← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 110

Sashe 64

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana tsaye tana tsaki saboda takaici, yana tafasa ta kashe ta É—auki mug ta zuba, ta fara buÉ—e buÉ—e har ta jawo wata drawer da kana ja zata biyo ka kamaar spring. A nan ta ga kayan tea da yawa, ta É—auki tea leave ta saka masa, ta saka sugar kaÉ—an kamar yadda Mamy ta ce, ta kashe hasken ta hau saman.

Kai tsaye É—akinsa ta shiga ta tarar ya kunna red light yana zaune a kan gadon ya dafe kansa da duka hannayensa.

Yana jin an buɗe ƙofar sai ya yi tunanim Mamy ce cikin muryar marasa lafiya ya ce, "Mamy kaina yana ciwo, ina jin ciwon cikin har yanzu bai daina ba."

Jin yadda ya yi maganar a sanyaye da shagawaɓa kamar ɗan shekara biyar sai ta yi siririn tsaki ta ce, "this boy is too lazy! Ko ni da nake fama da ciwon mara bana wannan rakin da yake yi” ta faɗa tana tsaki sannan ta ƙarasa ta tsaya nesa dashi tana harararsa.

Sai da ta gama harararsa sannan ta É—an matsa kusa da shi ta ce, "Ga tea,Mamy ta ce ka sha."

A hankali ya É—ago kansa ya kalle ta suka haÉ—a ido, Islaha ta ga yadda fuskarsa ta rame lokaci É—aya, idanunsa sun yi ja, kana ganinsa ka san da gaske ba shi da lafiya.

Sai ta ji ya bata tausayi kaɗan ba mai yawa ba, ta miƙa masa tea ɗin ta ce, "Mamy ta ce ka sha tea."

Cikin murya mai sanyi da ta ke nuni da yana cikin rashin lafiya ya ce, "tana ina?."

"Bata nan."

"Ki kira ta, ta zo ta bani tea É—in" yana faÉ—a yana komawa da baya ya kwanta, rigar jikinsa ta É—age cikinsa ya fito waje, har ana ganin navel É—insa a bayyane.

Idanunta suka sake sauka akan logon short ɗinsa, amma yanzu fari ne saɓanin na daren jiya, ta yi tsaki tana ɗauke kanta. Bata san meyasa logon Nike ɗin nan yake burge ta ba, ba yau ta saba ganin kayan kamfaninsu ba, amma in ta gani a jikinsa sai ta ji yana burge ta sosai. Ta ɗauke ta rasa me zata ce masa, sai kuma ta kira Mamy a waya kamar yadda ya ce.

Bugu ɗaya Mamy ta ɗauka kamar jiran kiran take yi, Islaha ta ce, "Mamy ya ce na kira ki ki ba sa tea ɗin ya sha.”

Mamy ta ce, "Ki ba shi da kan ki Islaha.”

Islaha ta yi shiru kawai bata ce komai ba tana jin maganar mamy kamar wasan yara, tana maimaita kamar ya ta basa tea da kanta ita bata gane ba, a baki zata basa ko ya ta kasa fahimta.

Muryar Mamy ta katse mata tunani ta ce, "ki yi feeding É—insa, in ba shi da lafiya yana da rigima Islaha, ya fi son komai a yi masa, ki kula da shi, ki yi masa duk abinda yake so, Please" tana gama faÉ—ar haka ta kashe wayar Islaha ta bi wayar da kallo cikin mamaki.

Islaha ta ce, “tabɗi! Ashe sai dai kar ya sha, ya shekara dubu yana ciwon ciki bai dame ni ba, bazan iya wahala da ɗaukarwa kai zunubi ba.
Shi ba ɗan uwana ba, ba mijina ba kawai na zauna ina ba shi tea a baki kamar wacce ya siyo ya ajjiye? Bazan yi iya wannan saɓon ba, ni bazan yi feeding dinsa ba wallahi, kwanciyar da ya yi a jikina ma Allah ya bi min...."

Sai kuma ta tuna wani abu ta ce, "Astagafirullah! Allah ka yafe min abinda na ce. Amma tsakani da Allah bazan iya feeding wannan lazy ba, dama ace wani mutumin kirki ne sai na yi saboda Allah, amma bazan bazan iya aikin da babu lada ba, ga rashin mutuncin da yake yi min son ransa. Wai yana da rigima, ƙato kamar wannan ace yana da rigima kamar yaro ƙarami? Yau kam bazai sha tea ba indai ni zan ba shi” ta faɗa tana kawar da kai gefe, sai kuma ta sake kallonsa ta ji ya bata tausayi.

Nana Haleema.

RDB3P49
Nana Haleema.

Islaha tana tsaye hannunta riƙe da mug bata motsa ba balle ta ƙarasa ta ba shi kamar yadda Mamy ta ce. Ta kawar da kai gefe daga, dan bata san me yake jan idanunta zuwa ga kallon logon short ɗinsa ba, bata san meyasa idanunta yake son kallon logon ba. Ƙirjinta sai bugawa yake yi cikin wani irin yanayi, ga tea a hannunta amma baza ta iya yin abinda Mamy ta ce ba.

Gajiya ta yi da tsayuwar sai ta waiwayo ta ga yana yadda yake a kwance bai motsa ba, ta sake kawar da kanta ta kuma kallonsa ta ga yana yadda yake a kwance. Ta kalli tea É—in hannunta sai ta lura har ya fara sanyi, ta sake kallon Rehaan sannan ta ce, "Ga tea in ji Mamy."

Rehaan yana jinta dan maganarta har tsakiyar kansa ya ji ta shiga, ya yi shiru bai motsa ba dan ya ji daÉ—in kwanciyar sosai. Islaha ta zauna daga gefensa a É—arare ta sake kallonsa, muryar ta a tausashe ta ce, "Ga tea."

Ya buÉ—e idanunsa ya kalle ta suka haÉ—a ido, sai ta yi saurin É—auke nata daga cikin nasa, dan yadda idanunsa suka koma kana gani ka san ba shi da lafiya.

Rehaan ya miƙe zaune a hankali, Islaha sai ta ga ya ruɗe yana juya kansa alamun ya tsokano ciwon, a hankali kuma sai ya dawo daidai, ita dai kallonsa take yi tana mamakin wannan wanne irin ciwo ne, duk kuɗin da yake da shi ace an kasa maganinsa.

Cikin muryarsa da bata fita sosai ta ji ya ce, "Ina Mamy?."

Islaha ta ce, "Bata nan."

Ya lumshe idanunsa ya ce, "call her, please."

Jin ya haɗa da roƙo sai ta ɗauki wayar ta kira number Mamy. Mamy tana ɗauka Islaha ta ce, "Mamy ya ƙi sha ya ce na kira ki." Mamy bata ce komai ba da katse kiran, ɗakin ya yi shiru idanunsa a lumahe ita kuma tana zaune tana tunanin wannan ciwo.

A lokaci aka yi knocking ƙofar daga baya aka buɗe aka shigo, Mamy ta shigo da sallama ta ƙaraso ta zauna a gefensa sai ya zama sun saka shi a tsakiya, Islaha tana dama, Mamy tana haggunsa.

Mamy ta riƙe hannunsa ta ce, "Gani Rehaan, meye, ciwon ne har yanzu?" Ta faɗa cike da kulawa tana kallonsa.

Rehaan ya kwantar da kansa a kafaÉ—arta ya ce, "Mamy bai daina ciwo ba."

Mamy ta shafa kansa ta ce, "Sannu, zai daina a hankali. Me ka ke so? Ga tea an kawo maka tun ɗazu ba ka sha ba" ta faɗa tana miƙawa Islaha hannu alamun ta bata.

Islaha dai kallonsa take yi tana taɓe baki, ganin yadda yake marairaicewa a jikin Mamy kamar wani yaro ƙarami, tana aiyana ko yaro ɗan shekara goma bazai abinda yake yi ba. Lokaci ɗaya ya sake bata haushi, ta yi siririn tsaki ta ce, "ina aka san namiji da raki? Sai a wajen Mr Rehaan"

Mamy ta ɗago da kansa daga kafaɗarta tana basa tea ɗin a bakinsa ta ce, "har ya fara yin sanyi, karɓi ka sha." Rehaan ya girgiza kai alamun ba ya so. Mamy ta ce, "Sai ka sha Rehaan, cikin ka babu abinci, karɓi a ka sha."

Rehaan ya É—ago kansa daga jikinta, ta saka masa mug É—in a bakinsa ya É—an sipping ya koma ya kwanta ba tare da ya yi swallowing tea É—in ba. Sai daga baya yake swallowing yana jikin Mamy a kwance tana shafa kansa ta ce, "Sannu Rehaan."

A haka ta sake ba shi ya sha har sau uku, sannan ya ce ya isa. Mamy ta ce, "zaka yi bacci?."

Rehaan ya É—aga mata kai alamun eh zai yi. Mamy ta waiwaya ta kalli Islaha da ta mayar dasu tv tana kallo, sannan ta sake kallonsa ta ce, "To ka kwanta ka yi baccin, ga Islaha nan, duk abinda ka ke so zata yi maka."

Duk da ba shi da lafiya sai da ya É—ago kai ya kalli Mamy jin abinda ta ke faÉ—a wanda bai saba ji ba, Mamy ta É—aga masa kai ta ce, "eh, zata yi maka duk abinda ka ke so. I trust her, shiyasa na bata ragamar kula da lafiyar ka a hannunta." Bai ce komai ba ya koma ya kwnata a jikinta.

Islaha da take gefe tana jin abinda Mamy ta ce, ta girgiza kai ƙasa-ƙasa ta ce, "Ka ji Mamy da wata magana don Allah, wai ga Islaha nan, ni zan dinga kula da shi? In aka bar ni da shi yana yi min wannan rakin kafin a awa ɗaya ya fusata ni wallahi" Ta faɗa yadda Mamy baza ta ji ba

Mamy ta ce, "ka kwanta, za ka ji daÉ—i." Sai kuma ta kalli Islaha ta ce, "Islaha ba ni ruwa a kofi."

Islaha ta miƙe ta fita tana girmama wannan soyayya da kulawar da take tsakanin Mamy da Rehaan, dole mutanen gidan su dinga cewa Mamy bata da kunya, Rehaan shine ɗanta na fari amma ta ke yi masa haka, abinda fulani bazasu taɓa yi ba kenan. Kunya ce a tsakaninsu da ƴaƴansu na fari, wasu ko iya haɗa ido ba sa yi da su balle a dinga rarrashinsu haka.

Ita kuwa hakan ya burge ta, sai ta ke ji ina ma itama tana da wacce zata yi mata haka, yadda take fama da cramp É—in nan da zata dinga samu wannan gatan da ta ji daÉ—i.

Tana wannan tunanin ta koma ta kaiwa Mamy cup ɗin ta karɓa ta ce, "thank you." Mamy ta yi masa tofi a ruwan ta ɗago kansa ta ba shi ya sha ruwan sannan ta ce, "Kwanta ka huta.."

Bai ƙi ba ba ya kwanta, Mamy ta miƙe a lokacin aka kira wayarta da take hannunta. Sai ta miƙawa Islaha cup ɗin da ragowar ruwa a ciki ta ce, "ki ɗaga rigarsa sama, ki shafa masa ragowar ruwan a cikinsa, ina zuwa."
Chapter 64 · 0% Book details