← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 110

Sashe 81

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rehaan da ya fita cigaba sallarsa ya yi, bayan ya idar da raka'a biyu ya kalli É—akin ya ga bata fito ba, tunani yake yi ta ce yunwa take ji kuma tana zaune tana kuka, me ya hanata fitowa ta je ta nemi abincin?. Ya É—auke kansa daga kallon É—akin yana rolling idanunsa a waje É—aya, tunanin abinda ya hanata zuwa ta yi girkin kawai ya ke yi, duk ya damu kansa akan rashin fitowar ta.

Rehaan ya kasa daure sake miƙewa ya koma ɗakin, ya same ta a kwance ta yi shiru amma ta bar kukan. Bai ce mata komai ba ya koma da baya ya ɗauki waya ya kira chef ɗinsa, yana ɗauka ya ce, "kana ina?."

Ya yi shiru alamun ana basa amsa kafin ya ce, "okay in zaka zo ka taho spicy noodles." Yana gama faÉ—a ya kashe wayar ya koma ya zauna a akan sallaya.

Cikin mintina goma Chef ya kirasa, bai ɗauka ba sai ya miƙe tsaye ya sauka ya buɗe ƙofar parlour. Chef ya shigo ya ba shi pack ɗin hannunsa, bai cewa Chef ɗin komai ba ya hau saman ya shiga ɗakinta kai tsaye.

Yana shiga ɗakin ya ƙara hasken ɗakin yadda bazai yi mata yawa ba, ta ɗago a hankali ta juyo ta kalle shi sai ya miƙa mata pack ɗin ta ce, "take it."

Ta miƙa hannn ta karɓa ta buɗe ta ga abinda tace tana so ne, korean spicy noodles ce mai kyau sai ƙhamshi take yi, harda disposable fork a ciki yadda zata ci hankalinta a kwance.

Islaha ta É—ago kanta ta kalle sa ta ga ita yake kallo sai ta ce, "Thank you" ta faÉ—a tana fara ci a hankali. Bai ce komai ba ya juya ya fita ya koma inda ya tashi ya cigaba da sallar yana jin daÉ—i ta samu abinda take so.

Islaha kuwa yajin abincin ya yi mata sosai, ta dai ci kaÉ—an ta sha ruwan da Safeera ta bata magani É—azu ta ajjiye sauran. Ta kwanta a kan gadon bayan ta kashe hasken, tana tunanin abubuwa kala-kala a haka bacci ya sake É—auke ta.

Washe gari bata shiryawa zuwa aiki ba, tunda ta yi wanka tana kwance tana juyi a kan gadon, yunwa take ji amma ƙiwar tashi take yi. Buɗe ƙofar da aka yi ya saka ta kalli ƙofar ta ga Mamy ce da Janan suka shigo.

Sai ta miƙe zaune ta ce, "Mamy sannu da zuwa."

Mamy ta ƙarasa ta dafa goshinta ta ce, "kin ji sauƙi?."

Ta ce, "na ji sauƙi, Ina kwana Mamy?."

Mamy ta yi murmushi ta ce, "kwana kuma daughter" sai ta kalli agogon da yake É—aure a hannunta ta ce, "an idar da sallar azahar." Islaha ta yi murmushi dan ta ga gudun lokacin sosai.

Janan ta ce, "Sis ya jikin?."

Islaha ta yi murnushi ta ce, "Alhamdu lillah."

"Daman kina fama da Dysmenorrhea ne?." Islaha ta É—an É—aga kai tana jin kunyar Mamy.

Many ta ce, "ya ki ke jin ciwon? Yana yi miki tsanani sosai?."

Islaha duk sai kunya ta rufe ta tana Allah wadai da wannan ciwo mai tona mata asiri. Sai daga baya Islaha ta ce, "yana yi sosai."

Mamy ta ce, "har yanzu ma kina jin sa sosai?."

Islaha ta girgiza kai ta ce, "bana ji sosai, in na sha magani yana raguwa kaÉ—an."

Mamy ta yi shiru ta ce, "kwana nawa ciwon yake É—auka kafin ki dawo normal?."

Islaha ta ce, "kwana biyu."

Janan ta ce, "kuma kina samun matsalar period É—in wani lokacin?." Islaha ta É—an É—aga kai alamun eh.

Janan ta ce, "Mamy i think it’s pelvic inflammatory disease."

Mamy ta girgiza kai ta ce, "ba shi bane Janan, i’ts normal primary Dysmenorrhea as you said, canjawar hormonse yana kawo canjin lokacin, ba lallai sai pelvic ba."

Mamy ta kalli Islaha ta ce, "kin yi breakfast?." Ta girgiza kai alamun bata yi ba, Mamy ta ce, "Janan je ki ki kawo mata breakfast please." Janan ta fita Mamy ta zuna a kusa da Islaha bata ce komai ba, ita kuma kunyar Mamy take ji.

Suna zaune zaman shiru har Janan ta dawo da tray mai girma, ta ajjiye mata akan table É—in da yake É—akin ta ce, "ga shi nan sis."

Islaha ta kalli Janan ta ce, "thank you sis."

Janan ta ce, "welcome Miss Islaha. I saw ypur interview, gaskiya kin yi ƙoƙari sosai, yadda ki ke magana lamar baki san Ray ba, kin yi hira da shi normal kamar ba mijinki ba, har kina tambayarsa da gaske ne ya yi auren sirri.”

Murmushi kawai ta yi ta taso ta zauna akan kujerar da kusa da table É—in, Mamy ta haÉ—a mata tea ta bata a hannunta. ita duk nauyi take ji in Mamy tana yi mata wannan hidimar, sai ta ga babba da ita itace zata haÉ—a mata tea kuma ta bata?.

Sai da ta sha tea sannan ta ci abinci, Mamy ta ce, "ki sha magani zai saka ki ji daÉ—i."

Islaha ta ce, "To Mamy."

Mamy ta ce, "na ga interview jiya, gaskiya kin yi ƙoƙari.”

Ta yi murmushin jin daɗi ta ce, “Na gode Mamy.”

“Kuma da gaske ana tambayar ya yi auren sirri?."

Islsha ta ce, "sosai Mamy, Chairman É—in mu da kansa ya saka wannan tambayar, dan ni ban tsara da ita ba."

Mamy ta murmusa ta ce, "gabaɗaya duniya a kan hirar ta ke magana, sannan mutane sun ce basu yarda babu alaƙa tsakaninku ba, kuma ko da ina cikinsu bazan yarda ba."

Janan ta ce, "kowa ma bazai yarda ba Mamy, yadda Ray yake yi mata magana ka san ba ranar ya fara magana da ita ba."

Mamy ta ce, "ba ki ga kallon da yake yi nata ba? Irin kallon na san ki É—in nan, like kamar ba a waje É—aya muka kwana ba."

Islaha ta yi dariya bata ce komai ba, amma ta ji daÉ—in zamansu Mamy a wajanta, hakan ya rage mata abubuwa da yawa. Mamy tana sakkowa ta fita sai ta ga Daada a tsaye Mamy ta ce, "Daada da kan ki?."

Daada ta ce, "An ce min Islama bata da lafiya, shiyasa nazo na ganta, zata iya sakkowa?."

Mamy ta riƙe Daada har falo ta zauna sannan ta ce, "ta ji sauƙi sosai."

Daads ta ce, "ni ban iya hawa sama ba, a kira ta in zata iya sakkowa na ganta."

Mamy ta ce, "Janan kira ta in zata iya zuwa." Janan ta koma, ba jimawa suka dawo tare da ita.

Daada ta riƙe hannunta ta ce, "Ishlaya me yake damunki?."

Islaha bata amsa tambayar nata ce, "Daada barka da rana."

"Ya jikin ki?."

"Da sauƙi."

Daada ta kalli Mamy ta ce, "ku ne likitoci, me yake damunta?."

Mamy ta ce, "Ciwon da ake yi ne yayin al'ada" ta faÉ—a tana kalkon Daada.

Daada ta ce, "ciwon al'ada kuma? Me zai haɗata dashi ita da ta ke da aure?…..”

A lolavin Rehaan yake shigowa parlor, Daada tana ganinsa ta ce, “Kai me zai haɗa mata ka da iriin wannan ciwon da ake dainawa bayan aure.”

Rehaan bai tanka mata ba, Daada ta kalli Mamy ta ce, "in mace ta yi aure ba tana dainawa ba? Me hakan yake nufi da Ishlaya? Hakan yana nuna min ajjiye ƴar mutane ya yi tsahon wannan lokacin yana ɗirka mata shinkafa? An faɗa masa shinkafa ta zo ci gidan nan?. Ko an faɗa masa talabijin aka kawo masa da zai dinga kallonta ko yaushe? Matarsa ce fa.”

Mamy ta tausasa murya ta ce, "Daada ba lallai sai an daina ciwon al'ada bayan anyi aure ba, wannan maganar duk ta manya ce, amma a lafiyance ba haka bane. Shi ciwon yana faruwa ne saboda mahaifa tana matsewa don fitar da jini (contraction) da kuma hormones (prostaglandins), ba dan rashin mu'amalar aure ba. Wasu matan suna iya lura da ciwon ya ragu bayan aure, amma ba hakan yana nufi kowa wacce mace ma in ta yi aure zai daina ba. Wasu bayan auren ba ya canjawa sai dai ma ya ƙaru fiye da yadda suka saba, duk da mu’amalar auren yana taimakawa wajan sakin wasu hormones (endorphins) ɗin, hakan shine yake rage muau zafin har su ga canji bayan aure.”

“Amma hakan ba yana nuna yin aure ko yin mu’amalar aure shine magani ga masu fama da ciwon ba, wasu ciwon yana iya zama babban ciwo ne, shiyasa ake so in abun ya yi yawa aje asibiti a duba a gani.”

“Wani Yana iya zama irinsu endometrioses, uterine fibroids, pelvic inflammatory disease. Irin wannan sai ayi ta fama, ba a san ciwo ne a jikin mace ba, a dinga tunanin me yake kawo shi, shiyasa zuwa asibiti yana da amfani akan irin wannan ciwon.”

Mamy ta sake cewa, “Daada wannan ciwon da take fama da shi ba lallai ne in an yi aure sai an daina ba, wasu har su haihu ba sa dainawa.”

Daada ta yi shiru sannan ta ce, "ni da aka ce min bata da lafiya ma wallahi na yi ciki gare ta, ashe babu cikin."

Mamy ta É—an murmusa kawai ta kalli Rehaan da ya zubawa Daada ido, shi Mamy ce ma ta basa mamaki da ta tsaya tana yiwa Daada bayanin da har abada bazata gane ba, hakan ya saka shi ya bar wajan ya hau sama bai ce komai ba.

Daada ta dafa Islaha da kunyar duniya ta kashe ta, amma ta ƙaru sosai daga bayanin Mamy, dan ita kanta da ta yi tunanin da anyi aure ake dainawa, ashe abin ba haka bane.

"Sannu, Allah ya baki lafiya."

Ta amsa da amin a kunyace, tana jin kamar ta ta shi ta gudu saboda kunyar da take ji sosai.

Daada ta ce, "koma saman ki kwanta ki huta, amma baza ki je aiki ba ko?."

Ta É—aga kai ta ce, "bazan je ba."

"Jiya ai na ga hirar ki da Muhammad a talabijin, meyasa ba ki faÉ—awa dumiya ke matarsa bace?."

Ta yi murmushi kawai amma bata ce komai ba, Daada ta ce, "ai da kin faÉ—a kowa ya sani, ko za a samu Æ´an matan dangi su daina kawo masa hari."
Chapter 81 · 0% Book details