← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 110

Sashe 67

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Islaha ta ɗaga kai ta ce, "Ban san mahaifina ba, amma na san fuskar Mamana, duk da ina gani kamar a mafarki na santa. Lokacin ya yi nisa da yawa, bazan iya tuna tsahon lokacin ba amma na santa, na san na yi rayuwa da ita. Bazan iya gane fukarta ba, amma ina iya hangen ta a idanuna, abu ɗaya na riƙe kawai, ina kiranta da Mama."

Mama ta ce, "kina shekara nawa aka kai ki orphanage?."

"Na taɓa sakawa an duba min file, ance min ina da shekara takwas na je gidan."

"Akwai sunan wanda ya ki ki gidan?."

"He is just wrote Islaha Muhammad Madibbo, ban sani ba ko sunan mahaifina haka, ko kuma shine kawai ya saka ban sani ba, shiyasa nake amfani da sunan Muhammad as my surnname."

Mamy ta girgiza cikin taushin murya da son rarrashinta da kwantar mata da hankali ta ce, "ba ki san wanda ya kai ki ba?."

"Hamma Saheer ne."

"Meyasa ba ki taɓa tambayarsa a ina ya same ki har ya kai ki gidan ba?."

Ta yi shiru bata ce komai ba, dan ta tambaye shi ba sau É—aya ba amma sai ya ce mata zai faÉ—a mata sai sun yi aure, ita kuma bata matsa masa sosai ba, amma yanzu kam zata yi.

Mamy ta shafa kanta ta ce, "is okay, Ki daina damuwa, in akwai rabo za ki ga iyayen ki wata rana." Bata ce komai ba sai ajiyar zuciya da ta yi.

Rehaan yana jinsu bai ce komai ba, amma tabbas ya ji tausayinta mai yawa, ya ji ina ma zai iya da ya nemo mata mahaifiyata ko dan ta samu soyayyar da yake samu daga wajan Mamy.

Kiran sallar ƙarfe ɗaya ya saka Islaha ta miƙe tsaye ta ce, "Mamy zan yi sallah sannan na wuce wajan aiki."

Mamy ta ce, "okay my love, sai kin dawo." Bata ce komai ba ta wuce ko kallon Rehaan bata yi ba, babu sannu babu ya jiki ta shiga É—aki.

Mamy ta kalli Rehaan da ya É—auke idanunsa daga kan Islaha yana stirring tea da har lokacin bai shanye ba.

Mamy ta ce, "Rehaan!."

Ya kalle ta ta ce, "Ina so a bincika min orphanage É—in da ta girma, ina so a nemo asalin min iyayenta, ina so ta fita daga maraicin da take ciki."

Ya gyaɗa kai amma ya kasa cewa komai, dan gabaɗaya tausayinta ya cika masa zuciya har ya kasa magana, tausayinta yake ji sosai, dan rashin iyaye ba ƙaramin abu bane.

Ya kasa riƙe maganar a zuciyarsa, ya kalli Mamy ya ce, "Ta bani tausayi."

Mamy ta ce, "nima haka Rehaan, shiyasa nake so a yi bincike mai kyau, if possible ka yi magana da Saheer É—in ka ji a ina ya same ta har ya kai ta orphanage. Tunda sai da ta girma aka kai ta ba tana jaririya ba, tabbas akwai dalilin da ya saka aka kai ta can, kuma duk wanda ya kai ta ya san a inda ya same ta. In aka ji inda aka same ta za a iya samun wani abu har a ga iyayenta."

Rehaan ya shafa goshinsa bai ce komai ba ya yi shiru ya fara shan tea É—in da yake hannunsa.

Mamy ta ce, “She looks very decent and modesty, i lover her as my daughter.”

Rehaan yana ji bai ce komai ba, ya cigaba da shan tea É—in yana tunanin ya kamata ya bincika ya nemowa Islaha iyayenta.

    Islaha ko da ta je wajan aiki haka take yin komai a sanyaye, kewar iyayenta take ji sosai, haka kawai Allah ya saka mata kewarsu fiye da yadda ta saba ji. Bata da cikakkiyar walwala har ta fito, a haka suka haɗu da Barr akan case ɗinsu suka tattauna, sannan ta tafi gida wajan Saheer dan sun yi da shi zasu je gidansa da ake ginawa.

Sai da ta je ƙofar gidansu sannan ta yi masa waya, ya fito ya saka ta ta shiga mota suka fara tafiya ba tare da ta san inda zasu je ba. Kallon ta yake yi cikin mamaki ganin fuskar ta babu walwala, kuma tun daga ina yini bata sake cewa komai ba. Hakan ya saka shi ya ce, "Islaha lafiya?."

Ta kalle shi ta ce, "Hamma in tambaye ka?."

"Ina jin ki."

"Za ka faÉ—a min?."

"Me zai hana naƙi faɗa miki?."

Ta sauke nunfashi ta ce, "A hannunwa ka karɓe ni har ka kai ni orphanage?."

Ya juyo ya kalle ta kafin ya ɗauke ya cigaba da tuƙa motar ya ce, "Meyasa ki ke tambaya?."

"Ina so na sani ne."

"na ce zan faÉ—a miki, sai ranar da ki ka zama matata."

"Lokacin ya yi min nisa, ni dai ka faÉ—a min don Allah."

Saheer ya sake kallon ta ganin tana tare da damuwa mai yawa, sai ya yi shiru bai ce komai ba, dan ya san abinda zai faÉ—a maya a damuwa zai sake jefa ta.

Islaha ta ce, "Hamma ka faɗa min, ina jin kewar iyayena sosai..." ta ƙarasa faɗa tana fashewa da kuka.

"Subahanallah!"

Saheer ya faɗa yana tsayar motar dan bazai iya cigaba da tafiya tana kuka ba. Ya ce, "meye na kukan? Ba kin yi min alƙawarin baza ki sake kuka akan hakan ba? Kin ce min baza ki sake tayar da maganar nan ba har sai ranar da muka yi aure. Meyasa za ki dawo da maganar yanzu?."

"Ina ganin yadda uwa take kula da ɗanta, tana hana idanunta bacci saboda shi. Ina ganin soyayyar mahaifiya ƙarara Hamma, ina ganin ƙauna da...." Sai ta kasa faɗa ta yi shiru tana kuka sosai.

Saheer ya haÉ—e rai dan ko bata ce ba ya san Rehaan da babarsa take nufi, ya kawar da kai daga kallonta sannan ya bata tissue ya ce, "ki goge idanunki."

Ta karɓa ta goge ta sake kallonsa ta ce, "ka faɗa min don Allah, ka taimaka ka sanar dani ko zan daina jin kewarsu da na ke ji a raina. Wallahi ban taɓa jin kewar mahaifiyata kamar yau ba, da na ga yadda uwa take sadaukar da komai nata saboda ɗanta, sai nake ji ina ma nima tawa uqar tana kusa dani, nima ta kula dani ta rarrashe ni har na yi kuka a jikinta. Ka taimake ni ka faɗa min Hamma, bazan jure sai wani lokaci ba, yanzu nake so."

"Islaha na faÉ—a miki, nima bani ke aka yi aka ce na kai ki, ni kaina bazan iya tuna waye ba. Amma ina kan bincike akan hakan. Da can bana bincike akan hakan, amma yanzu ina yi saboda ke, in na gano komai zan faÉ—a miki."

Ta girgiza kai tana kallonsa ta ce, "rana ta farko nake ji kamar ban yarda da abinda ka ce ba, rana ta farko da nake jin maganar kamar ƙarya ba gaskiya bace. Hamma ban yarda ba wallahi, ni na san ka san wanda ya baka ni ka kai ni gidan marayu ba, har cikin raina ina ji ban yarda da kai ba."

Saheer ya bita da kallo ya ce, "Islaha ni ki ke cewa ba ki yarda da abinda na ce ba?."

"Gaskiya ta kenan Hamma, dan ban yarda da wannan maganar ta ka ba wallahi."

Ya zaro idanunsa ya ce, "Harda wallahi?.

Ta yi shiru bata amsa ba, dan gwara ta faÉ—a masa gaskiya ko zai daina rufe mata. Saheer ya girgiza kai ya ce, "To ban san me zance miki ba tunda kin rantse ba ki yarda ba. Ni daman na kula da halayenki, tunda ki ka yi auren nan ki ka fara raina ni, ban sani ba ko dan kina da aure ne, ko dan kin fara sanin meye auren ban sani ba."

Ta É—ago jajayen idanunta ta kalle shi ta ce, "me ka ke nufi?."

"Kina ganin kin je level ɗin da ban je ba, kin auri mai kuɗi da suna a Yola, kina zaune a gida mai girma da kyau, dole ki dinga ƙaryata ni in na faɗa miki magana. Daman na ga kamar kin karɓi auren nan, dan ga kin zama very comfortable a kai, bakya yawan complain kamar farkon auren."

Ta kalle sa da mamakinsa da ya mamaye mata zuciyarta, sai ta kawar da kai sannan ta kuma kallonsa ta ce, "na zama comfortable da auren Rehaan ka ke faÉ—a? Kana so ka ce na yi accepting hndrent percent?."

"Abinda na gani a zahiri nake faɗa miki, kamar kin karɓi auren, ban san me ki ke aikatawa tare da shi ba."

Islaha ta kulle idanunta tana jin É—acin kalamansa, ta yi shiru tana ji in ba dan shi É—in bane da yanzu ta nunawa ko waye ya yi kuskurensa, amma shi É—in ma dole ta nuna masa ya yi kuskure ko dan ya kiyaye harshensa nan gaba.

Ta É—ago a fusace ta ce, "ka ce auri mai kuÉ—in da da ya fi ko wanne a Yola, mai kyau, kuma É—an babban gida da komai ma da ka ce. Hamma ina so ka sani, wallahi da ace kuÉ—insa ne a gabana da ba ka isa ka ganni ba, dah kafin ka ganni sai ka cike form, an turo min form É—in, na yi approving, sannan a yi ma ka iso ka zo zuwa inda nake, in ka samu damar ganin nawa kenan....."

Kafin ya yi magana ta ɗora ta ce, "Wallahi da na karɓi aure Rehaan da yanzu na canja, da yanzu Islaha da ka sani a baya ba itace a zaune a motarka ba. Amma gani a motar ka a zaune, na fito kawai saboda na yi maka magana, amma ka ke faɗa min haka dan kawai na tambaye ka asalina?."

Saheer manakin kalamnta sun gama kashe shi, bata taɓa faɗa masa magana haka ba, ko da wasa bata taɓa kuskuren faɗa masa maganar da ya ji zafinta a ransa ba sai a lokacin.

Ya ce, "a dah bakya iya faÉ—a min irin wannan maganar, amma yanzu ni ki ke faaÉ—wa haka, Islaha in ban ce kin canja ba me zance?."

A fusace ta ce, "na canja ɗin Hamma! Na auri mai kuɗi na canja, na canja, na canja, sai me!?…..”
Chapter 67 · 0% Book details