← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 110

Sashe 62

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abba ya san Rehaan ne lagon Mamy, yasan bata da yarda akan ƴaƴanta musamman Rehaan da take jinsa kamar ranta, hakan ya saka ya tausasa murya dan ya san halin kayarsa indai akan ƴaƴanta ne, bata iya ɗaga ƙafa ko kawar da kai, sai ta nuna maka ɗanta ɗanta ne.

Ya ce, "babu abinda zai same shi, addu'a za ki dinga yi masa, daga nan zuwa safiya zai samu lafiya in sha Allah."

Mamy cikin damuwa ta ce, "Bata san ya ake yi masa in yana ciwon nan ba, kuma har yanzu bata saki jikinta da shi ba, ta ya zata iya kula da shi yadda ya kamata?."

"Sai Ki faɗa mata yadda ake kula da shi ɗin, ni na san zata iya.”

Mamy ta sauke nunfashi ta yi shiru cikin tunani, bata taɓa barin Rehaan da kowa ba in bashi da lafiya, ita take kwana a wajansa ta kula da shi, ta ba shi duk abinda yake buƙata. Ta ya zata iya barinsa tare da matar da ba su karɓi auren da yake tsakaninsu ba? Ta ya zata bar Islaha da shi bayan ta san Islaha ba sonsa take yi ba?. Ba dan bata yarda da Islaha ba, ko dan tana tuna tunanin zata cutar dashi ba ita kawai bazata iya ba.

Abba ya katse mata tunani ya ce, "Ki je ki faÉ—a mata ki dawo, ina jiran ki."

Mamy kamar zata yiwa Abba kuka ta ce, “Ka san ko da Jafar bana iya barinsa, kana ganin daidai ne na bar shi da ita?.”

“Ta fi Jafar mahimmaci ai, ita matarsa ce, Jafar kuma ɗan uwansa ne. Babu abinda zai faru sai alkhairi, kasancewar ta a wajensa sai ya haifar da abinda ba mu yi tunani ba. Sai ki ga an samu maganin ciwonsa a tare da ita, sai ki ga silar zamanta a wajensa ya samu lafiyar da muka jima muna so ya samu. Ki yi fatan Allah ya sa zamansu waje ɗaya ya zama alkhairi.”

Mamy ta yi ajiyar zuciya sannan ta juya ta koma saman jikinta a sanyaye, tana tunanin yadda zata bar Rehaan a hannun Islaha. Ta shiga ɗakin ta ga Islaha a zaune a inda ta bar ta, kamar wacce aka saka remote aka danna mata pause haka ta ƙame a zaune cikin wani irin yanayi. Mamy ta ƙarasa ta janye Rehaan daga jikinta, ta riƙe hannunta suka fito parlour sannan ta ce, “Islaha!."

Islaha har lokacin jikinta a sanyaye yake saboda kwanciyar da ya yi a jikinta, daƙyar ta buɗe bakinta ta ce, “Na’am.”

“Rehaan ba shi da lafiya, yana fama da ciwon cikin da an rasa maganinsa, babu abinda ba a yi akan ciwon nan ba amma babu cigaba, babu ƙasar da ba a kai shi ba amma amsa ɗaya ce ko yaushe, sai ace ba a ga komai a cikinsa ba.”

Islaha cikin sanyin murya ta ce, "Allah ya ba shi lafiya."

"Amin. Zan ɗora miki nauyin kula dashi, na yarda da ke hundrent percent, shiyasa na amince zan bar Rehaan a wajanki ki kula da shi daga nan zuwa safiya. Islaha ban taɓa bawa kowa ragamar kula da Rehaan ba, indai ba shi da lafiya ni ce a gefensa, sai na tabbatar ya samu lafiya sannan hankalina yake kwanciya. Ko Jafar da ki ke ganinsu tare ban taɓa bashi amanar kula da lafiyarsa ba, indai Rehaan yana gidan nan ni ce nake kwana tare dashi har sai na tabbatar ya samu lafiya.”

Mamy ta riƙe hannun Islaha ta ce, "amma yau na bar shi a hannun ki, na bar Rehaan da lafiyarsa a hannunki. Islaha ki yi min alƙawarin za ki kula da shi kamar yadda za ki kula da lafiyar ki, ki yi min alƙawari za ki ba shi kulawar da ko ni ban taɓa ba shi irinta ba. Ciwon yana wahalar da shi sosai, har yanzu bai yi bacci ba, daƙyar bacci yake zuwa idanunsa in yana irin wannan ciwon. Ki kula da shi don Allah, kar ki bari wani abun ya same sa."

Islaha sai kallon hannunta da Mamy ta riƙe take yi, tana jin wani irin abu yana shiga zuciyarta, jin ana ƙoƙarin sakata ta yi alƙawarin da ta san baza ta iya cikawa ba. Jikinta ya yi sanyi, tana jin maganar mahaifiya tana shiga zuciyarta, tana ji mahaifiya tana damƙa mata amanar ɗan da ta haifa dan ta kula mata da shi, ita kuma ta san baza ta iya ba.

Mamy ta ce, “kin yi alƙawari za ki kula min da shi? Ba Rehaan ɗina bane a yanzu, na ki ne tunda kece matarsa.”

Islaha ta kalli Mamy suka haɗa ido, sai ta ji nauyin haɗa ido da ita ta sauke ido ƙasa ta rasa me zata ce. Dan gaskiya baza ta iya kula da Rehaan ba, baza ta iya ba shi kulawar da Mamy ta ke so ta ba shi irinta ba, amma kuma bazata iya cewa Mamy a’a ba.

Mamy ta ce, “kar ki kalli a yadda auren ku ya zo, ki kalli alƙawarin da nake so ki yi min, ki saka a ranki za ki yi komai saboda ni ba dan wani abu ba. Za ki yi min ko Islaha?.”

Islaha ta yi ajiyar zuciya tana jin nauyi a kanta, Mamy ta ɗaure ta da jijiyoyin jikinta, tsakani da Allah ta ya zata yi alƙawarin kula da wanda bata so? Wanda bata so ɗin ma kuma Rehaan da ta fi jin haushinsa sama da kowa a duniya?. Sai ta ɗago ido suka haɗa ido da Mamy, sai ta sake sunkuyar da kai ta ɗaga kai alamun eh.

Mamy ta yi murmushin jin daÉ—i ta ce, "Na gode Islaha, ki kula min da shi yadda ya kamata. In ya farka duk dare ki kira ni, kina da number ta?."

Ta girgiza kai alamun a’a, Mamy ta zare wayar Islaha da ta ke hannunta, ta saka number ta ta kira ta katse sannan ta ce, "kar ki ce dare ya yi, duk dare indai ya farka ina jiran ki."

Islaha ta ɗaga kai tana karɓar wayar ta da Mamy take miƙo mata. Mamy ta ce, "in ya farka yana shan tea, ki haɗa masa tea amma ba milk tea ba, black tea za ki ba sa with less sugar, sannan akwai towel a kan cikinsa, in kin koma ki shoga bathroom ki saka shi a ruwa mai sanyi sannan ki sake ɗorawa a kan cikinsa, if possible kina massaging cikinsa a hankali, kar ki yi da gaggawa, dan in ki ka taɓa cikinsa ko ya ya ne ciwon zai dawo baya."

Islaha sai da ta É—aga ido ta haÉ—a ido da Mamy jin wai ta dinga massaging cikinsa, wai ita ce zata yi massaging cikin Rehaan? Abin har mamaki yake bata.

Mamy ta ce, "ya saba kwanciya a jikina in ba shi da lafiya, bata iya bacci indai ba a jikina ya kwanta ba, yau ki maye gurbina ya kwanta a jikin ki."

Islaha gabanta ya faɗi matuƙa, amma bata ce komai ba tana tunanin yadda zata sauke alƙawari mai girma kamar wannan, dan ta san baza ta iya ba, kuma bazata yi ba. Mamy ta kuma riƙe hannunta ta ce, "kar ki manta, kin yi alƙawari."

Islaha ta É—aga kai ta ce, "zan cika in sha Allah."

Mamy ta yi murmushin jin daɗi ta ce, "Na gode Islaha. Mu je na raka ki…” ta faɗa tana niyar shiga ɗakin, sai kuma ta kalli Islahan ta ce, “but take off your hijjab, zai takura ki, kuma ɗakin babu ac sosai, za ki ji zafi."

Islaha ta buɗe idanunta waje jin wai ta cire hijjab sai ta ce, “ba sai na cire ba Mamy, i can manage it."

"No you can’t, take it off."

"Allah zan iya, ba sai na cire ba."

Mamy ta É—an yi jim kafin ta ce, "okay, mu je."

Mamy ta riƙe hannunta suka shiga ɗakin, suka same shi kansa yana kan pillow yana kwance yana kallon sama.

Mamy ta É—auke towel É—in da yake kan cikinsa, ta shiga bathroom É—insa dan ta ragewa Islaha aikin. Islaha ta kalli inda Mamy ta É—auke towel É—in, ta ga yadda numfashin yake tsayawa a cikinsa kamar baya sauka yadda ya kamata, ga cikin nasa flat kamar ba ya cin abinci, sai haske da kyakykawan gashin da yake kwance kaÉ—an-kaÉ—an.

Idanunta suka ja ta daga kallon flat tummy zuwa ƙasa, ta kalli short ɗin jikinsa da ya fito ta ƙasan dogon wandon jikinsa, idanunta ya kai kan logon da yake jikin short ɗinsa na kamfanin Nike, dan iya logon ne kaɗai ya fito. Haka kawai ta zubawa logon idanu kamar bata taɓa ganin logon Nike a duniya ba, haka kawai logon ya ɗauki hankalinta kamar wani abu na musamman ne a tare da shi.

(logo ne ya ɗauki hankalin ki Islaha kodai-kodai?🤣)

A lokacin Mamy ta dawo da towel É—in da ta É—auke masa ta sake É—ora shi a kan cikinsa, ta dafa goshinsa tana shafa gashin kansa cikin kulawa da soyayya.

Rehaan cikin wata irin murya wacce da bata zuwa cikinsa ya ce, "Mamy."

Mamy ta ce, "Na’am Rehaan."

Sai ya yi shiru bai ce komai ba, daman ta san maganar zata yi masa wahala, dan in yana fama da ciwon daƙyar yake magana.

Mamy ta kalli Islaha da ta ƙame a tsaye kamar soja, ta yi mata nuni da ta matso, Islaha ta ƙarasa a hankali tana kallon yadda yake sauke numfashi a daƙyar, Mamy ta nuna mata inda zata zauna.

Islaha gabanta faÉ—uwa yake yi, ta ji kamar zata kai kanta cikin wuta saboda tsoro da fargaba da bugawar zuciya, ita kanta baza ce ga dalilin tsoron ba, ta san dai tana jin zuciyarta tana bugawa sosai. Kamar mai tsoron wani abun haka ta hau kan gadon tana tattare hijjab É—in jikinta.

Mamy ta kuma yi mata alama da ta cire hijjab ɗin, Islaha ta shagwaɓe fuska dan ita gaskiya bazata iya cire hijjab ɗinta ba, iya rigar bacci ce a jikinta, kuma ko bra bata saka ba, ta ya zata iya cire hijjab ɗinta da rigar bacci a jikinta a ɗakin Rehaan?.
Chapter 62 · 0% Book details