← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 110

Sashe 53

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Islaha ta ce, "da farko haka take yi min, in ta ganni ta haɗe rai ita a lallai na auri ɗanta, bata  san da shi da banza duk ɗaya suke a wajena ba, wallahi bai isa na auresa dan kyau ko kuɗi ba. Daga baya ne na ga tana ɗan sakar min fuska, har ta yi murmushi. Mai kirkin gidan nan fa Mama ce, uwar gidan Abban. Ita kaɗai ce mai sona, daga Daada sai ita. Amma kin ga Umman nan, kin ga ta ƙarshen da suke cewa Anty? Duk ƴan iska ne."

Safeera ta ce, "Ke fa ba ki da hankali, Æ´an iska fa ki ka ce? Sirikanki ne fa."

Safeera ganin ta yi shiru tana dafe ciki sai ta ce, "Sannu, Ki sha maganin."

Ta langwaɓar da kai ta ce, "Ki bani don Allah, yana cikin jakata."

Safeera ta yi dariya ta ce, "Ke wato in kina period, kina so komai ayi miki."

Ta É—auko ta bata ta sha ta kwanta ta ce, "Ciwon ya fara damuna."

"Sannu."

Suka yi shiru kafin ta ce, "Ni zan wuce, ki kwanta ki huta, ba sai kin raka ni ba."

Sai ta miƙe zaune ta ce, "Ba ki da hankali, ki zo har inda nake na kasa raka ki? Dan ma bani da kuɗi, ai da har kuɗin mota zan ba ki."

Safeera cike da tsokana ta ce, "Matar Ray guda ace bata da kuÉ—i, abin kunya." Islaha jinta ta share dan ta san neman magana take yi, suka fito wajan Mamy.

A ina suka bar Mamy suka tarar da ita a zaune Ammi ta tafi. Islaha ta ce, "Mamy zan rakata, zata tafi."

Mamy ta ce, "Kiddo kira Ado ya zo ya mayar da ita, sannan ki É—auko min kuÉ—i a drawer."

Banisha ta tashi ta shiga ciki, Mamu ta kalli Safeera ta ce, "bara a mayar da ke gida."

Safeera ta yi murmushi ta ce, "Na gode." Mamy bata amsa ba sai murmushi da ta yi.

A lokacin Ikram ta fito daga ɗaki, Mamy ta kalle ta ta ce, "Ikram kira min Ado ya zo ya mayar da baƙuwar Islaha gida." Ikram ta kalli Safeera bata ce komai ba ta kira shi a waya.

Mamy ta kalle su ta ga suna tsaye kamar baƙi ta ce, "ku zauna kafin ya ƙaraso." A tare suka zauna suna ji Ikram tana yi masa waya.

Bayan ta gama kiran Ado ta kalli Mamy ta ce, "Na kira shi, ga shi nan."

"Okay ya yi sauri."

Ikram ta zauna ta kira Rehaan video call, kanta  babu ɗankwali sannan fuskarta ta yi kyau sosai, dan ta yi light makeup.

Rehaan yana ɗauka ta fara yi masa shagwaɓa ta ce, "Hamma Ray ba ka nema na."

Mamy ta kalli Ikram ta ce, "in kin gama bani shi, na manta É—azu akwai abinda zan faÉ—a masa."

Ikram ta cigaba da waya dashi tana zuba masa shagwaɓa tana magana kamar tana yi da mijinta, ita dai Safeera kallon ta take yi kawai, Islaha kuma ta kanta take y dan ciwon ya dame ta.

Banisha ce ta dawo da rafar dubu dubu ta bawa Mamy, Mamy ta miƙawa Safeera tana murmushi ta ce, "Mun gode da ziyara."

Safeera ta karɓa ta ce, "Na gode."

Mamy ta yi murmushi ta ce, "mu ma mun gode, ke ce first guest ɗin Islaha." Islaha ta yi murmushi Mamy ma haka, a lokacin driver ya zo, Safeera ta yiwa Mamy sallama suka miƙe suka fita.

Suna fita Safeera ta ce, "ke wannan mai waya da shi ɗin ma ƙanwarsa ce?."

Ta girgiza kai ta ce, "ƙanwar Jafar ce, cousin ɗinsa ce. "

"koda na ji, wannan shagwaɓa da take yi masa ba Yaya da ƙanwa bace."

"Ke tsaf za su iya hakan ba, su cousins ma kamar É—an uwan da suka fito ciki É—aya yake, dan ya rungumeta ta a gaban ki ba komai bane a wajansa, a wajensu normal ne. Ta ko ina bai dace dani ba, in da ace mijina ne na gaske kullum sai mun yi faÉ—a akan rungume-rugumen nan na banza da wofi, dan bazan jure ba."

"Au mijin wasa ne?."

"Ban sani ba."

Safeera ta yi dariya suna wannan hirar Safeera ta shiga mota suka tafi, Islaha kuma ta shiga part ɗin Rehaan dan tana buƙatar space bata jin daɗi.

Ciwon ya dame ta, tana ta juyi akan gado ita kaɗai, tana kuka mai ƙarfi kamar yadda ta saba, tana so ta sha ruwa amma baza ta iya tashi ba, ta jima a wannan yanayin tana kuka babu mai taimaka mata, a hankali ciwon ya fara lafawa, yana raguwa kaɗan-kaɗan tana ajiyar zuciya. Sai da ta ji ciwon ya ragu sannan ta iya tashi ta gyara kanta ta dawo ta kwanta bacci ya ɗauke ta.

Har bayan sallar i'sha bacci ta ke yi ita kaɗai a apartment ɗin Ray, sai daga baya ta farka tana jin  yanayinta ya canja gabaɗaya, zazzaɓi da ciwon kai da kasala sun rufar mata, ga yanayi da take kasancewa a ko wanne wata. 

A haka ta miƙe ta sake yin wanka ta fito ta zauna ta yi shiru, yunwa ta ke ji amma bazata iya cin abincin ba, da dai zata samu a bata abincin a baki da ya fi yi mata daɗi.

Knocking ƙofar aka yi sannan aka buɗe, Banisha ta shigo da sallama ta ce, "Sis ba ki fito ba, muna ta jiran ki."

Kafin Islaha ta ba ta amsa sai Banisha ta bita da kallo sannan ta ce, "Ba ki da lafiya?" Ta faɗa tana ƙarasawa kusa da ita, ta taɓa wuyanta ta ji da zafi sosai.

Banisha ta buÉ—e ido ta ce, "You are running temperature, bara na je na faÉ—awa Mamy, ko ta yi miki allura ko ta kira Janan."

Islaha ta ce, "Banisha bani ruwa na sha."

Banisha ta fita ta kawo mata ruwan, Islaha ta sha sannan ta ce, "zan ji sauƙi, ba sai kin kira ta ba."

"Amma ba ki da lafiya, jikin ki ya yi zafi."

Ta yi murmushi ta ce, "yanzu zan ji sauƙi, gani nan zan zo wajen Mamy." Banisha bata sake magana ba ta fita daga ɗakin.

Islaha ta miƙe a hankali dan har lokacin tana jin ciwo, ta ɗauki hijjab ta saka ta fito daga ɗakin tana ji kamar zata faɗi saboda jiri.

Tana shiga apartment É—in Mamy ta ga Jafar da Riyya da Banisha a zaune, Banisha tana ganin Islaha ta ce, "Mamy bata da lafiya, jikinta ya yi zafi sosai, amma ta ce kar na faÉ—a miki."

Mamy ta kalli Islaha cikin kulawa ta ce, "kar a faÉ—a kuma Islaha? Me ya same ki?."

Islaha ta zauna a hankali sannan ta ce, "zazzaɓi ne."

Mamy ta ce, "kuma sai ki ce kar a faɗa? Kin raina zazzaɓin ne?."

Islaha bata ce komai ba ta yi shiru, Mamy ta ce, "Banisha É—auko mata magani ta sha."

Banisha ta kawo mata maganin tare da ruwa a glass cup, islaha ta karɓa ta sha duk da yunwa take yi. 

Jafar ganin yanayinta ya canja sossi ya ce, "Sannu Islaha."

Islaha ta ce, "Yauwa, Na gode."

Riyya ta ce, "Allah ya ƙara lafiya."

Islaha ta ce, "Amin, na gode" ta sake faÉ—a tana rufe idanunta a hankali.

Islaha ta jingina da kujera ta lumshe idanunta, ta kasa zama waje ɗaya saboda ciwon mara, ta kasa samun nutsuwa. Mamy kallon Islaha yake yi, dan tunda ta shigo bata yarda iya zazzaɓi ne yake samunta ba, ganin yadda take frowning face ɗinta sai ta ce, "Ba iya fever ne yake damun ki ba Islaha."

Islaha buÉ—e idanunta ta kalli Mamy ta ce, "da ciwon kai."

Mamy ta ce, "Kin tabbatar?." Islaha ta É—aga kai bata ce komai ba. Mamy bata sake yi magana ba, ta yi mata sannu tana yiwa Jafar da Riyya magana da suka zo yi mata sallama zasu ta fi honeymoon.

Ta jima a zaune har ciwon ya ragu sosai, sai ta miƙe tsaye ta ce, "Mamy zan koma, akwai abinda zan ɗauko a can."

Mamy cikin kulawa ta ce, "za ki iya?."

Islaha ta ce, "zan iya."

Mamy ta ce, "to sai kin dawo." Islaha ta fita daga falon tana tafiya a hankali.

Nana Haleema.

RDB3P42
Nana Haleema.

Mamy suna ta hira da Jafar kafin ya miƙe ya fita, ya tafi ɓangaren Ray dan akwai abinda ya ce ya ɗauko masa a apartment. A main parlour suka haɗu da Islaha ya ce, "Sannu Miss."

Islaha ta yi murnushi ta ce, "Yauwa Mr Jafar."

"ya kamata ki faÉ—awa Mamy abinda yake damunki, sai ta ba ki magani."

"Na samu sauƙi."

Jafar ya ce, "Allah ya ƙara lafiya" ya faɗa yana hawa upstairs.

Sai da ya sakko daga upstairs É—in sannan ta ce, "Mr Jafar."

Jazy ya kalle ta bai ce komai ba yana jira ya ji ƙarin bayani. Islaha ta ce, "za ka haɗu da Mr Rehaan?."

Ya ɗaga mata kai ya ce, "zan je inda ya ke Miss, kina da saƙo ne?."

Ta ɗaga kai alamun tana da shi tana miƙewa tsaye, duk da ciwon da take ji amma baza ta iya shiru ba, dole ta aika masa da saƙo ko dan ya kiyaye gaba, dan ya san ita ba irin matan da ba su san ƴancinsu bane.

Islaha ce, "So nake ka faÉ—a masa, kar ya sake gangancin sakawa a hanani fita daga gidan nan. Ba haihuwata ya yi ba, kuma ba aurena yake yi ba balle ya ce yana da ikon hana ni zuwa inda na ga dama. Ina ruwansa dan zan fita zai kira Lawal ya ce kar ya kaini? Daman ni ban ce a bani driver da zai dinga fita dani ba, su suka haÉ—a meeting aka ce bazan dinga fita ni kaÉ—ai ba dole sai da driver."
Chapter 53 · 0% Book details