Sashe 33
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jazy ya shiga da sauri ya hana shi ya ce, "yi haƙuri Rehaan, Allah bazan sake yi mata komai yanzu ba, kar ka tafi da ita ka taimaka min."
"Na lura kashe ta ka ke so ka yi ko?."
"I'm sorry big bruh, zan gyara. Zo mu ne falo kar mu tashe ta."
Sai a lokacin Jazy ya lura da Islaha da take zaune a falon amma kamar bata ciki, waje ɗaya take kallo ba dan ta yin wani abun ba sai dan kunya da maganarsu take bata sosai, musamman Rehaan da yake haƙiƙicewa yana faɗa akan abinda aka yiwa Riyya. Har mamakin Ray take yi jin yadda yake magana cikin faɗa, bata ɗauka yana magana cikin faɗa haka ba kwata-kwata, sai ga shi yana yiwa mijin ƙanwarsa faɗa harda ƙoƙarin ɗauke ta.
Nana Haleema.
RDB3P27
Nana Halaeema.
Jazy sai ya É—an ji nauyin Islaha, ya shafa kansa dan bai san yaushe take a wajan ba, yana da tabbacin ta ji komai.
Ya daure ya kawar da kunya ya ce, "Miss tare ku ke ashe?."
Daƙyar Islaha ta ɗaga kanta tana kallonsa sai ta ɗauke kai haka kawai ta ji tana jin kunyarsa. Jazy ya juya yana kallon Ray yana nuna masa Islaha da ido.
Shi kuma da ba a sirri da shi akan Islaha sai ya ce, "Ban gayyace ta ba, itace ta zo ta shiga motar taho nan. Bani na ce tazo ba, ka daina yi min wannan kallon."
Jazy ya girgiza masa kai alamun meye haka, shi kuma ya yi tsaki ya zana a kan kujera yana tunanin Riyya. Islaha bata tanka masa ba, dan kunyar kalamansu take ji sosai, har Rehaan É—in kunya yake bata balle kuma Jazy.
Ray ya kalli Jazu ya ce, "dan ma ka raina ni, ka rasa wanda za ka kira a wannan yanayin sai ni?. Ka bar Mamy da ta ke O&G, ka bar Janan, bayan dukkan su healths workers ne."
"Mtsww! Kai fa kana da ƙarancin hankali Ray, an faɗa maka kowa irin ka ne mara kunya? Kawai sai na yiwa Mamy waya na ce ta zo ga abinda ya faru? Ko sai na kira Janan na ce ta zo?."
Bai bashi amsa ba ya yi masa banza, sai kuma ya tashi ya koma wajan Riyya ya taɓa jikinta ya ji zazsaɓii ya sauka har ta fara gumi. Ya kunna mata ac ya fito daga ɗakin bai ce komai ba kawai ya sauka Jazy ya bi bayansa.
Islaha ta bi bayansu da kallo ta yi tsaki ta ce, "Ko kunya ba ya ji, shi lallai ga mai ƙanwa." Sai itama ta miƙe ta biyo bayansu, ta tarar da Rehaan har ya shiga mota yana sake yiwa Jazy warning akan Riyya.
Islaha ta ƙarasa ta shiga motar ta zauna, tana ji yana sake yi masa warning ta waiwayo tana kallonsa cikin mamaki da harara, maimakon su haɗa ido da Rehaan sai suka haɗa ido da Jazy da yake tsaye suna magana ta window.
Jazy ya ce, "Ka ga matar ka ma tana kallon ka, nasan tana tana mamakin wannan wanne irin Yaya ne."
Ya waiwayo suka haÉ—a ido da Islaha, ta É—auke kai shima bai kuma ta ba, ya É—aga glass É—in Shams ya shiga motar su tafi.
Babu mai magana a cikinsu kowa harkar gabansa yake yi, tafiyar bata yi nisa ba ta ji ya kira Jazy yana tambayarsa ya jikinta.
Islaha ta kalle shi ta harare shi bata ce komai ba. Bacci take ji sosai, dan lokaci har biyu na dare ta wuce, ta kwantar da kanta a jikin ƙofar motar ta lumshe ido ya bacci yana ɗaukarta a hankali.
Hanyar da suka bi suka tarar an rufe, Shams ya tsaya a wajan, jin an tsaya ya saka Ray ya ce, "lafiya?."
Shams ya ce, "Sir an kulle hanyar ne."
Ray ya ce, "daman dare ya yi zasu iya kullewa, ka canja wata mana."
"Sir hanyar bata da kyau."
"Mu je kawai."
Babu yadda zai yi haka suka koma da baya zuwa wata hanyar.
Suna cikin tafiya a hankali kamar yadda Rehaan ba ya son gudu na wuce ƙa’ida, kawai sai suka ga saniya akan titin, Shams ya yi ƙoƙarin kauce mata amma ya kasa motar ta ƙwace suna tangal-tangal.
A lokacin Islaha ta farka jin yadda motar take juyawa akan titi dan har ta matso daf da Ray bata ma sani ba. Ƙaton dutse motar ta daka da ƙarfi, Islaha ta yi gaba kamar zata faɗi, kanta ya daki kujera ta dawo da baya, ta riƙe hannun Ray gam ba tare da ta sani ba cikin firgici.
Ray cikin firgici da tsoro ya ce, "Shams ya faru me haka?."
Shams zai yi magana aka zagaye motar su gaba da baya. Ganin haka sai Shams ya ce, "Sir attack ne."
Ray ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!."
Shams ya É—auko bindingar da take jikinsa yana kallonsu daga waje, dan yana cikin motar bai fita ba yana irga adadinsu dan ya san yadda zai yi dasu. Su kuma tayar motar suka harba, yadda baza su iya guduwa ba.
Ta inda Islaha take zaune aka aiko da harbi guda ɗaya, sai bullet ɗin suka gani ya daki glass ɗin ya koma bai fasa glass ɗin ba saboda motar bullet prove ce. Rehaan bai san ya jawo Islaha ta dawo jikinsa gabaɗaya ba, dan da silent gun suke amfani, ba ka jin ƙara sai dai ka ga bullet.
Shams yana niyar fita Rehaan ya ce, "kar ka fita, ka kira police kawai."
Harbin motar suke yi yi ta ko ina, Islaha ta dafe kunnenta duk da ba sosai ake jin sautin ba, tana jikinsa a kwance ta cusa kanta a ƙirjinsa jikinta yana rawa saboda tashin hankali.
Shima yana riƙe da ita, ya yi wrapping bayanta sun cure waje ɗaya saboda kar harbin ya same su.
Mutanen da suke harbin suka nufo motar kai tsaye, suka saka ƙaton ƙarfe suka da ki glass ɗin ɓangaren da su Rehaan suke amma bai fashe ba, aka sake duka da ƙarfi ya tsage amma bai fashe ba.
Shams cikin tashin hankali ya ce, "Sir ka bani dama na fita, zan iya maganinsu."
"No, kar ka fita" ya sake faɗa har lokacin yana riƙe da Islaha sun koma tsakiya sun bar jikin window.
Lokaci ɗaya hayaƙi ya cika motar gabaɗaya, numfashin Islaha ya fara hawa da sauka, ga tsoro ga hayaƙin da take ji yana mamaye ta lokaci ɗaya, ga zafin da motar ta yi ya mamaye ko ina.
Su kuma waɗanda suka kawo harin suna su yi amfani da damar su su kashe Rehaah, kar su rasa shi a wannan lokacin, hakan ya saka suka fara zubawa motar fetur za su ƙona su.
Hankalin Shams ya tashi ya ce, "Sir motar nan zata iya tashi ko yaushe, ta yi zafi sosai, kuma suna zuba mata fetur ya kamata mu fita!" Ya faɗa da ƙarfi dan Ray ɗin ya ji me ya ce. A lokacin suka sakawa motar wuta, ɓangare ɗaya ya fara ci su kuma suka gudu.
Da hanzari Shams ya buɗe motar ya fito, ya buɗe buɗewa Rehaan ya jawo su da ƙarfi suka faɗo ƙasa shi da Islaha.
Rehaan ya juya da ita a jikinsa, ta dawo sama ya koma ƙasa, ta dawo ƙasa ya koma sama har suka matsa daga kusa da motar suka koma gefe saboda wutar da take cin motar sosai.
Shams ya zauna kusa daahi ya ce, "sir are you okay?."
Rehaan iya cewa komai ba kallon motar yake yi yadda take ci da wuta, zuciyarsa tana bugawa yana ayyana da yanzu suna ciki suna ƙonewa.
Sai a lokacin motar police ta zo wajen, da kuma motar da aka kawo wacce Rehaan shiga. Shams ya nunawa police inda masu laifin su ka yi, suka rufa musu baya dan binciko su waye.
Rehaan ya ɗago Islaha da take kwance a ƙirjinsa ko motsi bai ji ta yi, yana ɗago kanta ya ga ta yi baya zata faɗi alamun bata nunfashi.
Sai a lokacin tuna kamar tana da asthma, ya kwantar da ita a gefen titi, ya miƙe tsaye sannan ya ɗauke ta ya saka a bayan motar shima ya shiga bayan. Shams ya shiga suka tafi motar ƴan sanda tana biye dasu.
Rehaan jijjiga Islaha yake yi gently amma bata motsa ba da alama numfashinta ya tsaya, ya cire mata hijjab É—in jikinta, gashinta ya baje akan kujerar.
Ganin da gaske bata numfashi sai kawai ya tsaya yana kallon fuskar ta yana tunanin ta yadda zai taimaka mata. Mouth to mouth recuscitation ne kawai ya dace da ita a wannan lokacin, tunda numfashinta ya tsaya, tana buƙatar a bata numfashi dan ya taimakawa na ta ya dawo. Tunanin yadda zai saka bakinsa a cikin nata yake yi, hakan ya saka shi ya zuba mata ido yana kallonta bai yi komai ba.
Sai kuma ya tuna shi likita ne, taimako aikinsa ne, zai taimaka mata a matsayin mara lafiya ba C wife ba. Ba shi da zaɓi haka ya matsar da fuskarsa kusa da ta ta, ya ɗora bakinsa a kan nata, ya rufe hancinta da hannunsa, ya buɗe bakinta da lips ɗinsa ya bata numfashi mai ƙarfi. Ganin bata motsa ba ya saka shi cigaba da bata numfashi saboda taimakon gagagwa ake so ayi mata kafin su je asibiti.
Bai farga ba ya tsinci kansa yana kissing lips a maimaikon recuscitation, ya riƙe tongue ɗinta da bakinsa, yana bata hot and soft kiss ba tare da ya san yana yi ba.
Kamar an tuna masa da abinda yake yi, sai ya zabura ya janye bakinsa, yana tunanin ya aka yi ya yi wannan gangancin? Da farko numfashi ya fara bata kamar yadda ya yi niya, bai san me ya É—auki hankalinsa ya zarce da kissing É—inta ba.
A daidai lokacin suka iso asibiti, aka shiga da Islaha a guje dan a bata taimakon da ya kamata.