Sashe 87
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar wacce ta tuna wani abun sai ta jawo wayar ta cire ta daga dnd nan ta ga messages da kira babu adadi. Kiran Hamma, Chairman, Safeera da abokan aikinta. Chairman ta fara kira ta faÉ—a masa rashin lafiya ce ta hanata zuwa, daga nan ta ajjiye wayar ko Saheer É—in bata kira ba.
Miƙewa ta yi ta jawo drawer ta ɗauko takarda ta buɗe tana karantawa.
A bayyane ta ce, "ai na ce masa in ya karya rule ɗaya daga ranar zamana ya ƙare, dole na je na same s...." Ta faɗa tana niyar fita sai kuma ta tsaya cak. A bayyane ta ce, "na je na ce masa meyasa ya cire min towel? Bayan ya gama ganar min jikina gabaɗaya, ko ina ya gani." Ta dafe kai cike da takaici, ta zauna tana ajjiye takardar zuciyarta tana suya saboda ɓacin rai da takaici.
Rehaan bai shigo gidan ba sai bayan sallar i'sha, wajan Mamy ya shiga kai tsaye ya same ta a É—aki a zaune tana amsa waya. Ya zauna a kusa da ita yana É—ora kansa a kafaÉ—arta ya yi luf yana jin bugun zuciyar, ta É—ora hannunta a kansa tana shafa gashinsa a hankali. Cikin harshen hindi take magana, hakan ya ba shi tabbacin da mutanen can india take waya.
Idanusa ya lumshe bai ce komai ba, gabaÉ—aya yinin ranar ya yi sa a wani bahagon yanayi, bai san asalin abinda yake damunsa ba, abinda ya sani kawai ba ya jin daÉ—in jikinsa gabaÉ—aya, yana ji kamar an canja shi, ya zama kamar wanda bashi da jini a jikinsa gabaÉ—aya.
Mamy ta kashe wayar ta kalle shi da kulawa ta ce, "Mr busy ina ka je yau?."
Ya kalli Mamy yana miƙewa zaune ya ce, "Ina guest house."
"Ka tafi can ka zauna, ka bar Islaha babu lafiya ko?."
Nan take gabansa ya faɗi matuƙa, ya ɗago suka haɗa ido ta ce, "eh, ta yi fama da zazzaɓi sosai, Banisha ce ta shiga ta same ta a haka shine ta zo ta faɗa min, sai da na yi mata allura."
Ya girgiza kai tana tuna yanayinta na É—azu a idanunsa, ya runtse ido yana shafa fuskarsa sannan ya ce, "ban san bata da lafiya ba."
Mamy ta riƙe fuskarsa tana kallonsa ta ce, "ba ka kula da lafiyar ta kenan ko?." Ya ɗan sauke ido ƙasa daga kallonta bai ce komai ba.
Mamy ta ce, "na san halin ka Rehaan, ko housemaid É—ina ce bata da lafiya in ka ganta kana ganewa har ka bata magani, balle kuma matar ka!."
_Matarka._
Ya maimaita a zuciyarsa jin yadda sunan ya shige sa sosai, har zuciyarsa ya ji shigar sunan da ƙarfi. Ya kalli Mamy amma ya kasa cewa komai, bakinsa ya ɗaure bai san me zai ce ba.
Mamy ta yi murmushi tana kallonsa da kulawa ta ce, "me yake damun ka?."
"Nima ban sani ba Mamy, ina jina kamar ba ni ba. Canjin babu daÉ—i, ina jin zuciyata tana bugawa.â€
"Sorry."
Rehaan a hankali ya ce, "Zan yi tafiya Mamy."
"Zuwa ina kuma, mr trip?."
Ya yi murmushi ya ce, "Norway."
"Allah ya kiyaye."
Ya amsa da amin tare da yin shiru kafin Mamy ta ce, “ka je ka dubata." Ya ɗaga kai ya miƙe ya fita.
Yana fita daga apartment ɗin Mamy ya hango ta daga can ƙarshen gidan ya hangota tana tahowa a hankali, ya tsaya yana kallon yadda take tafiya mai ɗaukar hankali, iska tana kaɗa hijjab ɗin jikinta, kanta a sunkuye tana tahowa daga ɓangaren Daada.
Yadda ya ganta a ɗazu a haka yake ganin image ɗinta tana tahowa, ya runtse idanunsa ya ce, "hasbunahallah!!" Ya faɗa cikin wani mai wahalar fassarawa, bai jira ta ƙaraso ba ya shiga apartment ɗinsa, ya hau sama tun kafin ta ƙaraso.
A falo ta same shi a zaune kamar bai san da zuwanta ba. Wata irin kunya da baƙin ciki suka mamaye mata zuciya, sai take ganin kamar a tsirara yake kallon ta. Idanunta suka ciko da hawayen baƙin ciki, babu namijin da ya taɓa ganinta a irin wannan yanayin sai shi, ko Salman ɗin ta san bai ga jikinta ba, lokacin da ta gan shi ta saka towel. Inda ace mijinta ne na gaske babu abinda zai dame ta, duk da zata ji kunya amma daga lokacin abin zai wuce. Amma Rehaan ne, mijinta na yarjejeniya.
Tana so ta yi masa warning akan hakan amma ta kasa, bakin ta ya ɗaure ya yi nauyi sosai, kunya mai cike da takaici ta lulluɓe mata jiki gabaɗaya. Ta ɗauke ido daga kansa, tana ji kamar ta je ta rufe sa da duka ta ko wanne ɓangare, a hankali ta ɗaga ƙafa da niyar barin wajan.
"Mamy ta ce ba ki da lafiya, i hope you are feeling well?."
Abinda ya faÉ—a ya dakatar da ita daga barin wajan, ta kalle sa suka haÉ—a ido, ta yi saurin É—auke kanta hawayen takaici yana sakko mata.
Ta goge cikin sanyin murya ta ce, "abinda ka yi min Allah yana kallon ka, a zamana da kai bamu rubuta haka ba, bamu ce zaka yi min duk abinda ka ga dama ba...." Ta faÉ—a tana sake share hawayenta.
Ta kuma kallonsa ta ce, "kana ta breaking conditions ɗinmu, ina ƙyale ka ne ba dan ka fi ƙarfina ba, sai dan ina so komai ya tafi cikin tsari. Na ga abin na ka is too much, zan ɗauki matakin da nake ganin ya dace da mu" ta faɗa tana shiga ɗaki ta bar sa yana kallon inda ta bari.
_Abinda ka yi min Allah yana kallon ka._
Kalamanta suka sake dawowa cikin kunensa, ya sake kallon inda ta bari yana mamakin abinda ta ce. Ya buɗe baki ya ce, "Me ta ke nufi, ko ta manta ni mijinta ne?" Ya tambayi kansa yana kallon ƙofar ɗakin da ta shiga, sai kuma girgiza kai kawai ya lumshe ido kafin ya tashi ya shiga ɗaki.
(Sai yanzu ka san kai mijinta ne kenan?ðŸ˜).
   **
Muslim ya kalli Ummi ya ce, "kin gani, a cikin daren nan zan aikata komai, so nake gobe duniya ta mamaye da magana akan Islaha." Ummi ta kalli abinda yake nuna mata ta ce, "Amma kana ganin iya wannan abun zai jawo mata baƙin jinin da mu ke da buƙata?."
"A guje ma kuwa. Ƴan arewa ne fa, mu a ko yaushe mun fi mayar da hankali akan ya shafi rayuwar mutum akan rayuwar da mu ke ciki a najeriya. Ba mu damu da matsalolin da suke addabarmu ba, mun fi mayar da hankali akan matsalolin wasu. Ke kin san yadda irin waɗannan videon suke zaga duniya? Cikin minti ɗaya za ki ga yadda kowa zai gani, zaki likes da comments, zaki ga yadda bloggers za su dinga reposting. Ko mutum dubu aka ce an kashe a najeriya, baza su yi magana a kai kamar yadda zasu yi magana akan Islaha ba. Ki zuba idanu zaki ga abinda zan jawo mata a goben nan."
"Shikenan Muslim, Allah ya kaimu."
"Bani wayar ki, zuwa anjima zan aiko miki da ita, yanzu da ita zan yi amafani."
Ta É—aga kai ta ce, "Shikenan, gata nan."
"Da sauri haka? Ba ki tambaye ni dalili ba kawai kin ce gata nan?."
Ta yi dariya ta ce, "Haba Muslim! Ni indai akan karya Islaha ne ko kaina ka ce na ara maka zuwa gobe zan bayar, indai zan samu ahinda nake so ."
Ya bita da kallon ƙasa ido ya ce, "Da gaske ki ke?."
Ta ɗan yi dariya tana buɗe motar ta ce, "ina jiranka, ina so gobe duniya ta harsgite akan tsanar Islsɓaha, kowa ya fita daga sabgarta, ya zama ta koma kamar mujiya saboda baƙin jini."
Ya gyara zamansa ya ce, "in na tabbatar da hakan meye tukuwici na?."
Ta kalle sa ta ce, "duk abinda ka ke so, shi zan ba ka."
"Har ke in na ce ina so, za ki bani?."
"Ka tabbatar komai ya tafi daidai, sannan ka dawo mu yi magana."
Ya yi dariya ya ce, "An gama Hajiyata." Ta fita daga motar shi kuma ya fara tsara abinda zai yi dan ganin bayan Islaha.........
Nana Haleema.
RDB3P64
Nana Haleema.
Yadda Chairman ya takura mata da waya ya saka ta fita da wuri, ko abinci bata ci ba ta tafi wajan aiki. Lawal yana ajiiyeta ta shiga ciki kamar ko yaushe, tunda ta shiga ta ga ana kallonta ana magana ƙasa ƙasa, bata damu ba ta wuce ciki ta zauna a desex ɗinta bata cewa kowa komai ba.
Sai kuma ta miƙe ta nufi wajan Chairman ta same shi baya nan, Program ɗinta ta gabatar sannan ta fito ta koma wajan zamanta ta zauna. A lokacin Safeera ta shigo, Islaha ta kalle ta ta ɗauke kai ta ce, "Tun ɗazu nake jiran zuwan ki, yaushe za a kawo lefen?."
Safeera fuskar ta babu walwala ta ce, "Islaha!."
Islaha ta kalle ta ta ce, "ya aka yi?."
Safeera ta yi shiru sannan ta ce, "ba ki ga abinda yake faruwa a social media ba?."
Islaha ta mayar da hankalinta kan Safeera ganin fuskar ta cikin damuwa harda alamun kuka sai ta ce, "ban gani ba, me ya faru?."
Safeera ta sake jan numfashi ta ce, "ki duba za ki gani."
Islsha ta jawo wayarta ta kunna data, notification suna ta zuwa bata tsaya dubawa ba ta shiga tiktok. Scrooling take yi bata ga komai ba, ta kalli Safeera ta ce, "ni ban ga komai ba, meye yak....." maganar ta maƙale da ta sake kallon wayar ganin abinda ya firgita mata tunani.
Gabanta ya faɗi lokaci ɗaya, ta miƙe tsaye tana kallon abinda yake jikin wayar jikinta yana rawa. Sai kuma ta kalli Safeera ta ce, "Safeera meye wannan?."
Safeera ta ce, "nima haka na gani, kuma kowa ya gani a cikin gidan nan, haka duniya ma ta gani."
Hannunta yana rawa, muryarta tana rawa idanunta sun firfito waje ta ce, "Safeera meye haka? Kaina nake gani babu kayana a jikina fa, ni ce a kwance da wani fa! Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Safeera me hakan yake nufi?."
Safeera ta riƙeta ta ce, "Zauna."
Ta fizge hannunta ta ce, "kamar ya na zauna! Safeera ki faÉ—a min meye wannan? Ki faÉ—a min ni ce da gaske?."