Sashe 5
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Na san bakya so shima ba ya so, amma ya kamata ki san yanzu dai matarsa ce, kuma ke É—in inlaw É—inta ce. Ya kamata wani abun ki dinga yin pretending ko dan mutanen gidan nan, ki duba kishiyar ki abinda ta bayar, yanzu da ta bayar ke ba ki bayar ba ya ki ke tunani?."
Mamy ta É—an sauke numfashi ta ce, "na yarda na yi laifi."
Ta ce, "ya kamata ki dinga haƙuri, kin san ya mutanen gidan nan suke kallon ki, kina yin motsi kaɗan za a ce kin ce." Mamy ta yi shiru bata ce komai ba.
A lokacin Abba ya kira ta a waya tana É—auka ya ce, "Kun yi magana da Rehaan ne?."
Kafin ta basa amsa ya ce, "ina ta kiransa wayar bata zuwa, na tambayi Jafar ya ce basa tare. In kin same shi ki ce nace ya zo gida duk dare, in ba haka ba ban san wanne irin fushi zan fuskanta daga Daada ba."
Mamy Allah ya so bata ce masa sun yi waya ba, sai ta ce, "zan gwada kiransa in sha Allah, in na same sa zan faÉ—a masa." Daga haka Abba ya kashe wayar ta bi wayar sa kallo.
Yayarta ta kalle ta ta ce, "ba yanzu ku ka gama waya da Rehaan É—in ba?."
Mamy ta ce, "yanzu ne, da alama Abbansa bai same sa ba." Bata ce komai ba itama bata ce ba, suka cigaba da hirar yadda komai zai kasance gobe in an kai Riyya gidanta.
Abba kuwa yana kashe wayar wajan Daada ya koma yana shiga ya tarar da ita da Mama. Yana shiga Daada ta ce, "Rehaan É—in ya taho?."
Ya girgiza kai ya ce, "Ban same sa a waya ba wallahi, na kira Jafar shima ya ce basa tare, amma na ce duk dare ya faÉ—a nasa ina neman sa."
Daada ta ta fara tafa hananye ta ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!….
Yaron nan so yake ya watsa min ƙasa a ido, so yake ya nuna min ban isa dashi ba. Tsakani da yarinya baƙuwa an kawo ta gidan nan, ƴan uwanta duk sun tafi an barta ita kaɗai ace bai zo ba? Me yake yi a inda da ya zauna? Sai ya nunawa duniya ban isa na saka shi ya yi ba ko?."
Abba ya ce, "ki yi haƙuri, in sha Allah a gidan nan zai kwana."
"Kaima ya raina ka balle ni, gwara ni ba haihuwarsa na yi ba ubansa na haifa, kai da ka haife sa ɗin ma ya nuna maka yanzu ya fi ƙarfinka, tunda yana da kuɗi kuma shi jinin indiayawa ne."
Mama da take gefe ta ce, "gaskiya dai Rehaan bai kyauta ba, ko dan mutanen da suke gidan nan ya kamata ace ya zo ko iya yau ne. Bakin mutane ake gujewa, meye aibu dan yazo ya shiga inda matarsa take? Ba fa wani abun aka ce ya yi da ita, kwana dai a kwana a tashi meye aibu a ciki?."
"In ma wani abun aka ce ya yi da ita ɗin ba matarsa bace, Aka san mata nawa yake yi dasu a ƙasar waje? Yadda mata suke yawo da ɗagaggun kayan nan meye ma bazai aikata ba?..."
Sai kuma ta yi shiru tana girgiza kai ta ce, "kawai yana so ya nunawa duniya ban isa ba, yana so ya nunawa duniya da baƙin da suke cikin gidan nan, da fararen fatar ƴan uwan uwarsa ban isa dashi ba. In har bai zo gidan nan yau ba, ya nuna min kai ɗin ma ba ya daraja ka balle ka saka shi ya yi."
Abba ya dafe kai cikin rashin jin daɗi ya ce, "zai zo ma in sha Allah, ki yi haƙuri."
Daada ta ce, "kar ma yazo ɗin, ya zauna a inda ya ga dama, tunda daman uwarsa bata son auren ai bazai zo ba. Nan ta zauna sai cin magani take yi, saboda na zaɓawa ɗanta mata tana ganin ban isa ba. Ta kiyaye ni, na rantse da Allah sai na aurar da Banisha yanzu, na ga abinda ta isa ta yi."
Abba ya ce, "Allah ya wuci zuciyar ki, ki yi haƙuri."
Abba ya miƙe ya fita zuciyarsa babu daɗi yana sake kiran wayar Reahan amma har lokacin user busy take saka masa.
Yana fita Mama ta ce, "Nadira bata san auren nan ko kaÉ—an, kuma na tabbatar ita baza ta saka samunsa a waya ba, itace zata ce kar ya zo."
Daada ta ce, "ai ba sai kin faÉ—a ba, na san halin munafurcinta tsaf zata aikata wallahi."
"ni ban ga aibun yarinyar nan ba, yarinya mai nutsuwa da girmama mutane. Ki duba yadda ta kasa haɗa ido da kowa a falon nan, tana magana kanta a ƙasa cikin mutunci da halin fulani. Wallahi in ka haɗa jini da wanda ba fulani na ma tashin hankali ne, gabaɗaya ta gurɓata mana yara sun koma kamar ba jininmu ba. Ko wacece yarinyar da take son aura masa ai baza ta kai Islahan ba, ga kyau ga ta jinin fulani."
Daada ta ce, "ki ƙara da girmama na gaba, sanin darajar tsoho, ilimi, ibada da kuma wayewa. Ko wacece yarinyar da take son aura masa ai baza ta kai haɗa waɗannan abubuwan ba."
Mama ta ce, "hmmm, ni fa na ji labarin Ikram take so ya aura."
Daada ta wani kalle ta baki buÉ—e ta ce, "wacce Ikram É—in?."
Mama ta ce, "Ƙanwar Jafar."
"Ƙanwar Jafar a gidan nan? Ke Saddiƙa ko dai Nadira tana shaye shaye ne?."
Mama ta murmusa ta ce "ba wani shaye shaye, tsabar iskanci ne tana ganin kamar itace da gidan, tunda É—anta shine lamba É—aya a gidan."
Daada ta ce, "Ɗanta dai shine lamba ɗarin gidan nan ba ɗaya ba, matuƙar ina da rai babu wanda zai zama lamba ɗaya sai ni. Wallaho bata isa ba, in dai ina raye wallahi bata isa ya auri ƙanwar Jafar ba. Ita ta isa? Dan an samu ma na amince da auren Juwairiyya da Jafar ɗin shine zata ɓullo da wannan wasan kwaikwayon? Lallai dole na yiwa tufkar hanci, Allah ya nuna mana gobe."
Mams ta ce, "ya kamata kam, dan yadda ta ke ji da kanta ya kamata dinga nuna mata gaba da gabanta." Daada ta girgiza kai bata ce komai ba, dan Mama ta gama zugata, kuma ta zugu sosai.
Mama ganin ta gama ɗora Daada sai ta yi murmushi, "Daada bara na koma ciki, ina da baƙi suma jirana."
Daada ta ce, "Na gode Saddiƙa, ba a banza ki ka zama kece gaba a gidan nan ba. Allah ya yi albarka."
Mama ta murmusa tana rusunawa ta ce, "Amin Daada, sai anjima."
Mama tana fitowa ta harari ƙofar falon Daada ta ce, "Kaf ƴaƴana da suka yi aure, ba ki basu kwatankwancin abinda ki ka bawa wannan figaggiyar yarinyar ba.
Sarƙar gold ki ka bata wacce kuɗinta zai kai miliyan talatin, ki ka haɗa da kuɗi da abubuwa. Ni nawa yaran da suka yi aurensu, da ƙaramar sarƙa ki ka haɗa matansu dashi, amma ita kalli irin kyautar da ki ka bata. Wallahi Allah bazan bar Rehaan ya zauna lafiya ba, ta jikin matar nan tasa zan san duk hanyar da zan bi na cimma burina. Babu ta yadda za ayi Rehaan ya fi ƴaƴana bayan su ne gaba dashi, biyayyar dole nake yi miki Daada, jira nake na gama da Rehaan na dawo kan ki, dan kema za ki iya hana ni rawar gavan hantsi."
Kai tsaye ɓangaren Umma ta wuce ta same ta a ɗakin Salman tana bashi maganinsa. Ganin Mama sai ta fito ta ce, "Kin ga abinda uwar mijinki ta yi mana ko? Sarƙar da mu ke sakawa a wuyanmu ita ta ɗauka ta bawa yarinyar da ko awa biyar bata yi a gidan nan ba. Matar Rehaan, Oh Allah, ya zamu yi da yaron nan ne?."
Mama ta ce, "Maza huɗu na aurar a gidan nan, amma bata taɓa basu kwatankwacin abinda ta bata ba."
Umma ta ce, "kema ai na yi mamakin ki, harda ba da lace É—in 2.7m kyauta ga yarinyar."
"Ya zanyi, Abbanssu ne ya saka ni a gaba don Allah nima na yi, dole ce ta saka na yi ai ba don ina so ba."
Umma ta haÉ—e rai ta ce, "Shi ya faÉ—a miki kema ki ba da kyautar?."
"Shinw mana, ke bai faÉ—a miki ba?."
"In da ya faÉ—a ai zan bayar."
"Wataƙila ya manta ne, kin san ana ta hidimar biki abubuwan sai a hankali. Amma jira nake a gama bikin nan, Allah sai na yi maganin Rehaan."
Umma ta ce, "haka ki ke faÉ—a ko yaushe, amma kin kasa yin komai."
Mama ta yi dariyar nishaÉ—i ta ce, "kina wasa dani, amma in kina ganin bazan iya ba zan iya cewa ki zuba idanu."
Umma gabaɗaya ranta ya ɓaci, jin abinda Abba ya faɗawa Mama ita bai faɗa nata ba. Wato har kuɗi ma ya bata ta siya, ita ga banza mara amfani, ya ajjiye ta a gefe kamar ba matarsa ba.
Mama ganin yanayin Umma ya canja sai ta ce, "sai mun haÉ—u gobe, bacci nake ji" ta faÉ—a tana yi mata wani irin kallon ba ki da wayo yarinya, sannan ta fita tana murmushin da ita kaÉ—ai ta san ma'anarsa.
Hajiya Mama ikon Allah😂🤣
Nana Haleema.
RDB3P004
Nana Haleema.
Islaha tunda su Safeera suka tafi ta koma ta zauna akan kujerar falon bata iya miƙewa ba. Kallon falon take yi babu sautin komai sai ac, ko sautin hayaniyar mutanen da ta gani a waje bata ji. Ta kasa ɗarawa daga falon, tana zaune ta yi tagumi tana tunanin Saheer. Ga ciwon kai, ga gajiya, ga tashin hankali, ga zazzaɓin da ya mamaye mata jikinta.
Cikin rauni da sanyin ta jawo wayarta ta kira Sadik amma bai É—auka ba, ta rufe ido ta rasa wa zata kira. Inda a dah ne sai ta kira Adda, amma yanzu Adda ta yi fushi da ita itama.