Sashe 40
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suka yi shiru basu ce komai ba, ya nuna su da yatsa ya ce, "Na rantse da Allah in aka kama É—aya daga cikin ku wani ya ambaci sunana kun san sauran, tunda ku ka yi aikin a bayan bank, kun sana akwai cctv a wajan, saboda shirme da rashin sanin makamar aiki. Yanzu ana kan bincike, na tabbatar za a ga fuskokin ku."
"Ai duk mun rufe fuska."
"ku ku ka sani kuma, ni dai ina sake maimaita mu ku babu ruwana a cikin maganar nan. In za ku tattar ku bar gaein ku yi, in komai ya lafa sai ku dawo."
Zasu yi magana ya ce, "na gama sauraron ku, ku wuce ku bani waje, bazan sake yin aiki da ku ba." Basu ce komai ba suka miƙe suka fita.
Ya saka ƙafa ya da ki kujera da ƙarfi, ya dafe kansa da yake sara masa saboda kishi da hassadar Rehaan ya ce, "Rehaan!."
Sai kuma ya girgiza kai ya ce, "wallahi baza ka kasance da rai ba, sai na ga bayanka, sai na ga bayanka wallahi!" Ya faɗa da ƙarfi yana dukan kujera cikin tsananin fusata da baƙin ciki.
"Ya zama dole na samo sabuwar hanyar ganin bayan Rehaan."
Hannunsa yana rawa ya É—auki waya ya saka a kunne ya ce, "ina son information akan yarinyar da aka aurawa Rehaan, ina son sanin wacece ita, aikinta da halayaenta duk ina son sani a yanzun nan" Daga ya yanke wayar yana ci kamar ya yi ta ihu saboda takaici.........
Nana Haleema.
RDB3P32
Nana Haleema
Ikram tunda ta koma gida ta shiga É—aki ta zauna a gefen gado ta yi tagumi tana tunanin masoyinta Rehaan da matarsa Islaha da ta kasa gano makusa a jikinta.
Mummy tun wucewarta É—aki ta kula da yanayinta, suna tare da Jafar a zaune har ta wuce bata ce musu komai ba, Jafar ya bita da kallo sannan ya ce, "ita kuma wannan lafiya?."
Mummy ta ce, "Ikram bata ji Jafar, ita ta dage akan Rehaan ta ke so kuma shi za ta aura."
Jafar ya yi murmushi ya ce, "To ai ya yi aure ko?."
"Ina jin mantawa ta ke yi da yana da aure a yanzu."
"Ya yi auren ma bata haƙura ba Mummy?."
Mummy ta ce, "bata haƙura ba, dan yanzu ma daga gidan take."
Jafar ya ce, "Zuwan ta gidan ba matsala bane Mummy, dalilin zuwan nata shine damuwa. Wallahi Rehaan bazai saurare ta ba, kin ji nace wallahi ko Mummy?."
Mummy ta ce, "Na sani Jafar, Rehaan yana kallon ta kamar Riyya da Janan, bazai iya kallon ta a matsayin matar aure ba. Na yi mata bayani amma ta kasa yarda."
Jafar ya ce, "Inda zai aure ta É—in duk za mu so hakan, amma bazai aure ta ba Mummy. Ba wai dan bata dace shi ba, sai dan bazai iya kallonta a wannan matsayin ba. Ko a Jeddah sai da mu ka yi maganar ta da shi, ya sake maimaita min babu shi babu auren Æ´ar uwarsa har abada."
Mummy ta ce, "na sani Jafar, ba sai ka maimaita min ba. A gaban idanun ku ita da Riyya suka girma, yadda yake yiwa Riyya haka yake yi mata, ni kaina na san bazai iya kallonta a matsayin matar aure ba."
Kafin ya yi magana Mummy ta ce, "bara na kira maka ita, wataƙila kai in ka faɗa mata zata yarda, tunda ta san kai da Rehaan kamar hassan da usaini ne" Mummy ta miƙe ta hau sama dan ta kira masa Ikram.
Babu jimawa suka dawo tare da Ikram da take tafiya kamar bata so saboda sanyin jiki.
Jafar ya miƙa hannunsa ya riƙo hannunta ya zaunar da ita a kusa da shi, cikin sigar rarrashi ya ce, "Iky faɗa min meye?."
Sai da gabanta ya faÉ—i dan Rehaan ne ya saka mata Iky, tunda ta girma ne bai cika faÉ—a ba, ya fi faÉ—ar full name É—inta.. ikram ta sunkuyar da kai bata ce komai ba.
"Talk mana, i'm here for you."
Muryarta ta fara rawa ta ce, "Hamma Ray...."
Jafar ya sake tausasa murya ya ce, "ki ke so?." Ta É—aga ido ta kalle shi sai kuma ta É—aga kai alamun eh, sai kawai ta saka kuka tana kwanciya a kafaÉ—arsa.
Ya sauke numfashi mai nauyi ya dafa kafaÉ—arta yana bubbugawa a hankali, sannan ya ce, "ki daina kuka, ki yi shiru mu yi magana."
Bata daina kukan ba, ya bata lokaci ta gama kukan sannan ya riƙe hannunta ya fuskance ta ya ce, "Ikram!."
Ta É—aga ido ta kalle sa ta ce, "Na'am."
"Kina so na faÉ—a miki gskiya?."
Ta É—aga kai alamun eh. Ya ce, "Ki cigaba da addu'a, ki dage da faÉ—awa Allah damuwarki. Amma auren ki da Rehaan abu ne mai wahala."
Ikram ta sake shagwaɓe fuska ta ce, "saboda ban dace dashi ba, bani da kyau ko Hamma Jafar?."
Ya yi murmushi yana goge mata hawayen fuskar ta ya ce, "kina da kyau Iky."
"to meyasa ka ce haka?."
"Saboda Rehaan kallon ƙanwarsa yake yi miki, ba kallon macen da zai iya aura ba. Da ke da Riyya da Janan duk ɗaya yake kallon ku, da ke dasu Adda Anisa yayyensa mata, duk ɗaya yake kallonku, bazai iya keɓance ki daga cikinsu a matsayin matarsa ba."
"Bazai iya sona ba?."
"Rehaan yana sonki, kina daga cikin mutanen da yake so, amma so na Æ´an uwa ba na aure ba."
"Zan iya manage da hakan, tunda Mamy tana so ya aure ni."
"ko Mamy tana so sai yana so, duk abinda Mamy ta ke so in Rehaan bai ba da goyan baya akansa ba ya lalace duk son da Mamy take yiwa abun, in kuma yana ƙin abu duk yadda Mamy take so itama zata daina so tunda ba ya so. Duk da tana son ya aure ki, amma in ya nuna ba ya so bazata yi masa dole ba."
"Amma Daada ta yi masa dole ya auri Islaha take ko waye oho."
Ya yi murmushi ya ce, "kema cewa ki ka yi ta yi masa dole, kin ga Mamy bazata yi masa dole ba. Kuma ke da bakya son kishiya, tunda ya yi aure ba sai ki watsar dashi ba?."
Ta turo baki ta ce, "ai ba sonta yake yi ba."
"Haka aka ce miki?."
"Kowa ya san dole aka yi masa."
"To yana son matarsa."
"Allah ba ya sonta, yanzu da mu ka je gidan ko kallonta ba ya yi."
"Na ji ba ya sonta, amma ke yana son na ki ne?."
Ta yi shiru bata amsa ba. Ya ce, "ki bar wannan maganar Ikram, ki yi addu'a Allah ya ba ki wanda yake sonki ba wanda ki ke so ba, ki ajjiye batun Rehaan a gefe, in ki ka aure sa ma yadda ki ka ga ya yiwa Islaha har ki ke bada labari kema haka zai yi miki. Yanzu ki ke bani shaidar ba ya sonta saboda ba ya kallonta, kema in ba ya son ki bazai kalle ki ba. Ki bar tunanin aurensa a ranki, dan ko kin aure shi baza ki samu lokacinsa ba, Rehaan busy man ne, lokacin kansa cikakke ba shi da shi balle na ki. Ikram ki nutsu ki cire Rehaan daga ranki, kina wahalar da rayuwarki indai a kansa ne. Ki nutsu ki cigaba da addu'a kawai."
Ikram ta ti ajiyar zuwa, ta san gaskiya yake faÉ—a mata amma ta kasa fahimtarsa yadda ya kamata.
Ta kalle sa ta ce, "Amma kai ma a dah ka ce baza ka iya auren Riyya ko Janan ba, nima ka ga zai iya canja ra'ayi."
Ya girgiza kai ya ce, "ba dai Rehaan ba, bazai canja ba wallahi, kin san nafi kowa sanin halinsa, ki yarda da abinda nake faÉ—a miki."
Ta ɗan yi shiru sai kuma ta ce, "Ni wajan Mamy zan koma" ta faɗa tana miƙwa ta hau sama ya bita da kallo.
Mummy ta yi dariya ta ce, "Soyayyar da take yi masa ma bata da wani auki, ga shi nan har ka fara canjata."
Jafar ta yi dariya ya ce, "Ba fa so bane ba Mummy, burge su kawai yake yi, suna so su auresa ko dan a nunawa ƙawaye ana auren Rehaan. Wannan gashin nasa ne yake ɗaukar hankalinsu, da yadda hotounansa suke yawo a social media, to sai kuma kyaunsa da yake sake ruɗa su."
Mamy ta yi dariya ta ce, "da gaskiyar su Jafar, Rehaan ta ko ina Allah ya yi masa baiwa. Ga kyau, ga tarbiyya, ga kirki, ga zumunci, ga kuÉ—i. Allah ya cigaba da kiyaye shi a duk inda."
"Amin Mummy. Dan yaron nan Rehaan da ki ke gani ya wuce tunanin ki, yana da madarar kuɗi a hannunsa wallahi, in na faɗa miki cewa za ki yi ƙarya nake yi."
Muummy ta ce, "Kai kuma kana da sikarin kuÉ—i?."
Ya yi dariya ya ce, "Mummy ki bar haɗa ni da Rehaan, shi na daban ne. Yana da sa'a, duk abinda ya taɓa da niyar kasuwanci sai ya samu riba. Yana da kwarjini sosai, mutum biyu ne kawai ba ya yiwa kwarjini a duniya."
"Su waye?."
"Daga ni sai miss."
"Kai daman na san ka raina shi, duk da Yayanka ne amma baka girmama shi. To wacece miss?."
Jafar ya sake yim dariya ya ce, "wata yarinya ce, in kinga yadda take yi masa sai abin ya ba ki mamaki, ta gama raina Rehaan sosai" ya faɗa yana miƙewa sannan ya ce, "Mummy na tafi, zan je gida."
Mummy da murmushi ta ce, "a gaishe da Riyya,
Yaush za ku koma ne?."
"Next week in sha Allah."
"Allah ya kaimu."
"Amin, sai anjima."
Mummy ta amsa ya fita yana É—aukar waya ya kira Rehaan, dan zuwa lokacin ya san sim card É—insa ya zama ready.
Islaha tun tana saka ran zata fita har ta cire dan gabaɗaya bata da ƙarfin zuwa ko ina, ta kira Safeera ta ce mata ta fasa zuwa. Haka ta yini a ɗaki ita kaɗai, sai dai ta danna wayar ta gaji ta kwanta.