Sashe 92
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Umma ta kalli Daada ta ce, "Kar ki amince ta cigaba da zama Daada, na rantse da girman Allah na ga abinda ban taɓa gani ba a wajan Salman sai da yarinyar nan ta zo.
Salman bai san ya ce ina son mace ba sai ita, har rungumar ta fa yake yi, in ba wanda aka koya ba ta ya Salman da yake da matsala zai yi haka?."
Daada ta ce, "bar ni da shi, ni na haÉ—a auren kuma sai na raba shi."
Nana Haleema.
RDB3P67
Nana Haleema.
Rehaan daf da zasu shiga apartment ɗinsa ya saki hannunta ya shiga ciki, itama sanyaye ta shiga ta tsaya a jikin ƙofa tana sauke numfashi wahala da tension da ciwon kai.
Bata taɓa jin kunya a rayuwarta kamar haka ba, bata taɓa jin ƙuncin zuciya kamar yadda take ji ba, ko lokacin da ta bar Hamma ta auri Rehaan bata ji abinda take ji a lokacin ba.
Ta kalli Rehaan da ya ke hawa sama bai ce mata komai ba, ta samu waje ta zauna ta yi shiru tana tunanin meyasa bai sake ta ba kamar yadda Daada ta nema?.
Islaha ta yi tagumi ta rasa abinda yake yi mata daÉ—i gabaÉ—aya. Na farko so ta ke ta tabbatar da jikinta ne ko kuma ba ita bace, ta kasa tsayawa ta yiwa videon kallon tsaf, tana so in ta kalla sai ta je ta kalli kanta a mirror ta ga ya jikinta ya ke, akwai banbanci da na wayar ko babu.
Tunawa da Safeera tana wajan Mamy sai ta miƙe ta koma wajan Mamy, Mamy tana ganinta ta ce, "zo ki zauna." Islaha ta kusa da ita Mamy ta ce, "Kar ki damu, Rehaan bazai sake ki ba babu abinda zai faru." Islaha ta kasa magana, ta sunkuyar da kanta ƙasa bata ce komai ba.
Mamy ta ce, "Safeera ki haÉ—a mata tea ta sha, ko zata ji daÉ—i."
Islaha cikin dashshiyar murya ta ce, "bazan iya sha ba."
Mamy ta ce, "za ki iya, Safeera kawo mata."
Safeer ta miƙe zuwa dining da ta ga komai akwai, ta zuba mata rabin kofi ta kawo mata. Mamy ce ta yi nata dole sai da ta sha ba dan tana so ta sha ɗin ba.
Wayar ce take vibrating, duk da screen ɗin wayar ya ɗauke amma waya tana shigowa, kuma in ka san kanta zaka iya ɗaukar wayar har ka amsa. Screen ne dai ya ɗauke, tun buga ta da ƙasa da ta yi sai dai ka ji vibrating amma screen ya tashi aiki.
Safeera ta É—aga wayar Islaha ta ji muryar Baffa ya ce, "Islaha kina ina, ina so na ganki."
Safeera ta ce, "Baffa Safeera ce."
"Safeera ina Islahan?."
"Gata nan Baffa, bata jin daÉ—i ne."
"Ya Allah! Kuna ina?."
"Muna gidan da take."
"Ina so na ganta Safeera, wannan abubuwan da suka faru ina so na ganta ido da ido, na san bata jin daÉ—i sosai."
Safeera ta kalli Islaha ta ce, "Gata Baffa, ku yi magana."
Safeera bawa Islaha wayar ta saka a kunne ta ce, "Baffa."
Baffa ya ce, "Islaha ya jikin na ki?."
Maimakon ta bashi amsa sai ta fashe masa da kuka Baffa ya ce, "ki bar kuka Islaha."
"Baffa ni ban san yaushe aka yi min video ba, wallahi ban san an yi ba."
"Ki daina kuka, Hamman ki ya faɗa min an shigar da ƙara, za a nemo wanda ya yi wannan aika-aikar, ko waye sai an hukunta shi, sai ya girbi abinda ya shuka."
Hawaye ya zubo mata ta goge ta ce, "kowa maganata yake yi, ana ta tsine min Baffa, kowa na duniya indai yana da wayar hannu ya ga tsiraina, kowa a fanko yake kallona Baffa, ana ta zagin iyayena. In sun mutu na san ana ta tashinsu a kabari ana cewa ga abinda Æ´arsu ta yi. Zuciyata zafi take yi min."
"Ki yi haƙuri Islaha, ki daina kuka Allah yana tare dake a ko yaushe. In ma an yi wannan abun da a tozarta ki Allah bazai bari ki tozarta ba, zai ba ki kariya in sha Allah."
"Baffa ai na tozarta, an gama tozarta ni a duniya, an gama wulaƙanta ni, babu tozartar da ta kai wannan a duniya. Baffa ji nake kamar na kashe kaina na huta, so nake na daina numfashi ko zan ji daɗi Baffaaaa!" Ta ƙarasa faɗa tana jan sunansa cikin kuka.
Baffa ya ce, "Islaha ki daina wannan maganar, kar na sake ji kin yi maganar za ki kashe kan ki, Allah zai kawo miki mafita in Allah ya amince."
Saheer da yake kusa da Baffa ya ce, "Islaha ki nutsu, komai zai warware, ni na tabbatar ba ke bace."
Ta ce, "Hamma ni ce, ni ce a jikin videon. Ni na san wannan jikina ne, ban san yaushe na aikata har aka yi min video ba. Shikenan an gama wulaƙanta ni Hamma, an cuce ni Hammaa!."
"Ya isa haka, ki daina faɗar wannan kalaman babu daɗin ji. Ki nutsu, zuwa nan da gobe komai zai zo ƙarshe in sha Allah."
Bata ce komai ba sai hawaye take yi, Baffa ya ce, "ina Safeera?."
Sai ta miƙawa Safeera wayar ta saka a kunne ta ce, "gani Baffa."
Baffa ya ce, "ki zauna da ita, kar ki bar inda take saboda tana cikin damuwar da jawo ta yiwa kanta illa. Zan faÉ—awa Baban naki, zan ce ni na ce ki kwana da ita saboda ita."
Safeera ta ce, "To Baffa, zan kira Mama na faÉ—a mata."
"Yauwa hakan yana da kyau, Allah ya yi mu ku albarka."
"Amin Baffa." Daga haka suka kashe wayar.
A lokacin Mamy ta fito ta ce, "Safeera ki kaita É—aki ta huta."
Safeera ta kalli Mamy cikin ƙauna da burgewa. dan yadda take faɗar Safeera ɗin burge ta yake yi sossi.
Ta ce, "To Mamy."
Ta kalli Islaha ta ce, "mu je." Ta miƙe suka shiga ciki.
Islaha ta ce, "Safeera nuna min video nan don Allah."
Safeera ta ce, "babu amfanin ganin Islaha, zai sake ɓata miki rai ne."
"Ina so in gani, ki bani."
"Bazan bayar ba, ki zauna."
Islaha taƙi zama ta ce, "In kina ƙaunar Allah ki bani."
"To meye abin gani a video?."
Cikin murya mai rauni ta ce, "ina so in gani."
Safeera ta sauke numfashi ta haska mata, ta karɓa tana kallo sai ta rufe bakinta da hannunta ta zauna tana juya ido akan wayar.
Babu abinda ya banbanta da ta jikin video, komai irin nata sak da sak, ta girgiza kai ta ce, "Safeera ni ce, wallahi ni ce" ta faÉ—a hawaye yana sauka akan screen É—in wayar.
Ta ce, "komai irin nawa ne, yaushe na sha giya har aka yi video nan ban sani ba? Ni dai na san ban taɓa aikata zina ba balle na ce ko an yi min video a lokacin."
Safeera ta ce, "Don Allah ki nutsu, ki daina wannan koke-koken, ciwo zai ƙara miki."
"Dole in yi kuka, ni ce a ji ki Safeera, wallahi jikina ne. Yanzu shikenan kowa ya san ya jikina yake ko? Kowa ya daina ganina da suttura sai tsirara."
Safeera ta ce, "don girman Allah ki daina wannan kukan, ki nutsu." Bata daina kuka ba sai hawaye da ya cigaba da ambaliyya, Safeera ta karɓi wayar ta ajjiye tana rarrashinta.
Abba kuwa kai tsaye saman Rehaan ya hau ya same sa a zaune ya jingina da kujera ya rufe ido har ya shigo bai sani ba.
Abba ya ce, "Rehaan." Ya buÉ—e ido yana kallon Abba.
Abba ya ce, "Ya ka ke ganin za a yi da maganar nan?."
Rehaan bai amsa ba Abba ya ce, "Yayana ya kira ni akan case ɗin nan, mutanen da suka san akwai alaƙa tsakanina da yarinyar nan sai kira na suke yi. Har Alhaji Rufa'i da na saka ya yi magana da mai riƙonta akan aurenku ya kira ni, yana faɗa min shi dai bai santa da irin wannan halayen ba ko kaɗan, bai sani ba ko ta canja. Nima ina tantama, ina jin kamar itace kamar kuma ba ita bace. Da kana da wannan halin da bazai ɓuya ba, irin binciken da na saka aka yi a kanta kafin aurenku babu halinta mara kyau da zai ɓuya."
Abba ya ja numfashi ya ce, "Ko itace ko ba ita bace Allah ne ya sani. Amma Rehaan kana da É—aukaka, duniya ta san fuskar ka, babban tozarci ne ace kana tare da ita a a matsayin matarka. Yadda na ba ka umarmin aurenta, ina sona baka umarnin sakin ta, tunda daman baka so kuma ba a san kana aurenta ba. Tunda aka fara yaÉ—a hotuna irin wannan, ko da ace ba ita bace ba mu san abinda za a yi nan gaba ba."
Rehaan ya sunkuyar da kansa ƙasa bai ce komai ba, dan bai san me zai ce ba. Abba ya ce, "daman saboda ni ka ke zaune da ita, to kuma yanzu na ce maka ina so ka sake ta."
Rehaan ya ja numfashi ya kalli Abban, kafin ya yi magana Abba ya ce, "ko dai ka fara sonta ne?."
Ya girgiza kai ya ce, "A'a."
"Meyasa baza ka sake ta."
"Saboda ina da dalili Abba."
"Meye shi da zai saka ka kasa sakin ta?."
"Lokaci....lokaci nake so a bani Abba, Ina bincike akan maganar."
"Meye naka na bincike tunda ba so ka ke yi ba? A ganina ka samu hanyar rabuwa da ita tunda daman ni na saka ka aure ta, kuma yanzu na ce a sake ta ba shikenan ba? Binciken me za a yi kuma?."
Rehaan ya sauke numfashi yana jin ɗacin kalmar nan da suke faɗa sannan ya ce "Abba Mamy ta ce na yi bincike a kai bana son ƙin yi, a wancan lokacin na karɓi aurenta saboda ka ce na karɓa, wannan lokacin kuma zan yi bincike saboda Mamy ta ce in yi."
"In ka yi ka tabbatar da ita É—in ce fa?."
"Baza ta sake yin sacan ɗaya da sunan matata ba, na yi maka alƙawarin sakinta a lokacin."