← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 110

Sashe 88

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

     "In ke ce, in ma ke bace wannan ke ya dama ba mu ba, rayuwarki ki ka yaɗa a duniya ba rayuwar mu ba!."

A tare suka kalli wanda ya shigo suka ga Chairman ne da Yayansa, wanda ya kasance mai gidan tv gabaÉ—aya.

Mai gidan tv ya kalli Islaha ya ce, "Muna yabon ki a ko yaushe, ashe kema yar iska ce, bakya son cigabanmu, kuma bakya son cigaban gidan tv nan. Wacce irin ƙauna ce ba mu nuna miki ba? Wacce irin ɗaukaka ce ba ki samu a gidan nan ba?. Amma ashe cin amanarmu ki ke yi, kina ɗaukar sirrinmu da mu ke yi tare da ke kina kaiwa wasu gidajen da a ba ki kuɗi. Kin ba mu mamaki wallahi, ban yi tunanin haka daga wajanki ba."

Cikin rashin fahinta da kiÉ—ima da tashin hankali Islaha ta ce, "Me na yi?."

"Bayan hotunan ki na iskancin da ki ke aikatawa sun fito duniya, kowa ya san wacece ke, wannan bai dame ni ba saboda rayuwar ki ce, ko me za ki aikata ke ya shafa bani ba. Abinda yake gabana cin amanar da ki ka yi mana, ina so ki san na samu labarin waɗanda ki ke kaiwa sirrin mu, duk abinda abu da ya faru ko zai faru ke ki ke zuwa ki faɗa musu. Duk ɗaukakar da fuskarki take da shi a duniya, duk son da ake yi miki a ƙarƙashin gidan nan ni bazan zauna da munafuka ba...."

Chairman ya katse sa ya ce, "Yaya amma...."

Ya dakatar da shi ya ce, "Wallahi sai ta bar aikin nan, ban ga amfanin zama da munafuki ba, da zama tare da munafuki gwara zama da ɓarawo. Da kanka ka ji saƙon da ta aika ta ke cewa burinta ta ga faɗuwar gidan nan, meye ribar zama da ita?. Ai ba ita kaɗai ce wacce ta iya aiki ba, suna nan da yawa a duniya."

Ya kalli Islaha da ta ƙame ƙam ta kasa motsawa sai juya ido take yi ya ce, "daga yau babu ke babu aiki a nan, na sallame ki, ki je ki fara yiwa sauran gidajen talabijin ɗin da ki ke kaiwa sirrin mu aiki, ni kam bani da buƙatar ki a nan. Sannan abinda ki ka aikata kin cuci kan ki, duniya gabaɗaya akan ki kaɗai ta ke magana, ana yi miki tofin Allah ya tsine!" Yana gama faɗa ya futa daga office ɗin.

Chairman ya kalli Islaha ya ce, "ki yi haƙuri, ina zuwa" ya faɗa yana ficewa da sauri.

Islaha ta kalli Safeera cikin sanyin jiki ta ce, "Me na yi, Safeera me na aikata?."

Safeera ta riƙe tana hawaye ta ce, "ki zo mu bar nan, zaman mu a nan ba shi da amfani."

Wayar Islaha ce ta fara ƙara Safeera ta kalla ta ga Saheer ne, ta ɗauka ya ce, "Islaha me yake faruwa ne haka, waɗanne hotuna ne suke yawo a duniya?."

Safeera ta ce, "Safeera ce Hamma."

"Safeera ina Islaha take? Me ya faru?."

"Wallahi ba musani ba, kawai mun wayi gari da waÉ—annan abubuwan. Yanzu mai gidan nan ya fita, yana ta faÉ—a wai tana kwashe sirrinsu ta kai gidan wata tv. Yanzu haka ya ce ta bar masa nan ya daina aiki da ita."

"Subahanallahi! Safeera ina Islahan ta ke?."

"Gata nan, bata cikin yanayin da zata iya magana shiyasa na É—auka."

"Kina ji, ku jira ni gani nan zan zo na É—auke ku" ya faÉ—a yana yanke wayar.

Safeera ta saka mata wayarta a jaka ta É—auki handbag É—in ta ce, "ki tashi mu tafi, zaman mu a nan ba shi da wani amfani."

Islaha ta kasa cewa komai, ko hawayen ma ta kasa yi gabaɗaya. Safeera ta riƙe hannunta suka miƙe tsaye, suka fito compound ɗin gidan kowa yana kallon ta.

Handbag ɗinta da take hannun Safeera ta saka hannu a ciki ta ɗauko wayarta, ta shiga media tana duba abubuwan da ake faɗa a kanta. Salati kawai take yi, ganin yadda hotunan tsaraicinta muraran suke yawo a duniya, ga kalamai masu muni da ake yi aka iyayenta, ana cewa daman cikin shege aka yi aka haife ta. Ƙafafunta suka fara rawa, ganin irin munanan kalaman da ake yi a kanta. Ta zube a wajan, ta cillar da wayar ta daki bango ta faɗi a ƙasa, sai a lokacin ta samu damar sakin kuka mai matuƙar ƙarfi.

Safeera tana kuka ta bi bayanta suka durƙushe a tare ta riƙe ta ta ce, "Ki yi haƙuri Islaha, ki daina kuka, ki tashi mu tafi kowa kallon mu ya ke yi."

Jikinta yana rawa saboda kuka, ta kasa magana sai kuka mai sauti da yake amsa kuwa a wajen, Safera ta riƙe ta sosai tana kuka itama, dan bata da abinda zata ce ba. Islaha kasa cewa komai, kuka take yi mai matuƙar ƙarfi tana ji zuciyarta tana bugawa da gudu.

"Safeera da gaske ni ce a hotunan nan, da gaske cikin shege aka yi aka haife ni, da gaske ni ce ko?."

Abinda take maimaitawa kenan tana kuka, Safeera tana ta ya ta kuka tana cewa, "ƙarya ne, ba ke bace, AI ne ya haɗa komai, don Allah ki daina kuka." Bata ce komai ba numfashinta da yake fizga da ƙarfi, ta kasa magana saboda tashin hankali.

A lokacin Saheer da Sadik suka ƙaraso wajan, ganin yanayin da take ciki tana kuka cikin fiyar hayyaci ya saka hankalin Saheer ya tashi, ya tsuguna a gabanta ya ce, "Islaha ki daina kuka, ki yi haƙuri mu je."

Jin maganarsa a kusa da ita sai ta zabura kamar mai taɓin hankali ta kalle sa ta ce, "Hamma ni ce ko? Kaima ka ga hotunan, da gaske ni ɗin ce?."

Ya girgiza mata kai ya ce, "ki daina kuka ki zo mu tafi, taso" ya faɗa yana miƙewa tsaye.

Safeera ta ɗago Islaha tana riƙe da ita ta kalli Saheer ta ce, "ga wayar ta can ta buga da ƙasa, ka riƙe mata."

Ya ɗauki wayar ya riƙe, a lokacin ɗaya daga cikin ma'aikatan ya ƙaraso inda suke ya ce, "Gaskiya Islaha kin ɓata wayon ki, ban yi tunanin haka ki ke ba, ban taɓa zaton haka halin ki yake ba. A haka kamar mutuniyar kirki, ashe ke ɗin ma ƴar iska ce lamba ɗaya. Haba! Daman kwana biyu muna ta ganin canji a tare dake, ga iphone 17 a hannunki, ga mota daga wannan sai wannan, yau a sauke ki a fara, gobe a baƙa. Ashe da walakin goro a miya, ashe ban gishiri in ba ka manda ku je yi, tunda ga shi har hotunan ki sun fito."

Hawaye ya ziraro daga idanunta, Saheer ya juya a fusace zai yi magana ta ce, "mu je hamma." Ya yi shiru suka shiga mota suka tafi.

        "Mama! Mama!!."

Sameer ya faɗa yana ƙwala maya kira da ƙarfi, dan ta ji a duk inda take. Mama ta fito daga banɗaki tace, "meye ka ke kirana haka kamar kana bina bashi?."

Ya nuna mata wayar ya ce, "kalli ki ga, wannan ba yarinyar da take tare da Rehaan ba ce?."

Mama ta karɓa tana dubawa sannamta wara ido ta ce, "itace mana, wannan Islaha ce. Mun shiga uku, yarinyar nan daman haka take?."

Sameer ya ce, "gashi kuwa kin gani. ÆŠaya daga cikin abokan iskancinta ne ya yi mata hotuna da video ya yaÉ—a a duniya. Kalli wannan, tare suke a kwnace fa" ya faÉ—a tana nuna mata wani.

Mama ta kawar da kai ta ce, "ƙazantar ta yi muni, bazan iya gani ba."

"Gaskiya bata da kunya, iskancin na ta mai lasisi ne. Dan kin san in dai video ko hotuna suka fara fita, tabbacin iskancin lamba É—aya ne."

Mama ta girgiza kai ta ce, "ai ni daman na san haka yarinyar take, an bani labarinta kaf tun kafin ta zo nan, har ƙasashen waje ake fita da ita a biyata. Ƙwanƙwararriyar ƴar iska ce fa, duk buɗewar idon Rehaan ta fisa wallahi."

"Ta zubar mana da mutunci dai, duk da ba a san sirikar gidan nan bace, amma mu ai mun sani. Ko banza mun kalli banza, mun fara ganin babban sirrin Rehaan, dan gaskiya tana da gashi Mama" ya faÉ—a yana fita daga É—akin.

Mama ta yi hanzarin É—aukar waya ta kira Abba, yana É—auka ta ce, "ka fita ne?." Amsar da ya bata ya saka ta kashe wayar ta skaa hijjab ta fita.

Tana shiga ɓangarensa ta fashe da kuka, Abba ya ɗago ya kalle ta cikin mamaki ya ce, "Saddiƙa lafiya?."

Mama tana goge hawaye ta ce, "wani mummunan abu ne yake faruwa."

"Wanne irin abu ne wannan da zai saka ki kuka a safiyar nan?."

Mama ta goge hawayenta, ta yi shiru bata ce komai ba. Abba ya ce, "Ki faÉ—a min meye, kin bar cikin tunani da faÉ—uwar gaba."

Mama ta basa wayarta ta ce, "kalli ka ga."

Abba ya karɓa yana gani, sai ya kalle ta ya sake kallon wayar sanann ya ce, "wannan ba Islaha bace, matar Rehaan?."

"Itace wallahi."

"Subahanallah! Meye hakan, hotunanta da maza kala-kala nake gani fa?."

"Ita ɗin ce wallahi. Yarinyar nan ashe haka take, sai yanzu nake jin asalin labarinta, har ƙasar waje ta je tana yawon iskanci. Na samu labarin har blue film an biyata ta yi, babu abinda bata aikata a duniya ba."

Abba ya ajjiye wayar cikin faÉ—uwar gaba ya ce, "da gaske ita É—in ce?."

"Itace wallahi, an tabbatar min da zata iya aikata fiye da haka, yarinyar da ta ɗauki blue film meye baza ta yi ba!. Lokacin da ka karɓi auren ta baka yi bincike yadda ya kamata ba, dan wallahi bata dace da Rehaan ba kwata-kwata."

Abba ya yi shiru sannan ya ce, "Ikon Allah! Anya itace kuwa? Kin san yanzu zamanin haɗa hotuna mu ke ciki.”

“tunda ka ji na rantse ka yarda kawai, wallahi itace.”

Wannan wanne irin zubarwa da kai mutunci ne?."

"Da naka mutuncin ma, tunda sirikar gidan nan ce. Allah na gode maka da ba a san matar Rehaan bace, wannan taɓargazar ai sai ta saka Rehaan ya samu matsala da kasuwancinsa."
Chapter 88 · 0% Book details