Sashe 78
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sannan ina so ki ta ya ni da addu'a, in ina da rabon auren Islaha Allah ya tabbatar min, in babu Allah ya cire min ita daga raina, dan shan wahalar rayuwa babu ita."
Safeer ta ce, "In sha Allah zan yi Hamma Saheer, Allah ya zaɓa mana abinda ya fi alkhairi, ya ɗora mu akan hanya madaidaiciya amin."
Ya amsa da amin suka yi sallama ta shiga gida shima ya shiga cikin gida yana tunani kala kala........
Nana Haleema.
RDB3P59
Nana Haleema.
Islaha tana shiga gidan ko ɓangaren Mamy bata shiga ba Mama ta hangota ta window a tsaye tana yi mata alama da ta zo tana kira ta. Islaha ta nufi wajan Mama ta shiga da sallana, ta same ta a zaune a kan kujera ta ce, "Yanzu na hango dawowar ki ta window, yau kin daɗe."
Islaha ta yi murmushi ta ce, "na yi interview ne shiyasa, ina yini Mama."
Mama ta ce, "lafiya lau, ya aikin?."
"alhamdu lillah."
"Ma sha Allah. Na ce ya maganin nan kuwa, ya sha?."
Islaha ta É—an yi jim kafin ta ce, "Eh ya sha a tea, amma bai ma san ya sha ba gaskiya, dan bai san na saka masa ba."
Mama ta saki fara'a cikin jin daÉ—i ta dafa Islaha ta ce, "Ai daman ba sai ya sani ba, na faÉ—a miki ba ya son magani, kina faÉ—a masa bazai sha ba. Yanzu ba ga shi ya sha É—in ba?."
Islaha ta ce, "ya sha kam."
Mama ta ce, "daman abinda zan tambaye ki kenan, in yana ciwon cikin nan tausayi yake bawa kowa, shiyasa na kira ki na tambaye ki, tunda ya sha mun gode Allah."
Islaha ta yi murmushi ta ce, "Bara na je Mama."
Mama ta ce, "To in kina son abinci akwai a kitchen."
Ta ce, "Na ƙoshi Mama." Mama ta bita da murmuahi har ta fita.
Tana bi bayanta da harara ta ce, "shashasha, zaki yi kuka da idanunki wallahi, wannan murmushin da nake miki na ƙarya ne bana gaskiya bane, iyakacinsa fuskata bai zuciya ba."
Islaha da ta je ɓangaren Mamy sai ta tarar dashi a rufe alamun bata nan, ta koma ta shiga na Ray ta hau sama tana jin jikinta a gajiya. Wanka ta fara yi sannan ta yi sallah ta sakko ƙasa ta tarar da an ajjiye abinci kamar ko yaushe.
Ta zuba ta ci sai kuma ta shiga tunanin dalilin da ya saka Mama take son Rehaan ya sha maganin da ta bata. A bayyane ta ce, "Meyasa Mama take so ya sha maganin nan har haka? Tsayawa ta yi tana dakon dawowata, ina shigowa ta kira ni tana tambaya, anya maganin na tsakani da Allah ne?." Sai kuma ta taɓe baki ta ce, "Ni dai bazan ba shi ba, haka kawai wani abun bazai faru azo ace ai ni na yi."
Wayar ta ta É—auka ta kira Jafar dan ta yi masa godiya, bata jima tana ringing ba ya É—auka yana É—auka ta ce, "Mr jafar."
Jafar ya ce, "Miss ƴar jarida, gaskiya na jinjina miki sosai, kina da ƙoƙari."
Ta yi murmushi ta ce, "na gode. Na gode da ka cika alƙawarin ka, na ji daɗin hakan sosai."
"Kar ki damu."
"Na gode."
"Welcome Miss" Daga haka ta kashe wayar ta.
Haka kawai ta ji tana sha'awar kunna tv, tunda ta zo gidan bata taɓa kunna tv ba ko da wasa, sai dai ta kalla ta wuce hannunta bai taɓa kaiwa kan tv ba. Ga ɗauki remote ta kunna tana duba channels ɗin, ta ga gabaɗaya channels ɗin babu na hausawa, daga na ball sai na labarai, sai american films da sauransu.
Ganin babu abinda ta saba kallo sai ta ajjiye remote ɗin ba tare da ta kashe tv ɗin ba. A lokacin aka buɗe ƙofar aka yi aka shigo, tun kafin ya ƙaraso ta ji ƙhamshinsa, ya rufe ƙofar ya shigo parlour. Ta san shine shiyasa bata ɗago kanta ba, ya wuce ya hau sama bai ce mata komai ba itama bata ce ba.
Tana nan zaune ya sake sakkowa, ya canja kaya
zuwa manyan kaya wanda bai cika sakawa ba, ya sake fita bai ce mata komai. Tana ji an fita da mota ta san shi ya fita, dan bai rufe ƙofar sosai ta ɗame ba, ta harari hanyar da ya bi ta cigaba da kallonta tv ba tare da tana fahimta ba.
Sai kuma ta cire hijnab ɗinta ta kwanta tana kallon americn film ɗin da ya fara ɗaukar hankalinta. Tana ganin kiran Hamma yana shigowa ta ƙi ɗauka, ta cigaba da kallonta kanta babu ɗankwali, a haka har bacci ya ɗauke ta wajan bata sani ba.
Salman ne ya turo ƙofar falon ya shigo ganin ƙofar a buɗe, ganinta a kwance sai ya ƙaraso ya zauna a kan carpet yana kallon fuskarta. Gashinta ya zube a kan kujarar, sannan doguwar riga ce a jikimta mai ƙaramin hannu.
Murmushi yake yana kallon ta, sautin tv ya saka ya kalli tv ya ga mace a kwance tana bacci kamar yadda Islaha take, sannan ga namiji a kusa da ita yana shafa gashinta. A hankali shima ya kai hannu ya taɓa gashinta sai ya yi dariya ya ce, "lah irin gashin Rehaan ne."
Sai kuma ya sake taɓawa ya ce, "A'a irin na Mama ne." Ya girgiza kai ya ce, "Kai ba irin nata bane....
" Sai ya tafi tunani ya ce, "irin na Banisha ne, na gane" ya faɗa yana cigaba da riƙe gashinta daga ƙasa.
Rehaan a hankali yake shigowa cikin falon, daidai lokacin da Salman ya ke leƙa fuskar Islaha, in kana shigowa sai ka ɗauka kissing ɗinta zai yi, amma shi fuskarta yake kallo dan ya ga bacci take ko idanunta biyu.
Rehaan ya ji wani irin dumm a tsakiyar kansa, gabansa ya faÉ—i, ya ji wani irin yarrr kamar abu yana tafiya a cikin jininsa, kansa ya yi mugun nauyi, ya ji zuciyarsa kamar ana bugata da abu mai nauyi.
Cikin wata irin murya mai amo wacce bai san yana da ita ba, ya yi hanzarin ƙarasowa parlour ya ce, "Hamma Salman!."
Yadda ya kira sunan ya saka Salman yin ƙara dan ya firgita, ƙarar da Salman ya yi saka Islaha ta buɗe ido a firgice cike da tsoro.
Salman ya waiwayo ya kalli Rehaan ya ce, "Rehaan ka tashe ta" ya faÉ—a cike da takaicin tashinta da Rehaan ya yi.
Rehaan ya haÉ—e ransa yana ji kamar ana busa masa iskar wuci zafin yana ratsa jikinsa ya ce, "me ka ke yi a nan?."
Salman kallonsa ya ke yi bai ce komai ba, Rehaan ya ce, "dare ya yi, ka tashi ka ka je ka kwanta?."
Salman ya noƙe kafaɗa ya ce, "ni bazan tafi ba."
Ran Rehaan ya sake ɓace ya rasa me zai ce masa. Salman ya nuna masa tv ya ce, "irin wannan wasan zan yi mata, tana bacci ba a tashe ta ba, kalli ka ga" ya faɗa yana nuna tv dan ya ga mace gana bacci ba a tashe ta ba.
Amma a lokacin da ya nuna tv a daidai lokacin wacce take baccin suka fara undressing kayansu. Islaha ma ta kalli tv sai ta yi saurin É—auke idanunta, ta dira daga kan kujerar ta baya, ta ja baya daga kusa da Salman.
Salman ya zaro ido kamar ƙaramin yaro ya ce, "lah lah lah! Ka ga suna cire kayansu, babu ruwana sai na faɗawa Umma" ya faɗa yana sake kallon Rehaan.
Rehaan ya yi tsaki mai tsaho ya kashe tv, ya kalli Salman cikin ɓacin ciki da takaici ya ce, "tashi ka je, ga Umma can tana neman ka."
Salman ya noƙe kafaɗa ya ce, "ni bazan tafi ba, wajanta na zo ba wajanka ba."
"Ka tashi ka je, gobe sai ka dawo yanzu dare ya yi."
"Ni bazan tafi ba."
"Salman ka fita!"
Rehaan ya faɗa cikin tsawa yana nuna masa ƙofa alamun ya fita.
Salman ya tsaya cak yana kallon Rehaan, lokaci ɗaya firgita jin Rehaan ya yi masa tsawa mai shiga zuciyarsa. Tunda ya san Rehaan bai taɓa yi masa tsawa, rashin faɗan da ba ya yi masa ne ya saka suke shiri har yake zama a wajansa, bai taɓa ɗaga masa murya ko ya ƙyare shi ba shiyasa yake son zuwa inda yake.
Salman ya kalli Rehaan ya ga yadda ya haɗe rai, sai miƙe cikin sanyi ya fita, Rehaan ya ƙarasa ya rufe ƙofar ya rufe, ya canja mata lock ya dawo falon yana kallonta ransa a ɓace.
"Living room wajen bacci ne? Meye amfanin É—akinki da baza ki kwanta a can ba?."
Islaha ita kanta tsawar da ya yiwa Salman ta firgirata, ga abinda Salman ya nuna ya ce shi zai yi mata har yana nunawa, gabaÉ—aya ta firgita tana tunanin ba dan Rehaan ya zo da me zai yi mata? Tana tunanin abinda ya yi mata tunda bacci ta yi bata san ya shigo ba.
Karo na farko a zamanta a gidan ta sanyaya murya, cikin rauni da sanyin kiki ta ce, "ban san na yi bacci ba, na kunna tv ina kallo sai na yi bacci."
"What's the use of your bedroom TV? Kin san tun lokacin da ya shigo ya ke a zaune a kusa dake? Kin san sau nawa ya taɓa ki?."
Islaha ta girgiza kai ta ce, "ban sani ba, kuma ni ban san ya san ya aka yi ya buɗe ƙofar ba."
"Jiya ki ka zo É—akina ki ka ce ya shigo nazo na fita da shi, ya aka yi ya sake zuwa yau?."
Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, tana jin yadda yake yi mata magana cikin faÉ—a amma ta kasa yin komai, ta kasa mayar masa kamar yadda ta saba, sai ma nutsuwa da tayi tana jin faÉ—ansa har cikin ranta.
Rehaan ya ce, "First and last, don't let me ever see you sleeping in the living room again,in kina son kallo ki je upstairs, Okay?."
Bata san ta É—aga masa kai alamun to ba, dan haka kawai faÉ—an yake shiga ranta. Rehaan ya yi tsaki ya hau sama, gabaÉ—aya haushin Salman yake ji a ransa dan ya fuskanci ya yi sake da yawa da ya bari yana zuwa inda Islaha take..