Sashe 17
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Ni daman na san baza ki taɓa aurensa ba, an bani labarin yadda larabawa suka buɗe miki ido da kuɗi a Jeddah, da yadda suka mayar dake kamar matarsu suna yin abinda suka ga dama dake. Ki je can ki cigaba da rayuwa, amma in na sake ganin ƙafar ki a gidan nan sai na saka an yi miki abinda ba ki taɓa tunani ba!."
Islaha ta kasa magana sai kuka, ba kukan komai take yi ba sai kukan kalmar ta zaɓi kuɗin ta bar halacci da suke faɗa, in suka faɗi maganar sai ta ji kamar ana soka mata kibiya a ƙirjinta, ta ya zata zaɓi kuɗi akan Hamma?. Wanne irin babban kuskure ta tafka a rayuwarta haka? Meyasa ta amincewa zuciyarta ta kai ta ga danasani, meyasa abinda ta ke yiwa kallon ƙaramin abu yana neman zamar mata ƙadangaren bakin tulu? Meyasa ta amince da wannan auren wani ba Hamma ba tun farko?.
Bata gama tunani ba, taji an ja hannunta da ƙarfi an fizgota daga cikin ɗakin. Ƙiris ya rage bata faɗi ba, ta juyo tana kallon Saheer da yake kallonta idanunsa sun yi ja sosai, ya kasa magana sai kallonta kawai yake yi, ga shi ya rame sosai.
Islaha ta zube a ƙasa ta ce, "Hamma ka yarda ni Islaha zan zaɓi kuɗi akanka?."
Mama zata yi magana Islaha ta dakatar da ita ta ce, "Mama don Allah, ki bar shi ya bani amsa da bakinsa, na san shi ya san wacece Islaha."
Islaha ta kalli Saheer ta ce, "Hamma ka yarda da kalamansu? Ka yarda na zaÉ“i kuÉ—i na bar ka Hamma? Na san na yi kuskure da na auri wanin ka, amma zan dawo gare ka, in ban dawo gare ka ba ni ba Æ´ar halak ba ce!.â€
Mama ta ce, “ai ba sai kin maimaita ba, daman ke ba Æ´ar halak ba ce, kuma za ki tabbatarwa da kowa kalaman ki da kanki.â€
Shi dai ya zuba mata ido kawai bai ce komai ba, kuma in bai yarda da gaske ta zaɓi kuɗin akansa ba da me zai yarda? Ga shi dai a gaban idanunsa ta yi aure a gidan da ya yi tambari a garin a kaf Adamawa.
Ɗan gidan shine lamba ɗaya a cikin masu kuɗin garin, duk wanda ya ji wannan maganar dole ya amince da ta auri kuɗi ta bar shi. Yana jin zafin hakan a ransa, yana jin ciwo da kishi mai tsanani, yana ji kamar zuciyarsa zata buga, yana ji kamar zata faso ƙirjinsa ta faɗo, amma bai san ta yadda zai yi maganin abun ba.
Hanan ta ce, "malama ki tashi ki bar mana gida, ki je can ki zauna a gidan da ki ka zaɓa. Ki bar Hamma a nan, ke ki je gidan masu kuɗin da ki ka zaɓa a matsayin gidan mijin ki. Kin cutar da Hamma, kin zaɓi kuɗi akan halacci!."
Mama ta kalle shi ta ce, "Kai Saheer! Ka kalle ta ka faÉ—a mata kar ta sake zuwa wajan ka, ta je ta zauna da mijin da ta aura saboda kuÉ—i."
Saheer ya kalli Islaha da take kallonsa tana kuka, ya ɗauka kai bai ce komai ba sai ya koma da baya ya shiga ɗaki ya rufe ƙofar.
Babu wanda ya cewa Islaha komai, suka shige ciki suka barta a wajan ita da Safeera. Safeera itama kuka take yi sosai, dan yanayin yadda suka yiwa ƙawarta ta abin bai yi mata daɗi ba, musamman in ta tuna yadda aka yi auren, da ya yadda ta sadaukar da rayuwarta da farin cikinta a kansa, sai ta ga basu yi mata adalci ba ko kaɗan, har suna cewa ta zaɓi kuɗi akan halacci. Ko shi Saheer ɗin da ya ƙi magana bai yi mata adalci ba, tunda ya san halinta ya kamata ya saurare ta ko ya ya ne.
Safeera ta goge idanunta ta dafa kafaÉ—ar Islaha ta ce, "tashi mu je Islaha."
Ta miƙe a hankali ta kalli Safeera ta ce, "Na faɗa miki daman ni ba ƴar halak ba ce, jikina yana bani a......"
Safeera ta rufe mata baki ta ce, "kar ki ƙara faɗar haka, Allah ya san zuciyar ki, nima na san silar auren, Sadik ma ya san dalilin auren. Mu mun san rayuwarki ki ka sadaukar saboda Saheer, shima kuma zai amince da haka, amma na faɗa miki sai ya nutsu sosai."
Islaha ta kwantar da kanta a kafaÉ—ar Safeera ta ce, "Ko magana ya Æ™i ya yi min, ya Æ™i ya kalle ni, na yi dansani ta fi dubu Safeera. Kina ji suna cewa na zaÉ“i kuÉ—i na bar halacci……â€
Muryarta tana rawa tana muna kanta ta ce, “Wai…ni ce na zaÉ“i kuÉ—i akan halacci, Safeera wai ni ake cewa na zaÉ“i Rehaan na bar Hamma. Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Safeera wai na zaÉ“i kuÉ—i akan Hamma…â€
Safeera tana kuka ta ce, “dukkanmu mun san gaskiya, kar ki damu kan ki.â€
“ina ji kamar naita kuka har a tashi duniya."
Safeera ta dinga bubbbuga bayanta cikin rarrashi ta ce, "ki yi haƙuri, ki daina kuka, Allah yana tare dake."
Ta goge hawayenta bata ce komai ba, ta É—auki handbag É—inta da ta cillar, sai kuma ta dafe kanta saboda yadda ya sara mata.
Ta ce, "Kaina yana ciwo, numfashina ba ya fita daidai" ta faɗa tana jan numfashi da ƙarfi.
Safeera ta ce, "Sannu. Ina maganin da aka ba ki a Jeddah?."
"Ya ƙare, inhaler kuma ban san inda take ba, na bar kwalayen a gidan nan, na san yanzu sun zubar."
Safeers ta ce, "zan duba miki ko an saka a cikin kayanki, mu je ki sha magani sai ki koma gida."
Ta girgiza kai ta ce, "wajan aiki zamu je, sannan ina so na je orpanage wajan Yafindo ko ta dawo."
Safeera ta ce, "to mu je."
"Islaha!."
A tare suka kalli wajan da suka ji an kira sunanta, suka ga Sadik ne ya shigo; yana ƙarasowa inda suke taaye yana kallonsu.
Ya bi su da kallo ya ce, "Lafiya dai ko?."
Safeera ta ce, "babu lafiya Sadik, tun ƙarfe bakwai da rabi tana unguwar nan, ta zo wajan Saheer amma ya gaza fahimtar ta."
Sadik ya ce, "Islaha Saheer bazai fahimce ki yanzu ba, Saheer ba a nutse yake ba kwata-kwata, yana buƙatar lokaci kafin ya gane abinda za ki faɗa masa. Abu ɗaya yake kallo yanzu, kin ci amanarsa kin auri wani ba shi ba, kuma su Mama suma sake ɗora shi akan hakan. Dole sai kin sake haƙuri na wani lokaci. Ke kin san halinsa, na tabbatar zai fahimce ki da zarar ya nutsu yadda ya kamata."
Safeera ta ce, "amma ko magana bai yi mata ba, at least ya kama ko sannu ya ce, ai ya fi kowa saninta, masu kuÉ—i nawa ta tsallake saboda shi?."
"Ba goyan bayansa nake yi ba Safeera, amma ina so ki tuna aure ta yi, wani ta aura daban ta bar Saheer; kuma shi bai san dalilinta ba, kuma a ransa yana jin haushinta, ni da ke ne kaÉ—ai mu ka san abinda yake faruwa shi bai sani ba. Ku ba shi dama ya huta tukunna, in ya huta zan yi masa bayanin komai daki-daki."
Islaha ta ɗaga kai ta goge ido ta ce, "shikenan, babu damuwa..." ta faɗa tana fara tafiya, sai jiri ya ɗauke tata yi baya zata faɗi, kafin Safeera ta riƙe ta ta tsaya da kanta.
Sadik ya ce, "ki yi a hankali, ki samu waje ki zauna."
Ta zauna a inda ta saba zama a compound É—in gidan, ta ja numfashi ta ce, "jiri nake ji kaÉ—an."
Safeera ta ce, "sannu, ki huta sai mu je."
Sai kuma ta miƙe tsaye ta ce, "Safeera mu je kawai" ta faɗa tana fita daga gidan da gaggawa.
Sadik ya bi bayanta da kallo cikin tsananin tausayin Islaha, kafin ya shiga wajan Saheer da yake tsaye a gaban window yana kallon duk abinda yake faruwa.
Sadik yana shiga Saheer ya ce, "Wanne abu ku ka shirya wanda ban san dashi ba? Akan me ku ke magana wanda ni ban san maganar ba?....
Nana Haleema.
RDB3P14
Nana Haleema.
Sadik ya kalle sa ganin ya kafe shi da idanu sannan ya ce, "ka zauna tukunna sai na faÉ—a maka abinda ya faru."
Saheer ya ce, "ka faÉ—a min kawai, wanne abu ku ka shirya kai da ita da Safeera?."
Sadik ya kalle sa na wani lokaci ya sauke numfashi ya ce, "Lokacin da ka ke hannun masu garkuwa da mutane, hankalin Islaha ya tashi sosai, in na ce maka ta fi kowa damuwa da halin da ka shiga kar ka musa. A wannan lokacin Baffa ya zo mata da maganar auren ɗan gidan AbdulAziz yola, ta ma kasa fahimtar maganar balle ta ɗauka. Tana ta ɓoye mana bata so mu sani, sai ranar da suka dinga dukan ka suka ce in ba a kawo kuɗi ba sai sun kashe ka, a lokacin ta ce kar a kashe ka zata nemo kuɗin."
Saheer ya zuba masa ido yana jin abinda yake faÉ—a, ganin Sadik ya shiru ya ce, "ina jinka, sai me?."
Sadik ya ce, "shine ta nemi wanda aka ce ana so a haÉ—a su auren, shima ya neme ta, ya ce zai aure ta saboda mahaifinsa yana son ya aure ta ba dan shi yana so ba, ita kuma ta ce zata aure sa in dai zai bata kuÉ—in da za a fanso ka. A kan wannan tsarin ake har yanzu, auren wata biyar ne a tsakaninsu.
Saheer ya zuba masa ido yana kallonsa, sai kuma ga girgiza kai cike da mamakin raina masa hankali da Sadik yayi ya ce, "Kana so ka ce min shi wanda ta aura ɗin, shine ya bata miliyan hamsin kawai dan ta zauna dashi na wata biyar, ita kuma ta amince ta karɓa dan a sako ni, haka ne?."
"Ya ka ke tambaya kamar ba ka yarda da abinda na faÉ—a maka ba?.â€