← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 110

Sashe 25

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_Ina jiran ki gobe a gida, ina so na ji bayanin komai daga bakin ki._

Islaha harari wayar a zahiri ta ce, "Sai yanzu za ka so ka ji, da ba raina min hankali ka ke yi ba?." Sai kuma ta fara yi masa typing tana faÉ—a masa bata son zuwa gidan in Mama tana nan.

Ba jimawa ya dawo da amsa ya ce, _Mama bata nan gobe, ki zo._

Bata ba shi amsa ba sai ajiyar zuciya da ta yi, sai ta ji duk damuwarta tana yayewa a hankali. Ta yi murmushi tana tuna Hamma ya daina ganin laifinta, ɓacin ran da Rehaan ya saka ta a ciki yana gushewa daga zuciyarta da kaɗan-kaɗan.

Sai kuma Zainab ta faɗo mata a rai ta sauke numfashi a bayyane ta ce, "A ina zan gano inda ki ke?."  Ta yi shiru dan babu mai bata amsa, ta juya ta shiga ɗaki.

Da Islaha asuba ta fito falo, ta manta laptop É—inta a falon kuma zata saka chaji kafin ta fita.

Tana fitowa yana hayowa saman yana amsa waya, tun daga takunsa tasan shine, amma ta yi buris kamar bata ganshi ba, nan kuwa tana kallonsa ta gefen ido. Ya saka jallabiyya blue, gashin kansa a sake yana amsa waya kamar baya son magana. Ta sunkuya tana ɗaukar laptop ya zo wajen zai wuce, tana ɗagowa suka yi karo laptop ɗin ta faɗi ƙasa.

Islaha ta kalle sa ya kalle ta, babu inda idanunsa ya kai a jikinta sai gashinta da yake sake ta sako shi ta gaba ya sauka har cikinta.

Ya bi tsahon gashin nata da idanunsa da sauka har cikinta, kafin ya ɗauke kai ya sake juyowa yana kallon ta. Islaha ta ɗaga masa gira alamun kallon na meye, bai ce komai ba ya raɓa ta zai wuce.

Islaha ta tare masa hanya ta ce, "ba ka ga abinda ka yar min bane? Ko ni ka ke so na sunkuya na É—auka?."

Daf da daf take yi masa magana, har ƙhamshin toothpast ɗin da ta yi brush yana ji a hancinsa. Ya ɗan lumshe ido ya buɗe a kanta, ya lura yarinyar tana da damuwa, in ya biye mata ciwon kai zata dinga saka masa.

Bai ce komai ba ya koma ɗaya side ɗin ya wuce ta, ta bi shi da harara ta ce, "ɗan rainin hankali kawai, mai jikin mata" ta faɗa tana ɗaukar laptop ɗin tana faɗin, "Wallahi in ta lalace sai ka biya ni." Ganin babu abinda ta yi ya saka ta yi ƙwafa ta shiga ɗaki.

Rehaan sai da ya shiga É—akin sannan ya yi ajiyar zuciya, ya cire rigar jikinsa ya zauna a gefen gado ya ce, "Me ya kai ni haÉ—a hanya da yarinyar nan oho."

Result É—in da ta zubar da ciki ya tuna, sai ya lumshe ido ya buÉ—e yana girgiza kai ya ce, "a haka da kamar mutuniyar kirki, amma ta banza ce.

" Ya yi tsaki ya miƙe ya ɗauki laptop dan yana da meeting na gaggawa.

Islaha ƙarfe shida ta gama shiryawa ta sauka downstairs, tana sauka ta ji motsi a kitchen ɗin da bata taɓa shiga ba. Chef ne ya fito sanye da apron ya kalle ta ya ce, "Good morning madam."

Ta bi shi da kallo sannan ta amsa, cikin ladabi ya ce, "the food is ready."

Ta kalli dining É—in ganin abinci ya fi kala goma a ajjiye, kamar table É—in Æ´an turkey da take yawan gani a drama, sai ga shi yau ta gani a zahiri, komai an yi decorating É—insa yadda ya kamata, ko ba ka yi niyar ci ba in ka kalla zai saka maka sha'awar cin abincin.

Islaha sai ta tuna jiya ma da daddare haka ta ga an jera abinci, kuma ita dai bata ci bata san ya aka yi dashi ba.

Islaha ta amsa ya koma kitchen ya cigaba da aikinsa. Ta ƙarasa wajen dining ɗin tana kallon abincin, wani abun ma bata san meye ba, kalolin abincin take gani kana gani ka san english breakfast ne ba irin nasu ba.

A lokacin Chef É—in ya dawo ya sake ajjiye wani abun, gashi yadda ya tsara table É—in sai ya burge dole sai ya ka. Islaha ta nuna masa É—aya daga cikin abincin ta ce, "What is the name of this food?."

Chef É—in ya kalla sannan ya ce, "Avocado toast."

Islaha ta girgiza kai tana kallon abin green dashi, tana ayyana sai dai avocado É—in daman.

Bayan ya bar wajen ta haÉ—a tea kawai ta sha, dan bata iya cin abinci da safe tea É—in ne zai zauna a cikinta. Bayan ta gama ta É—auki handbag É—inta ta fito daga falon tana kallon gate É—in da zai kai ta harabar gidan.

Nana Haleema.
KRBBK:
RDB3P21
Nana Haleema.

Compound ɗin gidan babu kowa a wajan sai motsin abinda yake kiwo, ta fito a hankali tana kallon wajan. Tana fitowa ta ga an ƙaraso inda take tsaye, ya duƙa a gabanta cikin fulfulde ya ce, "Barka da safiya."

Islaha ta kalli mutumin ganin ya girma, duk da ba tsoho bane amma yana da shekaru. Sai ta ji nauyin yadda ya duƙa mata ta ce, "barka dai."

"Ni ne lawal, ni ne zan dinga kai ki duk inda za ki je." Islaha ta amsa, ya nuna mata motar tare da buÉ—e mata bayan motar.

Islaha ta bi motar da ido, range rover ce baƙa mai kyau sai ƙyalli take yi kamar sabuwa. Islaha ta kalle shi ta ga yana riƙe da ƙofa yana jira ta shiga, ita duk sai ta ji kunya, amma haka ta shiga ɗin ya rufe motar ya shiga mazaunin driver suka tafi.

Ac motar ta yi mata yawa, kuma daman ita bata son ac a mota, hakan ya saka ta É—auki facemask ta saka ta faÉ—a inda zasu je. Gab da gate É—in ta saka ya tsaya, dan bata so a shiga da motar a ga ta fito daga ciki.

Yana tsayawa ya ce, "Ma'am yaushe zan dawo?."

Islaha ya É—an yi jim ta ce, "Bani numbar ka, zan yi maka waya." Jikinsa yana rawa ya bata lambarsa, ta saka a wayarta sannan ta fita daga motar ta shiga wajen aiki.

Tana shiga ta gano Safeera ta fito da sassarfa tana nufo inda take, suna haɗuwa a hanya ta ce, "ke wannan zuƙeƙiyar motar fa?."

"Munafuka, har kin gani?."

"Tuni ma. Ya aka yi haka, shine ya ce baza ki zo ba sai an kawo ki?."

"Shi a wa? Dallah can mu je" ta faÉ—a tana yin gaba, Safeera ta ce, "sai na zo jin labari, ki shiga studio ki fito." Bata cekomai ba ta wuce itama ta wuce.

Ƙarfe sha biyu na rana Islaha ta tashi daga aiki, ta fito ta samu Safeera tana haɗa kayanta Islaha ta ce, "Safeera zan wuce."

Safeera ta ce, "nima na É—auki excuse, Mama ce bata nan ina so na zauna a gidan na yiwa Baffa girki."

Islaha ta ce, "To mu tafi gabaÉ—aya, daman zan je wajan Hamma."

Safeera ta É—an dumm kafin ta ce, "Hamma kuma?."

"Eh shi" ta faÉ—a tana duba wayarta jin ana yi mata waya.

Ta ɗaga wayar daga can ɓangaren aka ce, "Islaha kina jina, Baba Tabawa ce."

Islaha ta ce, "Baba Ina yini."

"Lafiya lau. Daman faÉ—a miki zan yi jiya bayan ki bar nan, Hajiyan gidan nan tazo ta samu Yafindo, yau da sassafe ta yi min sallama ta tafi garinsu, kuma baza ta sake dawowa ba."

Fargaba ta mamaye Islaha ta ce, "ta bar aikin?."

"ta bari Islaha. Nayi-nayi ta faɗa min abinda ya faru amma taƙi."

"To Baba ina ne garin nasu?."

"A cikin garin zata zauna, babu nisa sosai."

"Don Allah kin san gidan, za ki iya yi min kwatance?."

Baba ta ce, "zan iya." Ta fara yiwa Islaha kwantance tana haddacewa kafin ta ce, "Na gode Baba, sai kin jini." Daga haka suka kashe wayar.

Safeera ta ce, "me ya faru?."

Ta ɗan yi shiru kafin ta ce, "zo mu je." Tare suka fito, daga can nesa ta hango driver kamar inda tace masa ya tsaya. Ta ƙarasa suka shiga, Safeera ta faɗa masa inda zasu je.

Yadda Baba Tabawa ta yi mata kwantace itama haka take yi masa, har suka zo ƙofar gidan da aka ce mata nan ne gidan.

Safeera ta ce, "wai ina ne nan? Na faÉ—a miki girki zan yiwa Baba, ina mu ka zo nan?." Islaha bata amsa ba ta fita dole itama ta bi bayanta.

Da sallama suka shiga gidan, Yafindo ta amsa ta É—ago suka haÉ—a ido.

Ganin Islaha sai ta yar da tsintsiyar hannunta ta ce, "Islaha don Allah ki taimaka min ki tafi, ni bazan yi magana dake ba, ki tafi don girman Allah."

Islaha ta ce, "Yafindo magana nazo mu yi, ki saurare...."

Cikin faÉ—a da tsawa ta ce, "bazan saurare ki ba, don girman Allah ki fita Islaha, don Allah ki tafi. Kar ki saka ni a matsala, kar ki saka rayuwata a matsala. Ni Zainab bata bani komai ba, babu abinda ta bani."

Islaha ta bita da kallo ta ce, "Ya aka yi ki ka san abinda ya kawo ni kenan Yafindo? Yadda muryar ki take rawa ya tabbatar min da akwai abinda ki ke so ki faÉ—a min. Meyasa baza ki sauke nauyi da aka ba ki ba?."

"Islaha ki je don Allah, ki tafi kin ji. Kuma kar ki sake zuwa."

Islaha ta ɗaga kai ta ce, "shikenan na tafi, kar ki damu. Amma ki sani, rayuwar matan da suke gidan da ki ka bari tana hannunki, in ta ɓaci alhakkin hakan yana kan ki.

Duk yaron da yake gidan amana ce a gare ku, an ba ku kuma kuna wasa da ita. Tunda bakya son ganina na tafi, Safeera mu je." A sanyaye Safeera ta juya ta ta fita Islaha ta bi bayanta.

Ko da suka shiga mota Safeera ce ta faɗi inda zasu je, Islaha tunda ta dafe kai bata ce komai ba har suka ƙaraso ƙofar gidan su Safeera.

Islaha ta kalli Lawal ta ce, "ka je ka dawo, zan kira ka."

Cikin girmamawa ya ce, "to ranki ya daÉ—e."
Chapter 25 · 0% Book details