← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 110

Sashe 69

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Alhamdu lillah."

"Allah ya ye maka wannan wahalar, anya baza mu je a farke cikin ka a duba ba?."

"inda hakan zai yu zan amince ko dan na rabu da wannan wahalar, amma kai ka san babu inda ban je akan ciwon nan ba."

Jazy ya ɗaga kai ya ce, "ƙaddarar ka ce kam, duniya ce kaɗai bamu bari ba akan neman maganin ciwon nan ba, Allah ya ya ye maka."

"Amin ya rabbi."

"Ina Islaha?."

Ya É—aga ido ya kallesa yana wani tunani daban, lokacin da tana gidan suna tare da Mamy tausayinta yake ji, amma tunda suka yi magana da Ubaid gabaÉ—aya sai haushinta ya dawo masa sabo fil, ga shi dai ba zancenta suka yi da Ubaid ba, amma haka kawai yake jin haushinta.

Rehaan a ƙufule ya ce, "tana jikina."

Jazy ya yi dariyar tsokana ya ce, "sai dai kai ka zama a jikinta, amma ba dai ita ba." Bai ce masa komai ba ya share sa.

A lokacin Riyya ta shigo ta ƙaraso kusa dashi ta yi masa side hug ta ce, "Hamma ya jikin?."

Rehaan yana murmushi ya ce, "na ji sauƙi my love, ya ki ke?."

"lafiya lau, Ka ji sauƙi?." Ya ɗaga mata kai yana kallonta da murmushi.

Riyya ta ce, "amma ka rame."

Bai ce komai ba ta ce, "ina sis Islaha take?."

Ya É—an yi shiru sai kuma ya ce, "bata nan."

Ta miƙe ta ce, "na kawo maka cocunot drink, yana wajan Mamy" ta faɗa tana miƙewa ta sauka daga saman.

Ray ya kalli Jazy ya ga yana kallonsa ya buÉ—e ido ya ce, "meye?."

Jazy ya ce, "ina da tambaya ne."

"i'm all ears."

"Kar ka yi deflecting maganar, ka fahimce ni a matsayin ka na likita ba Rehaan ba."

Jazy daman ya san Rehaan bazai ce komai ba, sai ya ce, "What is causing Riyya feel pain during intimacy?"

Wata irin É—agowa ya yi yana kallonsa jin tambayar da ya yi masa ta rainin hankali, ya ajjiye wayar hannunsa yana kallon sa kamar tv bai ce komai ba.

Jazy ya ce, "da gaske na ke ban sani ba, ina buƙatar na san me yake causing pain ɗin."

Ya yi tsaki ya ce, "Go and ask a doctor."

"You are a doctor."

"Ka je ka tambayi Mamy, she's a gynecologist.."

Jazy ya harare sa ya ce, "Mamy fa ka ce? Ni ka daina yi min irin maganar nan bana so, ta ya zan je na tambayi Mamy irin wannan maganar? Kai É—in dai."

"Wanda ka raina ko?."

Ya yi dariya ya ce, "Ba raini bane, kawai kai É—in kai É—in ne."

Zai yi magana kenan Islaha ta hayo saman cikin yanayin da ta baro gidansu Safeera, ganin Jazy a zaune sai ta yi murmushi ta ce, "Mr Jafar."

Jafar ma ya yi murmushi "Miss Islaha, ya ki ke?."

"lafiya ƙalau. Ya aiki?."

"Alhamdu lillah. Ya mai jiki?." Ta É—an kalli Rehaan da yake kallon Jafar sannan ta ce, "ga shi nan dai."

Tunda ta shigo yake tuna zaman ts s Jedda, da yadda alaƙarsu da Ubaid ta ke, da cikin da ta zubar, da video Ubaid da koma suka dinga dawo masa daki-daki. Haushinta ya mamaye masa zuciya, ya bita da kallo har ta zo zata gifta shi sai ya ce, "ka tambaye ta, zata iya ba ka amasa."

Kafin Jazy ya katse shi ya ce, "Can you tell us what causes pain during intimacy? Do you have any idea? I know you have experience with it."

Cak ta dakata daga tafiyar da take yi tana ji kamar an soka mata kibiya, ta waiwayo ta kalle shi daidai lokacin da Jazy ya ce, "Rehaan!."

Islaha ta zuba masa ido kawai tana kallo ta kasa cewa komai, ga ɓacin ran da take ciki ga abinda ya ce mata. Ta rasa abinda zata ce masa, ta buɗe ba ki zata ba shi amsa amma ta kasa, bata san hawaye ya sakko mata ba, kawai sai ta shiga ɗaki bata ce komai ba.

Jazy ya ji haushin abinda Rehaan ya yiwa Islaha sosai, cikin fusata ya ce, "Haba Rehaan! Meye haka? Ya za ka dinga faÉ—a mata magana anyhow?."

Rehaan bai ce komai ba dan shi kaɗai ya san me yake ji a ransa in ya tuna wacece ita. Jazy ya ce, "Ray ko da ace da gaske tana wannan ɗabi'ar bai kamata ka kalle ta ka ce mata haka ba. Wannan cin fuska ne, wulaƙanci ne, tozartawa ne, tunda rayuwarta ce ta sirri, bai kamata ka dinga faɗa a gaban kowa ba. Ka kalla ka gani, kuka take yi fa. Ina guje maka lokacin da za ka yi danasani akan kalamanka, ina guje maka ranar da zaka zubar da hawaye akan wannan furucin naka Rehaan. Zata tsane ka, za ka dinga bata haushi, zata ji…” Jazy ya yi shiru cikin takaici kamar shine Islaha.

Rehaan ya yi shiru bai ce komai ba, zuciyarsa tana bugawa sosai, yana jin wani abu mai É—aci in in ya tuna waye Ubaid. Jazy ya ce, "Ban san yaushe ka koyo cin fuska ba, da ba haka ka ke ba wallahi. Ka tashi ka je ka rarrashe ta, dan ba ka kyauta ba wallahi."

Rehana maimakon ya yi magana akan Islaha sai ya canja ya ce, "Tun yaushe ake samun matsalar?."

"Wacce matsala?."

"Wacce ka tambaye ni mana."

Ya yi tsaki ya ce, "ka fara solving wannan matslar malam, ka je ka rarrashi matarka."

Rehaan ya miƙe tsaye ya ce, "matsalar Riyya itace zata zo a farko Jazy. In pain ɗin ya fara tun last two weeks, it may be normal since she is a virgin and it might ease over time, amma in har yanzu tana jin zafin, it could be caused by a lack of vaginal lubrication. Amma tambayi Mamy, sai ta yi maka recommending abubuwan da zata dinga amfami dasu. Cikina ciwo yake yi min" ya faɗa yana shiga ɗaki ya bar sa a wajan.

Jazy ya yi tsaki cike da takaicin abin Rehaan ya yiwa Islaha, gabaɗaya bai ji daɗi ba, shi kansa ya ji zafin kalaman Ray balle ita. Yana miƙewa tsaye Islaha ta fito tunawa ta bar kayanta da ta ɗauko a gidansu Islaha a ƙasa. Jazy ya kalle ta cikin tausayi ya ce, "Islaha."

Ta kalle sa da jajayen idanunta ya ce, "i'm so sorry Islaha, na san...."

Islaha ta dakatar da shi ta ce, "kar ka damu Mr Jafar, lokaci ne, saura kwanaki kaɗan komai ya ƙare, nan gaba in aka ce ya faɗa min bazai iya ba."

"Duk da haka, ki yi haƙuri." Ta yi murmushin yaƙe bata ce komai ba.

Jazy baboda ya É—auke mata damuwa da takaicin Rehaan sai ya ce, "kin shirya interview É—in nan kuwa?."

Ta É—aga masa kai ta ce, "ko yaushe a shirye nake."

"To za a yi jibi in Allah ya kaimu, za ku je guest house ku same sa a yi a can. Mun yi gama magana da shi tun a englaand."

Islaha ta É—an É—aga kai ta ce, "Shikenan Mr Jafar, Amma ina son addreess É—in a rubuce, yadda zan kaiwa Chairman."

"Zan tura miki ta email in sha Allah."

"Na gode sosai, Amma ka kasance a wajan don Allah."

"Miss ni a ranar zan bar ƙasar nan da daddare."

"Ai da safe za mu yi in sha Allah, bazan iya tolereting waÉ—annan abubuwan nasa ba, bana so collogues É—ina su ga kamar akwai wani abu a tsakanin mu, in kana nan za ka iya hana wani abun."

Ya É—aga kai ya ce, "in sha Allah zan je."

Ta yi murmushi ta ce, "na gode" daga haka ya sauka ya fita, ita kuma tana jin tsanar Rehaan na shiga zuciyarta, kuma ta yi alƙawarin sai ta mayar masa da amsa daidai shi........

Nana Haleema.

RDB3P53
Nana Haleema.

Saheer haka ya koma gidansu Sadik ransa a ɓace, ya samu Sadik da abokinsa Musaddik a zaune. Ya ajjiye key ɗin motar ya zauna ya dafe kansa.

Sadik ya ce, "ya dai, har kun dawo daga gidan?."

Ya girgiza kai ya ce, "ba mu je ba."

Saheer ya ce, "kamar ya ba ku je ba, motar ce ta lalace?."

Saheet ya ce, "babu É—aya, fasawa mu ka yi kawai. Ka same ni a gida, na wuce" ya faÉ—a yana ta shi ya fita.

Sadik ya biyo bayansa dan ya san ba lafiya ba, ya tsayar da shi ya ce, "Saheer me ye ya faru?."

Saheer cike da jin haushi ya ce, "ni yarinyar nan zata dinga faɗawa magana son ranta? Ni zata kalla ta dinga faɗa min ai Rehaan mijinta ne in ma ta yi wani abun da shi sai me, shi yake aurenta ba ni ba?. Ina faɗa mata magana tana ƙaryata ni, ƙarshe ta fita daga motar, harda cewa wallahi baza ta dawo ba."

Sadik ya buÉ—e ido cikin mamaki ya ce, "Wai islahan ce ta yi maka haka?."

Shiru ya yi bai amsa ba saboda ɓacin ran da yake ji Sadik ya ce, "Ka yabi mutum in gaɓar yabonsa ta zo. Saheer na san halin Islaha, baza ta yi maka haka kai tsaye babu dalili ba. Ko dai kai ka fusata ta? Dan ka san halin kayarka, barkono ce."

"Tambayata ta yi akan iyayenta, tana so ta san ya aka yi ta tsinci kanta a gidan marayu. Ni kuma ka
san dalilina na ƙi faɗa mata, na ce mata sai mun yi aure zan faɗa mata, ta ce min ce ita yanzu take so. Shine dai na faɗa mata abinda zata fahimta, amma ta ce ita wallahi bata yarda ba, bata taɓa jin bata yarda da ni ba sai ɗazu."

Sadik ya ce, "to kai ka faÉ—a mata gaskiya ka huta mana, tana da gaskiya fa, kowa zai so ya san iyayensa. Tunda ta san ba a gidan marayu aka haife ta ba, kuma ba tun tana jaririya aka kai ta ba, dole akwai iyayenta a waje."

Saheer yi shiru bai ce komai ba, Sadik ya ce, "Kuma ana maganar gidan marayu me ya kawo batun auren ta da Rehaan?."
Chapter 69 · 0% Book details