← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 110

Sashe 9

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Islaha ta ce, “na yi ƙoƙarin na girmama ki amma na gaza hakan, ban damu da wacece ke a gidan nan ba, ban damu da ke matar waye ba, kawai na so na tuna miki wani abu, akwai karin maganar da hausawa suke faɗa suna cewa in babban bai ji kunya hawa jaki ba, jaki bazai ji kunyar kayar dashi ba. Da kin riƙe kan ki mun gaisa lafiya da shikenan, amma kin kasa, sai da ki ka fito da abinda yake….”

Maganar ta dakata saboda ganin Ammi ta É—aga hannu zata mare ta, Islaha ta kauce gefe a daidai lokacin da Mamy ta dawo zata yiwa Ammi magana.

Ammi ganin Mamy sai ta ce, “dukana za ki yi, rashin kunya da rashin ganin darajar manyan na ki har ya kai haka? Ni za ki ɗaga hannu ki kaiwa duka?.”

Duk abinda ya faru bai taɓa ɓatawa Mamy rai ba sai a lokacin, sai ta ji ranta ya ɓaci, bata son ganin ana yiwa na gaba rashin kunya, lokaci ɗaya sai ta ji haushi Islaha a ranta. Tana so ta ga ana yiwa kowa biyayya, bata so ta ga ƙarami yana yiwa babba rashin kunya, yanzu sai ta fara jin haushin ko waye.

Mamy ta ce, “me ki ke shirin yi? are you out of your mind?.”

Ammi ta ce, “ƙyale ta ta dake ni, tunda bata da tarbiyya bata san darajar na gaba da ita ba.

Mamy ta yi tsaki fuskar ta a haɗe ta ce, “let’s go please” ta faɗa tana fita Ammi ma ta bi bayanta.

Islaha ta bisu da kallo bayan sun fita, ko kaÉ—an bata ji wani abu akan abinda ta yiwa Ammi ba, a ranta bata ji ta yi ba daidai ba, dan yadda take jin kanta Allah ko Mamyn ce ta yi mata sai ta mayar, ba son É—anta take yi ba balle ta yi biyayyar dole.

A nan ta yi sallae azahar, tana idawar ta sake jin ƙarar door bell, ta harari ƙofar a bayyane ta ce, “ni na gaji, barin gidan nan nake so na yi wallahi, Hamma nake so na je na gaji, bana son takura.”

Maimakon ta miƙe sai ta gyara zama, ta kalli abincin da aka kawo mata ta harare sa ko buɗewa bata yi ba balle ta ci ko ta sha wani abun ba. Wani tsakin ta kuma yi jin an sake danna door bell, ta miƙe daƙyar ta buɗe lock ɗin.

Mama ta sake gani a tsaye da housemaids ga a bayanta. Housemaids ɗin suka gaishe ta, bata iya amsawa ba ganin kamar bata cancanci amsawa ba tumda ita matar bogi ce, suka shiga suka ajjiye mata abincin. Sun juyo zasu fita Islaha ta ce, “ku tafi da wannan ma.” Cikin gimamawa suka amsa, suka ɗauka suka fita dashi.

Islaha ta kalli Mama ta yi murmushi ta ce, “ina yini.”

Mama ta yi murmushi tana dafata ta ce, “Islaha ba dai ba ki ci abincin ba?.”

Islaha ta ɗan kalle ta ta ce, “bana jin yunwa.”

“Ki kwana ki tashi kuma kice bakya jin yunwa? Ko akwai matsala ne?.” Ta girgiza kai alamun babu komai.

Mama ta ƙarasa shigowa cikin parlour sannan ta mayar da ƙofar ta rufe ta ce, “ko rashin zuwa Rehaan ne ya saka ki ƙi cin abincin?.”

_Ji wata magana, to kar ya zo mana, ya shekara bai zo ba in ya ga dama. Ina ruwana da zuwansa? Mtsww! Ni ba ku san ko ganinsa bana son yi ba, ba ku san zaman kuÉ—i kawai nake yi a gidan nan ba._

Ta faÉ—a a ranta tana jin haushin kalaman Mama, amma bayyane sai ta É—auke kai bata ce komai ba.

Mama ta ce, “kar ki damu, zai zo in sha Allah.

Kin san ya raina kakarsa, ba wani ganin darajarta take yi ba, kuma Mamy tana goya masa baya, bata son laifin ɗanta, ko kaɗan bata son ta ga an ɓata masa rai. Sai kin yi haƙuri, amma za ki sha fama daNadira, dan baƙin hali ne da ita.”

Sai a lokacin Islaha ta ɗaga ido ta kalli Mama, Mama ta ɗaga mata kai alamun tabbatarwa sannan ta ce, “Kar ki damu, ina bayan ki a ko yaushe a cikin gidan nan, duk abinda ki ke buƙata ki nemi ɗaya daga cikin masu aikin gidan ki ce a raka ki wajan Mama, sai mu yi magana.”

Islaha ta yi murmushi dan haka kawai matar ta burge ta sosai, ta san darajar ɗan adam, kuma ta lura tana da kirki, kuma tana ƙaunar ta tsakani da Allah da zuciya ɗaya. Daga ita sai Daada ne kaɗai suke nuna mata ƙauna, duk da ba zama ta zo yi a gidan ba, amma ta ji daɗin yadda matar take nuna mata itama mutum ce.

Islaha ta ce, “To Mama, na gode sosai.”

Mama ta dafa kanta ta ce, “kar ki damu Islaha.” Ta yi murmushi bata ce komai ba.

Mama ta ce, “Ki ci abinci, kar ki zauna da yunwa kin ji?.” Ta ɗaga kai alamun to.

Wayar Mama da take hannunta ta yi ringing, tana dubawa ta ga Sameer ne, sai ta ɗauka ta saka a kunne ta ce, “Ina aparment ɗin Rehaan.”

Daga haka ta yanke wayar ta kalli Islaha ta ce, “Zan Koma Islaha, Amma za ki fito in anjima ko?.”

Islaha ta kalle ta alamun me zan yi in na fito, Mama ta ce, “Za a kai amarya Riyya, sannan a gidansu Jafar za a yi buɗar kai da ajo, ki fito in anjima sai mu je gabaɗaya.” Islaha ta ɗaga mata kai bata ce komai ba, dan gaskiya babu inda zata je…

Nana Haleema.

RDB3P07
Nana Haleema.

Mama ta fara nufar ƙofar da niyar fita, Islaha ta bi bayanta a hankali da niyar rakata bakin ƙofar, dan tana yi mata kirki sosai, kuma husawa sun ce ka gaida mai gaishe ka. Tana buɗe ƙofar suka haɗa ido da saurayin da yake tsaye a jikin ƙofar, hannunsa riƙe da wata yarinya sanye da ƙananun kaya.

Mama ta ce, “nan ka biyo ni?.”

Sameer ya ce, “sauri nake yi ne Mama.”

Mama ta kalli Islaha ta ce, “Ga Yayan Rehaan, sunansa Sameer.”

Islaha ta ɗago ido suka sake haɗa ido ta ce, “ina yini.”

Ya yi murmushi ya ce, “Islaha ko?.”

Islaha ta sake kallon sa tana ɗaga kai alamun haka ne. Ya yi murmushi ya ce, “na san ki a social media, ina bibiyar programs ɗin ki sosai, all the best.” Ta sake yin murmushi kaɗan ta ce, “na gode.”

“Mama Rehaan yana nan?.”

Suka ji muryar Salman daga bayansu, a suka kalli wajan ganin Salman ne a tsaye yana kallonsu. Mama ta haɗe rai, ta kalle sa kallo irin na ƙyama ta ce, “ba ya nan, ka tafi.”

“Ga wajansa nan a buɗe, ni dai sai na shiga.”

Sameer ya ce, “kai mahaukacin banza, ba ya nan matarsa ce a ciki.”

Salman ya kalli Islaha da take kallonsa ya ce, “ke ce matar sa?.” Bata amsa ba sai kallonsa kawai take yi, tana tuna kalamansu Mama da suke cewa mahaukaci zata aura.

Mama ta ce, “Sameer ja shi ku je, kar ya ɓata min rai.”

Sameer ya ce, “wuce mu je.” Tare suka tafi yana ta waiwayowa yana kallon wajen Rehaan.

Mama ta ce, “Yana da taɓin hankali, ba shi da lafiya sai kin kula, kar ki dinga barin ƙofar ki a buɗe, kar ya shigo miki.”

Islaha ta ɗaga kai ta ce, “To Mama.” Daga haka Mama ta tafi ita kuma ta koma.

Tana shiga falon a bayyane ta ce, “Daman shine mahaukacin da su Mama suke faɗa? Su a tunanin su wannan na aura?……”

Ta girgiza kai ta ce, “Da yake basa ƙaunata, na zo na auri mahaukaci salon kawai ya kashe ni, da yake bani da gata, marainiya baiwar Allah….”

“Allah sarki, amma ya bani tausayi sosai.”

Sai kuma ta tuna da Hamma, ta zabura ta É—auki wayarta ta kira lambar Safeera amma shiru bata É—auka ba, ta sake kiran Sadik bai É—auka ba.

Ta yi tsaki ta dafe kai dan gaskiya in aka kuma jimawa bata samu kowa a waya ba wallahi sai ta fita ta je wajan Saheer, sai dai duk abinda zai faru ya faru, ita kam ta gaji wallahi.

Rehaan tunda ya saka waya a dnd bai yi ganganci ya cire ta ba, duk tarin kiran da Abba yake yi masa yana gani amma bazai iya kiransa ba, dan ya san maganar akan Islaha ne.

A guest house ya yi baccinsa, baayan ya yi sallar asuba ya sake kwanciya bayan ya rufe ƙofa dan kar ma Jazy yazo ya dame sa. Ko kaɗan ba ya tunanin ya yi wani aure balle Islaha, hankalinsa a kwance yake baccinsa.

Sai bayan sallar azahar ya tashi, yana zaune a gefen gado ya dafe kansa da hannayensa jin jijiyoyin kan suna harbawa, ya miƙe daƙyar ya shiga wanka ya fito ya shirya ya fito falo.

Danna wayarsa ya yi da take gefe, ya ga tarin kiran da aka yi masa, ya ɗauke kai sai kuma ya ji ana knocking ƙofar. A haka ya miƙe ya buɗe ƙofar, chef ya shigo da tray a hannunsa ya ajjiye masa ya koma. Rehaan ya buɗe abincin ya ga american dishes ne, ya bi abincin da kallo kamar mai neman wani abun a ciki, kafin ya ɗauki ice matcha yana sha, sannan ya ci abinci.

Wayarsa ya ɗauka ya kira chef ɗin ya dawo ya ɗauke kayan da ya yi amfani, shi kuma ya miƙe ƙafa akan center table ɗin yana duba waya yana ganin tarin kiran wayar da aka yi masa.

Sai a lokacin ya cire wayar daga dnd, yana sake duba mutanen da suka kira shi da waÉ—anda suka yi masa messages, sai kuma ya buÉ—e mail É—insa nan ma ya yi karo da mails É—in da dole ya buÉ—e. Ya gama karanta ya ajjiye wayar a gefe yana ganin kira na shigowa amma bai iya É—auka ba.

Jin an buɗe ƙofar ya saka ya ɗago kansa dan ya san daman sai Jazy ɗin, dan shine yake da spare key ɗin da zai buɗe ya shigo without knocking.

Jazy ya ƙaraso da waya a kunnensa yana magana yana kallon Rehaan sannan ya ce, “Ga shi nan Abba.”
Chapter 9 · 0% Book details