Sashe 42
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya sauke numfashi ya ce, "Ni ko da wani abun zai haÉ—a ki da shi a nan gaba, indai za ki dawo gare ni ina son hakan, ke nake so ba jikin ba."
Ta yi shiru bata ce komai ba, tana aiyana mai zai haÉ—a ta da Rehaan ana zaune lafiya?.
Saheer sai ya yi nufin tsokanar ta ya ce, "Hmmm! In da a dah ne na yi irin wannan maganar da kina nan kin kulle fuska, amma yanzu...." Bai ƙarasa ba ta kawar da kanta gefe, sai ya yi murmushi ya ce, "Ina sonki."
Haka kawai sai ta kasa amsa masa kamar ko yaushe, ta yi murmushin yaƙe bata ce komai ba dan ta san shi kansa Hamman ya san ba daidai yake yi ba, amma tana jin daɗi da ya kasance ya samu lafiya kuma ya daina jin haushinta.
Saheer ya ce, "za ki je wajan Safeera ne ko kin je?."
Ta É—an yi jim sannan ta ce, "yanzu zan je."
Bai ce komai ba ya kaita har ƙofar gidan ya ce, "sai mun yi waya." Ta amsa tana fita daga motar ya bita da kallo yana tunani kafin ya ja motar ya nufi gidansu Sadik.
Saheer ajjiye motar ya shiga wajan Sadik, ya same shi a zaune yana ta lissafi, ya zauna Sadik ya ce, "Ya dai?."
Ya kalle sa ya ce, "Kana ganin Islaha zata dawo gare ni kuwa?."
Sadik ya taɓe baki ya ce, "it might be, tunda shima ba sonta yake yi ba, ita kuma ka san daman kuɗi basa gabanta, amma zama a cikin kuɗin zai iya canta ba."
"Ni dai burina ta dawo É—in, in ba haka ba ban san ya zan yi ba. Ina son islaha sosai, bazan iya jure rashinta ba."
Sadik ya ajjiye abinda yake yi sannan ce, "kasan me, in ni ne kai wallahi bazan tsaya ina asarar lokacina akan zata dawo ko bazata dawo ba, zan yi amfani da damar da na samu."
Saheer ya ce, "wacce irin dama?."
Sadik ya ce, "kai fa ka san wanda take aure, ka san meye kuÉ—i a wajansa, da ita zan dinga amfani ina tara kuÉ—i na gina kaina, na gina rayuwata na samu abinda na samu na kama gabana. Ita É—in banza, ai ba itace autar mata ta duniya ba, kuma ba cewa aka yi in ban aure ta ba bazan samu wata macen a duniya ba."
Saheer ya ce, "ban gane ba."
Sadik ya ce, "ka yi amfani da damar da ka samu, ka mayar da ita atm ka fanshe wahalar da ka yi mata, in ba haka ba kana kallon ruwa kwaɗo zai iya yi maka ƙafa ka faɗa ciki har wuta. Ka dinga yi mata waya ƴar miliyan ɗayan nan ta saka maka, ƴar miliyan biyar ɗin nan ga jefo maka ka chafe. Meye naira miliyan biyar a wajan matar Ray? Mutumin da duk juma'a sai ya ƙarar da miliyoyin kuɗi a wajen sadaka? Ai yanzu islaha ta wuce yin kyautar miliyan ɗaya wallahi."
Saheer ya ce, "baka da hankali ai, ni ita nake so ba kuÉ—in ba."
"Sai kai ta fama da wahala kuwa, dan babu yadda ban yi ka kawo ta yi aika tare ba ka Æ™i, kai ga mai kishi. Yanzu ga shi nan ta auri wani, ta yi auren sunna ba ka isa ka hana mijinta yin abinda ya ga dama da ita ba. Ga zunubin hira da matar aure da ka ke kwasarwa kan ka, itama kana É—ora mata.â€
"hakan bazai faru ba, domin a cikin rules É—inta ta haramta hakan."
Sadik ya yi dariya ya ce, "rules É—in nan ai gangan ne, in ka ji ana gangan to wannan yarjejeniyar ce. Shaidu sun shaida, an ba da sadaki, addini ya ba shi cikkakiyar dama akan matarsa."
"Amma ai auren contract suka yi, dole kowa ya bi abinda É—aya yake so."
"Kai! Asalin auren contract na ƙasar turai ba a tara shaidu, babu waliyai, babu sadaki, shiyasa malaman mu suka haramta shi a musulunci. Amma su a nasu auren duk akwai, aure aka yi kamar yadda ake ɗaura ko wanne aure a musulunci, wannan yarjejeniya a tsakaninsu take ba a cikiin addini ko al'ada ba. Ko yanzu ya so babu abinda zai hana bai yi amfani matarsa ba, bata isa ta hana shi ba, kuma bata isa ta ce ya aikata haramci ba. Ka ajjiye batun Islaha, ka ware ka nemi wata ka cigaba da shirin aure, ita kuma Islaha ta zama atm machine ɗinka, ka dinga cire kuɗi duk sanda ka so."
"Duk abinda ta aikata ta yi ne saboda ni Sadik."
"Na san ta yi saboda kai Saheer, kuma na jinjina mata, ba ko wacce mace ce zata yi abinda ta yi ba. Wallahi Islaha tana sonka, tana ƙaunar rayuwarka shiyasa ta sadaukar da rayuwarta saboda kai."
"Shiyasa nake ƙaunar ta, saboda soyyayar gaskiya take yi min."
"Kaima soyayyar gaskiya ka ke yi mata, kuma na yarda tana sonka so na tsakani da Allah, amma kuÉ—i zai iya canjata ko yaushe."
Saheer bai bashi amsa ba ya yi shiru, Sadik ɗin ma ya share sa, dan shi wallahi inda shine sai ya gina kansa da Islaha. Allah ne ya san manufar jaki da bai bashi ƙaho ba, wallahi da sai ya yi abinda ya ga dama da ita, sai ya tara kuɗi son ransa, taje ta cigaba da zaman aurenta sai me? Ai ba a kansa aka fara yin haka ba, ba a kansa mace ta saba yin aure ta bar saurayi ba.
   Islaha tana daga soron gidansu Safeera ta yi nata waya tana ɗauka ta ce, "ke ina wajen gidanku, fito."
Ba jimawa Safeers ta fito tana faÉ—in, "Yau kuma wani sabon salo ne, baza ki shigo ba?."
"Wallahi nauyin Mama nake ji, kuma nasan juma'a ce Baba yana nan."
"To meye, daga ina haka?."
"Na je aiki, sai na biya mu ka gaisa da Hamma."
"Kin kyauta. Ya jikin?."
"Na ji sauƙi, ki ƙa zuwa."
"ke ni bana son dizgi ne, kar nazo a hana ni shigowa shiyasa.
"Nima ranar da na fara fitowa hanani suka yi, sai da Mr Jafar ya zo sannan mu ka shiga."
Safeera ta ce, "balle ni karan kaÉ—a miya." Suka yi dariya tare da tafawa.
Islaha ta ce, "zan koma wajan Yafindo yanzu, ko za ki raka ni?."
"Gaskiya bazan je ba, sai kin dawo. Kuma ina ba ki shawara, ki daina saka rayuwarki a cikin hatsari."
"Yanzu na fara, dan so nake na gama da wannan case É—in, akwai wani binciken na musamman akan masu garkuwa da mutanen, Allah sai dai a tsire ni."
Safeera ta ce, "Allah ya taimaka, sai ki ta yi ai."
"Matsoraciya."
"Tsoro halak ne." Suka tsaya suna hira har driver ya ƙaraso ya ɗauke ta suka tafi.
Kamar wancan lokacin haka Yafindo ta yi mata, islaha babu yadda bata yi akan su yi magana ba amma ta ƙi. Islaha ta ce, "zan tafi kamar yadda ki ka ce, amma ki sani zan kuma dawowa, kuma duk abinda ya samu Zainab alhakkin hakan yana kan ki."
Yafindo kuka take yi tana son faÉ—a mata gaskiya amma tsoro ya hanata, tana son ta ba ta amanar da Zainab ta bata amma baza ta iya magana ba.
A haka islaha ta fito daga gidan cikin wani irin yanayi, ta matso kusa da motar tana tunani, daidai lokacin wani yana zaune a cikin mota yana kallonta tunda ta fito.
Tana fitowa ya ce, "ta fito."
Daga cikin wayar aka ce, "ka bi ta kanta da mota, ka tabbar ka taka ta ta daina numfashi, kuma tsohuwar za mu yi maganinta daga baya."
Islaha babu zato da tsaammi ta ga mota ta yo kanta da gudun tsiya, kafin ta farga har motar ta iso inda ta ke, ta ɗora hannu a kanta cikin firgici ta ƙwalla ƙara.
Nana Haleema.
RDB3P34
Nana Haleema.
Bata san ya aka yi ba kawai ta ji an cillar da ita gefe, bata gama dawowa hayyacinta ba har ta faɗi ƙasa a firgice. Bata gama nutsuwa ba, hangowa take yi mota ta taho da gudu zata take ta, gabaɗaya ta ruɗe ta fita daga hayyacinta, dan gani take har lokacin motar bata wuce ba.
Lawal da ya yi hanzarin janye ta ya tsuguna a gabanta ya ce, "Hajiya kina lafiya?."
Ta kasa ba shi amsa saboda tashi hankali, lawal sai ya ga kamar bata cikin hayyacinta, firgici ya fitar da ita daga ciki hankalinta lokaci ɗaya, numfashinta yana neman tsayawa lokaci ɗaya, firgici da tsoro da tashin hankali ya saka samu attack. Jan numfashi take da ƙarfi, tana ji kamar duniyar ta tsaya cak, dan bata jin iskar da zata wadaci numfashinta ko kaɗan.
Lawal hankalinsa ya tashi matuƙa, ya gigice ya rasa abinda zai yi mata, ga numfashinta yana fizgewa kamar zata sume a wajen.
Ya rasa yadda zai yi mata sai ya ce, "Madam lafiya? Kina jina?." Islaha bata jin abinda yake faÉ—a, numfashi take neman fitarwa, amma ta rasa inda zata samu.
A lokacin wasu mata suka zo wucewa ta inda Islaha take zaune. Lawal da yake neman taimako ya miƙe tsaye yana kallonsu ya ce, "bayin Allah ku taimaka min don Allah, ban san wanne irin yanayi take ciki ba, ku taimaka min ko a mota na saka don Allah."
ÆŠaya ta ce, “Subahanallahi! Me ya same ta?.â€
“Haka kawai numfashinta yake neman tsaywa.â€
“Tana da asthma ne?."
Lawal ya ce, "ban sani ba wallahi."
ÆŠaya ta É—an bubbuga fuskar Islaha ta cr, "baiwar Allah kina jina?."
Islaha bara ji su ba, dan idanunta sun fara lumshewa za su rufe. ÆŠaya ta ce, "athmatic patince fa, ki É—an rage mata rolling É—in nan na kanta. Malam É—an ba mu wani abu a yi mata firfita."
Da hanzari ya buÉ—e mota ya É—auko iv ya basu, aka dinga yiwa Islaha fifita suka rage roilling kanta.
"Kwantar da hankalin ki, ki nutsu" É—aya take faÉ—a a hankali cikin sigar kwantar da hankali.
“Ina da Inhaler, ban sani ba ko zata iya amfani da ita, kar na je na bata a samu matsala.â€
ÆŠayar ta ce, “bata kawai, zata taimaka mata.â€