← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 110

Sashe 76

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safeera ta yi dariya ta ce, "Ke kowa yana son inda zai ji daɗi, daga shigar ki gidan Rehaan zuwa yanzu nawa na samu? Ranar da na je Mamy dubu ɗari ta bani na sha ice cream, dole na miƙe tsaye da roƙon Allah." Islaha ta yi mata banza bata sake tanka mata ba.

A nan suka yi sallar azahar, bayan an idar aka cigaba da shirye-shirye dan ƙarfe huɗu da rabi aka yi za a fara hira. Bayan an idar da sallah aka hau mota aka tafi.

Rehaan kamar yadda Jazy ya takura masa ana idar da sallar juma'a suka wuce guest house ba tare da ya san me zai yi a cikin gidan ba. Suna shiga cikin parlour ya ce, "wai me zan yi a gidan nan da ka takura sai na zo?."

Jazy ya ce, "ai na faɗa maka, akwai channel ɗin da zasu yi interview da kai a nan, ka daina ƙoƙarin nuna min kamar ka manta."

"mtsww! Ka raina min hankali, kawai akan interview ka saka na taho nan ko wajan Mamy ban je ba?."

"ka ga! Kar ka kawo mana matsala don Allah, mun yi da kai kuma ka amince tun a Uk, dan haka ka je ka huta, saboda wannan shegen baccin na ka ya saka na ce sai bayan sallar la'asar."

"Sai aka ce maka na shiryawa amsa tambaya?."

"Kawai ka je." Rehaan bai ce masa komai ba ya shiga ciki.

Lokacin da motarsu Islaha ta tsaya a ƙofar gidan duk fito daga motar suna kallon gidan da aka tsaya. Suna tsaye sai ɗaya daga cikin guard ɗinsa ya fito daga gidan ya ce, "ku shigo." Suka bi bayansa Islaha da Safeera sune a can ƙarshe gabaɗaya jilkinta a sanyaye yake.

Safeera ta ce, "ki saki jikin ki mana, kar a fahimci akwai matsala a tsakaninku."

Islaha ta ce, "Rainin hankali ne bana so, yanzu sai ya yi creating abinda zai ɓata min rai wallahi."

Safeera ta ce, "ki daure, ki nuna kamar baki shi ba."

Chairaman ya waiwayo ya kalli Isalaha ya ce, "ki ɗago ƙafa Islaha." Suka ƙarasa aka buɗe musu ƙaton falon da khamshi da ac yake tashi a cikinsa. Basu zauna ba, masu camera suka haɗawa aka ba da light da komai ya zama ready sannan aka zauna zaman jiransa.

Yana ciki a zaune yana sanye da blue black É—in suit yana meeting throw video call, ya É—an jima a haka kafin ya rufe laptop É—in. Yana rufe laptop É—in Jazy ya ce, "suna jiran ka."

Rehaan ya ɗaga kai bai ce komai ba, dan kawai iya cewa Jazy a'a ba ne; amma da bazai yi ba wallahi, to babu yadda za a yi Jazy ya nemi abu a wajensa ya kasa yi masa, shiyasa ya amince har aka zo yau. Rehaan Ya miƙe tsaye yana gyara zaman rigarsa, Jazy ya rigasa fitowa duk suka miƙe tsaye har Islaha.

Jazy ya kalle su fuska ba yabo babu fallasa, suka gaisa da Chairman da Saleem da kuma camera mans. Sai ya kalli Islaha ta yi murmushi ta ce, "Good day Mr Jafar."

"How are you" ya faÉ—a yana zama a kan kujera kamar bai saba da ita sosai ba.

A lokacin Rehaan ya fito duk suka juya suka kallonsa yayin da shi ba su yake kallo ba wayarsa yake dannawa da alamun yana mayar da amsa. Sai kuma ya tsaya cak ya saka wayar a kunne tare da saka hannu a aljihu yana magana da turanci, mintina goma ya yi yana waya a tsaye, kafin ya kashe ya sake kiran wani ya canja yare zuwa hindi.

"Mtsww! Sai ya ɓata mana lokaci" Islaha ta faɗa ƙasa-ƙasa tana kallon sa.  Safeera ta kalle ta ta ce, "Don Allah ki yi shiru."

Ta ɗauke kai daga kallonsa a lokacin ya ɗago ido ya kalle su dukkansu, bai ga fuskar ta ba dan ta kawar da kai, ya ƙaraso cikin falon. Ya fara miƙawa Chairman hannu alamun su gaisa, jikinsa har rawa yake yi suka gaisa, ya bawa Saleem hannu suka gaisa, ya miƙawa Safeera hannu alamun su gaisa, sai ta kasa bashi hannunta saboda bata saba ba, kuma kamar ta ci amanar ƙawarta in ta gaisa da mijinta. Chairman ya ja mayafinta kaɗan alamun ta ba shi hannu mana, dole suka gaisa da Rehaan. Islaha sai ta ƙirƙiri gyaran mayafi dan kar ma ya bata hannu, ta yi nasara kuwa, ya tsallake ta ya samu waje ya zauna ya ɗora ƙafa kan ɗaya.

Ya nuna musu wajen zama ya ce, "Have a seat."

Sai sannan duk suka zauna Rehaan ya haÉ—e hannayensa waje É—aya ya ce, "so what next? Who is the presenter?...." Ya kalli agogon hannunsa ya ce, "Kuna da mintina sha biyar."

Chairman ya kalli Islaha da tunda Rehana ya shigo ta haɗe rai, bata ba shi hannu sun gaisa ba kuma bata gaishe ba. Chairman ya yi mata alamun ta miƙe ta gabatar da kanta. Sai ta yi ajiyar zuciya ta sauke numfashi ta miƙe tsaye ta ce, "ni ce. Sunana Islaha Muhammad Maddibo, daga toran giwa channel."

Muryar ta ya ji har zuciyarsa, ya ɗaga ido yana kalllonta, dan yadda ya haddace muryar tsiwar nan ko a cikin mata dubu ya ji muryarta zai gane, ita kuma taƙi yarda su haɗa ido ta kawar da kanta.

Rehaan ya kalli Jazy shima shi yake kallo, ya sake kallo Islaha sai ya yi shiru na wani lokaci. Gajiya ta yi da tsayuwa har ta juyo ta kalle sa, ta ga ba ita yake kallo ba, amma tana kallonsa suka haÉ—a ido ta É—auke ido ta kawar gefe.

Rehaan ya ce, "Okay, Can we start?."

Islaha ta zauna aka kunna light da camera da sound yadda ya kamata.

Chairman ya kalli Islaha ya ce, "Are you ready?."

Ta É—aga kai ta ce, "Yeah."

"Okay 1,2,3 start."

"Assalamu alaikum ma du kallo da sauraren wannan shiri na mu mai farin jini, shirin da yake ɗauko manya da ƙananun ƴan kasuwa da ma'aikata dan tattaunawa da su akan rayuwarsu, nasara da kuma ƙalubale."

"A yau shirin na mu ya yi babban kamu, ya ɗauko babban kifi a cikin ruwa, ya shiga lungu da saƙo ya ɗauko ɗaya tamkar da dubu. Yadda ruwa yake wahala a cikin sahara haka baƙonmu yake da wahalar samu, shi dai wanda mutane suke mararin ji da gani, suke burin ganinsa a cikin wannan shirin na mu. Kafin na faɗa mu ku waye, zamu kalli tallah mu dawo, Kamar dai kullum ni ce ta ku, Islaha Muhammad Maddibo."

Tunda ta fara magana yake kallon ta, yadda take maganar babu cracking, babu tsoro, tana yi tana smiling abin ya burgesa sosai, har yana tunanin ashe ba iya rashin kunya ta tsaya ba tana da skills. Amma da yake ita ce ba wata macen da zai yaba mata bace, sai ya taɓe baki amma bai daina kallon ta ba.

"Na san kun ƙagu ku ji waye wannan baƙon na mu, nima na ƙagu na sanar da ku. Baƙon bamu ba kowa bane sai Alhaji, ko na ce Sir, ko na ce Mr Rehaan AbdulAziz Yola, wanda aka fi sani da Ray. shugaba, kuma mamallakin duk wata ma'aikata da ta fara da RAY."

A lokacin ta juyo ta kalle sa ta ce, "Ranka ya daÉ—e barka da zuwa wannan shiri na mu mai albarka."

Kamar bazai amsa ba sai kallonta da yake yi, ba komai yake tunawa ba sai yadda idanunta suka fito a ɗazu, da yadda take shan madara bakinta duk ya ɓaci da madarar. Maimakon ya amsa sai ya yi murmushi sai kuma ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Barka."

Islaha ta ce, "Mutane da yawa suna cewa Mr Rehaan ba ya jin fulatanci balle yaren Hausa da ya tsallako ya shigo cikin garinmu na Yola, da gaske ne Mr Rehaan ba ya jin Fulfulde?."

Ya yi shiru kamar ba zai amsa ba sai ya ce, "Ba da hausa ki ke magana ba, ya aka yi na gane me ki ka ce?" Ya bata amsa da fulfulde.

Ta yi murmushi ta ce, "Kasancewar wannan shine karo na farko da ka fara hira da kai da harshen hausa, masu kallonmu zasu so su ji meyasa Mr Rehaan bai taɓa hira da yarensa ba?."

"Lokaci ne bai yi ba."

"ÆŠaukakarka ta zo lokaci É—aya, har ta kai ta kawo a cikin Yola in za a yi kwatance da matasa masu É—aukaka da kai ake farawa. Mr Rehaan meye matakin nasarar ka a rayuwa?."

"Iyayena and...."

Ya dakata yana É—auko bank cheque daga aljihun coat É—insa ya kalli Islaha ya ce, "Just tell me what you want from me, i promise i will give it to you, no matter how much it is."

Islaha jin ya koma magana da english sai ta kalle shi, ba dan a gaban camera take ba sai ta faÉ—a masa me zata yi da kuÉ—insa, amma sai ta ce, "Na zo nan saboda interview kawai Sir, ba dan a bani kuÉ—i ba."

Ya yi murmushi ya ajjiye cheaque É—in sannan ya ce, "The secret of my success is that, i never miss an opportunity, kamar dai ke."

Islaha ta yi murmushi ta ce, "I'm sorry Sir, hausar za ka É—an koma."

Yadda take magana kawai yake kallo, kamar ba ita mara kunyar nan ta apartment É—insa ba, ta nutsu tana murmushi kamar ba ita ba.

Islaha ta ce, "da yawan masu kuɗi in zasu kawo cigaba ƙasar nigeria suna farawa ne daga Abuja, Lagos da sauran garurun da suke kudancin nigeria da suka fi mu yawan kamfanoni. Babban asibitin da ka buɗe a cikin garin Yola, me ya ja hankalin ka har ka kawo babban asibitin da ake ƙiyasin ya fi ko wanne girma da tsari a nigeria cikin Yola?."

"Yola garina ne, so bani da inda ya Yola."

"Kasancewar ka ƙwararren likita a fannin tiyata, meyasa Mr Rehaan ba ya zama asibitin dan taimakawa ƙasarsa, bayan kowa ya san yana daga cikin likitocin da ake ji dasu a duniya?."

"Bani da lokaci."

"jama a da yawa suna yawan cewa ba ka yi kama da fulani ba, kuma gashi ka yi magana da fulfulde, za mu so mu a ina ka haÉ—a jini da fulani?."

"Babana fulani ne."

"Mama fa?."

"hindi."
Chapter 76 · 0% Book details