← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 110

Sashe 20

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rehaan ya ce, "Abba kar ka hana ni magana, ko yaushe kai ka ke cewa kar nace komai saboda mahaifiyarka ce, bayan ni tawa mahaifiyar take faɗawa duk abinda ta ga dama…..”

Ya ɗan dakata kafin ya ɗora ya ce, “Uwa ba ta fi uwa ba Abba…… Shikenan dan ta kasance ba jinin fulani ba sai ta dinga takurawa rayuwarta? Meyasa bata ƙaunarta bata ƙaunar ƴaƴanta?. Maganar da ake yi daban, maganar da ta sako daban, me ya sako Mamy a cikin maganar nan? Dan wata ta fita kawai sai ya zama da laifin Mamy?. Ni na ce mata ina son wacce ta haɗa auren ne, ba kai ka saka na amince da auren har aka zo yanzu ba?."

Kowa ya zuba amsa ido dan ya basu mamaki sosai, dan kowa ya san Rehaan yana da haƙuri, ba kowa ne zai jure cin kashin da Daada take yiwa babaraa a gaban idanunsa ba. Shi magana ba damunsa ta yi ba, in ba ya zama dole ba sai a haɗu a tashi bai ce komai ba. Tunda ya buɗe baki yana faɗawa Daada haka kowa ya dan ta ƙure sa, sai dai a ƙi faɗar gaskiya saboda baƙin ciki, Shiyasa ya fashe yake zazzage mata duk abinda yazo ransa.

Mama ta ce, "Rehaan! Daada ka ke faÉ—awa haka."

Ya jiyo ya kalli Mama ya ce, "Eh ita ɗin, nima uwata ta faɗawa ai. Yadda Abba yake jin zafin abinda na faɗa a yanzu, nima haka nake ji a duk lokacin da ta faɗawa Mamy magana, Yadda yake sonta haka nake son Mamy, maybe ba ya yiwa Daada son da nake yiwa Mamy. Komai ace Mamy, me ta tarewa mutanen gidan nan?.”

Abba ya dafa kafaÉ—arsa ya ce, "Rehaan kar na sake jin bakin ka, ya isa."

Rehaan ya sunkuyar da kai, sai kuma ya kalli Mamy da bata ce komai ba kuma baza ka fassara yanayinta akan fuskar ta ba.

Sai gani suka yi Daada ta miƙe ta ƙaraso inda Rehaan yake ta zauna a ƙasa ta ce, "dake ni." Ya yi mata banza bai ma kalle ta ba.

Ta sake cewa, "Sai ka dake ni za ka tabbatar min da kai É—in ruwa biyu ne, ba jinin fulani ne kaÉ—ai a jikin ka."

Ya É—auke kai daga kallon ta bai ce komai ba, dan Abba ya hana sa ne amma da ya tambaye ta su fulanin nan larabawa ne? A ganinsa babu wani tribe da ya kai su tunda a cikinsu annabi yake.

Abba ya ce, "Daada ki yi haƙuri ki tashi."

"Bazan tashi ba, sai Rehaan ya dake ni, in bai dake ni ba babu inda zan je."

Abba ya ƙaraso ya kamata ya ce, "Don Allah ki yi haƙuri, ki tashi."

Daada ta daki ƙasa ta ce, "Babu inda zan je, sai ya dake ni sannan zan miƙe daga wajan nan. Babu inda zan je daga nan, ya dake ni ya huce haushinsa. Sai ya dake ni sannan zan san shi jinin indiyawa ne.”

Abba ya ce, "Rehaan bata haƙuri."

Cikin fulatanci Abba ya yi magana, shima da yaren ya bata haƙuri kamar yadda Abba ya ce.

Daada ta harare sa alamun daman haƙurin ta ke jira ta ce, "Kuma wallahi ka je ka nemo ƴar mutane, ka dawo da ita cikin gidan nan….”

Sai kuma ta sake kallonsa ta ce, “Wai ya aka yi ma aka bari ta fita daga gidan nan? Akwai driver da ya tafi kaita ne?."

Mama ta yi caraf ta ce, "ita kaÉ—ai ta tafi Daada,
Kuma a matsayin da take da shi a gidan nan fita kan titi ta hau abin hawa na haya ba matsayinta bane, yadda driver zai ja Rehaan a mota itama haka ya kamata ayi mata tunda aurenta yake yi. Haba, ko masu aikin gidan nan in za a yi aike zuwa kasuwa ko wani waje mota suke hawa, babu mai hawa napep in dai aiken gida ne. Balle ita, matarsa guda ace ta hau napep, wannan bai kamata ba kuma zubar da ƙima da sunan gidan nan ne.”

Sai kuwa ta sake zuga Daada ta ce, "Ai da yake ya raina ni, ya raina abinda ya fito daga hannuna shiyasa yake wannan wulaƙancin. Gida kamar wannan, miji kamarsa ace matarsa ta hau abin hawa ta fita, meye ribar hakan?" Ta faɗa tana kallon Abba.

Abba ya ce, "ba a kyauta ba kam, amma a yi masa uzurin rashin sanin ta fita É—in, kin ga yanzu sai ya samar mata da wanda zai dinga kai ta duk inda zata je. Itama kuma fita a wannan yanayin bai kamata ace ta fita ba, ina zata je haka da safe tana amsa sunan amarya?."

"Yana É—aure mata fuska da harara ba dole ta fita ba? Wannan auren kawai sunansa auren je ka na yi ka."

Rehaan ya ce, "Daman ai ke ki ka haÉ—a, akwai wanda ya ce miki yana so ne?" Ya faÉ—a yana kallon Daada.

Daada ta ce, "kuma dole ka zauna da ita ba, ba ka isa ka rabu da ita ba indai ina da rai. Zama da Ishlaya daram, babu wanda ya isa ya ce ta bar gidan nan." Ya É—auke kansa daga kallonta bai ce komai ba

Daada ta ce, "kira wayarta mu ji tana ina."

Ya yi mata banza kamar bai ji ba, Abba ya ce, "magana ake maka, ka kira ta aji tana ina."

"Ita wa zan kira Abba?."

"Ita matarka."

"Da wayata kuma? Ka san ba kowa nake kira da wayata ba."

Daada ta sake fusata ta ce, "shikenan! Ta tabbata ya raina ni ya raina ubansa, ubansa yana faɗa shima yana faɗa, Daman ance in mutum yana yana samun kuɗi sai ya raina kowa har iyayensa…..”

“Rehaan baban naka ka ke faɗawa haka?."

Shi bai ma kalle ta ba waya yake dannawa a nutse, dan ya daina ƙyaleta tana faɗa masa abinda ta ga dama.

Abba jin abinda Daada ta faÉ—a sai ya girgiza kai ya ce, "ka kira ta Rehaan."

A gajiye da maganar ya ce, "Abba ni..." sai kuma ya yi shiru ya yi kamar yana kiran waya, kafin ya kalle su bai ce komai ba ya kifa wayar a jikinsa yana kallon Mamy.

Daada ta ce, "daga yau ban amince ta sake hawa napep ta fita ba, kuma duk inda zata je ka san ta tafi, ba rayuwar fararen fata zaka yi mana a gida ba, ka ji ko?."

Ya kalle ta bai yi magana ba sai daga baya ya ce, "abinci da ake kaiwa apartment É—ina, a daina."

Daada ta harare shi ta ce, "In aka ƙi fa uban ƴan iyayi? Ni ka ke bawa umarni ko baban ka?.”

Sai bai tanka mata ba ya yi shiru kowa ya yi mamakin yadda take faɗa yana faɗa, duk da daman yana yi amma da alamaa yau ta kai shi ƙarshe.

Bai ce komai ba kawai ya miƙe ya fita daga falon.

Yana fita suka haÉ—u da Salman Rehaan ya yi murmushi ya ce, "Ka yi kyau."

Salman ya ce, "wajan ta zani."

"Ita wa?."

"Wacce ka ce tana sona."

Rehaan ya yi dariya dan yadda Salman ya yi maganar ya ba shi dariya sosai ya ce, "Bata nan, amma in anjima ka dawo sai ka ganta."

"In aka yi kiran sallah na nawa?."

"In aka yi kiran sallah na huÉ—u."

Salman ya yi shiru yana irga sallah ta nawa ya rage ayi, sai kuma ya juya ya koma yana murna zai ga Islaha har ya je wajenta.

Anya Rehaan ba ka yi ganganci ba?.

Nana Haleema.

RDB3P17
Nana Haleema.

Rehaan wajan Mamy ya shiga ya kwanta a kan kujera ya lumshe idanunsa yana jin takaici a ransa akan abinda ake yi masa akan Islaha. Mamy ta shigo da sallama ya amsa ya ga ta É—auki handbag ta ce, "Zan je guest house, daga nan zamu je airport zasu wuce india."

Ya miƙe zaune ya ce, "da wuri haka? Na yi tunanin za a haɗa outing ayi shopping kuma a faɗa min zasu koma?."

"Gaskiya baza su zauna ba, amma nima very soon zan je, sai mu je gabaÉ—aya."

"Komai ya zama ready?."

"Muna magana da Bilal, komai ya yi ready. Daga nan sai India in sha Allah."

Ya É—aga kai ya ce, "Allah ya kai su lafiya, ko in raka ki?."

Mamy ta yi murmushi tana kallon sa ta ce, "in za ka je sai mu je, in za ka huta kuma ka huta kawai. Riyya ta kira ni tana ta kuka, wai she missed me."

Ya yi murmushi tunawa da ƙanwartasa tana hannun Jazy da ya gama zubawa cikinsa magani, ya san Jazy ba ɗaga mata ƙafa zai yi ba, ga abubuwan da ya sha kama sa yana sha. Amma ya yi alƙawarin ba shi mamaki, in ya cutar masa da ƙanwa Allah sai ya hukunta shi.

Mamy ta ce, "Rehaaan!."

Rehaan ya kalli ta ce, "bana son yarinyar nan da aka haɗa ku ko kaɗan, tana zama silar ɓacin ranka, ni kuma duk abinda zai ɓata maka rai bana ƙaunarsa."

Ya miƙe tsaye ya ce, "Mamy nima bana sonta, ta silarta ake mocking ɗin ki. Amma kar ki damu, zan kawo ƙarshen komai, ba za a ɗauki lokaci ba in sha Allah."

"Maganar auren ka ta yaɗu fa, duk da ana ta kokwanto akan gaskiya ne ko ƙarya."

Ya É—aga kai ya ce, "na gani, nana so a sani ne saboda ba aure na yi ba, in na yi aure kowa zai sani."

Ta shafa kansa ta ce, "Auren Rehaan kamata ya yi duniya ta sani ba ki É—aya, ba iya nigeria ba."

Ya murmusa ya ce, "za a yi bikin da ba a taɓa yin irinsa ba."

Mamy ta yi dariya ta ce, "Allah ya kaimu. Ka kula da kyau, kar ka saki jiki da yarinyar nan, zata iya cutar dakai."

Ya yi murmushi bai ce komai ba, Mamy ta ce, "na haÉ—a maka lunch, yana ciki a dinning. Ka tashi Banisha daga bacci sai ku ci tare, tana ta bacci ko breakfast bata yi ba."

"Okay Mamy."

"Sai na dawo" ta faɗa tana fita da sauri ya koma ya zauna yana lumshe idanunsa cikin ƙaunar Mamynsa.....
Chapter 20 · 0% Book details