Sashe 28
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
" Sai kuma ta É—ago ta ce, "Ni wallahi ba akan aurenmu nake so Hamma ya daina fushi ba, kin san waye Hamma a gare ni, kin san shine dangina gabaÉ—aya. Na kasa jure fushinsa a kaina, na kasa jurewa in na tuna Hamma baya yi min magana, wannan shine ya É—aga min hankali har sai da na ga ya sakko hankalina ya kwanta. Shine mai yi min faÉ—a, shine mai tsawatar min, shine mai kaini inuwa ya bani ruwa, duk da yan gidansu basa sona haka ya ce ya ji ya gani. Ta ya zan iya jure fushin wannan mutumi mai mahimmaci a gare ni?."
Safeera ta ce, "kin ji nace miki wani abu a kansa ne? Cewa na yi iya gaisawa itace a tsakanin ku ba maganar aure ba, in za ku yi maganar aure ya jira Rehaan ya sake ki daga nan sai ku ɗora. Amma a yanzu saɓon Allah ku ke yi."
Islaha ta ɗaga kai ta ce, "Na gode da tunatarwa Safeera. Daman daga ke sai shi ne masu nuna min kuskurena in na kauce hanya, wataƙila da ina da mahaifiya bazan aikata abinda nake yi ba yanzu...." Ta yi murmushi tana goge idanunta tana ɗaga kai ta ce, "Ke ƙawata ce kuma ƴar uwata, ba dan ku ko wuta zan faɗa babu mai dakatar da ni. Ta ya zan iya jure fushin Hamma?" ta faɗa hawaye yana sakko mata, ta sake sharewa ta ce,"Maraici!" Ta faɗa tana murmushi.
Safeera ta bita da kallo bata ce komai ba ta fita daga É—akin cike da tausayin Islaha da haushin Saheer a ranta, duk da Islaha ce mai laifi amma da ya nuna mata hakan kuskure ne da bata yi ba, kamar yadda ta faÉ—a shine mai faÉ—a mata gaskiya, shi take kallo a matsayin na gaba da ita har ya faÉ—a mata taji, kallon dangi gabaÉ—aya take yi masa, yana da mahimmaci sosai a wajenta, amma ta rasa meyasa akan auren nan idanunsa ya rufe, ya kasa tsawatar mata kamar yadda ya saba, ya kasa faÉ—a mata gaskiya kamar yadda ya saba, har yake so ya jefata a cikin halaka saboda son kai.
Sai bayan sallar magrib sannan driver ya zo ya É—auke ta suka wuce gidan.
Nana Haleema.
RDB3P23
Nana Haleema.
A daidai apartment É—in Mamy ya ajjiye motar, tana fitowa daga motar Banisha tana fitowa. Suka haÉ—a ido ta yi murmushi sai Islaha ma ta murmusa tana kallon ta.
Banisha ta ƙaraso ta ce, "Sis Islaha ko na ce Sia Islam, ki zo mu je wajan Mamy." Babu yadda zata yi ta musa haka suka shiga wajan Mamy da sallama ,Mamy ta amsa tana kallonsu.
Islaha bata kula da waye a kusa da Mamy ba, ta zauna a kan carpet ta ce, "Barka da dare Mamy."
A ciki Mamy ta amsa sannan ta ce, "Daga ina?."
Islaha bata fahimci tambayar ba sai ta ce, "na je wajan aiki."
"i mean wacece ke?."
Wani irin bugawa ƙirjin Islaaha ya yi, ta ɗago ta kalli Mamy suka haɗa ido, sai a lokacin ta lura da Rehaan a kwance akan kujerar ya ɗora kansa a kan ciyar Mamy yana danna waya.
Banisha ta ce, "Mamy Sis Islaha ce fa."
Ta kalli Banisha ta sake kallon Islaha ta ce, "ohh, sai na ga ta canja kamar ba ita ba, sannun ki."
Guiwar Islaha ta yi sanyi, ta kasa motsi daga wajan saboda ƙasƙancin da aka gwada mata a wajan. Ta yi shiru ta kasa magana, tana jin hawaye yana taho mata tana mayar da shi dan bata so ya zubo.
"Mamy na gaji sosai, bayana ciwo yake yi." Muryar Rehaan ta katse mata tunani, ta É—aga ido ta kalle sa ta ga Mamy tana shafa kansa tana cewa, "Yau ka yi aiki ai, in dai za ka je asibiti haka ka ke dawowa a gajiye. Sannu, ko za a zo a yi maka massage?."
Ya sake gyara kwanciya a jikunta ya ce, "No need" ya faÉ—a yana lumshe ido kamar bai san Islaha tana wajan ba.
Takaicinsa ya saka ta yi ƙaramin tsaki bata sani ba, haushi yake bata matuƙa, bata so ta ga namiji yana shagwaɓa ko yana faman kiran ya gaji, wannan dalili yana ɗafa daga cikin abinda ya saka ko burge ta bazata taɓa ji ya yi a ranta ba, saboda gabaɗaya duk abinda take so shi akasinsa ne da shi.
A hankali ta miƙe ta ce, "Sai anjima." Mamy ta amsa Islaha ta fita daga falon.
Mamy ta ce, "Rehaan."
"Mamy."
"Anya yarinyar nan bata da wani shiri kuwa?."
"na me?."
"ni sai nake ganin kamar turo ta aka yi fa, wallahi ban yarda da ita ba kwata-kwata. Sannan bata yi min ba, saboda bata da kunya."
Ya É—an yi murmsuhi kawai bai ce komai ba, yana aiyana da kin san wacce ita da kin sake jin haushinta.
Islaaha tana fita suka haɗu da Mama ta fito daga ɓangarenta da hijjab, ganin tana yi mata murmushi tun daga nesa sai Islaha ta dakata har Mama ta ƙaraso.
Islaha ta gaishe ta amsa cikin sakin fuska ta ce, "ÆŠazu na zo bakya nan, aka ce min kin tafi aiki. Kawai sai na kai channel É—in ku, sai na ga ana haska ki kina labarai. Gaskiya kin iya aikin sosai, Allah ya taimaka."
Ta yi murmushi ta ce, "Amin Mama."
"Yanzu ina za ki je?."
"Zan je na gaishe da Daada, daga nan sai na yi sallah."
"Mu je wajan nata, nima can zan je. Kina iya cin abincin chef É—in nan nasa kuwa?."
"Ni ban taɓa ci ba."
"Haka ki ke fita ba ki ci komai ba?."
"Bana iya cin abinci da safe ne."
"To na daren fa?."
"Bana so, gwara na sha tea."
Mama ta girgiza kai ta ce, "haka yaran nan ku ke, kowa baya son ya ajjiye kiɓa, Ai shikenan." Islaha ta murmusa tana jin ƙaunar Mama har cikin ranta, dan kaf gidan ita kaɗai ce mai sakar mata fuska sai Daada, har tana ji a ranta dama itace a matsayin Mamy, da ta ji daɗi ba a wulaƙanta ba. A haka suka shiga ɓangaren Daada da sallama....
Daada tana ganin Islaha ta fara murmushi ta ce, "maraba da Eslama ko na ce Ishlaya, dan wannan al'adar basu riƙe ta dakyau ba, mantawa suke da sunan buɗar kai, lokacin mu indai aka saka maka suna shikenan ya bika har mutuwa. Sannu da zuwa."
Islaha ta ƙarasa suka gaisa, Daada dafata ta ce, "Ya aikin naki?."
"alhamdu lillah."
"wannan aikin wai ba a bada hutu ne in aka yi aure?."
Ta É—an yu murmushi ta ce, "Aikin ne da yawa, kuma a hannuna yake shiyasa."
"ÆŠazu ai na ga shirin naki, Allah ya dafa miki." Islaha ta amsa da amin kafin Daada ta ce, "ki je ki huta, kar na zaunar dake."
Islaha bata musa ta yi mata sallama ta tafi. Daada ta bita da kallo tana murmushi ta ce, "Kaf sirikan gidan nan ban ga wacce zata shiga raina kamar yarinyar nan ba." Fuskar Mama sai ta canja, amma bata nuna ba ta yi yaƙe suka gaisa ta fita.
Islaha sai a lokacin ta tuna da kayanta a motar, ta kira shi ta ce ya kawo mata, ba jimawa sai ga shi da kayan ta karɓa tana kallon ƙofar dan ita ta manta code ɗin ma wallahi.
Ta tsaya tana danna code ɗin ta ji an riƙe hannunta, gabanta ya faɗi ta juyo dan ganin waye mai wannan aikin. Kafin ta gama banbance waye aka sake riƙe ɗaya hannun, ta kalle sa ta ga sai murmushi yake yi mata yana jan hannunta alamun su yi tsalle-tsalle.
Lokaci ɗaya tsoronsa ya shiga ranta, ta kasa ƙwace hannunta daga riƙon da ya yi nata. Salman shi dai kallon ta yake yi, bai taɓa ganin abinda yake son zama tare da shi kamar Islaha ba, bai taɓa ganin wacce yake so ya dinga gani ko yaushe kamar islaha ba.
Yana ta yi mata murmushi ya ce, "Za mu yi wasa, ki zo mu hau keke da mota da jirgin ƙasa."
Islsha kamar ta kurma ihu saboda tsoro da tashin hankali, muryar tana rawa ta ce, "to ka sakar min hannu."
Salman ya saki hannunta amma ya riƙe gefen hijjab ɗinta dan kar ta gudu.
Ita dai a tsorace ta danna code ɗin aka yi sa a ta saka daidai, ƙofar ta buɗe tana shiga ya bi bayanta.
Yana shiga ya ji muryar Umma tana ƙwala masa kira, sai kuwa ya ɓuya a bayanta ya ƙanƙame Islaha ta baya yana faɗin, "Ga Umma nan, ki ɓoye ni, ni a wajan ki zan zauna, ki ɓoye."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Na shiga uku" ta furta a bayyane jin yana ƙoƙarin yar da ita ta faɗi a ƙasa.
Salman kwata-kwata bai san abinda yake yi ba, so yake ya ɓuya kar Umma ta zo ta tafi da ahi. Jikin Islaha ya hau rawa, ta tsorata sosai, hankalinta ya tashi, ta rasa ya zata yi masa, ta kasa ƙwace kanta kuma ta kasa motsin kirki sai yadda ya juya ta.
"Salman kana ciki..." maganar Umma ta maƙale ganin ɗanta a bayan Islaha ya riƙe ta.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Me ki ke koya masa?" Ta faɗa da ƙarfi tana shigowa falon, ta dage ta ja shi da ƙarfi amma yaƙi sakin Islaha.
Umma ta ce, "za ka cika ta ko sai na mare ka, baza ka sake ta ba?."
"Ni dai Umma bazan bi ki ba, a wajan ta zan kwana, ni ki tafi" ya sake faɗa yana sake riƙe Islsha da take tsakiyarsu ta rasa ya zata yi.
Ita dai wani namiji bai taɓa yi mata haka ba tunda tazo duniya, babu namijin da ya taɓa haɗa jikinsa da ita ya riƙe ta ƙam ƙam haka sai shi. Ko ya ta motsa sai jikinta ya gogi nasa, ta rasa ya zata yi.
Umma ta kwaÉ—a masa mari mai zafi, ta finciko hannunsa ta ce, "ina magana kana faÉ—a min haka, yaushe ka raina ni haka ne?."
Sai kawai ya fashe da kuka yana faÉ—in, "ni bazan bi ki ba, ni a wajanta zan zauna."