Sashe 18
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saheer ya yi masa wani kallo ya ce, "kana tunanin zan yarda da wannan shirmen ne? Na lura kai da ita da Safeera bakin ku ɗaya, an sace ta, daga baya ta dawo kuma ta hana ayi bincike, ta tafi ƙasar waje ta dawo da kuɗin da ban san na meye, yanzu kuma ta ɗaura aure da wani, shima kuma ana faɗa min saboda ni ta yi hakan?."
"Tafiyar ta Jeddah wannan bana goyan baya, sace ta ma ban san anyi ba. Amma wannan na sani, a ko ina zan bugi ƙirji na ce dani aka yi. Duk da nayi ƙoƙarin nuna mata illar hakan, ta nuna min ita a kanka babu abinda baza ta yi ba. Duk abinda ta yi saboda kai ta yi, zata zauna da wani a matsayin mijinta na wata biyar saboda ceton ranka da rayuwarka. Ko ka yarda, ko kar ka yarda, wannan maganar itace gaskiya, wallahi bata yi niyar cin amanarka ba, bata yi niyar wulaƙanta ka ko ta zaɓi kuɗi ta barka ba. Wannan shine zance na gaskiya, amma na san babu lallai ka amince."
"Kaima ka san ba ka É—auko layin da zan amince ba, ka san wannan maganar ta ka da wasan yara ta yi kama ba da maganar gaskiya ba, bazan amince da wannan tatsuniyar ba ba Sadik. Haka kawai saboda mahaifinsa sai ya bata miliyan hamsin? Waye shi a garin nan? Shine AbdulAziz Yolan ko kuma shine Rehaan Yolan?."
Sai kuma ya É—an tafi tunani kafin ya ce, "wait! Da farko ta ce mana Rehaan Yola ne ya sace ta har ta É—auko masa kuÉ—i, daga baya ta tafi Jeddah ta ce a can ma ta haÉ—u dashi, yanzu kuma ta dawo ta yi aure a gidansu da sunan auren contaract."
Ya dafe kai yana murmushi mai ciwo ya ce, "na jima ban ga ƴan wasan kwaikwayo kamar Islaha ba, na daɗe ban ga wacce ta ƙware a iya buga game kamar Islaha ba. Gabaɗaya ta mayar da ƙwaƙwalen mu empty, ta saka mun koma yaranta, sai saka mana igiya take tana jan mu inda ta ga dama."
Sadik ya yi shiru dan shima sai yanzu tunaninsa ya kai inda na Saheer ya kai. Tabbas akwai ayar tambaya akan Islaha, meyasa Rehaan yola yake shigowa rayuwarta ta fuska mara daɗi?. Da fari ta ce shi ya sace ta, ta zo ta ce ai shi ta ɗaukowa kuɗi zata je Jeddah ta nemo kuɗin dan ta biya sa, sai kuma ta tafi aiki wata ƙasar, ta dawo tace musu a gidan Rehaan ta yi aikin a can Jeddah. Yanzu kuma batu ake na itace matarsa ce ta aure, duk da yadda abin ya faru da ta yadda suka yi auren, a addini da al'ada matarsa ce ta halak ba ta yarjejeniya ba, tunda ko a lokacin Rehaan ya bar duniya sai ta yi masa takaba ko da bata yi iddah ba. Tabbas akwai abinda Islaha ta shirya, shi kansa yanzu bai yi na'am da lamarinta ba, akwai lauje a cikin naɗi.
Saheer ya katse masa tunani ya ce, "Haka kawai AbdulAziz Yola zai zo wajen Baffa ya ce shi Islaha yake so a aurawa É—ansa? To wanne É—an nasa a ciki?."
Sadik ya ce, "Wannan ita za ka tambaya bani ba."
"Meyasa sai Islaha, duk matan da suke Yola da wajen Yola sai Islaha za a gani ace za a aura? Me yasa Baffa ya amince da auren, shima ya san wannan tatsuniyar ta ku?."
"Baffa bai sani ba, amma shine ya ba da auren Islaha. Shima akwai manufarsa a akan hakan, dan ba dan shi ba da baza a yi auren ba."
Saheer ya girgiza kai ya ce, "Shikenan, an kyauta min kuma na gode. Na yarda da batunsu Mama, Islaha mage ce mai kwanciyar ɗaukar rai, tabbas akwai abinda take burin cimmawa a cikin rayuwarta, da biyu take waɗananan abubuwan. Na gode da sakayyar da na samu daga wajenta, na gode da abinda ta yi min†ya faɗa yana barin wajen.
Sadik ya bi shi da kallo har ya shige É—aki, ya É—an shiru yana tunani sannan ya fita shima zuciyarsa cike da tunanin wannan chakwakiyar ta Islaha.
Islaha suna fita daga gidan ta tsaya a ƙofar gidan ta kawar da kai gefe.
Safeerw ta ce, "idanunki sun yi ja, mu je gida ki wanke fuska."
Ta girgiza kai ta ce, "ki É—auko abinda za ki É—auko daga gidan mu wuce kawai, bazan koma ba." Sanin halinta na taurin kai sai bata takura mata ba ta koma ba, ta koma ta É—auko handbag É—inta suka hau napep suka tafi wajan aiki.
Tunda suka tafi babu wanda yake yiwa kowa magana, Islaha tana jikin window ta saka kanta waje tana shan iska idanunta a kulle. Har suka je bakin gate É—in babu wanda ya ce kanzil, suna sauka Safeera ta biya kuÉ—in suka nufi ciki.
Suna shiga suka haÉ—a ido da Ummi, ta bi su da kallo Islaha kam kallo É—aya ta yi mata ta É—auke kai ta nufi ciki da hanzari.
Da Chairman suka fara haÉ—uwa, ya saki murmushin jin daÉ—i ganin Islaha ya ce, "Barka da zuwa Islaha, da alama an sa ki masoyin na ki ko?."
Islaha ta ƙaƙalo murmushi ta ce, "ina kwana."
"lafiya lau. Ya dawo?."
"Eh ya dawo."
"Allah ya kiyaye gaba, ya kare mu daga sharrinsu."
"Amin ya rabbi, na gode."
Chairman ya ce, "da na san za ki zo ai da na kira ki tun safe kin yi mana labaran ƙarfe shida. Ko da yake, an canja timetable za ki iya zuwa board ki duba. Sannan akwai interview, akwai mutane uku da zamu yi invinting ɗinsu, kuma kin san aikin ki ne. Ki same ni a office in kin huta, akwai maganar da zamu tattauna."
Ta É—aga kai ta ce, "To."
Chairman ya wuce itama ta wuce office cikin sanyin jiki da tunanin mafita.
Tana shiga ta ajjiye jakar ta, ta dafe kai da duka hannayenta ta kunna fankar office ɗin. Sai kuma ta miƙe ta fita zuwa board ɗin da ya ce an canja timetable. A nan ta ga har an canja sunanta an sakata a wacce zata gabatar da labaran safe a satin, sannan akwai inverview da talkshow guda ɗaya. Ta lumshe ido ta buɗe ta riƙe ƙugu tana cigaba da sauke numfashi dan sarƙewa yake yi.
"Hajiya islaha, amarya."
Gabanta ya faÉ—i jin sunan amarya da aka kira ta da shi daga bayanta, ta haÉ—É—iye yawu ta juyo a hankali suka haÉ—a ido da wanda yake tsaye a bayanta.
Nana Haleema.
RDB3P15
Nana Haleema.
Tana juyowa suka haɗa da Muslim, sai ta ƙirƙiro murmushi ta ce, "Alhaji Muslim, ango."
Ya yi dariya ya ce, "da zan samu na zama angon mace kamar ki ai da na more. Ya ki ke, ya Saheer ɗin? Ina fatan yana cikin ƙoshin lafiya."
Ta É—aga kai ta ce, "Lafiya lau yake."
"ma sha Allah, haka ake so daman. Jiya na je gidan ku akan maganar interview É—in da ake so a gayyaci minister of depence amma aka ce min bakya nan, na kira ki sau babu adadi ba ki É—auka ba kuma ba ki kira ni ba.â€
Ta kalle sa ta ce, "ba ka tambayi Safeera ba?."
"ba mu yi magana ba."
"Ina gidansu Safeera."
Mulsim ya harare ta ya ce, "Ni ce min aka yi kin yi aure."
Ta ɓoye tashin hankalin jin maganar auren a bakin Muslim ta ce, "Wanne irin aure, na gaske ko na wasa?."
Ya yi dariya ya ce, "kin fini sani."
Islaha murmusa ta ce, "To na ji kana wani batu ne kamar wata Æ´ar tsana. Yanzu tsakani da Allah sai na yi aure ba ku sani ba? Auren kamar wasan yara, ace har an yi an gama babu wanda ya sani a gidan nan?."
Muslim ya ɗan taɓe baki ya ce, "kin san yanzu celebrities auren sirri suke yi, na sani ko kema shi ki ka yi."
"Nima celebrity É—in ce?."
"Itace mana, waye bai sanki ba, Hajiya Islaha?."
Ta sake murmusawa tana tattaro nutsuwa da dakiya amma bata ce komai ba. A lokacin Saleem ya zo wajan ya ce, "Islaha zamu je É—aukar report, in kin fito daga wajan manager ina jiran ki." Ta É—aga kai ta bar wajan ta nufi office É—in manager.
Muslim ya bita da kallo har ta ɓace sannan ya ce, "meyasa bata so a san ta yi aure? Bayan wanda ya faɗa min ina da tabbacin bazai yi min ƙarya ba? Meyasa ta yi irin wannnan auren na gaggawa haka?."
Ya sake yin shiru yana nazari kafin ya ce, "ya zama dole na nemo abinda yake faruwa, in ma auren sirri ne ni zan buÉ—e sirrin."
Islaha tana shiga wajan manager ta same sa a zaune, itama ta zauna sannan ya ce, "yauwa Islaha, a tsara iv da ya kamata a tura musu ta email, in saƙon bai yu ba sai mu je a kai musu. Ga list ɗin waɗanda nake so in da yuwa mu gansu a satin nan, ko ina suka ce mu je zamu je, dan muna da buƙatar mu tattauna dasu."
Islaha ta karɓi list ɗin ta ce, "in sha Allah zan yi ƙoƙari."
A lokacin aka ƙwanƙwasa ƙofar aka shigo, Safeera ta ƙaraso ta ce, "Chairman ga file ɗin." Ya karɓa yana dubawa.
Daidai lokacin da aka hasko fuskar Rehaan Yola, ana labarin bikin ƙanwarsa da ya tara manyan mutane ciki harda shi da kansa. Islaha bata san ta yi tsaki ba, ta haɗe rai tana ɗauke kanta daga kan tv.
_magana tana ta yaɗuwa akan Rehaan Yola ya yi auren sirri, da gaske hakan ta faru ko kuma ƙaryar mutane ce.?_
Abinda É—an jaridan ya faÉ—a kenan, ta ja wani dogon tsakin da sai da Chairman ya É—ago ya kalle ta, ya kalli tv ya ce, "ba ki gayyato mana shi ba har yanzu, muna ta jira mu ganshi a tv mu Islaha, amma shiru."
Islsha fuska a haɗe ta ce, "Har yanzu bamu yi magana da Mr Jafar ba, daman shine ya yi min alƙawari."
"Ai ya kamata ku yi magana Islaha, bana so wata channel É—in su riga mu gayyato shi har ya yi magana da yarensa, ina so mu zama mu ne na farko."