Sashe 30
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daada ta buɗe ido cikin mamakin kalamansa ta ce, "kana son wa? Kai Salmanu matar ƙaninka ce fa."
Salman ya kalli Daada ya ce, "Ni dai ina sonta, kuma ya ce itama tana sona, ko Rehaan?." Ya faÉ—a yana kallon Rehaan, shima ya kalle sa amma bai ce komai ba yana jin zafi a zuciyarsa
Daada ta ce, "dallah ka yi mana shiru, shashashan banza. Matar wani ka ke cewa kana so? Na faɗa maka matar ƙaninka Rehaan ce. Kuma mace in tana da aure ba a cewa ana sonta, ka ji?."
Idonsa ya ciko da hawaye ya ce, "Ni dai ina sonta, kuma tunda kin ce matar Rehaan ce ba ɗan uwana ne zan iya cewa ina sonta. Ni dai ina sonta, kuma a wajanta zan kwana, ina sonta!" Ya faɗa da ƙarfi, sai kuma ya zabura ya yi kan Islaha da nufin ta ɓoye shi, babu shiri ta miƙe da hanzari ta yi bayan kujera gabanta yana faɗuwa.
Kafin ya kai ga ƙarasa sai ya yi baya ya faɗi a ƙasa, duk suka yi kansa ana salati cikin tashin hankali.
Umma ta kalli Daada ta ce, "wallahi bana son yarinyar nan, bana ƙaunar ganinta ko kaɗan. Tunda ta zo gidan nan Salman ya canja, tunda ta zo yake irin waɗnanan surutan da da bai saba dasu ba. Rabon da ya yi irin wannan faɗuwar har na manta, amma daga zuwanta zata dawo min da hannun agogo baya. Kawai dan an ga yana da matsalar kwakwalwa sai a dinga cutar dashi? Dan ita matar Rehaan ce kowa yana jin tsoronsa saboda kuɗin da yake da shi shiyasa baza a bata laifi ba ake ƙoƙarin ɗora masa?. Wallahi bazan amince da wannan abun ba, ko ita da Rehaan su bar gidan nan, ko kuma ni da shi mu tafi" ta ƙarasa faɗar haka tana zubar da hawaye tana jijjiga Salman amma ta san sai an yi masa allura zai farfaɗo.
Abba ya kalli Rehaan ya ce, "A É—auko allurarsa a yi masa."
A fusace Umma ta ce, "bana so ya taɓa min ɗana, Janan ta zo ta yi masa, bana buƙatar ko shi ko babarsa wani ya saka hannunsa a jikina."
Mama da take zaune ta ce, "Ina Janan ɗin ta ke, bara na kira ta da kaina†Ta faɗa tana tashi ta fita, jim kaɗan suka dawo da Janan da allura a hannunta, Janan ta yi masa a jijiya ta koma ta zauna.
Falon ya yi shiru babu mai cewa komai, Islaha tana daga inda ta yi tsalle ta haura a tsaye cikin wani irin yanayi na tsoro da tausayin Salman.
Daada ta ce, "Dawo ki zauna Ishlaya."
Islaha ta dawo ta zauna tana sunkuyar da kanta. Daada ta ce, "Ke Salamatu! Kar na sake jin magana akan za a lalata miki É—a, a gaban ki dai ga abinda ya faru, a kan idanun ki ga shi ya tashi a guje zai je wajanta."
Umma ta ce, "In bata koya masa ba ai da bazai yi ba, itace ta É—ora shi a kan hakan shiyasa yake yi a gaban kowa."
Cikin faÉ—a Abba yake kallon Umma ya ce, "har yaushe ta san Salman É—in da zasu yi irin wannan sabon? Yau kwananta uku a gidan nan, yaushe ta san Salman da zasu yi wannan sabon?. Me yake damun ki ne Salamatu? Ana magana kina karkacewa dan kin raina mana hankali?. Tana da ilimi fa, ta san duk abinda take yi, ya za ki dinga Æ™oÆ™arin tarwatsa mana kan gida a ko yaushe?. Ko yaushe ke ki ke kawo rabuwar kai a gidan nan da Æ™ananun maganganun ki, yanzu meye amfanin kalaman da ki ke yi akan matar É—an ki?.â€
Umma ta ce, "shikenan sai a dake ni a hana ni kuka? A cuce ni ace bazan yi magana ba? Dan kawai an ga yana da matsala baza a yi amfani da maganarsa ba?."
Mama ta ce, "Salamatu don Allah ki yi haƙuri, ba ga shi kin kawo maganar wajan Daada ba?."
"Bakya jin abinda Daadan ta ke faÉ—a ba? A ko yaushe Rehaan shine a kan daidai, yanzu ga matarsa ma tazo, ana nuna mana itace dai matar Rehaan mu kuma mu ne banzaye. Ba a yi min adalci a gidan nan kwata-kwata, ana nuna min banbanci."
Rehaan ya bita da kallo yana taɓe baki jin wai ana nuna mata bambanci, a ganinsa kaf cikin gidan Mamy ce ya kamata ta ce ba a yi mata adalci ba ita ba, amma wai itace take cewa ana nuna mata banbanci saboda rashin tsoron Allah.
Mama cikin gajiya da maganar ta ce, "ki yi shiru don Allah."
Daada ta ce, "ƙyaleta Saddiƙa, ƙyaleta ta gama yi min rashin kunyar.
" Umma ta É—auke kai bata ce komai ba.
Daada ta ce, "haka kawai yarinya baƙuwa daga zuwanta za ki fara ɗora mata sharri? Shi ɗan naki da yake da matsalar ƙwaƙwalwa ba ki ɗora masa ba sai ita? Shi duk abinda aka ce zai aikata ai zai aikata ɗin ne, tunda ba hankali ne da shi ba. Ita kuwa daga zuwanta yau kwana uku har kin fara ɗaga mata hankali da sharrin ki na banza da wofi, wacce irin rayuwa ce wannan?."
Umma ta yi shiru bata ce komai ba, amma a zuciyarta ji take yi da tana da dama sai ta fitar da Islaha daga cikin gidan ta ƙarfi.
Abba ya ce, "daga yau kar na sake jin magana irin wannan a gidan nan. Salman kuma tunda abinda zuciyar ki take ba ki kenan ki hana sa zuwa wajan Rehaan, in ki ka yi haka ba shikenan ba?."
Ita dai bata amsa ba, haushi take ji jin an É—auki laifi gabaÉ—aya an É—orawa É—anta, bayan ga mai laifi nan a zaune.
Haka taro ya watse kowa ya kama gabansa, masu farin ciki suna yi masu jin haushi suna yi. Islaha tana wajan Daada a zaune. Daada cikin rarrashi da kwantar mata da hankali ta ce, "kar ki damu Ishlaya, haka gidan nan yake, haka mijinki yake a gidan nan, ba kowa ne yake ƙaunarsa ba, kema kuma dole abin ya shafe ki tunda matarsa ce. Ki yi haƙuri, kar hakan ya dame ki kin ji?."
Islaha ta ce, "In sha Allah."
Daafa ta ce, "Janan da Banisha ku raka ta ɓangaren ta." A tare suka miƙe suna nufar apartment ɗin Rehaan babu mai yiwa wani magana a cikinsu.
Nana Haleema.
RDB3P25
Nana Haleema.
Sai da suka shiga falon sannan Janan ta ce, "i’m sorry Sis, abubuwan gidan na mu ne sai a hankali."
Islaha ta yi murmushi ta ce, "na gode."
Janan ta miƙa mata hannu ta ce, "Dr Janan."
Islaha itama ta ta bata hannu suka gaisa sannan ta ce, "Islaha."
Janan ta murmusa ta ce, "ƴar jarida Islaha dai, amma mu da Islam zamu kira ki, In kina buƙatar wani abu za ki iya yi min magana."
Islaha ta ce, "Na gode Janan."
"Kar ki damu" ta faÉ—a suna fita ita da Banisha.
Islaha bata bar abin ya dame ta ba ta yi alwala ta yi sallar i'sha, sannan ta kalli dining ta ga akwai abinci ajjiye ta zuba ta ci dan tana jin yunwa sosai.
Bayan ta gama ta ɗauki kayanta da laptop ɗinta ta hau sama. In ta tuna abinda ya faru bata sanin tana hawaye, sai dai ta share ido ta yi ƙoƙarin kawar da tunanin dan ba shi da amfani a ta shiga wanka. Bata jima ba ta fito ɗaure da ƙaramin towel, ta ɗaura wani a kanta tana fitowa tana kwance na kanta gashinta ya sauka har ƙugunta.
A daidai lokacin aka buɗe ƙofar, tana juyowa da niyar ganin waye suka haɗa ido da Rehaan da ya buɗe ƙofar a karo na farko.
Islaha sai ta dirririce, karo na farko da wani namiji ya taɓa ganinta a haka, daga ita sai ƙaramin towel, ga shi kanta babu ɗankwali. Gabanta ya faɗi sosai, amma da ta tuna kallon ƴar iska yake mata sai ta ɓoye yanayinta, ta dake ta ɗauke kai daga kallonta amma fa zuciyarya bugawa take yi.
Rehaan kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kansa, ya sake kallon ƙafafunta da take ɗage su sama kamar wacce take taka wuta, tun daga toes ɗinta yake kallo har laps ɗinta, sannan ya ɗauke kai kamar ba ya son magana ya ce, "Mamy tana jiran ki" yana faɗa ya kulle ƙofar ya koma.
Islaha ta yi tsaki mai sauti ta ce, "aikin banza, ni na gaji da matsalar gidan nan wallahi, daga wannan sai wannan kamar gidan haya."
Tana shiryawa tana mita a haka ta gama saka kaya ta sako hijjab ta fito ta samu Mamy a zaune a kan kujera shi kuma yana gefenta ya É—ora kansa a kafaÉ—ar ta.
"Shugaban masu shagwaɓa da son jiki, kalle shi don Allah, ƙato dashi ya dinga kwanciya a jikin babarsa" ta faɗa ƙasa ƙasa tana ƙarasowa ta zauna a kan carpet tana harararsa ta gefen ido..
Cikin sanyin murya Islaha ta ce, "Mamy ina yini."
Mamy ta kalle ta ta ce, "Lafiya lau. Kina ji, a yanzu a matsayin inlaw É—ina ki ke, kina cikin part of my family, duk da a yanayin da auren ku yazo amma bazan canja sunan ki daga sirikata ba. Islaha ki dinga kiyaye duk wasu abubuwa da suka shafi gidan nan, ki dinga sanin abinda za ki yi saboda magana. Kowa a gidan nan jira yake a ce É—an É—akin Mamy ya yi wani abu, ana cewa za a haÉ—a meeting a zauna ana faÉ—ar magana mara daÉ—i a kaina. Ki dinga kiyaye duk abinda zai jawo magana, bana son yawan abubuwan nan da suke faruwa tunda ki ka zo, kin ji?."
Islaha jin yadda Mamy take yi mata magana a tausaahe sai ta É—aga kai ta ce, "In sha Allah."
Mamy ta ce, "na duba cctv, na ga clip ɗin abinda ya faru kafin ki shigo falon, na tabbatar ƙarya aka yi miki abinda aka faɗa ba gaskiya ba ne. Ki cigaba da kiyayewa, in ba haka ba wata ran abinda zasu ce kin yi abinda ya fi haka."
Islaha sai ta ji hankalinta sai ya kwanta, ta yi murmushi har ta É—ago suka haÉ—a ido da Mamy sannan ta ce, "In sha Allah Mamy."