← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 110

Sashe 86

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ray miƙe zaune sosai ya haɗe yatsunsa waje ɗaya ya kalli Jazy, kamar zai yi magana sai ya sauke numfashi a hankali, ya rufe ido yana girgiza kai sannan ya ce, "I caught him….” Sai ya kasa ƙarasawa yana share fuskarsa da hannunsa, takaicin faɗar maganar yana mamaye masa ko ina na jikinsa.

Ya giegiza kai ya rufe iso sannan ya ce, “i caught him peeping at that girl in the bathroom."

Jazy ya buÉ—e idanu cikin mamaki ya ce, "which girl, Kiddoo?."

Rehana ya yi masa wani irin banzan kallo kafin ya koma ya jingina da kujerar bai ce komai ba.

Jazy ya ce, "Na ga Riyya bata nan, kuma na ji ka ce yarinya, shiyasa na yi tunanin Banisha ce."

Ya yi tsaki yana cize lips É—insa yana girgiza sannan ya ce, "C wife."

Jazy ya bisa da kallon mamaki ganin yadda ya canja gabaɗaya kawai dan an leƙa islaha a banɗaki. Jazy ya ce, "What! Islaha kuma? To garin ya ya hakan?."

"I don't know Jazy!" Ya faɗa cikin wani irin yanayi yana jan numfashi mai ƙarfi.

Sai kuma ya ɗago ya ce, "amma laifinta ne...." Ya sake dakatawa yana fizgo numfashi dan iya maganar sake ɓata masa rai yake yi.

"Meyasa zata yi using public bathroom? Duk bathrooms ɗin da suke cikin apartment ɗina sun yi mata kaɗan ne……?…..”

“Why sai sai guest bathroom Jazy…?” Ya ƙarasa faɗa a sanyaye kamar mai shirin yin kuka.

Jazy ya yi murmushi yana karantar yanayin Rehaan ya ce, "Kuma shi window É—insa ta waje ya ke ko? Amma sai na ga kamar ya yi tsayin da Salman bazai gano ba."

"Ya yi using bench É—in da masu gadi suke zama."

Jazy ya ce, "Subahanallahi! Har Salman ya san ya taka abu ya leƙa ta a bathroom? Kai Amma bai kyauta ba ko kaɗan, amma sai dai a bata haƙuri, saboda ba shi da hankali."

Ya yi tsaki mai tsaho cikin takaici ya ce, "Dan bashi da hankali sai ya dinga binta har bathroom yana kallonta?."

Jazy bai ce masa komai ba sai kallonsa yake yi yana mamakin wannan soyayya da ta yiwa Rehaan mugun kamu lokaci É—aya haka. Ray yana girgiza kai ya ce, "dan ba shi da hankali sai akace masa ya dinga yiwa kowa hauka ba? Har ya dinga kallonta a bathroom?."

Ya sake fizgar numfashi da ƙarfi sannan ya ce,
“Daga yau, bazai sake shiga apartment ɗin nan ba, zan saka security a wajan. And.......god!" Ya kasa faɗar abinda zai ce jin zuciyarsa tana bugawa, ga wani irin ɓacin rai da yake ji a ƙasan zuciyarsa.

Jazy dai kallonsa yake yi yana girgiza kai, ya yi murmushi yana mamakin Rehaan ganin ya faɗa da wuri har haka, shi ya ɗauka sai contract ɗin nasu ya ƙare ta bar gidan sannan zai damu, sai ga shi tun ba a je ko ina ba ya fara nuna soyayya mai ɗauke da zazzafan kishi.

Jazy ya ce, "Allah Sarki! Amma ita ya kamata a bawa haƙuri."

"bata da hankali fa, bata san abinda yake damunta ba. Na je na yi mata magana kuma wai ni take kallo tana cewa ai daman ta saba, ba yau aka fara ganinta haka ba."

"ai gaskiya ta faɗa maka, ba rashin hankali bane, da gaske ba yau ta saba wanka da maza ba. Ba a haka ka ke kallonta ba?.”

Baice komai ba ya É—aga kansa sama yana kallon p.o.p, sai kuma ya sauke a hankali ya ce, "Zan samu Abba, ya kamata a san abinda za a yi akan Salman, bazan dinga tolerating wannan shirmen ba."

Jazy bai san ya yi ƙaramar dariya ba, kamar ya tambayesa dalili sai ya share, dan ba ya so ya fargar da shi da wuri har sai ya tabbatar ya gama kamuwa ta ko ina, sannan sai ya ritsa shi ya tambayesa ya aka yi aka haihu a ragaya.

Jazy ya ce, "ni ban ga abin damuwa a nan ba, tunda matar contract ce ba abin ɗaga hankali bane, kuma jikinta aka gani ba jikin ka, kuma Salman ba hankali ne da shi ba.”

“Na ji ba shi da hankali, amma ya ganta ko?…”

Jazy zai musa cikin tsawa ya ce, “Ya ganta ko Jazy..!.”

“Ya ganta Rehaan, ka manta ka ce min suna kwana tare? Sai na ga normal ne.”

Rehaan ya ja tsaki mai tsaho, ya buÉ—e baki zai yi magana amma sai ya kasa ya rufe idanunsa.

Jazy ya girgiza kai cike da mugunta sannan ya ce, “ni ban ga abin damuwa a lamarin nan ba, amma tunda kana ganin hakan daidai ne fine. Lokacin na ku ma ai ya kusa ƙarewa, saura kwanaki kaɗan ku rabu kowa ma ya huta."

Ya kalli Jazy kamar mai karanta wani abu akan fuskarsa, sai kuma ya É—auke kai ya tashi ya hau sama.

Jazy ya yi dariya mai isarsa sannan ya ce, "Islaha kin yi nasara, kin saka zuciyar Rehaan ta girgiza, kin saka ya tashi daga duniyar mara aure zuwa ta masu aure. Good job! Ina so a yi dramar nan da ni, ina so na ga yadda komai zai kasance, dan na san Islaha baza ta taɓa karɓar Rehaan ba, dan ba shi take so ba. Shi kuma Alhaji Rehaan ɗin Mamy bazai rabu da ita ba...."

Ya girgiza kai yana dariy ya ce, "Wow! Akwai sabuwar drama a nan gaba, zamu kwashi hawayen Mamies boy, dan Islaha daidai dashi take" ya faÉ—a yana dariya sai kuma ya kira Riyya suna waya, yana jin nishaÉ—i yana ratsa zuciyarsa. Dan shi ba ya so auren nan ya rabu, ya fi so auren ya É—ore ko dan ya ga ya Rehaan zai yi da munanan kalaman da ya dinga faÉ—a mata.

Nana Haleema.

RDB3P63
Nana Haleema.

Tun daga ƙasa Banisha take kiran Islaha amma bata amsa ba, harta shiga ɗakinta same ta a kwance jikinta yana rawa. Da sauri ta ƙarasa ta cire duvet ɗin da ta rufe kanta ta ce, "Sis lafiya?."

Jin jikinta da zafi sosai, sai sauri ta koma ta faÉ—awa Mamy suka dawo tare. Mamy jin yadda jikinta ya yi zafi sosai sai ta tallafota ta kwantar da kanta a jikinta ta ce, "Islaha me yake damunki haka?."

Islaha bata iya cewa komai ba sai hawaye kawai take yi takaici tana nuƙurƙusar zuciyarta, tana ji kamar ta ɗauki bindiga ta harbe kanta.

Mamy ta kalli Banisha ta ce, "jeki ki samo min injection, na ji kanta yana ciwo sosai, É—auko min." Kiddo da sauri ta koma babu jimawa ta dawo ta, ta haÉ—a mata allurar a sring.

Throw vein Mamy ta yi mata tana shafa gashinta sannan ta ce, "sorry." Islaha ta yi shiru ta kwanta lamo a jikin Mamy tana jin zuciyarta tana bugawa, tana jin ina ma a jikin mahaifiyarta take a kwance haka, da ta yi kuka son ranta ko zata ji sauƙin abinda aka yi mata. A hankali zazzaɓin ya sauka ta fara gumi, Banisha ta ƙaro ac Mamy ta gyara mata kwanciya bacci ya ɗauke ta.

Wayar Islaha ake ta kira, Banisha ta saka wayar a dnd saboda kar a tashe ta. Sai da suka tabbatar ta yi bacci sannan suka bar apartment É—in.

Sai bayan sallar azahar ta tashi, ta miƙe garau da ita bata jin ciwon kai da zazzaɓin, ta miƙe zaune tana jin bugun zuciya har lokacin. Screen ɗin wayarta ta taɓa ta ga lokacin sallah ya wuce, ta miƙe a sanyaye ya shiga banɗaki ta yi alwala ta tayar da sallah.

Tana idarwa aka fara kiran sallar la'asar, ta sake yin sallah ta jingina da gado ta rufe ido abinda ya faru yana dawo mata a idanunta.

"Wayyo Allah!"

Ta faÉ—a tana rufe ido dan bata so ta tuna abinda ya faru ko kaÉ—an, ta zare hijjab É—in jikinta cikin wani irin yanayi. Ta yi tsaki cike da takaici, ta dafe kai ta rasa tunanin da ya kamata ta yi.

A hankali aka buɗe ƙofar aka shigo, bata kalli ƙofar ta ga waye ba dan ɗakin babu haske ko kaɗan, aka kunna hasken ɗakin sai ta juya ta ga Mamy ce riƙe da plate a hannunta.

Ganin Mamy ce sai ta gyara zama ta ce, "Mamy."

Mamy ta ƙaraso ta zauna ta ce, "Ya jikin ki?" Ta fafaɗa tana taɓa jikinta ta ji babu zafi ko kaɗan.

Islaha ta ce, "na ji sauƙi Mamy, Ina yini."

"Lafiya lau. Karɓi ki ci, zaki ji daɗi sosai."

Islaha bata musu ta karɓi plate ɗin ta ci kaɗan sannan ta miƙe ta sha ruwa ta dawo ta zauna.

Mamy cikin kulawa ta ce, "meye ya yi causing zazzaɓin nan daughter?."

_ÆŠanki ne ya kwance min towel Mamy._

Ta faɗa a zuciyarta tana jin haushin Rehaan mai matuƙar yawa, amma a bayyane sai ta sunkuyar da kanta ƙasa ta ce, "Stress ne kawai Mamy, shiyasa ban je aiki ba."

Mamy ta dafa kanta tea ce, "Ayya sorry, In baki da lafiya ki dinga faÉ—awa Rehaan, zai dinga kula da ke, in ba ya nan ki faÉ—a min ko Janan. We are all health workrs, kin ji?."

Ta É—aga kai ta ce, "In sha Allah."

"Allah ya ƙara lafiya. Daada tana neman ki, kwana biyu bata gan ki ba."

"Zan je mu gaisa in anjima."

"Yana da kyau" ta faÉ—a tana fita daga É—akin.

Islaha ta bi Mamy da kallo, Mamy tana burge ta sosai dan tana kula da ita sosai, tana nuna mata soyayyar irin wacce uwa take nunawa ƴarta, tana nuna mata ƙauna da soyayya a zahiri bata kallonta ta fuskar sirika ko kaɗan. Tana son Mamy, tana girmamata sosai, zata iya yin komai saboda ita saboda yadda take kula da lamarinta. Babu wata mace a duniya da ta taɓa kulawa da ita kamar yadda Mamy take yi mata, babu macen da take kallonta a matsayin ƴa sai Mamy kaɗai. Sai dai kuma bata son ɗanta ko kaɗan, bata ƙaunar Rehaan musamman wannan mummunan abun da ya aikata mata, sai yanzu take jin haushinsa, dah da take kukan bata sonsa ba komai take ji ba yanzu ne ta tabbatar bata ƙaunarsa ko kaɗan.
Chapter 86 · 0% Book details