← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 110

Sashe 85

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kowa ma zai iya!" Ya furta yana cize bakinsa, cikin wani irin yanayin da bai taɓa jin irinsa ba.

Ya ɗan girgiza kai yana kallonta, kafin ya sake yin ƙasa da muryarsa, cikin soft vioce ya ce, "tunda kowa zai iya ban ga amfanin rufe jikinki ba, I can also see you without a towel!" ya faɗa yana zagawa da hannunsa bayanta, ya saka hannunsa a inda ta ɗaure towel ɗin ta baya, ya ja shi da ƙarfi ya zare shi gabaɗaya.

Nana Haleema.

RDB3P62
Nana Haleema.

Babu zato babu tsammani ta ji ya fizge towel ɗin jikinta, tsabar gigicewa da ruɗewa a wajan ta tsaya cak, kanta yana ƙara irin ƙuuuu kamar wacce ta buge a kanta bata dawo daidai ba, ganinta ya ɗauke, kunnenta ya toshe, komai na ta ya tsaya cak ta rasa a wacce duniya ta ke.

Cikin sacanni sanyi a.c ya ratsa sassan jikinta, sai hankalinta dawo jikinta, ta gigice ta rasa inda zata saka kanta, ta yi ƙara mai ƙarfi, ta rasa inda zata saka kanta saboda tashin hankali. Ta jawo bedsheet a gigice ta kulle jikinta har tsakiyar kanta, kawai ta fashe da kuka mai sautin da ya dawo da Rehaan duniyar da ya tafi.

Ray duk yadda ya so tsayar da idanunsa a iya fuskarta kasa ya yi, shi bai cire mata towel dan ya kalli jikinta ba ko kaÉ—an, ya yi ne dan ta ce kowa ma zai iya, shiyasa ya yi ba dan ya kalle ta ba sai dan ya ga yadda fuskar mara kunya zata koma.

Amma sai ya kasa sarrafa kansa, sai ya kasa tsayar da idanunsa a iya fuskar ta, sai ya kasa sarrarafa ganinsa a iya fuskarta, bai san lokacin da idanunsa suka sauka daga kan fuskarta zuwa wani wajen ba, bai san me ya faru ba kawai ya tsinci kansa dumu dumu yana kallon ko ina na jikinta.

Duk da ɗaki ba shi da wadataccen haske, amma hakan bai ɓoye bayyanar brown and shining skin ɗinta ba, babu inda bai gani a jikinta ba, babu abinda idanunsa ba su ganar masa ba, babu abinda bai haddace tsaf a cikin idanunsa ba. Duk ya so idanunsa su tsaya a kan fuskar ta kawai, ko dan ya ga yadda idanun mara kunya zai yi. Amma dai kash! Ya kasa yin hakan.

Islaha da ta gama gigicewa jikinta karkarwa yake yi saboda tashin hankali, jinta take yi kamar ba a duniya take ba saboda tsabar tashin hankali da ruɗewa. Duk da ta rufe jikinta har kanta, ji take yi kamar har lokacin yana tsaye yana kallon jikinta da babu komai, ji take kamar ƙare mata kallo yake yi. Ta dafe kanta ta yi ƙara mai ƙarfi, tare da fashewa da kukan da yake zuciyarta.

Ƙarar da ta yi ita ta sake fargar da Ray daga duniyar da ya afka, ya ɗan sauke ajiyar zuciya yana kallon yadda ta cukwikuye bedsheet ɗin, ga shi yana shaking alamun jikinta rawa yake yi.

Sai ya kasa motsawa, yana jan numfashi mai ƙarfi yana saukewa a hankali, apple adam ɗinsa yana up and down, tsigar jikinsa ta tashi, gashin jikinsa na ko ina ya fito ya miƙe, yana jin tsirgawar wani abu kamar wanda ya sha lemon tsami.

Cikin wannan yanayin ya fara ja da baya, ya fara tafiya a hankali har lokacin yana kallon yadda take kuka a cikin bedsheet, ya shafa gashinsa tare da lumshe idanu yana hango abinda ya gani a jikinta musamman ƙirjinta da nan ya fi fitowa sosai, ya fi ko ina tsayawa cak a idanunsa wani abu yana fizgarsa da ƙarfi kamar zai kayar dashi. Da zafin nama ya juya ya fita daga ɗakin da sauri.

Islaha ta jima tana kukan da bata san na meye ba, ta yi kuka mai yawa wanda bata san adadin lokacin da ta ɗauka ba. Kanta ya fara ciwo, ta fara jin numfashinta yana sarƙewa aalamun zata iya samun attack a ko yaushe. Ta buɗe kanta da ta rufe iya jikinta, fuskarta ta tasa saboda kuka ga kanta ya yi nauyi.

In ta tuna babu komai a jikinta ta tsaya a gabansa bata sanin hawaye yana cigaba da zuba daga idanunta. Jikinta ya yi sanyi, zuciyarta bugawa take yi saboda tashin hankali, ta kwanta lamo tana tuna abinda ya faru. Kawai sai ta fara marin kanta, ta ko ina dukan kanta take yi ko zata wuce takaicin da yake zuciyarta.

Tana ji wayarta tana ƙara amma ta kasa kallonta balle ta duba, zazzaɓi ya rufe ta lokaci ɗaya, ciwon kai ya sake saukar mata.

_Rehaan fa, shine ya ganni babu kaya a jikina._

Abinda take maimaiwa kenan a zuciyarta, ga shi ta kasa tashi ta saka kayan ko zata ji sauƙin sanyin da take ji, ta jima a haka tana tunani, komai ya tsaya mata kamar ba a dumiya take ba.
Daƙyar ta iya motsawa ta saka doguwar rigar ta ta bacci, ta koma ta kwanta tana ji kamar har lokacin yana tsaye yana kallon mata jiki.

    Rehaan da ya fita daga ɗakin a parlour ya zauna ya yi shiru yana kallon waje ɗaya bai yi komai ba, a hankali yake sauke numfashin da ya tsaya masa a ƙirji yana haɗɗiye yawu, apple adam ɗinsa yana up and down, jijiyar kansa tana harbawa, har lokacin tsigar jikinsa bata daina tashi ba. Ya saka hannu ya hargitsa gashin kansa, ya jingina da kujera ya furzar da iska mai zafi. Da ya rufe ido ita ce ta ke zuwar masa a tsaye babu komai a jikinta, sai ya yi sauri ya buɗe yana ji zuciyarsa tana bugawa da ƙarfi.

Ya kalli ƙofar ɗakin da ya daina jin kukanta da ya ke jiyowa tunda ya fitowa. Ya yi ruf da ciki akan kujerar ya yi shiru, itace kawai take gilma masa a idanunsa da ƙwaƙwalwarsa, zuciyarsa tana harbawa na wuce ƙa'ida. Yanayin ya zamar masa baƙo, bazai ce ga asalin abinda yake damunsa ba, ya san dai yana jin kansa kamar ba shi ba. Ya jima a haka a kwance, kafin ya miƙe tsaye sai wayarsa ta fara ringing, da ya duba ya ga Jazy ne sai ya share bai ɗauka ba.

Kamar zai É—auki key É—in mota sai kuma ya fasa dan yadda yake jin cikinsa bazai iya driving ba, ya shiga É—aki ya wuce bathroom ya sakarwa kansa ruwan sanyi ba tare da ya cire kayan jikinsa, ya rufe idanunsa yana hango fuskar Islaha da surarta suna gilma masa a idanunsa.

Ya jima a haka sosai a tsaye yana fitar numfashi a wahale, ya jima a tsaye ruwa yana dukan jikinsa, kafin ya fito daga shower glass ɗin, ya tsaya yana kallon kansa a madubi yana ji kamar ana canja shi gabaɗaya, sai ya ga kamar ba wancan Rehaan ɗin bane wani daban ne wannan. Daƙyar ya samu ya yi drying gashinsa, sannan ya fito closet ya canja kaya ya kira driver ya sauka ƙasa.

Har zai gifta kitchen sai ya ji motsin chef a ciki, ya tsaya cak yana kallon kitchen É—in amma ya kasa shiga. A lokacin Chef É—in ya fito da tray a hannunsa zai ajjiye, ganin Rahaan sai ya tsaya cikin girmamawa ya ce, "Sir What do you want?."

Ya zuba masa ido kawai bai ce komai ba, yana tuna shima ya ga Islaha da towel a jikinta. Ya runtse ido yana taune lips ɗinsa, ya buɗe ido ya kalle shi ya ce, "go back to England, sandra will replace you and continue the work here.” Abinda ya faɗa masa kenan ya fita daga falon yana jin haushin kowa a zuciyarsa.

Guest house suka wuce da driver, yana shiga ya cillar da wayarsa a akan kujera, ko haske parlour bai kunna a falon ba ya zauna. Ya yi shiru yana kallon wani waje daban kamar mai karanta wani abu, duk inda ya waiwaya ita yake kallo, sai ya ga kamar tv aka saka aka kunna masa surarta yana gani.

"Ya Salam! Ya Salam!!"

Ya furta cikin wani irin yanayi yana hargitsa gashinsa, yana fitar da numfashi mai ƙarfi, yana ji dama yana da dama da ya goge abinda ya gani daga ƙwaƙwalwarsa. A lokacin Jazu ya shigo parlour, ganin Rehaan a zaune sai ya kunna haske sannan ya ce, "Kai kuma fa? Ina ta kiran ka ba ka ɗauka, daman ina so na tambaye ka ne."

Rehaan ya ɗago ido ya kalli Jazy da yake ƙarasowa, Jazy ya ga yadda idanun Rehaan suka canja ga fuskarsa ta yi ja, ga wani irin yanayi da bai taɓa ganinsa akan fuskarsa ba, sai ya ji tsoro ya kama shi ya buɗe idanunsa ya ce, "ciwon cikin ne ya motsa? Na ganka wani iri.”

Rehaan bai iya ba shi amsa ba ya lumshe idanunsa bai ce komai ba, dan bazai iya buÉ—e baki ya yi magana ba, in ya buÉ—e baki ya yi magana gani yake kamar Jazy bazai ji abinda zai faÉ—a ba saboda raunin da zuciyarsa ta yi. Jazy sai ya share sa bai ce komai ba, ya É—auki file É—in da yake gefensa yana dubawa.

Ƙarar wayar Ray ya saka Jazy ya kalle shi, ya ga ya ɗauka kamar baya son magana ya ce, "Kiddo Please, i will call back" yana faɗa ya kashe wayar ya ajjiye.

Jazy ya cika da mamaki mai matuƙar yawa, bai taɓa ganin yanayin da ya canja sa haka ba, har Kiddo zata kira sa a waya ya ce zai kira ta anjima, duk busy da yake cikin indai Mamy ko wani nasa zasu kirasa sai ya ɗauka, ko da meeting yake yi.

Jazy bai ce masa komai ba dan yasan in ya tambaya shiru zai sake yi masa, gwara ya ƙyale sa in ya gaji ya san zai faɗa masa da kansa.

"Salman...."

Jin hakan sai Jazy ya kalle sa yana mamakin wannan wanne irin yanayi ne da ya canja masa muryarsa haka? Hakan ya saka Jazy ya tsaya cak da abinda yake yi, dan yana so ya ji musabbin wannan canjin da inda ya fito, dan shi dai tunda yake da Rehaan bai taɓa ganinsa haka ba.

Jazy a nutse ya ce, "ciwonsa ne dai?."
Chapter 85 · 0% Book details