← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 110

Sashe 56

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Islaha bata ce komai ba sai kallon Mama da ta ke yi tana murmushin da ita kaÉ—ai ta san ma'anar kayanta, dan ita ta san abinda yake faruwa wanda su basu sani ba, ba ta ji haushi akan abinda Labiba ta ce ba, dan ita ta san dawar garin.

Islaha ta ce, "Mama ina yini."

Mama ta bita da harara ta ce, "Lafiya lau, sannun ki." Daga haka bata sake cewa komai ba ta miƙe ta fita.

Karima ta ce, "Ka ga shegiya, wato ni bazata gaishe ni ba?."

Mama ta yi dariya ta ce, "bar Æ´ar iska mu cigaba da abinda yake gaban mu. Yara biyu ne kuma Æ´an mata, kuma zasu yi abinda ake so. Sai dai iyayensu basu sani ba."

Karima ta ce, "wannan su ta shafa ba mu ba, mu kawai mu sanu kuÉ—i."

"Gaskiya ne, tunda za su yi zan yi musu waya su zo mu san abinda za a yi."

"Hakan ya kamata." Daga nan suka cigaba da tattaunawa akan abinda ya shafi aikinsu.

Islaha ko gidansu Safeera bata shiga ba, Barr ya kira ta ya ce ga shi ya ƙaraso, ta ƙarasa ta shiga motarsa tana kallonsa.

Suraj ya kalle ta ya ce, "Kin yi kiɓa abin ki Islaha."

Islaha ta ce,  "Hamma ya aka yi, ka samu Yafindon kuwa?."

Ya girgiza kai ya ce, "har yanzu ina kan bincike a kan hakan."

Islaha ta ce, "Na shiga uku! Allah ka kare wannan mata, Allah ya kiyaye ta daga sharrin masu sharri."

Ya amsa da amin sannan ya ce, "In Allah ya yarda babu abinda zai same ta."

"Allah ya sa hakan. Ni wani abu nake so na yi."

"Ina jin ki."

"Bincike nake so na yi mai ƙarfi akan masu garkuwa da mutane, ina so na je inda ake kai mutane in kama su na ga abinda yake faruwa."

Suraj buÉ—e ya ce, "ke Islaha! Wai me yake damun ki ne? Daga wannan sai wannan?."

Islaha ta ce, "ina so na zama silar kawo ƙarshen abun."

"Ke a wa? Dan kawai an sace saurayinki sai ki kawo ƙarshen kidnappers a Nigeria?."

"Ba dan haka ba, kawai ina so."

"To ki bari a gama da wannan case É—in, sai ki yi abinda ki ke so."

"Sai mu yi dai Hamma."

Suraj ya buÉ—e baki ya ce, "Wa! ni? A'a, Islsha ke dai ki yi."

Islaha yi shiru bata ce komai ba sannan ta ce, "Don Allah a cigaba da dubawa, a gano inda Yafindo ta ke, bana so wani abun ya same ta."

Suraj ya É—aga kai ya ce, "kar ki damu, in Allah ya yarda babu abinda zai same ta."

"Allah ya sa hakan, na gode Hamma Suraj."

"Kar ki damu Islaha."

"Zan koma."

"To sai kin ji ni" daga haka ta fita daga motar.

Tana fita ya É—auki wayarsa yana danne danne sannan ya ce, "na gama da case É—in, komai yana hannuna, zan yi komai yadda ya kamata in sha Allah" ya faÉ—a yana jan motar ya bar unguwar.

Nana Haleema.

RDB3P44
Nana Haleema.

Islaha haka ta koma gidansu Ray, ta shiga ɓangaren Mamy ta same su a zaune duna ta hira kamar ko yaushe.

Mamy ganinta ta ce, "Islaha har kin dawo?."

"Na dawo Mamy."

"ki je ki huta."

"To Mamy" ta faɗa tana wucewa ta shiga ɗakin ta rufe ƙofa. Babu irin tunanin da bata yi ba akan kuɗin da Baffa ya bata, tana tunanin ko ta ragewa Rehaan wani abun a wanda ta karɓa? Sai ta tuna tunda ba duka zata bawa Rehaan ba gwara kar ta bayar. Sai dai ko ta bawa Hamma ya ƙarasa aikin gabansa, da wannan tunanin ta yi bacci.

Washe gari da wuri ta gama abinda zata yi ta tafi bank suka yi mata upgarading account ɗinta komai yana zama normal sannan ta fito, kai tsaye  ta turawa Baffa kuɗin sannan ta turawa Saheer masu yawa.

Bata jima da tura masa kuÉ—in ba ya kira ta, tana É—auka ya ce, "Islaha ke ki ka sa ka min kuÉ—i?."

Ta ce, "ni ce."

"A'a ba ke ba ce, ko dai an yi hacking account É—in ki?."

"Ni ce Hamma."

"Islaha kin san nawa ne kuwa?."

"Ten millions."

"Kenan kin sani?."

"Ina wajan aiki, in na fito za mu yi magana" ta faÉ—a tana kashe wayar.

Saheer ya kalli Sadik da suke tare ya ce, "kenan ta san ta saka min kuÉ—in."

Sadik ya ce, "ga shi ka ji ta faÉ—a."

Saheer cikin mamaki ya ce, "A ina ta samu wannan kuÉ—in? Ba fa dubu goma ba, miliyan goma."

"Kana bani mamaki Saheer, ka manta wanda ta ke aure ne?."

Saheer ya yi tsaki ya ce, "Islaha bazata karɓi kuɗinsa ba, baza ta karɓi komai na sa ba balle har ta tura min, kuɗi meye ta saka min?."

Sadik dai ya taɓe baki bai ce komai, shi kuwa so ya ke kawai su haɗu da Islaha su tattauna ya ji kuɗin waye sannan a ina ta samu.

Sai yamma Islaha ta fito ita da Safeera ta ce, Safeera raka ni gidansu Hamma Sadik don Allah, zan yi magana da Hamma."

Kafin ta Safeera musa ta katse ta ta ce, "wani abu ne mai mahimmaci zai kai ji wajensa, ba akan abinda ki ke tunani bane, nima na san abinda nake yi." Safeera sai ta yi shiru bata ce komai ba, suka hau napep suka tafi.

Bata shiga gidan ba sai waya ta yi masa ta ce gata ta zo, yana fitowa kafin su gaisa ya ce, "kuÉ—in nan na me ye ki ka saka min, sannan a ina ki ka samu?."

Islaha ta kalli Saheer sannan ta kalli Sadik, ta sake kallon Saheer sannan ta ce, "Hamma ko gaisawa?."

"tambayar ki nake yi Islaha, a ina ki ka samu kuÉ—i irin wannan kuÉ—in da ki ka tura min? Sannan na meye ki ka saka min?."

Islaha ta yi shiru sannan ta ce, "Jiya Baffa ya tura min su, ya ce min kuɗin da aka ba shi ne lokacin ɗaurin aurena, akace wai na yi hidimar aure da ake yi kafin ɗaurin aure, irinsu lefe da sauransu. Ni kuma shine na je bank aka yi min ugrading account ɗina, na tura maka na turawa Baffa. Sai Safeera da Hamma Sadik da zan turawa gobe, dan limit ɗin transfer ɗin ya ƙare."

Saheer mamaki ya kusa kashe shi ya ce, "Miliyan goman ki ka bani Islaha?."

"Eh mana, taka ce. Da na yi tunanin na biya Rehaan kuɗin da ya bani na fansar ka, sai kuma naga basu kai adadin da ya bani ba, na san bazai karɓa ba raina min hankali zai yi, gwara na ba ku."

Saheer ya ce, "kin ce an ba ki dan ki yi hidimar biki wacce ba a yi miki, ni me zan yi dasu?."

Ta ce, "Amma nawa ne ko? Ni kuma kyauta na bayar a cigaba da yi mana ginin gida kawai, so na ke da zarar kwanakin nan sun cika na san inda zan zauna, dan bana son sake zama a gidanku kamar wancam lokacin. Baffa ma kyauta na ba shi, kaima haka. Safeera da Hamma Sadik ma zan tura musu kyau, har Saleem da duk wanda mu ke mu'amalar mutunci da shi. Dan bana buƙatar ko sisi daga wajan Mr Rehaan, balle kuma na yi amfani da kuɗin da aka ba ni akan hidimar aurensa.

Saheer ya ce, "Islaha..."

Ta yi hanzarin katse shi ta ce, "Na san baza ka ji daɗi ba, zaka ga kamar na raina ka tunda har na yi maka kyauta da kuɗin kuɗinsa. Hamma ba haka ba ne, ban baka dan baka da ƙarfinsu ba, kuma ba kuɗinsa bane nawa ne. A al'ada ba laifi bane in an bani, tunda su Baffa da iyayensa basa san maganar yarjejeniya ba, kaga ba laifi ba ne dan an bani ni kuma na bayar. Don Allah kar ka ce baza ka karɓa ba, ka riƙe a cigaba da hidima da su.

Jiya jiyan nan ka ce min babu kuÉ—i sosai a wajen, ka ga gasu an samu, ayi abinda ya kamata kafin Allah ya kai mu wata biyar."

Ta faÉ—a tana duba wayar ta da take ringing ta ce, "Baffa ne yake yi min waya, sai na koma zan kirasa mu yi magana."

Sadik ya yi caraf ya ce, "Hakan ma kin kyauta Islaha, mun gode sosai da ƙoƙarin ki. Gaskiya kina da halacci, kin son saka alkhairi da alkhairi."

Sai ta ji daÉ—i a ranta har ta yi murmushi, "Ni ce da godiya Hamma. Sha biyu na dare in sha Allah, zan tura maka naka da kai da Bestie" ta faÉ—a tana ksllom Safeera da take kallonta ta kasa magana.

Sadik ya ce, "mun gode, Allah ya saka da alkhairi."

Islaha ta sake kallon Saheer ta ga ya kasa yi mata magana sai kallonta kawai da yake yi sai ta ce, "don Allah kar ka ce baka so Hamma, ka karɓa don girman Allah, kar ka yi wani tunani akan kuɗin, ka tuna nawa ne ni kuma na baka. Zan koma yanzu, zamu yi waya in anjima, bana jin daɗi, ina so na huta kaina ciwo yake yi."

Saheer ya É—aga kai kawai bai ce komai ba, ta ja hannun Safeera da bata ce komai ba suka fara tafiya.

Suna barin wajan Sadik ya daki kafaÉ—ar Saheer ya ce, "mutumina ka kama da wuta fa, miliyan goma daga sama? Lallai da ace auren nan na Islaha mai É—orewa ne, da mun ji daÉ—i."

Saheer ya kalle sa ya ce, "ni mayar mata da kuÉ—in nan zan yi, bazan iya cin ko sisi a kuÉ—in Rehaan ba."

Sadik ya riƙe kunnensa ya ce, "ɗan maimaita, kamar ban ji daidai ba."

Saheer ya yi tsaki ya ce, "bazan karɓa ba, bana so."

Sadik ya ce, "ba kada hankali ai, Naira miliyan goma ce ba dubu goma bace, in ka mayar sai ka kusa ƙare rayuwarka ba ka same ta nan kusa ba."

Saheer cikin kishi da ƙunar ya ce, "me zan yi da kuɗin mijin da ta ka aure a yanzu?."

"Ka ci mana, ina ruwan ka da na mijinta ne? Ita kyauta ta baka, kuma ba roƙa ka yi ba."
Chapter 56 · 0% Book details