Sashe 59
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yadda ya jawo ta da ƙarfu ƙiris ya rage bata faɗa jikinsa ba, ta yi gaba zata faɗi, kafin Allah ya bata iko ta ta tsaya.
"Kai Salman! Me ka ke yi haka."
Duk suka juya suna kallon wanda ya yi magana.
Ameer ne ɗan Mama, Salman bala'in tsoronsa yake ji, kaf gidan babu wanda yake tsoro kamar Amir. Lokaci ɗaya ya nutsu, ya sunkuyar da kansa ƙasa.
Amir ya ƙaraso ya ce, "sakar mata hannu."
Bai musa ba ya saki hannunta, ya kalle sa ya ce, "Wuce ka tafi wajan Umma."
Da sauri ya bar wajan yana gifta su ya fashe da kuka mai sauti kamar yaro ƙarami. Sai islaha sai ta ji babu daɗi, ita wallahi tausayi ya ke bata, babba da shi yana cikin wannan rayuwa ai abin a tausaya masa ne.
Amir ya kalle ta ya ce, "Ki yi haƙuri, ina kallon duk abinda yake yi miki."
Ta yi murmuahi ta ce, "babu komai." Ta wuce sa ta tafi wajan Mama dan ta gaishe ta.
Ya bi ta da kallo ganin ta nufi wajan babarsa, sai ya bi bayanta dan shi ya É—auka daga apartment É—in Mamy ta ke.
Yana shiga ya ga yadda Mama ta ke yi mata da dariya da fara'a. Mama ta kalle sa ta ce, "Wannan shine Amir, Yayan Sameer ne, na san kin san Sameer." Ta É—aga kai alamun ta sani tana murmushi.
Amir ya ce, "Mama ban santa ba."
Mama ta ce, "ba ka nan lokacin bikin su Riyya shiyasa ba ka santa ba. Wannan ai itace wacce Daada ta aurawa ƙaninka Rehaan."
Ya buɗe ido cikin mamaki ya ce, "wow! Ai ban sani ba, kawai naga Salman yana yi nata hauka yanzu, har yana riƙe mata hannu fa."
Mama ta ce, "kai dai bari, yaron nan ya takura mata wallahi, kullum cikin bibiyarta yake yi."
"Ku kuka bar shi da ba ku hukunta shi ba."
Islaha sai ta miƙe ta ce, "Zan koma Mama."
Mama ta ce, "Na gode." Daga haka Islaha ta fita daga falon.
Amir ya ce, "Æ´ar jarida ce, na santa a social media, wannan Daada ta bashi?."
Mama cikin son ji me zai ce ta ce, "tana da aibu ne?."
Ya É—an girzgiza kai ya ce, "ko É—aya, kawai dai...." Sai ya yi shiru bai ce komai ba ya fita.
Tana shiga wajan Mamy ta samu Ikram da Janan da Banisha da sauran yara a tsaye. Banisha ta ce, "Sis zamu je outing, ki zo mu tafi."
Islaha murmushin da yake bayyanar da kyawawan haƙoranta ta ce, "Ina da aiki Banisha, zan je wani lokacin."
Janan ta ce, "Sis ba jimawa za mu yi ba, za ki iya joning."
"Na gode Janan, in sha Allah next time zan je."
"Shikenan" janan ta faÉ—a suna fita ita kuma ta koma ciki.
Tana shiga É—aki ta kira Baffa a waya, Baffa yana É—auka bai bata damar magana ba ya ce, "Ba ki kyauta min ba Islaha, sai da ki ka saka kuÉ—in nan?."
Islaha ta ce, "Baffa kuÉ—in da yawa, kuma ni ba wani amfani zan yi dasu sosai ba, shiyasa na tura maka."
"Amma ai na ce kar ki saka ko?."
"Baffa ka wuce matsayin wannan kuɗin a gare ni, wallahi ko duniya na samu ni mai iya bar maka ce. Don Allah ka karɓa, ba dan wani abun na bayar ba sai dan kyautatawa. Allah ya saka maka da mafificin alkhairi."
Baffa da murmushin jin daÉ—i sannan ya ce, "Amin Islaha, na gode sosai, Allah ya yi miki albarka."
"Amin Baffa."
Daga haka suka kashe wayar ta kalli kanta a madubi. Ita kanta ta san ta canja, cikin kwana goma da ta yi a gidan jikinta ya canja ya yi kyau, ga wani glowing na musamman da fuskarta take yi.
Ta koma gefen gado ta zauna, maganar Safeera tana faɗo mata a rai a ranta, tabbas ya kamata ta ba da kuɗin nan a orphanage, akwai abubuwan da ake buƙata da yawa a gidan wannan babu, kuma kuɗin gwamnati ba ko yaushe yake iske gidan ba, rayuwar gidan marayu indai ba ta bace private ba yana da wahala, ko rashin suttura zaman kanaa yake yi. Ta sauke numfashi mai ƙarfi, ta kwanta da baya tana lumshe idanunta.
   *
Ummi zaune take a motar Muslim ya ce, "ta tabbata Islaha ta yi aure, kuma auren bata so a san ta yi, tunda kin ga ko a gidan tv ba a sani ba. Kuma bata son auren wanda ta aura, har yanzu tana ƙudurin fitowa ta auri Saheer."
Ummi ta ce, "meye na ɓoyewa dan ta yi aure? Wa ta aura?."
"Ban san wanda ta aura ba, amma an tabbatar min da estate É—in AbdulAziz Yola ta shiga, amma ba a tabbacin gidan da take, dan kin san shi da Æ´aÆ´an sane a kewaye da estate É—in."
Ta É—an yi shiru sannan ta ce, "me take yi a estate É—in to?."
"Ban sani ba, kuma an tabbatar min da yadda aka ga ta shiga ba baƙuwa bace, kai tsaye ta wuce babu wanda ya hanata shiga."
Ummi cikin mamaki da É—aure kai ta ce, "dole akwai wani abun, me zata yi a waÉ—annan manyan manyan gidajen?."
Muslim ya ce, "yadda na gano ta yi auren shima mijin zan gano, sannan za mu yi maganinta a cikin kwanakim nan. Ki buÉ—e sabon gmail amma ba da sunanki ba, da wata number daban ba number ki ba, sai ki yi creating account a duk wani platform, ig, tiktok, facebook da ko ina."
"Amfanin me hakan zai yi mana?."
Ya kalle ta ya ce, "za ki gani, ki yi a yau, yadda kafin lokacin da za mu aiwatar da aikin mu zai daina nuna new account."
Ummi ta ce, "shikenan zan yi in sha Allah, sai na jika" ta faÉ—a tana fita daga motar, shi kuma ya ja motar ya tafi yana shirya yadda zasu biyowa Islaha.......
Nana Haleema.
RDB3P46
Nana Haleema.
*Madina.*
Umma ta shiga damuwa sosai, kwana biyu mafarkan yaranta take yi cikin yanayi na damuwa da kewar ta da suke yi, gabaɗaya ta tayar da hankalinta tana so ta koma gida. Ta rasa yadda zata yi, ga wahala, ga kewar yara, duk ta rame ta yi duhu kamar ba a ƙasar waje ta ke rayuwa ba. Ga rashin mutucin matar gidan kullum ta'azzara yake yi, sun mayar da dukanta ba komai ba, yarinya ƙarama sai ta mare ta kuma bata isa ta rama ba.
A ranar bayan ta kammala aikin gidan, ta samu matar gidan a zaune ta hakimce tana kallon tv. Umma cikin yaren da ya fara zama a bakinta ta ce, "Ina so zan je na siyo magani." Kallon banza ta yi mata Umma kafin ta yi magana ta fice, dan wani lokaci bata É—aukar raini ramawa ta ke yi.
Tana fita ta shiga gidan da yake kallon gidana da take aiki, ta shiga har parlour gidan, tana shiga wata babbar mace wacce zata yi sa'ar Umman ta kalle ta ta ce, "Ahh sannu da zuwa."
Umma ta ce, "matar gidan bata nan ne?."
Matar ta É—aga kai ta ce, "bata nan, ni kaÉ—ai ce. Zauna mana" ta faÉ—a tana nuna mata waje sannan suka zauna.
Umma ta ce, "in tazo ta ganni baza ta yi miki faÉ—a ba?."
Ta yi dariya ta ce, "haba, ai ba a yi min faÉ—a a gidan nan, suna da kirki sosai. Kin ce kina so mu yi magana."
Umma ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Lami ina cikin matsala, zamana a ƙasar nan nake so ya zo ƙarshe, na gaji."
Wacce aka kira da Lami ta É—an buÉ—e ido ta ce, "Kamar ya kenan, kin gama biyan kuÉ—in da aka kawo ki ne?."
Umma ta girgiza kai ta ce, "ban gama ba."
"Amma ki ke son tafiya?."
"Na gaji, wahala nake sha a gidan da nake, ban wuce duka a wajensu ba, ga wahala da tsawa. Kalli hannuna" ta faÉ—a tana nuna mata hannunta da fashe.
Unma ta ce, "tsabar aiki ne wallahi. A rana sai na gyara kaji hamsin, ga wanki, girki, wankan yara. Na gaji da wannan azabat, gwara na koma gida na yiwa yarana na san su na yiwa."
"Ai kuwa komawar ki gida bai ta shi ba, dole ki haƙura zuwa lokacin da za ki tara musu kuɗinsu, in kin biya su sai ki san hanyar da za ki bi ki koma."
Umma ta ce, "bazan iya ba wallahi, na gaji Lami, zuciyata ta jima da komawa nigeria, gida nake so na koma cikim yarana."
Lami ta ce, "kin san da yaran naki ki ka taho ai, ni ban ga abin É—aga hankali a nan ba, Ba dai kina samun kuÉ—i ba?."
Umma ta ce, "ina kuɗin? Har nawa nake samu da zan so na cigaba da wannan wahalar saboda shi. Har yanzu ban tara riyal dubu uku ba, kuɗin magani da ƙananun abubuwa a nan kuɗi suke ƙarewa. Kuma ni ko nawa nake samu na gwammace na haƙura na koma cikin ʼƴaƴana wallahi."
"Ba kin san inda ki ka bar su ba?."
Umma ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Basu san na taho ba, akan zuwa aikin nan sai da mijina ya sake ni, ƴan uwana suka daina nemana. Amma duk da haka na tsallake na taho aikatau ƙasar nan saboda roman bakan da ake yi min. Sai ga shi na ƙare a wahala da rainon yara da girki da wanke-wanke."
Lami ta bita da kallon mamaki ta ce, "mijinki ya sake ki saboda tahowa nan, ki ka ɓata da kowa saboda nan, ki ka bar yaran ki a nigeria ba tare da kin san a hannun wanda ki ka barsu ba?."
Umma ta ce, "abin takaicin ma duk mata ne, babbar har an kusa auren ta."