← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 110

Sashe 27

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Islaha kin abinda yake faɗa sai ta ce, "Ka ɗauka na mutu kawai, amma matuƙar ina da rai auren nan zai ƙare kuma zan fito. Ni ta ka ce, wani daga waje bai isa ya zo ya ɗauke ni ba bayan tarin wahalar da ka sha dani. Zan iya jure ko wacce matsala indai a kan ka ne, kamar yadda na yi auren jarjejeniya saboda kai, zan iya ba da rayuwata saboda kai. Abinda yake bani matsala da kai, kana da ƙarancin yarda dani."

Ya lumshe ido ya ce, "Ba rashin yarda bane, na kasa sarrafa kaina ne. Kawai na wayi gari ance kin yi aure, ya ki ke so na yi miki?."

Ta sauke numfashi ta ce, "Nima na wayi gari ana kirana da matar aure ba dan na shiryawa hakan ba, sai dan saboda rayuwarka ta kuɓuta daga azaba da kuma uƙuba. Har yanzu ba ka dawo daidai ba, kowa ya ganka ya san akwai wahala a tare da kai, ta ya zan iya barin ka a can bayan na samu dama Hamma."

Sai ta yi murmushi ta ce, "Wata biyar ne kawai, da zarar ya ƙare aurensa zai saula daga kaina. Babbar matsala kuma Mama ce, ta yi rantsuwa ta ce babu ni babu kai."

Saheer ya ce, "Ba iya Mama ba, harda Baffa. Baffa zai yi wahalar sha'ani a wannan lokacin."

Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, kanta yana ƙasa bata ɗago ta kalle shi ba.

Saheer ya É—aga kai ya ce, "Kar Mama ta dame ki, babu abinda Mama zata yi, zata janye kalamanta da zarar lokacin ya yi. Musmaman yanzu da zata daina ganin ki na wata biyar wasu abubuwan zasu ragu in sha Allah."

"Allah ya sa, haka nake fata."

"Kuma da gaske za ki iya barin auren Ray ki zo ki zauna dani?."

Bata san ta yi siririn tsaki ta miƙe tsaye ba ta ce, "shi waye? Baka a kaf duniya babu wanda nake jin haushi kamar shi ba? Ba ka san duk duniya babu wanda nake jiran ƙiris da shi kamar sa ba?. Hmmm! Ban sake jin haushinsa yana ninkuwa a raina ba sai yanzu da nake ganinsa ko yaushe, ina jin kamar na soke idanuna da allura ko dan ya daina tozali da fuskarsa."

Saheer a sanyaye ya ce, "Meyasa ki ka amince da auren nan, meyasa ba ki bari an kashe ni ba?."

"Bazan iya hakan ba, bazan iya gani ina da dama a hannuna na bari wani abu ya same ka ba, shiyasa na amince ba dan zuciyata tana so ba Hamma. Amma babu yadda zan yi, hakan shine mafita a gare mu ba ki É—aya. Ga shiyanzu ka dawo, har kana zaune muna magana da kai, da ba a kai kuÉ—in ba fa?."

Ya gyaÉ—a kai yana lumshe ido ya ce, "bazan iya jiran wata biyar ba, ina ganin kamar shekara biyar ne."

"nima ina wannan tunanin, irin raina min hankalin da yake yi sai nake ganin kamar bazan iya ba kai wa wata biyar tare das shi ba, amma in na tuna na karɓi kuɗi sai jikina ya yi sanyi."

Saheer miƙe tsaye ya ce, "Zan jira ki daga nan zuwa ko yaushe, zan zauna zaman jiran ƙarewar contract ki dawo gare ni...."

Ya ɗan dakata da magana sannan ya ce, "Islaha ki yi min alƙawarin baza ki canja maganar ki ba, ki yi min alƙawarin duk daren daɗewa za ki dawo gare ni ba tare da iddarsa akan ki ba!. In ki ka yi haka zan tabbatar da ina da mahimmaci a rayuwar ki, zan tabbatar da maganar su Mama ba gaskiya ba ce.”

Islaha ta kalli cikin idon Hamma gabanta ya faɗi matuƙa, ta sunkuyar da kai bata ce komai ba sai kuma ta ɗago ta ce, "Na yi maka alƙawari zan dawo Hamma, yanzu ma ina zaune a can ne saboda kai, amma zan dawo gare ka in sha Allah. In Allah ya amince, in sha Allah  sai na zama matar ka, mu cigaba da addu'a."

Saheer ya yi murmushin da tunda ya baro daji bai yi irinsa ba, itama ta yi murmushi tana sunkuyar da kanta zuciyar ta tana bugawa sosai ba tare da ta san dalili ba ya ce, "Islaha."

Bata É—ago ba ta ce, "Na'am Hamma."

"Ki yi haƙuri."

"Babu komai, ai ya wuce."

"Na gode, ban san soyayyar da ki ke yi min ta kai haka ba."

Islaha ta yi murmushi ta ɗago zata yi magana, ya yi saurin tarar numfashin ta ya ce, "Na san kina sona Islaha, amma ban taɓa tunanin soyayyar ta kai ki sadaukar da kan ki saboda ni ba. Na gode, Allah ya sa muna da rabon zama ma'arauta."

Islaha ta sake sunkuyar da kai bata ce komai ba ko Amin É—in ta kasa faÉ—a, sai take jin bakinta da zuciyarta sun hanata amsa addu'ar.

Buɗe ƙofar da aka yi ya saka suka juya suna kallon wandw ya buɗe ƙofar gabaɗayansu.

Safeera ta bisu da kallo ganin ko wanne da murmushi a fuskarsa, da alama Islaha ta faÉ—a masa komai kuma ya yafw mata.

Safeera ta ce, "Islaha ke nake jira fa, ki yi sauri."

Islaha ta ce, "Hamma zan tafi, akwai aikin da yake gabana wanda nake so na kammala shi, sai mun yi magana a waya."

"Wanne irin aiki ne?."

Zata yi magana Safeera ta ce, "Islaha!."

Islsha ta kalle sa ta ce, "zan faÉ—a maka, sai anjima" ta faÉ—a tana É—aukar jakarta ta fita daga É—akin suka tafi.

Saheer bi Islaha da kallo yana tunani, zuciyarsa tana so ta gasgata Islaha amma wani ɓangaren ya hana shi hakan. Gani ya ke kamar ta riga ta yi masa nisa, gani yake ya rasa Islaha kenan har abada. Kalamanta sun ba shi ƙarfin guiwa, amma ta ya ya hakan zai kasance? Ya zai yi da Mama da ta yi rantsuwa akan bazai auri Islaha ba?.

Ya ya ajiyar zuciya ya zauna a akan kujera ya dafe kansa yana lumshe ido cikin tunani kala-kala. Hankalinsa ya kwanta sosai da kalamanta, ya ji daɗi da ya ke da tabbacin har wata biyar ta ƙare babu abinda zai haɗa Islaha da Rehaan na auratayya, amma tunaninsa ta ya auren zai rabu, in ya rabu shi ya zai yi da Mama?.

Islaha tunda suka koma gidansu Safeera take yi mata faÉ—a, cikin masifa da son nuna mata kuskure Safeera ta ce, "ina hankalin ki ya shiga Islaha, ina tunanin ki da ilimin ki ya tafi?. Kin manta wai kina da aure, kin manta ke matar aure ce, kin manta zama a waje É—aya kina hira da namijin da ba muharramin ki ba haram ne balle kuma irin Saheer?. Maganar aure fa ku ke yi, da auren wani a kanki ki ke biye masa kuna zancen aure, meyasa akan Saheer idanunki suke rufewa har bakya gane daidai da ba daidai ba?."

Islaha jin yadda take yi mata masifa ta ce, "ke ji mana, ba fa auren gaskiya mu ka yi dashi ba, auren bogi ne. Meye na tayar na jijiyoyin wuya akan auren da ko shi bai É—auke sa da daraja da mahimmaci?."

"Ke a wajan ki ne ya ke auren bogi, amma wajan Allah auren gaske ne. An tara mutane sun shaida, an ba da sadaki, an karɓi amanar ki a hannun waliyin ki, an tamƙa ki a hannun waliyinsa. Duk duniya haka ake ɗaura aure a duniyar musulmai, in ɗaurin aure bai yi kama da wannan ba to bana musulumci bane."

"Auren yarjejeniya da yake tsakanin ki da shi wannan a tsakanin ku biyu yake, ban da a wajan wanda ya halicce ku. Aure sunan sa aure, indai an shaida an ba da sadaki magana ta ƙare. Wallahil azim duk dariyar nan da ki ke yiwa Saheer zunubi Allah yake rubuta miki, duk bibiyarsa da maganar nan da ki ke yi azaba ki ke jawowa kanki. Ke matar Rehaan ce ba matar Saheer ba, tsakaninki da Hamma gaisuwa ce, in maganar ta wuce haka kun keta iyakar halaccinku."

Safeera ganin Islaha ta nutsu tana jin abinda take faɗa sai ta ce, "Kuma babu mai babban mai zunubi sai ke, domin ke ki ka biye masa har ki ka tsaya kina yi masa dariya. Ban san ina hankalin ki ya tafi ba, ban san me ya rufe miki ido ki ke so ki shiga wuta da ƙafar ki ba!."

Islaha sai jikinta ya yi sanyi sosai, dan ta san duk kalaman Safeera gaskiya, kuma ta san ta yi kuskure babba. Ta kalli Safeera ta ce, "Wallahi Safeera shine ya saka nake ɗaukar auren nan a haka, Yayansa mahaukaci ya nuna ni ya ce wai ina sonsa, har yana faɗa min in zan....." sai ta yi shiru bata ƙarasa.

"Shiyasa na ce miki wannan tsakanin ku ne, abu ɗaya nake so ki tuna, wallahi duk lokacin da ki ka sake kula Saheer da sunan soyayya ko maganar aure ke Allah zai kama ba Rehaan ba. Domin kin san kina da aure ki ke maganar aure da wani, sai Allah ya tsayar dake ya karɓawa Rehaan haƙƙinsa na wulaƙanta aurensa da ki ka yi, ban da azabar da Allah zai yi miki akan haka!."

Islaha ta sauke numfashi cikin nadama da danasani ta ce, "shikenan na ji, na yi kuskure bazan sake ba in sha Allah."

Safeera ta ce, "Ki tuba."

Islaha ta ce, "Astagafirullah!."

Safeera ta ce, "ya fi miki. Ki mayar da hankali akan abinda ya ke gabanki, in ba haka ba tarin zunubi ya saka ki É—aiÉ—aicewa. Yiwa Saheer magana da fuskar soyayya kamar yadda ki ka saba kamar kin yi zina ne."

"Ke Safeera! Zina fa?."

"Eh, indai za ki dinga yi masa magana yana jin daÉ—in kalaman ki zina ce mana amma ta baki,
Ko kina so ki ce min baki san akwai zinar baki ba?. Ƙawancen mu ya yi ƙarfi a islamiyya, lokacin da ki ka dawo gidansu Hamma. Ni na san wacece ke a islamiyya, amma yanzu na ga kamar kina daga cikin waɗanda Allah ya basu ilimi amma basa aiki da shi."

Islaha cikin sanyin jiki da kunya ta ce, "Allah ya kiyaye mu, zan kiyaye in Allah ya yarda.
Chapter 27 · 0% Book details