← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 110

Sashe 107

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Islaha ta ɗora ta ce, "meye dalilinka na faɗa? Kawai dan ka wulaƙanta ni? Saboda ka nunawa duniya bani da wani mahimmaci shiyasa ka yi min haka? In faɗar zaka yi ka faɗawa abokanka a waya mana, amma meye na faɗa a gaban ƴan jarida? Kawai dan ka ɓata min rai ne ko?.”

Rehaan bai ce komai ba dan shi farin ciki yake ji a zuciyarsa ba tare da ya san dalili ba, kallonta yake yi yana jin shauƙi da bugawar zuciya, dan yadda take yi masa faɗan ma kyau take yi ƙarawa, sai ya ji dama zata cigaba da faɗan shi kuma yana kallonta.

Ita kuwa Islaha da gaske ta ji haushin abinda ya yi mata, dan ta san yanzu ta shiga uku a social media, inda bata yi tunanin videon zai je ba ma sai ya je. Daman ga abinda ya yi mata jiya yana ranta, ga wani ya sake maimaitawa.

Ganin tana yi masa magana ya ƙi kulata sai ta sake fusata, ta kalle shi shi ta ce, "don Allah ka kira ƴan jarida ka faɗa musu ni ba matar ka bace wasa ka ke yi, wallahi bana so" ta faɗa idanunta yana cikowa da hawaye zata yi kuka.

Rehaan da yake kallonta ta ya ce, "Kema Æ´ar jarida ce ko? Why not ki yi min video sai in faÉ—a?."

Islaha ta ji kamar ta tsinka masa mari saboda  takaici, ta tsaya tana kallonsa dan da zata iya tsaf zata mangare sa ya zube a wajen. Kawai sai ta zube a wajan ta saka masa kuka, shi dai yana tsaye yana kallonta ya rasa me zai ce mata ganin da gaske take kukan, tun yana kallon ta har ya fara jin zafin kukanta a cikin ransa.

Muryar ta tana rawa ta ce, "meyasa za ka yi min haka? Meyasa za ka cewa ƴan jarida ni matarka ce?. Ka san ni matar contract ce ba matar aure ba, lokaci kaɗan ne ya rage contract ɗin mu ya ƙare, meyasa zaka faɗa ka ce ni matar ka ce?. Tun meyasa baka taɓa faɗa ba sai yanzu? Kawai dan ka wulaƙanta ni, kawai saboda mutane su san ka aure ni bayan na bar gidanku?.”

Kafin ya yi magana wayarta ta fara ƙara, ta kallah ga sunan Hamma a kan screen ɗin yana yawo, ta ɗago ta kalli Rehaan da yake kallonta ta ce, "Ni ba mu yi haka da kai ba, ba mu yi za ka dinga karya min rules ɗina ba. Amma yanzu sai breaking ka ke yi kana yi min duk abinda ka ga dama, sai da lokaci ya zo ƙarshe zaka dinga canjawa?" Ta faɗa tana kuka.

Kukan da take yi ya ba shi mamaki sosai, kukan da take yi akan ya faÉ—awa Æ´an jarida ita matarsa ce ya saka ya ji zuciyarsa cike da takaicin É—ora aurensu akan contract, ya saka shi yana jin ina ma bai amince da duk wasu rules ba an yi auren haka kamar ko wanne ai, da hakan ne ya kasance baza ta dinga yin kuka dan ya ce ita matarsa bace.

Zuciyarsa tana faɗa masa akan Saheer ta ke wannan kukan, kishi yana mamaye masa zuciyarsa, abinda bai taɓa ji akanta ba yana mamaye masa zuciyarsa. Shi da yake mijinta bai yi kuka akan kalamanta ba sai ita ce zata yi kukan rashin dalili?.

Ta rufe fuska da hannayenta tana kukan da bata san dalilinsa ba, tana ji wayarta tana ƙara ta kasa ɗauka dan tasan Saheer ne, kuma ta san akan video zai yi mata magana ita kuma bata so.

Rehaan kallon ta kawai yake yi yana jin kishin Saheer a zuciyarsa, bai taɓa jin kishin abu kamar yadda yake jin kishin Saheer a lokacin ba, bai san haka kishin ya ke ba sai yanzu da take kuka saboda wani daban ba shi ba. Zafi yake ji a jikinsa kamar ana tasafa jininsa, zafin jinin yana zaga ko wacce jijiya ta jikinsa har cikin ƙwaƙwalwarsa. Ya kasa ce mata komai, ya yi shiru kawai yana kallon yadda take kuka.

Da baya-baya ya shiga ciki ya barta a falo, ya tsaya ya jingina da bango yana jin zuciyarsa tana bugawa da gudu, ya dafe zuciyarsa da hannunsa na dama, yana jin yadda ƙirjinsa yake ɗagawa saboda bugun zuciya. Zafin kishin da yake ji ya saka shi ya cire rigar jikinsa ya ajjiye ya, ya cire dogon wandon ya zauna a gefen gado yana ji kamar ya yi kuka saboda takaici.

Jazy ne yake kiransa a kira shi a waya ya É—auka Jazy ya ce, "weldone! You shake the world, my guy. Ka ga yadda ku ke trending a duniya kuwa? Kuma ni wallahi ka burge ni, yanzu Saheer zai san Islaha ba matarsa ba ce."

Cikin wata irin murya mai cike da rauni ya ce, "Like how? Kana ganin yadda take kuka kawai dan na ce ita matata ce? Tana parlour tana kuka saboda shi, tana kukan kar ya ga na ce matata ce."

"Ka bata lokaci yanzu baza ta fahimta ba, amma nan gaba zata gane."

Ray ya ce,"Jazy zuciyata bugawa ta ke yi."

"Kishi ne, ba ka fara jin komai ba indai akan soyayya da kishi ne Rehaan."

"ina ji kamar na yi kuka, Jazy jikina rawa yake yi."

Jazy ya ce, "kishin kenan, yanzu ka fara son Islaha shiyasa za ka yi kishin da Saheer, kuma ya cancanci ka yi kishi da shi. Tun farko kai ka ba da matsala, da ka É—ora auren ku akan hanya mai tsafta da haka bai faru ba."

Ray ya lumshe ido yana sauke numfashi ya ce, "na yi danasani, ina jin kamar na koma baya na yi erasing contract agreement. Ka bani shawara Jazy, zan rasa hankalina."

"Rehaan ka yi abinda ya kamata kawai."

"Kamar me?" Ya faÉ—a cike da gajiya da maganar.

"Kana mijinta har sai na faÉ—a maka abinda ya kamata ka yi? Think."

Rehaan ya yi shiru yana tunani, lokaci ɗaya ƙwaƙwalwarsa ta harba ya hau kan layin da Jazy yake so ya hau, sai ya buɗe idanun waje cikin bugawar zuciya ya ce, "Jazy!."

Ya katse shi ya ce, "ba lokacin jira bane yanzu, ba ka da cikkaken lokacin da zaka ce jira sai kun saba kafin wani abu ya haɗa ka da ita, ka yi amfani da duk damar da ta zo hannun ka, in ba haka Islaha bazata saka a ranta kai mijinta bane, zata cigaba da kallonka a matsayin mijin contract ba mijin aure ba. In kuma ka yi abinda nake faɗa maka abubuwan za su zo mana da sauƙi, ban san ka da losing oppurtunity ba Ray, kar ka fara daga yau, kar ka fara daga kan Islaha."

"Kar ka bari tunanin conditions ya hanaka, duk abinda ka ke ji a kanta ka yi kawai, ka donga tunawa ita ɗin matarka ce, kana da iko da ita a ko yaushe. Ni premarital test nake tunani tunda ba ku yi, na san genotype ɗinka AA bani damuwa da shi, but Rhesus Factor and Hepatitis B & C shine abin jin….”

Rehaan cikin rashin damuwa ya katse Jazy ya ce, “Ni ban damu da wani premarital test ba Jazy, ko wacce cuta ce a jikinta i can take it. Ni da ita na damu ba da wani test ba, bana so na rasata, in na rasata za ku iya rasa ni Jazy!” Ya faɗa cikin sanyin murya.

Nana Haleema.

RDB3P79
Nana Haleema.

Jazy ya yi dariya jin baturen mutuminsa yana cewa shi bai damu da test ba, mutumin da yake da taka tsan-tsan akan lafiya, komai sai ya ce sai an yi gwaji. Akan Islaha ya fara É—aukar housemaid ba tare da gwajin jini ba, ya saba sai an yi gwajin ciwon hanta da hiv wani lokacin harda gwajin TB. Amma yau Rehaan ne yake cewa shi bai damu da gwaji ba saboda soyayya.

Jazy ya sake yin murmushi sannan ya ce, “Ahhh kamar lokacin da ta yi signing ta taho da takardar, na tuna ta yi test ɗin tabbas.”

Rehaan a gajiye ya ce, “Jazy ni ba batun test nake yi maka ba, ina yi maka magana akan rayuwata. In ka bari ta tafi nima zan tafi.”

Jazy kamar ya tsokane shi ya ce daman ai ba shi ya kawo ta ba balle ya hanata tafiya, amma a yanayin da yake ciki bazai iya tsokanarsa ba hakan ya saka ya ce, “Rehaan in ka bar wannan damar ta wuce ka baza ka sake samun wata ba, kawai ka yi amfani da ita a duk inda ta zo maka. Ni dai so nake ka tabbatar da maganata akanta, yadda zaka sake ninka wata uku nan gaba akan ragowar da suka rage maka. Koda rabuwa ta gifta dole sai ta jira ta yi maka iddah, kuma wannan ma lokacin ka ne. Balle bana fatan a rabu, kawai ka san abinda ya kamata ka yi kafin ka buɗe ido ka ga babu Islaha.”

Ray ya yanke wayar ya kwanta a kan kujera ya dafe kansa yana juya maganganun Jazy a ransa. Tunani yake ta ina zai fara? Ta wacce hanya zai É—auki layin da Jazy yake so ya É—auka? Shi ba ya son saka ta a damuwa, ba ya son ya yi mata abinda bata so, ba ya so ta cigaba da kallonsa a a tsayin mai karya nata sharuÉ—a kamar yadda take faÉ—a ko yaushe. Yanzu ya zai yi? Shawarar Jazy zai É—auka ko kuma zai cigaba da zuba mata ido har lokacin rabuwarsu ya yi?.

Yana ta jin shigowar saƙo wayar, ya kalli notification ya ga messages ne ana ta ya sa murna da ake yi na auren da ya ce ya yi, ya danna power wayar ta ɗauke, ya yi shiru yana jin zuciyarsa tana bugawa a guje.

Islaha tana zaune a parlour mararta tana É—aurewa, ita kanta ta yi mamakin jin ciwon tana tunanin kamar lokacin bai yi ba, tana kukan Rehaan ya ce ita matarsa ce tana kukan ciwon mara.

A lokacin aka sake kiran wayarta da ta ke kusa da ita, sai ta É—auka ta saka a speaker kafin ta yi magana Saheer ya ce, "Islaha!."
Chapter 107 · 0% Book details