Sashe 51
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ita kuma ta harari Banisha ta ce, "ni za ka nunawa jan aji? Kana kallona ina kallonka ka ƙi yi min magana kana zaman jira nace maka sannu? In aka zo ɓangaren class na dame ka na shanye wallahi" ta faɗa tana cigaba da abinda take yi.
Rehaan kuwa ko ta kan Kiddo bai bi ba datse kiran, duk tarin rainin hankalin da Islaha take yi masa bai taɓa jin haushi ba kamar abinda ta yi masa yanzu.
Ya miƙe zaune ransa yana suya saboda ɓacin rai, a matsayin da yake da shi har wata mace ce zata yi masa wannan shirmen dan ta samu dama daga gare sh?. Ya yi tsaki yana girgiza kai, haka kawai ya ji ransa ya ɓaci ba tare da ya yi zato ba, shi kansa ya san abinda ta yi masa bai kai ya ɓata masa rai haka ba, amma ya kasa dakatar da kansa daga ɓacin ran. Ya sauke ƙafafunsa ƙasa ya jawo wayarsa yana dubawa.
Sai ya kira Jazy yana É—auka kafin ya yi magana ya ce, "wanne driver ne yake fita da yarinyar nan?."
Jazy ya ce, "wa kenan."
"C wife."
"oh Islaha?."
"Ka ji ai."
Jazy ya yi dariya ya ce, "meyasa ka ke so ka sani?."
Rehaan ya ce, "Jazy ba wasa nake yi maka ba, ka faÉ—a min kawai."
Jazy jin maganar Rehaan É—in so serious abin ya bashi mamaki, bai tambaye shi dalili ba ya ce, "Lawal ne." Bai kuma cewa komai ba ya datse kiran ya tafi binciken neman number lawal a wayarsa. Ya duba ko ina amma na shi da lambarsa, hakan ya saka ya kira Shams.
Shams yana É—auka ya ce, "Good Sir."
Ray bai amsa gaisuwar ba ya ce, "ka san Lawal dirver?."
"Yes Sir."
"Tura min details ɗinsa" kafin ya Shams ya yi kashe wayar yana jin haushinta yana sake ƙaruwa a ransa.
A bayyane ya ce, "Allah ya kawo five months É—in nan a rabu a huta" ya faÉ—a yana shafa kansa cikin yanayin da ya kasa fassara shi.
Sai ya yi tsaki, yana tunawa duk bala'i dai ta cuce shi, dole ace ex wife ɗinsa ce. Alert ɗin shigowar saƙon Shams ya shigo wayarsa, ya duba ya ga Shams ɗin ne ya turo, yana ganin kiran Shams ya yi rejecting ya kira Lawal.
Bata jima tana ringing ba ya É—auka, cikin fulfilde Lawal ya yi sallama. Rehana shima cikin yaren ya amsa sallamar, bai tsaya sun gaisa ba ya ce, "Ka san dawa ka ke magana?."
Lawal ya ce, "Ban sani ba."
"Rehaan ne."
Lawal ya dabarbarce ya ce, "Barka da safiya yallaɓai, ban san kai bane."
"Wa ka ke É—auka a mota in zata fita?."
"Ranka ya daÉ—e madam ce."
"ta kira ka ta ce maka zata fita?."
"bata kira ni ba."
"In ta kira ka kar ka je, ka ce mata na hana ka kaita ko ina. A yau ban yarda ka kai ta ko ina ba, ka ji?."
"In sha Allah."
"Sannan ka faÉ—awa gate mans, na ce kar a barta ta je ko ina."
"An gama, ranka ya daÉ—e.
Rehaan bai amsa ba ya datse kiran ya cillar da wayar yana shafa fuskarsa, yana jin ɓacin ran da ya jima bai ji irinsa ba.
Nana Haleema.
RDB3P40
Nana Haleema.
Gabaɗaya zama waje ɗaya da ita ya fara fice masa da rai, just one week kaɗai har ta fara saka masa ciwon kai. A yadda Allah ya halicce shi sai ya yi kwana da kwanaki ba a ɓata masa rai ba, dan ba ya damuwa da damuwar kowa balle ta ɓata masa rai, amma tunda ta shiga rayuwarsa ko yaushe ransa a ɓace yake. Ba ya jure damuwa kuma ba ya jure rainin wayo.
Ya yi ƙwafa yana girgiza kai cikin ƙunar rai, sai kuma ya fahimci abinda ya aikata, ya ɗan yi shiru ya ce, "Ina ruwana da ban bata kula ni ba?" Ya tambayi kansa cikin mamakin kansa. Ya yamutsa gashin kansa ya ce, "meyasa na ce kar a kai ta inda zata je? Ina ruwana da ita?" Ya faɗa yana ɗaukar waya zai kira Lawal sai kuma ya fasa, ya ajjiye wayar ya ɗora hannunsa duka biyun akan fuskarsa, ya kwanta a jikin kujerar yana tunanin abinda ya yi.
Islaha sai bayan sallar azahar sannan ta kira Lawal dan ta faÉ—a masa zata fita. Lawal yana É—auka ya gaishe ta, itama ta gaishe shi sannan ta ce, "In an idar da sallar la'asar in sha Allah zan fita."
Lawal ya yi gyara murya ya ce, "Madam tun ɗazu yallaɓai ya kira ni, kuma ya bani umarnin kar na kai ki ko ina a yau."
Islaha cikin mamaki ta ce, "waye yallaɓai?."
"Mr Rehaan nake nufi."
Islaha ta buÉ—e idanu waje ta ce, "shine ya ce maka kar ka kai ni?."
Lawal ya ce, "haka ya ce min, ya ce min indai a yau ne kar na kai ki ko ina."
Ta É—an yi shiru tana tunani sai kuma ta ce, "na gode" ta faÉ—a tana kashe wayar.
"Kai! me mutumin nan yake nufi dani? In ruwansa dani da zai kira Lawal ya ce kar ya kai ni inda zan je? Ya aka yi ya san zan fita?" Ta faɗa cikin mamaki tana riƙe da ƙugu.
Sai kuma ta gyaÉ—a kai cike da tsiwa da neman magana, har sauri ta ke yi ta gama abinda zata yi ta fita saboda neman fitina. A dah sai bayan sallar la'asar zata fita, amma yanzu tunda aka yi haka a lokacin zata fita sai ta ga wanda zai hanata.
Dan ya ce kar a kai ta a mota daman ba ita ta nema ba, amma bazai hanata fita da ƙafar da Allah ya yi mata ba. Ta saka hijjab ta ɗauki facemask ta saka ta ɗauki wayar ta fito.
Falon shiru kamar ko yaushe babu motsinsu, ta san bacci suke yi dan sun mayar da baccin rana kamar ibada.
Ta fitowa daga falon Mamy ta ga rana ta buɗe sosai dan lokacin ƙarfe uku na rana ta kusa. Amma da ya ke bala'i da neman rigima take ji dasu bata ji ranar ba ta nufi gate ɗin.
Duk da ta rufe fuska amma ana gane wacece, ana ta gaishe ta akan hanyar ta, ita kam ba wani amsawa take ba dan bata son wannan gaisuwar.
Tana zuwa gate bakin gate masu gadin da suke zaune sanye uniform duk suka miƙe tsaye cikin girmama ta. Babban cikinsu ya duƙa ya gaishe ta kafin ya ce, "Hajiya fita za ki yi?."
Islaha cikin girmama shi ta ce, "Eh fita zan yi Baba."
Shima cikin girmamawa ya ce, "Ki yi haƙuri, Yallaɓai Rehaan ya ba da saƙo ya ce a faɗa mana, yau kar mu bar ki ki fita."
Islaha ji ta yi kamar ta yi ashar saboda takaici da baƙin ciki, ta kama ƙugu tana kallonsu cikin yanayin da ita kaɗai ta san me take ji. Wanda ta kira da Baba ya ce, "ki yi haƙuri, shine ya ba da umarnin hakan, kuma baza mu iya tsallake umarninsa ba."
Wata irin masifa da bala'i islaha ta ji tana tasowa daga zuciyarta, ranta ya ɓaci, ta ji kamar ta rufe su da duka ta huta. Ta gyara tsayuwa ta ce, "ku kira shi ku faɗa masa, ni kuma na ce sai na fita, duk abinda ya ga dama ya saka a yi min."
A firgice wanda yake yi mata magana ya ce, "ki yi haƙuri, amma baza mu bari ki bar wajan nan ba. Kuma ba mu isa mu kira shi ba, saƙo ya bayar a ba mu."
"Kuma sai ku ba da saƙon, ku ce masa nima na ce sai na fita."
Dukkansu mamakim kalamanta suke yi, na gefe suka fara fara ƙus-ƙus ana tattaunawa akan aurenta dashi, daman ga yan aikin gida da gulma.
Baba ya ce, "Ki yi haƙuri."
"In na zo fita za ku É—auke ni ne?."
"Mu mun isa? Amma ki yi haƙuri ki koma."
Zata sake magana wayar hannaunta ta yi ƙara, kamar baza ta ɗauka ba sai ta ɗauka. Safeera ta ce, "Gani a bakin estate ɗin gidanki, tsoron mutanen nan nake ji, ki turo a shigo dani."
Islaha ta yanke wayar tana wuci ko amsa bata bawa Safeera ba.
Baba ya sake tausasa murya ya ce, "don Allah ki yi haƙuri, baza mu iya tsallake umarninsa ba."
Ganin babba da shi yana bata haƙuri sai ta daure ta ce, "shikenan, akwai ƙawata Safeera, tana farkon estate ɗin nan, a je taho min da ita." Jikinsu yana rawa suka amsa, mutum biyu suka fita da sauri, ita kuma ta gefe ta tsaya tana ji kamar ta yi kuka saboda takaici. Ta so ta nunawa Rehaan bai isa ya ba da umarni akanta ba, ta so ta nuna masa ba shi da iko da ƙafafunta, da mota yake da iko.
Babu jimawa Safeera ta shigo inda Islaha ta ke, ganin Islaha a tsaye sai ta bita da kallo ta ce, "ke kuma me ki ke yi a nan?." Islaha bata ce komai ba kawai ta juya ta koma, Safeera ta bi bayanta suka nufi cikin gidan.
Babu a compound ɗin kowa kasancewar rana ce, sai masu aiki da suke ta aikinsu. Maimakon ta shiga wajan Mamy, kai tsaye ta nufi ɓangaren Rehaan.
Safeera tana kallon yadda take typing ƙofar, ko magana ta kasa yi mata saboda ɓacin rai. Safeera tana shiga ta rufe ƙofar, ta waiwayo ta kalli Safeera ta ce, "Wai ni mutumin nan zai rainawa hankali, ni zai saka a wulaƙanta a cikin gidansu?."
Safeera ta ce, "ni tunda na ga fuskar nan ta ki na san ba lafiya wallahi, na yi tunanin ko kina period ne, dan na ga lokacin na ki ya yi. Me ya faru?."
Islaha ta cire hijjab É—in ta cillar, ta dafe kanta yana zaga falon sannan ta ce, "Wai ni zai saka a hana fita daga gidan nan, ni zai saka masu gadi su tare su hanani fita dan ya raina min hankali."
Safeera ta ce, "Akan me zai hana ki fita, wani abun ne ya faru?."