← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 110

Sashe 96

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ina so case ɗin nan a kawo ƙarshensa a gobe, bana so a kai ya wuce gobe Jafaar."

"Za a yi, ai ba wani case mai wahala bane, da an kama mai account É—in shikenan. So calm down, za a yi komai in sha Allah."

"Ina faɗa maka ina so a kawo ƙarshensa and you're telling me I should calm down, Jazy in ba a kawo ƙarahen case ɗin nan ba hankalina bazai kwanta ba."

Jazy ya yi dariya kamar ya tambaye shi dalili sai kuma ya share ya ce, "Okay! Zamu yi magana" ya gaÉ—a yana kashe wayar ya ajjiye.

Riyya ta ce, "Case É—in Islaha?."

Ya É—aga mata kai ya ce, "shine, kuma ya rasa lokacin da zai kira ni sai yanzu."

Ta murmusa ta ce, "amma ban taɓa jin voice ɗinsa cikin damuwa haka ba, ban taɓa jin yana magana cikin irin wanann yanayi ba sai yanzu."

Ya yi dariya ya ce, "ke kuwa matarsa fa, aka samu wani ya haÉ—a AI video da fuskarta aka watsa a duniya, dole ya damu."

"Is that means he loves her?."

Ya kalle ta ya ce, "sai yana sonta zai damu?."

"No, ban taɓa jin voice ɗinsa a haka ba, in ka ga ya shiga damuwa da damuwar wani to tabbas mutum ne mai mahimmaci a gare sa, kamar Mamy. Hakan yana nufin...." Sai bata ƙarasa ba tana kallon Jazy.

Ya miƙe tsaye ya ce, "Yana nufin me?."

"Ya karɓi aurenta a matsayin mata da miji, dan  na san da farko bai yi accepting ba."

Ya yi dariya yana girgiza kai, shi kaÉ—ai ya san irin kalaman da ya tanada waÉ—anda zai mayarwa da Rehaan a ranar da ya tabbatar yana son Islaha, shi kaÉ—ai ya san irin abinda zai faÉ—a masa dan ya tuna masa baya har ya yi danasani akan furucin da ya dinga yi akan Islaha.

Shi dai hasashensa ya nuna masa Rehaan ya faɗa tarkon ƙauna, kawai ba ya so ya fargar da shi sai ya yi nisa a cikin tafkin soyayyar, yadda yana faɗa masa zai amsa bazai musa masa ba.

Ya kalli Riyya ya ce, "mu cigaba da sallah, ki bar yayan nan na ki kawai." Ta miƙe tana dariya suka cigaba da ibada......

Nana Haleema.

RDB3P70
Nana Haleema.

Islaha ta jima tana bacci, dan bata samu bacci ba sai bayan sallar asuba hakan ya saka ta yin dogon bacci har azahar. A firgice ta farka dan a cikin baccin ta tuna da abubuwan da suke faruwa, sai ta buɗe tana bin ɗakin da kallo, komai a kashe ya ke babu haske ko kaɗan, sai ƙarar ac da take tashi a hankali, ɗakin ya yi sanyi sosai.

Waige-waige take yi tana neman wayarta amma bata gani ba, ta sauka daga kan gadon har lokacom kanta yana yi mata ciwo sosai ta shiga banÉ—aki. Bata jima sosai ba ta fito, a sanyaye take yin komai cikin mutuwar jiki da sanyin zuciya, ta canja kaya ta yi sallah.

Buɗe ƙofar aka yi hakan ya saka ta ta kalli wanda ya shigo, duk da babu haske amma tana iya ganin mutum. Safeera ce da Mamy suka kunna hasken ɗakin, Mamy ta bi Islaha da kallo ganin yadda ta rame lokaci ɗaya, fuskarta ta canja ta nuna alamun damuwa mai yawa.

Mamy ta ƙarasa ta zauna kusa da ita cikin damuwa ta ce, "Islaha are you okay?."

Islaha ta ce, "Mamy Ina yini."

Mamy ta ce, "ya jikin ki?."

Ta ɗaga kai ta ce, "na ji sauƙi."

Mamy ta ce, "taso mu je falo ki yi breakfast."

Bata son yiwa Mamy musu saboda kulawar da take bata, hakan ya saka dole ta miƙe suka fita daga ɗakin Mamy tana riƙe da hannunta.

Falon babu kowa sai ƙhamshi da yake yi mai daɗi, suka zauna Mamy ta yi serving ɗinta sannan ta miƙa mata ta ce, "ki sha tea sai ki ci abinci."

Ta karɓa ta fara shan tea ɗin, sai kuma ta kalli Safeera ta ce, "Safeera ina wayata?."

Safeera ta ce, "wayar ki tana nan, screen É—inta ya lalace, ba a ganin komai sai fari."

Mamy ta kalli Safeera ta ce, "meyasa baki faɗa min ba? Ai da sai a kawo mata wata…amma yanzu a ɗauko ta a ayi mata backup a computer, sai ta canja wata, tunda wannan ya lalace, kawo min kar a manta."

Safeera ta dinga kallon Mamy jin wai ta lalace, dan kawai screen ya yi fari sai ace waya ta lalace? Ba screen É—in kawai za a saka ta cigaba da aikinta ba? Ta gyaÉ—a kai tana aiyana masu kuÉ—i sun ji daÉ—insu, ta koma ta É—auko ta bawa Mamy Islaha dai bata ce komai ba.

Sai da Islaha ta sha tea ɗin ta ɗan ci abincin, Mamy ta bata magani ta sha dan ta ji daɗin jikinta. Mamy ta riƙe hannunta cikin sigar kwantar da hankali ta ce, "Rehaan zai ji da komai, babu abinda zai same ki. Abinda ya faru a daren jiya kar ki saka shi a ranki duk plan ne."

Islaha bata ce komai ba, sai kuka da take ji yana taho mata, ita É—auka mafarki ta yi shiyasa take neman wayarta dan ta shiga ta ga da gaske akwai abinda ya faru É—in, ashe gaskiya ne ba mafarki bane tunda ga shi Mamy ta faÉ—a.

Mamy ta É—ago fuskar ta ta ce, "kar ki yi kuka, komai zai warware."

Ta kwantar da kanta a kafaÉ—ar Mamy tana hawaye, Mamy ta shafa kanta ta ce, "Ki daina kuka." Islaha bata ce komai ba ta yi shiru tana kwance a jikin Mamy. Mamy ta ce, "Ta so mu je apartment É—ina, akwai Baffa ki da Hammanki sun zo ganinki."

Da sauri ta ɗago ta kalli Mamy, Mamy ta murmusa alamun da gaske ne abinda ta ji. Ta miƙe tsaye suka sauka tare su uku suka fita. Islaha bata bari ta kalli kowa ba, dan ta san kowa kallonta yake yi har suka shiga apartment ɗin.

Suna shiga main parlour ta ga Baffa a zaune sai Saheer da ya kame a zaune fuskarsa babu walwala ko kaÉ—an.

Islaha ta nufi inda Baffa yake ta zube a ƙasa ta ɗora kanta a guiwarsa tana kuka sosai, Baffa bai hanata ba, ya yi shiru yana jin kukanta har zuciyarsa. Ko Labiba da Hanan ne su ke kuka, baya jin kukansu har zuciyar kamar yadda yake jin na Islaaha.

Sai da ta jima tana yi sannan ya ce, "ya isa Islaha, ki bar wannan kukan ni ba shi na zo ki yi min ba, na damu da ke, ina so na gan ki shiyasa na kasa haƙuri na nemi Safeera a waya har na zo gidan nan. Ki daina kuka, ki nutsu mu yi magana."

Ta ɗago fuskar ta kaca-kaca da hawaye ta ce, "Baffa ban yi komai ba, ni ban san waye ya ɗauki video na ba, kuma abinda aka ce jiya na yi a gidan nan ban yi ba, ni ban san me ya faru ba” ta faɗa cikin ruɗewa ta manta da Baffa bai san abinda ya faru a gidan ba.

Baffa yanÉ—aga mata kai ya ce, "na sani, ki nutsu mu yi magana, in kina kuka baza ki saurare ni ba."

Ta goge hawaye sannan ya ce, "Allah ne ya rubuta miki wannan ƙaddarar, dole sai ta faru dake. Ki kwantar da hankalin ki, komai zai warware in sha Allah, ni na san ba ki aikata komai ba, duk wanda ya yi nufin cutar dake asirinsa zai tonu.”

Ta ja numfashi ta ce, "Baffa kowa a banza yake kallona, kowa ba ya yi min kallon mutunci, kowa ya ga hotona jiya, ana ta tsine min Baffa."

"Ki yi haƙuri, da gaskiya ta bayyana shikenan kowa zai zo yana ba ki haƙuri, duk wanda ya ga laifin ki a cikin rashin sani ne, ki daina kuka."

Safeera ta ce, "ka yi maya faÉ—a Baffa, saboda wannan kukan har attack ya saka ta samu."

"Subahanallahi! Ki yi haƙuri ki daina kuka, kin san kina da matsalar numfashi.”

Islaha ta juya ido ta kalli Saheer da ya ke kallon ta ta ce, "Hamma ni ban yi komai ba."

Kallon ta kawai yake yi bai ce mata komai ba, dan ko kaɗan bai so zuwa gidan ba Baffa ne ya yi masa dole sai ya rako sa, ya zo kuma sai ya ji ransa ya ɓaci gabaɗaya, bai san meyasa ya ji har ita kanta haushi take ba shi ba.

Daƙyar ya buɗe baki ya ce, "Ki daina kuka, komai zai wuce, mun kai maganar human right, suna nan suna bincike."

Mamy ta kalli Saheer dan tsaf ta san shine wanda take shirin aure in ta bar gidan, a binciken da ta saka aka yi mata har hotonsa ta gani. Ta ce, "kar ka damu, babu abinda human right zasu iya a kan case ɗin nan, wahala zasu dinga baka har sai ka gaji. Rehaan yana kan aikin case, an tabbatar min da har an gano mai account ɗin da aka fara fitar da nude ɗin, so a yau komai zai ƙare."

Saheer ya yi shiru kawai yana kallon Mamy, yadda take magana ma abin kallo ne balle fuskar da kyaun da Allah ya yi mata. Ya sauke numfashi, dan ya zamar masa dole ya yi ƙoƙarin gano wani abu kafin Rehaan ya riga shi, ya zama dole ya zama silar farin cikin Islaha ba Rehaan ba. Amma ta ya zai bi? Wa zai samu da maganar a shige masa gaba a yi komai a gama kafin Rehaan ya riga shi?.

Baffa ya dinga rarrashinta fa kalamai masu daÉ—i har ta nustu, kafin ya yi musu sallama suka fita ita kuma ta zauna a falon.

Rehaan yana ɓangaren Abba, bai san da zuwansu Baffa ba, yana zaune yana jiran Abba har ya fito ya zauna yana kallonsa ya ce, "Rehaan yarinyar nan baki ya yi yawa a kanta, kana jin ahinda ake ta faɗa akan ɗan uwanka.”

Rehaaan ya ce, "Abba duka zan yi bincike a kai, in na tabbatar abinda ya faru gaskiya ne zan yi abinda kace, amma a yanzu ka bari na cikawa Mamy alƙawarinta don Allah."
Chapter 96 · 0% Book details