ta bar gidan. Hakan alamu ne da an yi mata barazana a kan zuwan ki, shiyasa ta bar gidan."
Ta dafe kai ta ce, "na shiga uku! Hamma na raba mata da muhallinta."
Jin zata fara kuka sai Suraj ya ce, "Kar ki damu, aikin zai zo da sauƙi, yanzu nemo inda take zamu saka a gaba, daga nan sai mu san abinda zamu yi."
"A ina zamu san inda take?."
"Wannan ba matsala bane zan duba, dan ya zama dole sai mun nemo ta, itace mace ta ƙarshe da ta yi magana da Zainab, kuma Zainab itace kaɗai hujjarmu, dole mu nemo ta."
Islaha tankasa cewa komai sai kuka da take yi. Daƙyar ya rarrashe ta ya kaehe wayar. Yana kashewa kiran Saheer ya shigo, tana ɗauka ta fashe masa da kuka mai sauti......
Hankalim Saheer ya tashi sosai ya ce, "Lafiya ki ke kuka, faÉ—a min me ya faru?."
Cikin kuka ta ce, "Na shiga uku Hamma."
"islaha meye?."
Bata ce komai ba sai kuka da take yi, sai da ta gaji sannan ta ba shi labarin komai.
Ta ɗora da cewa, "Yanzu ina za a ganta, in aka cutar da ita fa?. Na zama silar ɓacewar mutum biyu, ga Yafindo ga Zainab."
Saheer ya ce, "Ki daina kuka, in Allah ya amince babu abinda zai same ta."
Jin ta sassauta murya kukan ya ragu sai ya ce, "Na faÉ—a miki ki dinga bin komai a sannu bakya ji, yanzu da an kashe ki fa? Meyasa za ki je wajan ke kaÉ—ai ba ki tafi da police ba? Da sun taka ki da mota kin mutu me gari ya waya?."
"Hamma na damu ne, ina so na kawo ƙarshen....."
"Nima na damu, damuwar ki damuwata ce. Ki tambayi Sadik, babu inda ba na zuwa a kan neman Zainab, babu information É—in da ba na samu akan gidan saboda na taimaka miki ki yi nasara akana binda ki ka saka a gaba. Kin cika gaggawa, bakya bin komai a hankali, ke ko yaushe sai ki ce a take ki ke so ki yi abun. Ko yaushe abinda ki ke so shi za ki yi, bakya shawara da kowa sai dai kawai ki zartar."
Jin yana ta yi mata faÉ—a sai ta yi shiru. Saheer ta ce, "ga shi nan har an fara harin ranki akan maganar, da sun taka ki da mota da ba ki cuce mu ba?."
"To ka yi haƙuri."
"ya zan yi miki in ban haƙura? Ai dole na haƙura."
"To ka daina yi min faɗa, Allah na damu ne shiyasa ka ga ina waɗanan abubuwan. Ina so na kawo ƙarshen abun, bana so abun ya cigaba da gaba saboda yara masu tasowa. Lokaci yana ta tafiya, na kasa yin komai shiyasa na damu."
Ya sauke numfashi ya sassauta murya ya ce, "Na sani, nima ina fatan hakan. Yanzu me Barr ya ce?."
"ya ce ya zama dole a nemo ta, ita kaÉ—ai ce hujjar mu take hannunta."
"A ina za a ganta?."
"Bamu sani ba."
"shikenan, Allah ya sa a ganta É—in. Da alama abinda yake hannunta babba ne, tunda ki ka ji ana maganar an neme ta an rasa."
"Shine abinda nake nima."
"Shikenan, Allah ya bamu sa a. Amma ki dinga yi a hankali, ki dinga bin komai a nutse, kin ji?."
"In sha Allah."
Saheer ya ce, "Zan kira ki in anjima" ya faÉ—a yana kashe wayar. Ta bi wayar da kallo tana lumshe ido, tana tunanin ina Yafindo ta tafi?........
RDB3P37
Nana Haleema.
Har dare Islaha bata san Rehaan ba ya nan ba, tana ɗaki yin komai a sanyaye cikin tunanin abinda ya kamata ta yi akan matsalar da ta yi mata dabaibayi. Bayan sallar i'sha tana zaune a sama ta ji ana hayowa saman, sai ta zubawa ƙofar ido har ta ga Banisha ta shigo.
Suna haÉ—a ido Banisha ta yi murmushi tana kallon Islaha ta ce, "Sannu Sis, Mamy tana neman ki."
Islaha ta yi murmushi ta ce, "To mu je tare" ta faÉ—a tana gyara mayafin da ta yi sallah da shi suka fito tare.
A zaune ta samu Mamy a falo ita da Ikram suna zaɓen kaya a waya. Sallamar ta ya saka suka ɗago suna kallonta duka su biyun, Islaha ta ƙarasa ta zauna sannan ta ce, "Mamy barka da dare."
Mamy ta ce, "Barka dai Islaha. Ya ki ke?."
"Lafiya lau."
"Kin san Rehaan ya yi tafiya?."
Islaha ta kalli Mamy suka haÉ—a ido, sai Mamy ta yi mata kwarjini sosai, hakan ya saka ta sunkuyar da kai ta ce, "ban sani ba."
Mamy ta ce, "Ya koma Englaand, bazai dawo ba sai nan da two weeks. Ban sani ba ko chef É—insa yana zuwa?" Ta faÉ—a da sigar tambaya tana kallonta.
Islaha ta ce, "Yana nan, ko yanzu ma an yi dinner."
Mamy ta ce, "Good. Na yi tunanin babu abinci ne shiyasa na kira ki na faÉ—a miki, in kina son abinci sai ki faÉ—awa maids É—ina su dinga kawo miki, tunda akwai abinci a can shikenan."
Islaha ta yi shiru tana so ta yi magana amma ta kasa, sai kuma ta buɗe baki daƙyar ta ce, "Mamy ni....." sai ta yi shiru ta kasa ƙarasawa.
Mamy cikin kulawa ta ce, "Ina jin ki, faÉ—i abinda yake bakinki."
"Bazan iya kwana ni kaÉ—ai ba, tsoro nake ji."
Mamy ta ce, "babu matsala, ki dawo nan sai ki zauna har sai ya dawo."
Islaha sai ta ji daÉ—i a ranta ta ce, "To, na gode."
Mamy ta ce, "za ki iya komawa, in kin gama abinda ki ke yi sai zo sai Kiddo ta nuna miki inda za ku zauna." Islaha ta amsa cikin jin daɗi kafin ta miƙe ta fita.
Mamy ta kalli Ikram ta ce, "Kamar tana da hankali ko Ikram?."
Ikram ta É—an saukse numfashi ta ce, "Babu laifi." Mamy ta murmusa suka cigaba da duba kayan da suka yi order.
Islaaha tana komawa apartment É—in Ray ta ce, "Haka kawai a bar ni na kwana ni kaÉ—ai a nan sai wannan mahaukacin ya zo ya É—aga min hankali? A zo a sake yi min sharri a ce ni na kawo shi da yake ga shugabar Æ´an iska. Gwara na je can É—in na zauna, ni da ace ma Mamyn zata yarda da ko yana nan a can zan zauna, bana son haÉ—a inuwa É—aya da shi. Allah na tuba zaman kwana nawa ne? Balle ma yanzu da zan daina ganinsa da wuri zan ga lokacin yana gudu. Kafin ya yi two weeks ya dawo, ni kuma na yi three weeks a gidan nan, lokaci yana ta raguwa. Allah ya raka taki gona" ta faÉ—a tana hawa sama, har wani daÉ—i ta ke ji a ranta in ta tuna ya bar garin, bata son haÉ—a ido da shi ko kaÉ—an.
Harda hararar ɗakinsa sannan ta shiga ɗaki ta ɗauki abinda ta san zata ɗauka, ta kulle ƙofar ta fita dan ita zaman ne baza ta iya ita kaɗai ba, tsoron Salman take ji sosai.
Da sallama ta shiga apartment É—in Mamy Banisha ta amsa ta ce, "Sis sannu da zuwa, mu je na nuna miki É—akin."
Islaha ta yi murmushi ta riƙe hannunta kamar yadda ta miƙo mata hannu, suka shiga ciki dan Mamy bata parlor Ikram ce kaɗai a zaune.
Banisha ta buɗe wata ƙofa suka ga dogon corridor wanda ya sha decor kayan adon parlour, sai ɗakunann a jere. Banisha ta buɗe mata ɗakin ta ce, "Shigo Sis, kina san nan ina ne?."
Islsha ta ce, "sai kin faÉ—a."
"Tsohon É—akin Ray, har yanzu in ya so bacci a nan yake zuwa ya kwana, kin san yana son bacci a wajan Mamy."
Islaha ta murmusa tana kallon Banisha, dan ta lura iyalan Mamy suna da magana, irin faÉ—i ba a tambaye ka É—in nan bane, har ita kanta Mamyn tana da magana, Rehan É—in ne dai sama-sama.
Islaha ta ajjiye kayan hannunta tana kallon É—akin, É—aki ne babba mai kyau sosai, komai akwai a cikinsa kamar ana kwanciya a ciki.
A lokacin Mamy ta zo wucewa, ta gan su a cikjn ɗakin ta ce, "Kiddo ku dawo falo a gyara ɗakin nan, akwai ƙura."
Islaha ta kalli Mamy da take tsaye a bakin ƙofa, ta ga kanta babu ɗankwali har ta canja kaya zuwa kayan night wears.
Islaha ta zuba mata ido tana kallon ta, in ka kalle ta baza ka ce itace ta haifi ƙaton saurayi kamar Rehaan ba, baza ka ce ta aurar da ƴa kamar Riyya ba, tana da kyaun jiki sosai, shekarunta ba su nuna a fuskarta ba.
Islaha bata saba ganin haka a al'adarsu ta fulani ba, duk da ba wata shiga mara kyau Mamyn ta yi ba, doguwar riga ce ta bacci, sai gashinta da yake a buÉ—e ta naÉ—e ahi a tsakiyar kanta, sai hular sa take hannunta wacce zata saka.
Kiddo da Islaha suka dawo falon, ita dai Islaha bata ga ƙurar da za a share ba, da ace akwai ƙura a ɗakin tana shufa zata jita a hancinta, ɗaki sai ƙhamshi yake yi a dinga zancen ƙura?.
Suna fitowa falon Riyya da Jafar suka shigo, Ikram da Kiddo su ka yi tsalle suka suka rungume juna ita da Riyya suna murnar ganin juna.
Riyya cikin farin ciki ta ce, "My Sisters" Suka É—aga daga jikinta, Ikram ta ce, "Sis kin ga yadda ki ka yi kyau?."
Murmushi ta yi ta ce, "Ina Mamy?."
Mamy ta fito tana murmushi ta ce, "Gani nan Riyya." Riyya ta tafi da gudu ta yi hugging ɗinta, Mamy cikin murna ta riƙeta ta ce, "Amarya sannu da zuwa."
Riyya ta É—ago ta ce, "Mamy na yi kewar ki." Msmy bata ce komai ba ta ja kumatunta ta kalli Jafar.
Jafar ya murmusa ya ce, "Mamy ina yini."
"Ya ka ke Jafar?."
"Lafiya lau Mamy, Rehaan yana nan kuwa?."