Sashe 35
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunanin yadda bakinta ya kasance a cikin nasa ya so ya rinjayi addu'ar da ya ke yi, sai yi yi saurin kawar da tunanin, ya sake lumshe ido yana addu'a. Daƙyar ya iya zama har aka yi sallar asuba, a prayer room ɗin bacci ya ɗauke sa ba tare da ya sani ba.
Gari yana wayewa labaran ƙarfe shida na safe da abinda aka fara kenan, hotunan motar sun baza duniya, da yadda aka yiwa motar kaca-kaca da bullet gashi kuma ta ƙone.
Duk mutanen gidan a waya suka ga abinda yake faruwa, hankalin Mamy ya tashi matuƙa, tun ƙarfe bakwai na safe ta kasa komawa bacci, ta shiga wajan Rehaan ya fi sau babu adadi amma sai ta tarar bacci suke yi.
Abba ma sai da ya kira Shams ya zo har gida, sannan Abba ya ce, "Me ya same su? Ina ku ka je a daren har haka ya faru?."
Shams ya ce, "mun je gidan Sir Jafar ne."
Abba ya ce, "shi da wa?."
Shams ya ce, "shi da madam, a hanyar mu ta dawowa abin ya riske mu."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Amma babu abinda ya samu Rehaan ko, meyasa baka sanar damu tun a dare ba?" Mamy ta faÉ—a hankali a tashe tana kallonsa.
Ya ce, "shi ya ce kar na sanar da kowa, da safe za ku ji labari. Babu abinda ya same shi, ita ce dai ta É—an samu É—aukewar numfashi shine muka je asibiti."
Abba ya ce, "Amma an kama su ko?."
"Har yanzu ba a same su ba, ana kan aikin hakan."
Mamy kamar zata yi kuka ta ce, "Me ya fitar da shi a daren nan? Me ya je yi gidan Jafar?."
Shams ya ce, "Ban sani ba Mamy, amma da ya shiga ya É—an jima kafin ya fito."
Mamy ta fara kuka tana cewa, "Rehaan ba ya jin magana, na hana shi fita babu security amma ya ƙi ji. Tsakani da Allah ya fita da daddare a irin nan lokacin ba dole a yi ƙoƙarin kashe shi ba?."
Shams ya ce, "nima na ce mu tafi da su ya ce no need."
Abba ya ce, "Shikenan Shams. Amma daga yau in zai yi irin wannan fitar duk dare ka sanar dani ka ji?."
Cikin girmamawa ya amsa sannan ya ce, "Æ´an jarida suna son magana dani akan abinda ya faru, zan iya magana dasu?."
Abba ya ce, "ka yi magana dasu ɗin, ka tabbatarwa da mutane yana cikin ƙoshin lafiya." Shams ya amsa sannan ya fita.
Mamy da take ta kuka Abba ya ce, "Ki daina wanann kukan, ki yi haƙuri ya farka mu ji abinda ya faru."
Mamy ta goge idanunta ta ce, "Me ya fitar da shi da dadare kuma shi kaÉ—ai? Me zai je ya yi a gidan Jafar a cikin daren?. Yanzu da sun kashe min shi ba?."
Abba ya murmusa ya ce, "basu kashe shi ba, kuma baza su kashe shi ba sai lokacinsa ya yi. Ki yi haƙuri."
A lokacin Abba ya dinga amsa kiran wayar jajen abinda ya faru, labari babu inda bai zaga a duniya ba, waÉ—anda basa Nigeria abokan aikinsa duk sun gani ana ta nemansa a waya an kasa samu.
_Rehaan yola yana cikin ƙoshin lafiya, bayan tattaunawa da muka yi da babban na hannun damansa Shams, ya tabbatar mana da yana cikin ƙoshin lafiya babu abinda ya same su. Sai dai har yanzu ba a yi nasarar cafke waɗanda suka kai masa harin ba, amma ƙoƙarin hakan._
Abinda yake ta yaÉ—uwa kenan bayan hira da Shams, hankalin abokan cinikinsa ya É—an kwanta, dan kowa ya san shi da Shams, sai dai har lokacin an kasa samun Rehaan a waya.
Islaha sai ƙarfe tara na safe ta buɗe ido, ta miƙe zaune a hankali tana tuna abubuwan da suka faru. Gabanta ya faɗi ta ware ido ta bi falon da kallo ta tabbatar a cikinsa take, ta kalli kanta ta ganta daga ita dai vest kanta ko ɗankwali babu. Ita dai ta san daga lokacin da aka fara harbin motar bata sake sanin abinda ya faru ba.
Ta kalli agogo ta ga safiya tayi sosai, ta miƙe dan bata yi sallah ba ta hau saama, ta shiga ɗaki ta yi alwala ta yi sallah ta zauna tana tunanin duk abinda ya faru.
Tana iya tuna lokacin da ya jawota ta yi ƙasa saboda harbi, ya riƙeta ita kuma ta kwantar da kanta a ƙirjinsa cikin tsoro. Daga lokacin bata san abinda ya faru ba, ta dai san a mota suke, kuma ta san da hijjab a jikinta, amma yanzu ta ganta a falo kuma babu hijjab. Ta sake kallon kanta dan ko bra bata saka ba, iya vest ɗin ce a jikinta sai hijjab, tunda ta yi shirin bacci ta ga zai fita, kuma bata saba kwanciya da bra ba.
"Haka kawai sai ya cire min hijjab?" Ta faɗa cikin jin haushi, sai kuma ta yi tsaki ta miƙe ta shiga wanka har lokacin ƙirjinta bai daina bugawa ba saboda tsoron harbe-harben da aka dinga.
Sai da ta fito ta shirya sannan ta kula da wayarta da take ajjiye wacce ta bari bata fita da ita ba. Ta É—auki wayar ta ga tarin missed call da yawa, Saheer, Safeera, Saleem, Chairman da Baffa.
Baffa ta fara kira, aka yi rashin sa'a bai É—auka ba sai ta kira Saheer. Yana É—auka ya ce, "Islaha kina lafiya, dake a cikin motar da aka kai harin?.
" Islaha ta yi ajiyar zuciya, a lokacin ta tabbatar da maganar ta gama baza duniya.
A sanyaye ta ce, "Eh dani a ciki, amma ina lafiya."
Sai kuma ta ji muryarsa ta canja ba kamar yadda ya yi magana a farko cikin ruÉ—ewa ba, ya ce, "tare ku ka fita kenan?."
Islaha ta ce, "ina jin tsoro gidan ne, da zai fita shine kawai na bi shi, ashe rabon wannan abun ne."
"Okay, tunda lafiya ki ke haka mu ke fata. Daman shi ance yana lafiya." Bata amsa ba ta yi shiru dan ita bata san me zata ce ba.
Saheer ya ce, "za ki iya fitowa yau?."
Islaha ta É—an yi shiru kafin ta ce, "zan iya, amma sai zuwa anjima." Bai ce komai ba ya yanke wayar ta bi wayar da kallo dan ta san kishi yake yi akan sun fita tare, ta yi shiru dan ita bata san me zata ce masa akan hakan ba, ta yi shiru tana tunanin abinda ya kamata.
Chairman ta kira yana É—auka ya ce, "Islaha lafiya yau ba ki shigo ba? Ga labarai masu kyau da ya kamata ace ke ki ka hau kai amma ban gan ki ba."
Ba ta bashi amsar farko ba ta ce, "Ina kawana."
"Lafiya lau."
"na É—an samu attack ne jiya, ban farka ba sai yanzu."
"Ayya, Allah ya ƙara lafiya." Ta amsa da amin sannan suka yi sallama.
Zata kira Safeera kenan sai ga kiranta ya shigo, itama tambatar farko akan harin ta bata labarin duk abinda ya faru.
Safeera ta ce, "Allah ya yi da kwanan ku a gaba. Ana ta yaÉ—awa an kai masa hari, ashe har ke aka kai wa harin. Chairman yana ta neman ki kamar ke kaÉ—ai ce presenter a gidan, sai da ya gaji sannan Saleem ya hau. Bai san tare aka kusa kashe ku ba."
"Yanzu muka gama waya dashi."
"Allah ya kiyaye gaba. In na tashi daga aiki zan zo, sai dai bana so na zo a hanani shigowa."
"Ki zo kawai, baza a hana ki ba." Daga haka suka yi sallama ta kashe wayar.
Rehaan bai farka ba sai bayan sallar azahar, ya miƙe duk jikinsa yana yi masa ciwo saboda kwanciyar kan carpet, ya fito daga prayer room ɗin ya zauna a gefen gado yana shafa kansa.
Wayarsa yake nema sai kuma ya tuna ta faɗi a motar kuma yana da tabbacin ta ƙone. Ya sauke numfashi rashin mafita, ya miƙe ya shiga wanka. Sai da ya shirya tsaf sannan ya fito, ya yi sallar azahar ya ɗan zauna yana tuna abubuwan da suka faru.
Sai kuma ya miƙe ya fito falon a lokacin Mamy da Abba suka shigo. Mamy tana ganinsa ta nufe sa ta riƙe hannunsa ta ce, "Kana lafiya?."
Ya É—aga mata kai ya ce, "lafiya lau Mamy."
Suka zauna a tare Abba ya ce, "Tun É—azu nake jiran tashin ka amma shiru, Ina fatan babu abinda ya same ka?."
Kamar ba ya son magana ya É—aga kai ya ce, "Babu komai Abba, bacci ne kawai."
"Ya aka yi hakan ya faru?."
"Ban sani ba Abba, kawai mun ga an zagaye mu an fara harbi."
"Me ya fitar da kai a wannan lokacin, bayan ka san yanayin da ake ciki?."
Ya sauke nunfashi ya ce, "na je wajan Riyya ne."
Abba ya ce, "kawai a cikin daren zuciyarka ta faÉ—a maka ka je wajanta? Ka rasa lokacin zuwa wajanta sai da daddare?."
Ya yi shiru bai ce komai ba, dan bazai iya faÉ—awa Abba dalilin zuwan ba, yana jin kunya sosai.
Abba ya ce, "dan ganganci, ƙarfe ɗaya na dare ka saka a ɗauko mota ka fita? Kuma dan shirme sai ka fita kai kaɗai babu masu kula da kai?. Yanzu in ba dan Allah ya saka motar bullet prove bace da ya kenan?." Kansa yana ƙasa bai ce komai ba yana jin faɗan da Abba yake yi.
Abba ya ce, "Ka ga yadda motar ta ƙone?."
Ya girgiza kai ya ce, "ban gani ba."
"Ga labari nan ya cika duniya, har yanzu mutane basu da tabbacin kana lafiya."
"wayata ta ƙone a motar, sai na nutsu."
Abba ya ɗuako wayarsa ya nuna masa yadda motar ta yi, Rehaan ya dinga kallon motar kafin Abba ya ce, "kana ganin yadda aka ƙona motar, da da kai a ciki haka zasu ƙona ka saboda ganganci irin naka." Shi dai kallon motar yake yi, dan ta ƙone kam sosai.
Abba ya ce, "Kar ka sake yin wannan gangancin, wannan Allah ya kiyaye, kar na sake ji ka fita da daddare, in fitar ta zama dole ka tafi da jami'an tsaro, ka ji?."
Ray ya É—aga kai cikin gamsuwa ya ce, "in sha Allah."