Sashe 44
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mama ta ce, "Allah ya ƙara sauƙi, ko a kawo miki abinci? Sinasir muka yi, na san za ki so ci, kin jima ba ki ci abincin gida ba. Kina tare da Rehaan baza ki ci abincin gida ba, sai na turawa."
Islaha ta ce, "Na ƙoshi Mama."
"Aa, sai kin ci Islaha" ta faɗa tana miƙewa da kanta ta shiga kitchen.
Islaha ta murmusa cikin jin daÉ—i, ta fi jin ta zama comfortable in tana tare da Mama akan Mamy, ko dan Mama ta fi sakar mata fuska dai bata sani ba. Dan lura kamar Mamy tana da mulki kaÉ—an, Mama kuwa akwai kirki da sakin fuska.
Tana wannan tunanin Mama ta dawo ta ajjiye mata abinci ta ce, "Gashi nan ki ci." Islaha ta kalli abincin, sinasir ɗin ya yi fari ƙal, gashi ya soyu sai ƙhamshi yake yi. Lokaci ɗaya ya shiga ranta, ta ji tana son ci dan da gaske ta kwana biyu bata ci abincin gida ba sai na ƙetare. Mama ta ce, "Babu uzuri fa, sai kin ci Islaha. Ga shi can na saka miki a flaks, sai ki tafi da shi ki sake ci in anjima."
Islaha ta miƙe cikin jin daɗin kulawar Mama ta ce, "zan wanke hannuna."
Mamy ta nuna mata sink É—in dining area ta ce, "Bismillah."
Islaha ta ƙarasa ta wanke hannu ta dawo ta fara ci tana jin kanta a takure. Mama bata ce mata komai ba tv kawai take kallo, sai ta canja channel ta kai channel ɗin su Islaha a lokacin ana maimaita shirin da Islaha ta gabatar a safiyar.
Mama ta ce, "Gaskiya kina Æ™oÆ™ari, kin iya gabatarwa sosai.â€
Murmushi ta yi bata yi magana ba, a lokacin Janan ta shigo ta ce, "Ahh sis, ke ce a nan?."
Islaha ta ce, "Ni ce Sis, sannu da zuwa."
Ta ajjiye labcourt É—inta ta ce, "Yauwa Sis, na dawo daga aiki na gaji."
Mama ta ce, "Kawo mata ruwa."
Janan ta kawo mata ruwa sannan ta ce, "Hamma Ray yana nan? Ina da case da shi."
Islaha ta É—aga kai ta ce, "Yana nan."
Janan ta ce, "Sai anjima zan zo, zai koya min assigment. Yau na ga ya sha yawo, hotunansa sai yawo suke duniya, ana sake tabbatar da lafiyarsa lau babu abinda ya same sa."
Ita dai bata ce komai ba dan kamar maganar bata shafe ta ba, sinasir ɗin ma ta ajjiye ba dan babu daɗi ba sai dan ta ƙoshi.
Ta miƙe ta wanke hannunta ta dawo ta zauna ta ce, "Na ƙoshi Mama, na gode."
Mama tana murmushi ta ce, "kar ki sa ke cemin kin gode, me aka yi da za ki gode?." “
Islaha ta miƙe ta ce, "Mama zan koma."
Mama ta ce, "to Islaha, za a biyo ki da abincin. Janan kira min Shamsiyya ta bita da abinci, yana kitchen a pack." Ta amsa Islaha ta fita tana girmama ƙarfin kirkin Mama.
Tana fita Mama ta bita da kallo tana murmushi a bayyane ta ce, "Yaro man kaza, Islaha kenan, ba ki san wacece Saddiƙa ba. Duk da na ga Nadira ta fara sakin jiki da ke, ni kuma ba haka nake so ba, zan yi maganin sakin jikin da ta fara yi dan bana so, bana so ki dinga kallon kowa a gidan nan sai ni kaɗai, ni kaɗai nake so ki dinga yiwa kallon mai kirki a kaf gidan nan. Da hakan zan yi amfani na gyarawa Rehaan zama, kema na gyara miki zama. Yanzu na barki ki huta na ɗan lokaci, da na waiwayo ki babu labari."
Islaha sai da ta shiga falon sannan ta karɓi abincin ta hau dashi sama dan kar ma chef ɗinsa ya gani ya kwashe. Bata gansa a falo ba ta shige ɗaki ta zauna a kan gadon.
Sai a lokacin motar da ta taho zata takata tazo ranta a bayyane ta ce, "nima na ga motar tun tsayuwar mu, to kenan bina ake yi?"
Ta ɗan yi shiru ta ce, "to su waye suke bina? Me na yi musu da suka yi ƙoƙarin kashe ni?. To ya aka yi aka san zan je can, meyasa zasu yi ƙoƙarin taka ni da mota?."
Ya ɗan daki kanta ta ce, "su waye haka? Meyasa za a yi ƙoƙarin kashe ni, ko dai an gano ni ce a tare da Rehaan a motar da aka yi ƙoƙarin kashe mu?."
Sai kuma ta girgiza kai ta ce, "akan me dan kawai an gano ni ce za a kashe ni? Akwai wani abun a ƙasa, ni na san akwai abinda yake faruwa tabbas." Waya ta ɗauka da niyar faɗawa Saheer, ta kira sa bai ɗauka ba sai ta kira Brr.
Yana ɗauka suka gaisa ta ba shi labarin abinda ya faru, ya ɗan yi murnushi sannan ya ce, "ba akan komai aka so kashe ki ba, sai akan case ɗin nan. Islaha maganar nan ba ƙarama bace, da bana ɗaukar ta da mahimmaci, amma yanzu na ɗauka. Tabbas kashe ki aka so yi, ni a ganina sun yi tunanin Yafindo ta ba ki saƙon da Zainab ta bata."
Islaha ta ce, "innalillahi! Hamma Suraj kisa fa.â€
"ki fa Islaha, ko shakka bana yi ke aka so kashewa. Ina ne gidan da Yafindon ta ke? Ki yi min kwatance da hanzari dan itama rayuwarta tana cikin hatsari."
Sai jikin Islaha ya fara rawa jin zata sake saka Yafindo a cikin hatsari, ta faɗa masa inda gidan yake ya ce, "zan je n duba da kaina, amma maganar ta tsaya iya ni dake, kar ki faɗawa kowa Islaha†bai tsaya ya ji me zata ce ba ya kashe wayar.
Ta ajjiye wayar ta ce, "Kashe ni aka yi niyar yi kenan, dan ina ƙoƙarin yaƙi da zalumci shine za a kashe ni?." Ta rasa tunanin da zata yi, gabaɗaya hankalinta ya koma kan Yafindo da bata san abinda zai same ta ba.
••••••
A yana zaune yake a babban falo yana danan waya, fuskarsa gabaɗaya babu walwala, tunda aka rasa damar kashe Rehaan a karo na biyu ransa yake a ɓace sosai.
Maza guda biyu ne suka shigo suka zauna suna jira ya basu damar magana. Sai da ya ga dama sannan ya ce, "ina jin ku."
ÆŠaya ya ce, "Ranka ya daÉ—e mun samo komai akan matar Rehaan."
Sai ya ajjiye wayar hannunsa jin an ambaci wanda ya fi tsana sama da kowa a duniya ya ce, "ina ji."
"Sunanta Islaha, ƴar jarida ce a gidan tv toron guiwa. Auren da suka yi da Rehaan ba a son ranta aka yi shi ba, an tabbatar min da neman kuɗin fansar saurayinta shine ya kai ta ga auren Rehaan ba dan tana so ba. Kuma ko a yau ta haɗu da saurayinta kuma suna soyayya sosai, kuma tana da niyar kashe auren Rehaan ta fito ta dawo gare shi. A taƙaice ba zaman auren take niyar yi dashi ba, akwai wani abun da ta shirya. Dan tana son saurayinta sosai, shima kuma yana sonta."
Ya É—aga kai É—ayan ya ce, "Ina da shawara ranka ya daÉ—e."
Ya ɗaga masa kai alamun ina ji ya ce, "A ganina saurayin ya kamata mu samo, mu ba shi kuɗi sosai, dan na tabbbatar yana tare da ciwon rasata a zuciyarsa, tunda yana ƙaunar ta. Tunda har yanzu tana sonsa kuma tana haɗuwa da shi, ta hanyarsa zamu iya samun damar ganin bayan Rehaan."
Ya kalle sa ya ce, "kamar ya kenan?."
"Tunda ita tana sonsa kuma tana jin maganarsa, in ya bata wani abun ya ce ta bawa Rehaan zata iya karɓa tunda tana sonsa kuma tana ganin kamar ta cutar da shi tunda ta auri waninsa. Ka ga sai mu jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, mun yi nasara a akansa sannan mu ɗora mata laifi. In muka bi ta hanyarta baza mu yi nasara ba, kowa ya faɗa mana bata da saurin yarda da mutanen da bata sani bsa, da shi kaɗai ta yarda a duniya."
Ya ƙyalƙyale da dariyar samun nasara ya ce, "shawarar ka ta yi, a ina za a gano saurayinta?."
Suka yi dariya jin sun kawo shawara kuma an karɓa suka ce, "Wannan mai sauƙi ne, zuwa gobe za mu zo da shi."
Ya tafa hannunsa ya ce, "Dakyau, ina jira na ga hakan, a tabbatar an yi komai yadda ya kamata, kar a yi kuskure.â€
“an gama ranka ya daÉ—e.â€
“Za ku ji alert, da kun ɓata min rai, amma yanzu kun faranta min ɗari bisa ɗari."
Suka yi dariya suka miÆ™e suka fita, ya miÆ™e yana dariya, ya Æ™arasa gaban window yana kallon waje ya ce, "….mu je zuwa....â€
Nana Haleema.
RDB3P35
Nana Haleema.
Labiba tun bayan faruwar komai ta tsangwami kanta, ta koma wani iri ko kaÉ—an bata so ayi mata magana, ta killace kanta, ko wajen Aisha bata zuwa ko yaushe tana waje É—aya tana tunani.
Tana ɗaki a zaune ta yi tagumi tana tuna abubuwan da suka faru, bata taɓa tunanin zata aikata abu mai muni da ƙazantar abinda ta yi ba, kuma babban abinda yake sake ɗaga mata hankali a cikin garin Makkah ta aikata wannan ƙaton saɓon. Ko ya ya ta so ta manta sai ta kasa, da ta motsa sai tunanin ya zo ranta.
Da sallama Aysha ta shiga ta ajjiye mata abinci a gabanta sannan ta ce, "Wallahi Labiba kamar ba wayayyiya ba, ni na rasa meye abin damuwa a cikin abinda ki ka aikata, ke da ki ka bi Ubaid ma balle kuma mace Æ´ar uwarki?."
Labiba ta kalli Aisha ta ce, "har gwara shi, gwara na cigaba da sauraren irinsu guda dubu akan abinda na yi, ni ban taɓa tunanin zan aikata neman mata a rayuwata ba."