← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 110

Sashe 103

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jazy ya kalle sa ya ce, "kai da gaske ka yarda tana neman Salman? Mu ajjiye maganar Ubaid a gefe, amma a ranka ka yarda zata nemi Salman?."

Rehaan ya yi shiru bai ce komai ba, dan shi kansa ya san ƙarya ne, yana amfani da maganar ne dan ya sake kushe ta a zuciyarsa.

Jazy ya ce, "kai ma kana faÉ—ar tana neman Salman ne yi dan ka samu abinda zaka kore sonta daga ranka, amma kaima ka san plan kawai mutanen gidanku suke haÉ—a mata. Kai ka ce min yarinyar Ubaid ce, wacce take kula irin su Ubaid me zata yi da wani Salman?."

Rehaan ya yi shiru bai ce komai ba Jazy ya ce, "Rehaan ko da ace da gaske ta aikata abubuwan da ka ke tunanin ta yi, rayuwarta ta baya ta wuce, karuwai ma da suka amsa sunansu karuwai in suka tuba ana aurensu kuma a zauna lafiya. Tunda har kana sonta ka goge wannan tunanin, ka karɓe ta ku yi zaman aure kamar kowa. Kana sonta, ita kuma ka san ba dan wani abu naka take zaune da kai ba, ka ga an yi eqaual."

Rehaan cikin sanyin murya ya ce, "Ta ya zata zauna dani Jazy? Bayan ka san abinda yake tsakanin mu da ita?. Sannan ka san tana da saurayi, that guy Saleem yake ko waye ban sani ba, a gabana tana yin waya dashi suna lissafin lokacin da zata bar gidanmu, lissafin ƙarewar kwanakin mu take yi kullum, ta ya zan zauna da ita? Ya zan yi Jazy?..." ya ƙarasa faɗa cikin tsananin rauni yana lumshe idanunsa.

Nana Haleema.

RDB3P75
Nana Haleema.

Jazy da yake kallonsa ya girgiza kai yana aiyana baƙo ne a soyayya shiyasa ya rikice ya fita daga hankalinsa har haka ya ce, "Abinda na ke so na tambaye ka guda ɗaya ne, kuma ka faɗa min gaskiya, ban da kushewa ko faɗar Ubaid ko wani Salman...."

Rehaan ya zuba masa ido yana jira ya ji me zai ce, Jafar ya ce, "Rehaan ka yarda kana son Islaha?."

Ya sauke numfashi ya lumshe idanunsa ya buÉ—e akan Jazy, ya kawar da kai gefe yana girgiza kansa sannan ya ce, "ban sani ba Jazy."

Jazy ya yi murmushi ya ce, "ka jira ka tabbatar, sai mu yi magana, ka ga in lokaci ya ƙare shikenan sai ka haƙura, kana ji kana gani zata auri saurayinta kai ta bar ka da rauni a zuciyar ta."

"Ka bani solution."

"Aa, sai ka fara tabbatar da abinda ka ke ji a kanta sannan sai na faÉ—a maka yadda za a yi."

Ray ya yi shiru bai ce komai ba, ya rufe ido ya É—aga kansa sama apple adam É—insa yana up and down. Jazy ya zuba masa ido kana kallonsa, kallo É—aya zaka yi masa ka san tension É—in soyayya ne ya fara walagigi da shi tun ba a je ko ina ba. Jazy ya ce, "ka san daga ranar da na fara noticing feeling É—inka a kanta?."

Bai yi wani motsi ba, sai dai ya buɗe idanunsa Jazy ya ce, "ranar da aka yi attacking ɗinku kai da ita a mota, har aka kai ta asibiti na ce ka bar Shams ya ɗauke ta amma ka ƙi, ka ɗauke ta da kan ka ka saka ta a mota, har kana rufe mata jikinta da blanket saboda night wears ne a jikinta. Ray daga ranar na saka maka question mark. Yadda ka dage ka ƙi sakin ta duk da abubuwan da aka ce tayi ya saka na sake yi maka alama, yadda ka tashi hankalinka akan ta samu attack jiya a nan na tabbatar da kana son Islaha, kuma baka so wani abu mara kyau ya same ta."

A ƙagauce Ray ya ce, "Daman bana so wani abu ya same ta saboda a ƙarƙashina ta ke, ina so mu rabu lafiya ba tare da wani abun ya same ta ba."

Jazy ya ce, "to kawai ka kawo ƙarshen zaman na ku mana, a ƙarar da contract ɗin a huta kawai."

Ray ya sake lumshe ido ya buɗe ya ce, "abinda nake ƙoƙarin yi kenan, but......."

Jazy ya katse shi ya ce, "But you can't ko?."

Bai ba shi amsa ba sai kallonsa da yake yi rauni da bugawar zuciya. Jazy ya yi murmushi ya dafa kafaÉ—arsa cikin kwantar da hankali ya ce, "Rehaan!..."

Ya kalle shi suka haÉ—a ido ya ce, "Wallahi you are in love, ko ka yarda, ko kar ka yarda, wallahil azim kana son Islaha."

Rehaan ya ce, "Let assume ina sonta É—in, ya zan yi da saurayinta da ta ke burin aure?."

"In ni ne kai, a waɗanan kwanakin da suka rage mana wallahi sai na saka ta manta da wani Saheer da abinda ya shafe sa, zan yi ƙoƙarin ƙirƙirar alaƙa mai a tsakanina da ita, kafin mu rabu sai na samar mata da scar a zuciyarta wanda bazai taɓa gogewa ba har abada. Saheer ɗin banza, waye shi da zan tsaya ina tuna shi akan matata?. Ka fi shi komai, babu ta inda Saheer zai kamo ka, tazararka dashi bazata taɓa kwatantuwa ba. Ka daina kawo shi cikin tunaninka, Islaha itace abin tunani ba shi ba."

Rehaan ya yi shiru bai ce komai baya jingina da kujera yana lumshe idanunsa. Jazy ya ce, "Kai ne mijinta ba shi ba, kai ka ke da ita a hannu ba Saheer ba. Ka nuna mata kai mijinta ne, shi kuma saurayinta ne na dah ba yanzu, kai ka ke da iko da Islaha ba shi ba. Hmmm! In ni ne kai ko? Bazan sake bata damar tunawa da wani Saheer ba, tuni zan goge mata hadda na saka ta manta da shi ya zama duk duniya babu wanda take tunawa sai ni."

Rehaan yana jin kalaman Jazy yana shiga har cikin ransa, ya yi luff bai ce komai ba yana tunanin mafitar da ta dace daahi a halin da yake ciki, dan gaskiya bazai iya rabuwa da ita ba, ji yake in ya rabu da ita kamar zai rasa numfashinsa zai bar gangar jikinsa, ya zama dole a san abinda za a yi kafin ya rasa tunaninsa.

   Islaha da ta tafi wajan aiki bayan ta tashi wajan Barr ta tafi, ta same sa a chamber ya fito ya same ta jingina da motarsa ya ce, "Hajiya Islaha."

Ta kalle sa ta ce, "Hamma meyasa kwana biyu baka son É—aukar wayata ne?."

Ya yi murmushi ya ce, "kawai sai in ƙi ɗaukar wayar ki? Aiki ne ya yi min yawa."

"Ban gane aiki ne ya yi maka yawa ba, ka san akwai case É—in da na bari a hannunka, meyasa ka ke yi min wasa da hankali?."

Ya ce, "in nan ina aiki akan hakan."

"Kullum haka ka ke faÉ—a, ni kuma bana ganin improvement É—in da ake samu, kullum jiya i yau ake abin nan. Ina Yafindo take? ka yi magana da ita ko baka yi ba, duk ba ka faÉ—a min abubuwan da suke faruwa. Ga Hafsa ta tura min da message akan tana son yin magana dani, na je kuma na kasa ganinta. Hamma Suraj in bamu dage ba rayuwar yara tana cikin hatsari."

Suraj ya ce, "me ta ce miki a saƙon?."

"Ka fara bani amsa, ka yi magana da Yafindo ko an samu Zainab?."

"Ban yi magana da ita ba har yanzu, na je gidan da take an tabbatar min da ta tashi. Islaha ina iya bakin ƙoƙarina akan case ɗin nan, yadda ki ke ji ƴan uwanki ne nima haka nake jinsu a matsayin jinina, gabaɗaya tare muka tashi a gida ɗaya, ba ke kaɗai ki ke jinsu a ranki ba. Kuma wannan abu ne da sai an yi bincike mai ƙarfi, baza ku shigar da ƙara ba sai muna da hujja mai ƙarfi a hannunmu. Zainab ita ce kaɗai hujjar mu, ita ma ta ɓace mun daina gaminta.

Islaha ta dafe kanta ta ce, "Yanzu ya za a yi?."

"Ki bar komai a hannuna, zan yi komai yadda ya kamata."

Ta ya yi tsaki ta ce, "Allah wadaran nigeria, kana gani ana aikata laifi amma baka da ikon yin wani abu a kai."

Suraj da ya ke yi mata kallon ƙasan ido ya ce, "Kar ki damu, komai zai zo ƙarshe." Sallama ta yi masa ta wuce, ya bita da kallo yana ɗan murmushi ya koma inda ya fito yana saƙa da kwancewa.

Islaha lokacin da ta koma gida tana shiga upstair parlour suka haÉ—u da Mamy, duk suka yiwa juna murmushi a tare Mamy ta ce, "daughther an dawo?."

Islaha ta ce, "na dawo Mamy."

Many ta ce, "jeki ki huta ki ci abinci, in kin gama ki same ni a É—akin Rehaan."

Islaha gabanta ya faÉ—i jin ta ce ta same ta a É—akin Rehaan, amma bata nuna mata ba ta shiga É—aki. Tana wanka tana tunanin abinda zata yi a É—akin, ta fito ta yi sallah, bayan ta idar ta tsaya a gaban mirror tana dambe da gashin kanta akan sai ta tuke sa, tana yi tana hutawa a haka ta yi yadda ta saba, dan preiod É—inta yana kan hanya.

Da ta sauka ƙasa ma tea ta sha ta ci abinci, ta yi sallar i'sha sannan ta nufi ɗakin kamar yadda Mamy ta ce. A zaune ta samu Mamy shi kuma yana kwance akan cinyarta, gabanta ya faɗi sosai, dan kallo ɗaya ta yi musu ta san ba shi da lafiya.

Mamy ta ce, "ƙaraso ki zauna." Islaha ta ƙarasa, kafin ta zauna Mamy ta miƙe ta bata wajan da take ta zauna ta ce, "Zauna."

Islaha haÉ—É—iye yawun tashin hankali, dan yadda Mamy ta yi mata alamu ne na a kan cinyarta zai kwanta, amma haka ta zauna bata ce komai ba saboda girman Mamy ya wuce haka. Tana zama Rehaan ya mayar da kansa jikinta, ta rufe ido ta buÉ—e ta kasa cewa komai.

Mamy ta ce, "take care of him Islaha, bashi da lafiya, jikinsa ya yi zafi sosai, ki taimaka masa ayi reducing temperature ɗinsa, in kina buƙatar wani abun ki kira ni. Good night" ta faɗa tana kashe hasken ɗakin ta fita.
Chapter 103 · 0% Book details