Sashe 72
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Islaha tana ji Safeera tana jan hannunta alamun tsokana, ta share ta ta ce, "ai tambayar nan dole ta zo a farko farko, kowa yana da buƙatar ya san amsar ta."
Chairamn ya ce, "kamar na jawo gobe haka nake ji, Allah ya kaimu" Ta yi dariya ta amsa da amin ta fita daga office É—in.
Sai da suka fita sannan Safeera ta ce, "Mata da miji za su yi interview, mata zata yi hira da mijinta, kuma zata tambaye sa da gaske ne ya aure ta. Kai i can't wait wallahi, ina so na ga yadda lamarin nan zai kasance wallahi."
Islaha ta harare ta ta ce, "sai na fasa zuwa da ke."
"Yi haƙuri boss, dan na ga alama nan gama ke za ki zama Chairman." Su ka yi dariya Islaha ta wuce itama ta shiga wajanta.
Saheer ya damu sosai, sai yanzu yake ganin rashin kyautawa a kalaman da ya yi amfani dasu wajan yiwa Islaha magana. Ya yi tsaki ya fi sai hamsin, yana kallon number ta da ya kasa kira, sai daga baya ya danna ya kira ya kira ta, amma har ta gama ringing bata É—auka ba.
Ya ajjiye wayar dan ya san ta yi fushi, ya san halin kaayarsa sai ya sha wahala sannan zata sauko har ta saurare shi. Ya yi shiru yana tunani, lokaci É—aya fuskar Sudaisa ta gifta masa a idanunsa.
Da hanzari ya buɗe ido ya ce, "ko tana hannunsu, ko an karɓe ta ban sani ba. Allah ka kuɓutar da wannan yarinya, ka bata kariya daga cikin kariyarka, Allah ka kai mata ɗauki cikin gaggawa. Ba ita kaɗai ba, duk wanda ya maƙale a wajan waɗanann mutane Allah ka karɓo su."
Sai jikinsa ya yi sanyi da ya tuna da Sudaisa, gabaÉ—aya sai ya ji damuwa ta mamaye masa zuciya fiye da damuwar Islaha. In ya tuna yadda take kuka tana kiransa da Hamma, da yadda aka ba shi amanar ta, sai ya ji kamar ya ci amanar Sudais.
Amma kuma Allah yana gani, ya san babu yadda zai yi ne, wajen nan kowa ta kansa yake yi, babu mai tunawa da wani duk wanda ya samu dama guduwa yake yi. Tunda ya bar hannunsu kullum sai ya yi mata addu'a, in dai zai saka goshinsa a ƙasa zai faɗawa Allah ya bata kariya. A bayyane ya ce, "Allah ya kai mata ɗauki" ya faɗa yana jan numfashi a hankali.
Sadik ya kira a waya yana ɗauka ya ce, "Ya zan yi ne, islaha ta ƙi ɗaukar wayata, ina son magaa da ita."
"Ahto, ai na faÉ—a ma ka ba ka kyauta ba ka ke ganin kamar ba haka ba, sai ka sake kiranta."
"Baza ta É—auka ba, kaima ka san halinta.
"Ka nemi Safeera, wataƙila zata taimaka."
"Haka ne, na san tana wajan aiki yanzu, zan neme ta mu yi magana."
"Ya dai kamata, dan ba a faÉ—a da mai kuÉ—i." Saheer ya yi tsaki ya kashe wayar ya jingina da bango
_Anya ba dakon wahala nake yi ba? Soyayyar Islaha zata zama riba a gare ni ko wahala? Ta ya zan mallake ta bayan tana ƙarƙashin wanda ya fi ni sau babu adadi?. Anya bazan yi amfani da shawarar Sadik ba?._
A bayyane ya ce, "ina sonta, Allah ya sani ina ƙaunarta sosai."
_Amma ƙaunar amfanin me zata yi maka tunda tana da aure? Furta kana sonta ma da ka ke yi babban zunubi ne. Gwara ka ajjiye son da ka ke yi mata, ka yi amfani da shawarar Sadik ka samu abinda ka samu. In sun rabu shikenan daman haka ka ke so, in basu rabu ba ka ga samu abinda ka samu, in ka zauna a haka wataƙila ka yi biyu babu, babu ita babu kuɗin._
Saheer ya da iska ya miƙe tsaye yana zaga ɗakin cikim tunani. Yana son Islaha sosai, yana fatan ta fito daga can ya aure ta kamar yadda aka tsara, amma sai yake gani kamar fitowarta ta da wahala, anya baxai ɗauki shawarar Sadik ba?.
Sai kuma ya É—an yi jim yana tunani, kafin ya kawar da tunanin ya ce, "bazan iya yi mata haka ba, zan iya jiranta daga nan zuwa ko wanne lokaci, zan jira ta fito ni kuma na aure ta. Da ita kaÉ—ai nake so na rayu, ba kuÉ—i ba." Ya yi ajiyar zuciya ya fita daga É—akin, dan in ya cigaba da zama bai san tunanin da zai yi ba..............
Nana Haleema.
RDB3P55
Nana Haleema.
Islaha sai bayan sallar magrib ta koma gidan, wajan Mamy ta fara shiga ta same su a zaune a kan dining table ita da Rehaan da Banisha. Duk ranar litinin da alhamis haka suke kasancewa, duk satin cikin azumi suke.
Islaha ta girgiza kai tana tunani, tana sake tabbatarwa masu kuɗi suna yiwa talakawa wayo, ta ko wanne ɓangare mai kuɗi ya yi kane-kane ya mamaye komai. A fika kuɗi, a fika kyau, a fika gayu, ibadar ma a fika. Sun samu duniya, kuma suna gida lahirarsu da abinda suka samu a duniyar.
_(Ƴan uwa mu dage da ibada, gidajen masu kuɗi sun yi mana wayo, Allah ya ba su duniya kuma suna neman lahira da abinda suka samu a duniyar. Da wahala ki ga gidan mai kuɗin da ba a azumin nafila, ga sallar dare, ga walha, ga sadaka, aje umra da hajj. Amma sai ka ji talaka yana alfahari yana cewa ni rabona da azumi tun ramadan, kuma bazan sake yi ba sai wani ramadan ɗin. Tun a zamanin Annabi Muhammad SAW akwai wani sahabi da ya ke cewa Annabi masu kuɗi sun tafi da lada. Annabi Muhammad S.A.W ya ce dukkan tasibihi sadaka, dukkan hailalaha sadaka ne, umarni da kyakykawan aiki sadaka, hani da mummuna sadaka ne, ɗauke abin cutarwa a hanya sadaka ne. Mu dage ƴan uwa, an fi mu a duniya, kar mu yarda lahirar mu a wuce mu. Allah ya sa mu dace.)_
Mamy ta kalli Islaha ta ce, "Shigo mana."
Islaha ta ƙarasa ciki ta ce, "Sannu Mamy."
Mamy tana murmushi ta ce, "ya aikin?."
Islaha ta zauna sannan ta ce, "alhamdu lillah."
Banisha ta ce, "Sis ki zo mu yi iftar."
Islaha ta kalli Banisha kalle ta ta ce, "ban yi azumi ba."
"Ai ba sai kin yi ba, ki zo ki ci."
Zata musa ta ce bata ci Mamy ta ce, "Taho ki ci abinci."
Babu yadda zata yi haka ta miƙe ta je ta zauna a kusa da Banish. Rehaan bai ce komai ba, white couscous ne a gabansa yana ci hankalinsa kwance, kamar bai san da wanzuwar ta a wajen ba.
Islaha ta zuba abincin ta fara ci babu wanda yake magana a cikinsu. Kiran wayar Rehaan ya katse shirun parlour, zai É—auka Mamy ta É—auke wayar ta ce, "zaman ka a wajan nan sau nawa kana receiving calls? Ka ci abinci, ka yi maganar in anjima." Bai ce komai ba sai murumushi da ya yi ya cigaba da cin abincinsa.
Islaha gabaɗaya ƙhamshin turarensa ya cika mata hanci, duk da ba cutar da ita yake yi amma yana hawar mata kai.
Mamy ta kalli Islaha da bata cin abincin yadda ya kamata ta ce, "Daughter bakya cin abincin, ko ba ki da lafiya?."
Islaha ta langwaɓar da kai ta ce, "na gaji ne kawai."
Mamy ta ce, "Ayya ki gama ci sai ki je ki huta."
Islaha ta ce, "To."
Wayar ta da ta ajjiye a kusa da ita aka kira, ta kalli screen ɗin ta ga Hamma sai ta yi ƙaramin tsaki ta kashe ƙarar wayar.
Banisha ta É—auki wayar Islaha ta ce, "iphone 12 Sis?" Ta faÉ—a tana buÉ—e idanu irin wacce ta ga abin mamakin da ya ba ta tsoro.
Banisha ta ce, "You're still using this old phone?."
Islaha bata ce mata komai ba dan bata san me zata ce ba, ta dai yi murmushi kawai ba. Mamy ma bata ce komai ba, Islaha ta É—auki wayar ta ce, "Mamy zan je in huta."
Mamy ta ce, "Take care" ta yi murmushi ta É—auki jakar ta ta fita.
Mamy ta kalli Rehana da ya yi kamar bai san da zamanta ba har tashinta, nan kuwa yana kallonta yana tuna idanunta da suka fito waje da ya ritsa ta ta kasa yin komai, bakin rashin kunya ya mutu.
Mamy ce, "Rehaan Islaha matarka ce, ba girman ta bane ace tana using ƙaramar waya kamar wannan."
Ya kalli Mamy ya ce, "Mamy ni ban san wayarta ba, ban taɓa ganin wayar ba har yanzu."
"Yanzu ka ji ai."
"Okay Mamy, ki canja mata kawai, ni na gaji Mamy" ya faÉ—a yana tashi ya fita.
  Islaha sai da ta yi wanka sannan ta yi sallar i'sha ta canja kaya ta zauna tana tsara tambayoyin da zasu yi guest ɗinsu gobe.
Knocking ƙofar ɗakin aka yi ta kalli ƙofar sai ga Banisha ta shigo da sallama. Islaha ta yi murmushi ta ce, "Kiddo shigo mana."
Banisha ta ƙarasa kusa da ita ta miƙa mata leda ta ce, "ga shi in ji Mamy."
Islaha ta karɓa ta buɗe ta ɗauko kwalin iphone, ta kalli Banisha da har ta juya ta fita.
Islaha ta buÉ—e kwalin ta ga iphone 17 orange colour, ta fito da wayar tana juyata a hannunta cikin mamaki ta ce, "maganar da Banisha ta yi akan wayata shine har an canja min wata? To me tawan ta yi?" Ta faÉ—a tana É—aukar wayarta tana juyata a hannunta, sai kuma sake kallon sabuwar.
Islaha ta rasa me zata yi, murna zata yi ko akasin haka?. Mamy tana da kirki sosai, haka Banisha tana da kirki kuma suna sonta shiyasa suke kyautata mata, amma ita bata so wata alaƙa mai ƙarfi ta dinga shiga tsakaninta da ƴan gidan, tunda ba zama tazo yi ba, lokaci take jira ta kama gabanta. Amma ta ga alama Mamy da gaske ta ke yi, da gaske ta karɓe ta hannu biyu a matsayin matar ɗanta ba kamar farko ba.
Tana wannan tunanin sai ga Banisha ta dawo ta ce, "Kawo wayar ki na yi miki backup Sis, ba class É—in ki bane a gan ki da Iphone 12, tun 2020 aka yi ta" ta faÉ—a tana É—aukar wayar.