← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 110

Sashe 89

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abba ya É—an yi shiru yana nazarin abun cikin wani irin yanayi mara daÉ—i, sai kuma ya É—auki waya ya kira Rehaan amma bai same shi ba.

Abba ya ce, "in dai haka ne ban ga amfanin zama da ita ba, wanne irin tozarci da iskanci ne wannan? Hotunan tsaraici tare da wasu mazan a duniya, kuma a gidana?. Bazan ɗauka ba wallahi, bara na je na samu Daada, dole ta bar gidan nan tunda dmana ba a san da auren ba, kuma daman ba ƙaunar ta yake yi ba" ya faɗa tana miƙewa ya fita Mama ta bi bayansa tana murnar haƙarta ta cimma ruwa.

Nana Haleema.

RDB3P65
Nana Haleema.

 Islaha tunda suka tafi ta ke kuka, kuka take yi mai taɓa zuciya duk sun yi shiru suna jinta. Saheer ya juyo ya kalle ta ya ce, "Islaha don girman Allah ki daina wannan kukan." Bata daina ba har zuka je gidansu Saheer.

Da yake ba a nutse ta ke ba tare suka shiga har falon Baffa da ba ya nan. Saheer ya ɗauko mata ruwa ya miƙa mata ya ce, "ki sha ruwa."

Kai take juyawa kawai amma bata iya magana, numfashinta ya fara sarƙe ta saboda takura kanta da ta yi. Sadik cikin sanyin jiki  ya ce, "waye ya fitar da asalin hotunann nan? Wanne account ne ya fara posting?."

Safeera da ta ke riƙe da Islaha ta ce, "babu wanda ya sani, kawai an wayi gari sun baza duniya, tun ƙarfe huɗu na safe aka saka su har yanzu ba a daina ba."

Sadik ya sake kallon hotunan sannan ya kalli Safeera ya ce, "wannan hotunan haɗawa aka yi, ba Islaha bace, amma kuma bai yi kama da AI ba ko kaɗan, ya yi kama da real hoto na haƙiƙa."

Saheer ya miƙe ya ce, "duk wanda yake da hannu akan yi mata haka wallahi sai na yi ƙararsa a human right, sai an ƙwatar mata haƙƙinta."

    "Haƙƙinta ɗin ubanka za a ƙwatar mata? Ka ga yarinya tsirara muraran ka ce wai za ka ƙwatar mata haƙƙinta?. Kai yanzu sai an faɗa maka ta cikin hoto nan Islaha ce? Ko kana so ka ce min  arhar jikin bata bai zo inda ka ke ba balle ka banbance itace ko ba ita bace haɗawa aka yi?."

"Ni daman nasan ya san za a rina, ko ba a faɗa ba an san Islaha tantiryar ƴar iskar yarinya ce, kuma bana shakka cikin shege iyayenta suka yi suka haife ta, in ba shege ba babu mai aikata abinda ta aikata. Shi kansa auren da aka ce ta yi ban yarda da shi ba wallahi, tana can suna sheƙe ayarsu da sunan aure, amma waye zai ɗauki wannan ragowar ƙartin a matsayin matar aure? Sai dai zaman bariki!!" Mama ta faɗa tana shigowa tana kallon su.

Saheer zai yi magana ta dakatar da shi ta ce, "na hana ka shiga sabgar yarinyar nan ka ƙi ji, ko da yake ba laifin ka bane, laifinta ne. Ita da ke da aure tana bibiyar ka dan ance tana kwana da wasu mazan ba abin ƙin yarda bane, kaima Allah ne ya kare ka da yanzu kana cikin lissafi, wataƙila da hotonka yana nan yana yawo. Ni Islaha ko me akace min ta aikata da gudu zan amince, tunda ni na san yar iska ce!."

Islaha ta miƙe da gudu ta fita daga falon, Safeera ta rufa mata baya a guje suka fita.

Saheer zai bita Mama ta ce, "kar ka sake ka fita, ka dawo ka zauna, su dai su je, amma kai ban aike ka ba."

Ya kalli Mama ya ce, "Don Allah Mama..."

Mama ta ce, "wallahi baza ka je ba, ka zauna a nan."

Ya zauna kamar ya kurma ihu, abu ya haɗar masa goma da ashirin. Mama ta zauna ta ce, "aje can a ƙarata, ɗana dai wallahi ya fi ƙarfin ki."

Islaha tana fita ta samu napep kawai ta shiga, Safeera daƙyar ta iya shiga itama ba tare da ta san inda zasu je ba.

Kuka Islaha take yi sosai, cikin tashin hankali Safeera ta ce, "don Allah ki daina wannan kukan, ki nutsu mu gano daga ina matsalar take." Bata ce komai ba sai kuka, ta ɗago ta jingina da ƙarfin napep ɗin tana kuka.

Mai napep É—in ya kalle ta ta mirror, ya kalli wayarsa sannan ya ce, "wannan ai itace wacce take trending yau ko? ÆŠazu na gama kallon video ta, gaskiya mun ga banza."

Islaha ta nufi fita ta window machine ɗin yana tafiya, Safeera ta dakatar da ita cikin ɗaga murya ta ce, "ki nutsu Islaha, ki tsaya mu warware wannan matsalar, ki daina wannan abubuwan don Allah!!." Hanata motsi Safeera ta yi, ta riƙe hannunta da ƙarfi yadda baza ta motsa ba, sai juya kanta take yi wanda ya yi mata nauyi ga ciwo.

A farkon estate ɗin napep ɗin ya tsaya, ta fita da sauri Safeera ta ba shi kuɗin ta bi bayanta. Babu wanda ya yi musu magana, ko takalmin babu a ƙafar Islaha ta shiga gidan a guje.

Rehaan yana zaune a parlour ya ke ganin abinda ta faru, gabaÉ—aya sai ya rasa nutsuwarsa ya rasa abinda zai yi, ya rasa me zai yi dan komai ya tsaya masa cak kamar wanda aka tsayarwa da gudun jini. Sai daga baya ya É—auki waya ya kira Jazy yana É—auka ya ce, "me yake faruwa ne haka?."

Jazy ya ce, "na ga hotuna da video Islaha yana ta yawo a duniya, Shi ka ke nufi?."

Cikin kasala da damuwa ya ce, "Na faÉ—a maka yarinyar nan bata dace dani ba, ni na san halinta tun a Jeddah. Ka kalli abinda yake faruwa a yanzu."

"Ina zuwa, yanzu zan kawowa Mamy saƙo, zan shigo" ya faɗa yana yanke wayar.

Rehaan ya sake kallon video yana runtse idanunsa, wani irin abu yake ji a ƙirjinsa wanda dole sai da ya kife wayar tana tattauna lips ɗinsa.

A lokacin Islaha ta faɗo kamar an cillo ta, kawai ta zube a corridor da yake a farko kafin ka shigo ta haɗa kai da guiwa tana kuka mai sauti da taɓa zuciya.

Safeera ta shigo ta zauna a kusa da ita tana hawaye ta ce, "Islaha wannan kukan ba mafita zai bamu ba, ya kamata ki nutsu."

"Safeera ni ce, jikina ne!...."

Sai kuma ta dakata jikinta yana karkarwa ta ce, "Ni na san ni ce, ni na san jikina ne.....!"

Ta É—ago tana kallon Safeera ta ce, "amma kin san ni ba Æ´ar iska bace ba ko? In kowa bai yarda dani ba ke za ki yarda Safeera...."

Ta sake dakatawa da magana, tana jan numfashi ta ce, "Ki faÉ—awa duniya ni ba Æ´ar iska bace, ban san ya aka yi haka ya faru ba."

Safeera tana kuka ta ce, "Ba ke bace, wallahi bake bace Islaha."

"ki tashe ni daga baccin nan Safeera, ki saka na farka kafin na mutu a cikinsa."

"Baza ki mutu ba Islaha, ki daina faɗa kin ji" ta faɗa tana kuka itama mai taɓa zuciya.

Numfashin Islaha ya fara sarƙewa, saboda wajan babu a.c ga zafi ga shi tana kuka ga damuwa mai tsanani. Hankalin Safeera ya sake tashi ta ce, "Islaha ki nutsu don Allah, kar ki samu attack, ki dawo hankalinki, don Allah ki daina kuka."

Islaha bata jin abinda Safeera take cewa, numfashin ya fara tafiya inda bata yi zato ba, saboda yanayin ya gigita ta sosai.

Rehaan yana zaune yana kallonsu, yana ji yadda ta ke magana tana kuka, hakan shi ya zuba mata ido kawai yana yi kamar ana yi masa wanka da ruwa mai sanyi, tsigar jikinsa tana tashi, gabaÉ—aya jikinsa ya gauraye ya yi sanyi sosai.

Ganin yadda take yi alamun zata samu attack bai san ya miƙe ya ƙaraso inda take zaune ba, sai da ya ƙarasa sai kuma ya rasa me zai ce, kawai sai ya tsaya tana kallonta zuciyarsa tana bugawa.

Safeera ta kalle sa ta ce, "Mr Rehaan Islaha!....."

Cikin kuka ta ce, "ka taimaka mata kar ta mutu" ta faÉ—a tana hawaye.

Ambaton mutuwa da Safeera ta yi ya saka ƙirjinsa bugawa da ƙarfi, ya kalli Islaha ya ga abaya ce a jikinta kuma na ta naɗe kanta da mayafi, kamar mai jin tsoro ya tsunguna a kusa da ita yana kallon yadda numfashinta yake ƙoƙarin fizgewa daga jikinta.

Yadda fuskarta ta koma yake kallo, yana ji zuciyarsa tana rawa sosai, ɗaci da zafi yana mamaye masa ko ina har kan harshensa. Ya haɗɗiye yawu apple adam ɗinsa yana up and down, ya miƙa hannunsa ya zare pin ɗin mayafinta ya warware sa ya buɗe.

Rehaan ya kalli Safeera ya ce, "ina inhaler É—inta?."

Safeera tana kuka ta ce, "ba a san inda take ba."

Rehaan ya sake kallon Islaha yana ganin yadda hawaye ya ke zarya akan fuskarta. Ya haɗɗiye abu mai ɗaci, yana jin zubar hawayenta a cikin zuciyarsa, yana ji jikinsa yana karkarwa saboda kukan da take yi, sai ya matsa kusa da ita sosai, ya miƙa hannunsa ya kwance gashin kanta. Ya kalli kalli ƙirjinta, ya ɓalle buttons biyu a gaban abayar jikinta.

Ya waiwayo ya kalli Safeera da take hawayw ya ce, "kunna switch."

Ta miƙe ta kunna ac, shi kuma ya zuba mata ido yana kallon ta, gashinta ya rufe mata fuska ya janye mata gashin fuskarta ta fito sosai.

Ya kalli Safeera ya ce, "ki bata fresh air."

Ya faɗa yana miƙewa ya koma parlour, ya ɗauko mata ruwa ya dawo ya tsuguna a kusa da ita, Safeera tana gefe tana yi mata firfita da mayafinta, shi kuma ya saka mata robar ruwan a bakinta.

Ta haɗe haƙoranta taƙi ba da damar da zai saka mata ruwan, cikin raunin murya ya ce, "Take it!."

Ta buɗe bakinta ya bata ruwan ta sha, ya rufe ya ajjiye yana kallonta bai motsa ba. A hankali ta nutsu, ta kwanta a ƙasa tana jan numfashi mai ƙarfi, hawaye yana cigaba da sauka daga idanunta har lokacin basu tsaya.

Jazy yana tsaye yana kallon komai ba tare da sun san ya shigo ba, dan Islaha ta ba shi tausayi matuƙa, yana ji kamar shima ya yi mata kuka saboda tausayu.
Chapter 89 · 0% Book details