Sashe 60
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lami ta yi dariya ta ce, "ashe ba a banza ki ke shan wahala ba, sharar masallaci ce ba ki yi shiyasa yanzu ki ke share coci. Kin bar na ki yaran kin taho kina rainon wasu, kin bar mijinki kin zo nan mijin wata yana ƙoƙarin danne ki ya yi amfani da ke, kin bar aikin gidan ki kin taho nan kina aikin gidan wata da babu lada. Ga wahala, ga zagi, ga duka. Na sha jin case ɗin masu zuwa babu izinin iyayensu, da masu zubar da ciki saboda zuwa, amma ban taɓa jin wacce ta haɗa abu uku ba sai ke. Kin kashe auren ki, kin bar yaran ki, kin bar ƴan uwanki kin taho inda ba ki da kowa sai Allah. To in ba ki sha wahala ba a tunanin ki daɗi za ki ji?."
Umma ta goge hawayen da suka sakko mata ta ce, "nima na san sakkaya ce, wallahi babu abinda na rasa a gidan mijina, daidai gwargwado yana yi mana iya ƙarfinsa, amma neman kuɗi ya rufe min ido."
"Son zuciya ya rufe miki ido, ga shi yanzu kina so ki koma gida babu hanyar komawa, dole haka za ki cigaba da zama."
Umma ta ce, "wallahi bazan zauna ba, tafiya zan yi."
"Ta ya za ki tafi? Visar ki ta ƙare, ke kin san risk ɗin da yake cikin zaman ki a ƙasar nan, kin san irin abinda za a yi miki in aka kama ki?. Izinin zama na wata uku aka ba ki, amma kin zo kin kai wata biyar a nan. Zaman da ki ke yi gabaɗaya ba a kan doka ki ke yinsa ba, kin shigo musu ƙasa kin zauna ba tare da ƙa'ida ba, kuma yanzu ba ki da visa, kuma ki zo ki ce zaki koma gida?."
Umma ta ce, "Amma ai visa shekara É—aya suka ce sun yi mana."
"Na faɗa miki ƙarya suke yi miki, ta wata uku ce wallahi, kuma ta jima da ƙarewa. In suka kama ki kaf zasu cilla ki a gidan yari."
"ni wallahi ban san haka abin yake ba, da bazan zo ba."
Lami ta ce, "ai daman idanun ku rufewa yake yi a lokacin da ku ke son zuwa nan ɗin, bakwa hango matsala, bakwa bin tsarin da za ku zauna lafiya. Kin ga ni, ta kamfani na zo nan, hotona aka turowa ƙasar nan suka ce na yi musu, aka zo dani aka yi min gwaji da duk abinda ya kamata. Zamana a gidan nan ina da lasisi, ƙasar nan ta san dani, na zauna tsahon wata uku a nan kafin masu gidansu ce suna son cigaba da aiki dani. Yanzu ina sauran zama na shekara biyu, duk inda zan je babu ruwana da za a kama ni, dan ina da id card ɗin zai tabbatar da aiki nake yi. In shekara biyu suka ƙare, za a mayar dani kamfani in an samu waɗanda suka ce suna so a sake kai ni, in ba a samu ba a sallame ni na koma gida. Ku kuwa kun shigo da visa ta wata uku, kun zauna har na wannan lokacin kuna faman wahala. Ki gode Allah a Madina ki ke, wallahi da Makka ne da yanzu kin zama ɓera wajan gujewa askar."
Umma ta ce, "gani a Madina, amma ban taɓa shiga masallacin Annabi ba."
"daman ba nan ya kawo ki ba, aiki ki ka zo yi ba ziyara ba. Ni kuwa ina damar shiga masallaci na yi sallah, babu É—ar É—ar É—in za a kama ni."
"Ni dai ina so na koma."
"Ki daina wannan maganar, ki yi fatan Allah ya cigaba da ɓoye ki har lokacin ki ya cika, in aka kama ki wallahi sai an mayar dake gida, sannan sai an yi miki thumbprint ɗin da sai kin kwana biyu baki shigo ƙasar nan ba. Ko shekara biyar ko goma, sai kin ɗauki wannan lokaci ba ki zo ba. Ko ɗanki shugaban ƙasa ya zama, kina ji kina gani baza ki zo ki sauke farali ba."
Umma ta dafe ƙirji cikin firgici sai kuma ta ɗan yi shiru kafin ta ce, "da zan samu na shiga masallacin Annabi kafin na tafi da na ji daɗi."
"Kina nufin za ki je inda za a kama ki É—in kenan?."
"ban san abinda hali zai yi ba, amma gwara na shiga É—in."
Lami ta ce, "zan je sallar asuba masallacin, ki zo ƙarfe biyu na dare sai mu tafi."
Umma cikin zumuÉ—i ta ce, "Zan zo in Allah ya yarda, ko matar can bata sani ba wallahi sai na fito. Na gaji, sai na je na ga masallacin nan in Allah ya yarda."
Lami ta murmusa suka É—an cigaba da hira sama-sama, kafin Umma ta koma gida.
***
Islaha haka ta cigaba da zama a wajan Mamy, Mamy tana lura da duk wani motsinta, duk inda zata je tana sakawa ana yi mata binciken akan inda take zuwa da waÉ—anda take mu'amala dasu. Har kiran wayar da take yawan yi tana sakawa a bibiya, kuma an tabbatar mata da babu wani abu na rashin gaskiya a tare da ita.
Har labarin Saheer da kowa Mamy ta sani, ta kuma tabbatar da maganar Jafar da ya ce auren contaract ne a tsakaninsu, kuma ta tabbatar ba son Rehaaan take yi ba, lokaci take jira ta ta kama gabanta.
Hakan ya yiwa Mamy daÉ—i sosai, ta ji a ranta ta samu wacce ta ke burin Rehaan ya samu, wacce zata aure shi ba dan kuÉ—i ba, wacce zata zauna da shi ba dan yana da wani abun ba. Islaha ta yi daidai da ra'ayin Mamy, tana yi musu fatan É—orewar aurensu har abada.
Islaha ta É—an saki jiki a wajan Mamy, Banisha ta zama yar É—akinta kullum suna tare suna hira. Ikram ce sama-sama suke gaisawa, kuma ta fahimci son Rehaan take yi, kishi ta ke yi da ita shiyasa bata sakar mata fuska. Ita kuwa kallo ma bata ishe ta balle ta tanka.
Janan ma suna shiri da ita, zata zo su yi hira kafin ta fita.
Islaha ta yi mamakin ganin Mamy ta saki jiki da ita sosai, ta daina É—aure mata fuska, in tana yi mata magana kamar tana magana da Banisha saboda kulawa, ko me ta gani a waya sai ta kira Islaha ta nuna mata dan ta ji ra'ayinta akan abun, sai hakan ya yiwa Islaha daÉ—i ta rage zaman kaÉ—aicin da take yi.
Ranar tana zaune a É—aki tana danna wayarta, ranar sai bayan azahar zata je aiki bata fita da safe ba, tana zaune cikin atamfa riga da siket suna hira da Saheer.
Da sallama Mamy ta shiga ɗakin tana kallon Islaha, Islaha ta amsa tana kallon ta har ta ƙaraso.
Mamy ta ce, "baza ki je aiki bane?."
Islaha ta ce, "Zan je Mamy, sai an jima."
Mamy ta ce, "Zo ki raka ni mu gaishe da Salman, kwana biyu jikinsa ya tashi, zo mu je sai ki samu lada."
Islaha ta miƙe tsaye tana neman hijjab ɗinta dan ta saka ta raka Mamy dubiya. Mamy ta bita da kallo tana murmushi, dan Islaha ta yi daidai da ra'ayin Rehaan, dan ta fi kowa sanin irin type ɗin macen da Rehaan yake so, kuma Islaha ta cike duk wani abu a cikin abubuwan da yake lissafawa. Ita kanta ba san meyasa Allah ya ɗora mata ƙaunar Islaha lokaci ɗaya ba, duk da farkon zuwanta gidan haushinta take ji, saboda an bawa ɗanta ita ba ya so, amma yanzu bata jin hakan a ranta, tana girmama Islaha sosai.
Islaha ta saka hijjab ta juyo suka haÉ—a ido da Mamy da take kallon ta tana murmushi. Mamy ta ta shafa fuskarya ta ce, "Mu je."
Tana faɗa sai kuma wayarta ta fara ƙara alamun shigowar kira, kuma video call ne ya shigo.
Mamy ta É—aga ta ce, "Rehaan."
Islaha da yake a kusa da Mamy take sai ta ji ya ce, "Mamy na gaji, na yi aiki sosai, bayana ciwo yake yi."
Islaha bata san ta yi tsaki ba, ta kawar da kai tana maganganu a zuciyarta, gabaɗaya haushi yake bata, bata son wannan ɗabi'ar shagwaɓar da yake yi ki kaɗan, in aka cigaba da yin haka a gabanta wata ran zata iya rufe shi da dukan takaici.
Mamy ta ce, "kaine ka ke takura kan ka Rehaan, ban meyasa ka ke haka ba."
Islaha ta kalli Mamy jin yadda take yi masa magana kamar wani yaro ƙarami, ta taɓe baki bata kalli inda yake ba.
Mamy ta ce, "Rehaan zan shiga duba Salman, in na dawo zan kira ka." Tana ji ya amsa sannan Many ta kashe wayar.
Mamy kalli Islaha ta ce, "Ba ki taɓa cewa na ba ki Rehaan ku gaisa ba, ko kuna waya da shi?."
Gaban Islaha ya faÉ—i sosai, rana ta farko da Mamy ta yi mata zancen Rehaan har ta nuna tuna mata ita wata ce a wajansa.
Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, dan bata dan me zata ce mata ba gwara ta yi shiru. Mamy ta murmusa ta ce, "Mu je."
Tare suka fito a jere kamar Yaya da ƙanwar ta, islaha sai take jinta wani iri, tana jin nauyin Mamy sosai a cikin ranta. Mamy kuwa ko a jikinta tafiya suke yi har ɓangaren Umma.
Suka shiga da sallama aka amsa, Umma da Mama suna zaune ana ta fama da Salman akan ya sha magani amma yaƙi. Daman Rehaan ne kaɗai mai iya basa magani, bayan shi ko Amir ɗin da yake tsoro bai isa ba in dai akan magani ne.
Umma cikin fusata ta ce, "wallahi sai ka sha maganin nan."
Salman ya ƙi karɓa yana kawar da kai gefe suka haɗa ido da Islaha. Sai ya miƙe zaune ya kalli Umma ya ce, "Umma kin ganta tazo." Umma ganin Mamy da Islaha sai ta haɗe rai ta kawar da kai gefe.
Islaha ta yi murmushi tana kallon Salman bata ce komai ba. Mamy a tausashe ta ce, "Salman ka sha maganin mana."
Salman ya noƙe kafaɗa ya ce, "ni ita ce zata bani."
Umma ta ce, "Wace zata ba ka?." Salman ya nuna Islaha da take tsaye a wajan.