← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 110

Sashe 63

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata gama tunaninta ba ta ga Mamy da kanta ta ƙaraso ta fara zare mata hijjab ɗin, Islaha ta yi sak kamar tana turo baki tana ji kamar tsiraea Mamy zata yi mata. Babu yadda ta iya da Mamy, tana ji tana gani ta cire shi ta ajjiye, kunya ta lulluɓe islaha dan rigar bacci ne kaɗai a jikinta mai ƙaramin hannu, gabɗaya hannayenta a waje suke, ga rigar tana da wuya mai faɗi, gabaɗaya wuyanta a waje yake.

Mamy ta koma wajan Rehaan cikin sanyin murya ta ce, “Rehaan ɗago ka kwanta” ta faɗa tana ɗago shi tana kwantar da kansa a cinyar Islaha.

Islaha ta runtse ido tana jin kamar an soke ta da allura a lokacin da ya kwantar da kansa a jikinta, tana jin yadda gashinsa yake taɓa jikinta tana jin wani irin abu yana zaga jininta. Mamy bata ce komai ba ta kashe musu hasken ɗakin ta fita tana jan ƙofar.

Islaha bata buɗe ido ba har Mamy ta fita, tana jin yadda ya riƙe jikinta zuciyarta tana cigaba da bugawa da ƙarfi. Ta buɗe idanunta tana kallonsa cikin ƙaramin hasken ɗakin, ta ga idanunsa a rufe su ke har lokacin, numfashinsa kuma a cikinsa yake tsayawa. Islaha ta yi ajiyar zuciya, ta ɗarare jikinta ko hannunta bata motsawa sosai, ta ƙi sakin jikinta dan ji take kamar tana cikin wuta, ta takure kanta a jikin gadon tana ji kamar ta zura da gudu.

Motsi ta ji ya yi a jikinta, Islaha ta kalle shi ta ga ya juya yana miƙewa kamar zai tashi zaune, sai kuma ya mayar da kansa ƙirjinta, yana goga fuskarsa a fatar ƙirjinta yana sauke numfashi mai zafi.

_Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Na shiga uku ni Islaha marainiyar Allah. Me hakan ya ke nufi wai?._

Abinda take faɗa kenan a zuciyarta, jin zafin numfashinta har tsakiyar fatar ƙirjinta, dan ya kifa kansa a ƙirjinta, gashin fuskarsa yana taɓa fatar ƙirjinta dan babu komai a jikinta sai rigar, kuma tana da faɗi daga sama sosai.

Nana Haleema.

RDB3P48
Nana Haleema.

Rehaan juya kansa yake yi a ƙirjinta alamun yana jin ciwo, har lokacin numfashin yake saukewa kamar yadda ya saba yi indai zai canja kwanciya, ya kasa kwantar da kansa yadda yake so a ƙirjinta, in ya kwanta sai ya ji bai yi comfortable ba kamar yadda yake so, akwai abinda abinda yake hana kansa kwanciya yadda ya kamata, sai ya ji kamar akwai abinda ya tokare masa kansa.

Islaha tana zaune kamar an dasa ta, ta kasa motsi tana jin yadda yake juya kansa a jikinta, yadda yake juya fuskarsa a ƙirjinta kamar da gangan yake goga mata gashin fuskarsa a ƙirjinta.

Salati kawai take a ranta tana ji kamar tana aikata wani abu mara kyau, danasanin yiwa Mamy alƙawari ya mamaye mata zuciya, tana jin ina ma ta faɗa mata gaskiya ta ce mata baza ta iya ba kowa ya huta.

A hankali ta ji ya daina numfashi mai ƙarfi kamar yadda yake yi da farko, ya kwantar da kansa a ƙirjinta, ya zagaya da hannunsa ya riƙe shoulders ɗinta yadda zai fi kwanciya yadda yake so. Bai riƙe ta sosai ba, hakan ya saka tana iya moving yadda take so.

Gashin kansa take kallo dan fuskarsa gabaɗaya ya kifa a ƙirjinta, iya gashin kaɗai take kallo gabanta yana faɗuwa, ta tabbatar yana jin bugun zuciyarta a kunnensa, dan yadda take bugawa ko ita tana jin sautinta balle shi da kansa yake ƙirjinta. Kallon gashinsa kawai take yi, ta jima tana so ta taɓa gashin nan ta ji ya yake, irin nasu ne na fulani ko kuma nasu daban yake.

Kamar mai jin tsoro haka ta kai hannunta zata ɗora akan gashin kansa sai kuma ta fasa, ta sake kai hannu ta kuma kasawa, sai a karo na uku ta ɗora hannunta a gashin kansa ta shafa dan ta ji banbanci da na su, sai ta ji sa kamar roba-roba bai yi laushin nasu ba. Ƙhmashin da gashinsa yake fitarwa ya mamaye mata hanci, ta cire hannunta daga gashin tana kallonsa.

Sun jima a haka, ya jima a jikinta a kwance bata ji alamun ya yi bacci ba, dan ta san idanunsa biyu bata sani ko ya san itace a tare da shi ko bai sani ba. Bakinta ya rufe ruf, ta kasa ce masa komai balle ta ce ya ɗagata, tana jin yadda zafin da kansa ya yi yake ratsa ƙirjinta, tana jin yadda ya ɗora lips ɗinsa a ƙirjinta amma ta kasa cewa komai.

Ta juya ta taɓa wayarta da ta ajjiye akan bedside drawer, ta ga awanta biyu kenan a haka, ita kanta ta gaji da zaman, so take ta kwanta amma babu damar hakan.

A hankali ta ji yana sauke numfashi alamun ya samu bacci, jikinsa ya saki a jikinta ba kamar É—azu ba. Ta yi ajiyar zuciya jin ya yi bacci, ta sake kallonsa a lokacin ya juyo da fuskarsa tana kallon gefe, duk da ba ganinsa take yi sosai ba amma ta ga yadda fuskarsa ta É—an rame.

Ta harare shi ta ce, “Sarkin masu rakin duniya gabaɗaya, da na ce sarautar iya ta Yola ce, to na ga ta fi ƙarfin Yola kaɗai sai dai ace duniya gabaɗaya" ta faɗa tana kallon fuskarsa.

A hankali ta ke so ta zame ta gudu ba tare da ya tashi ba, dan babban abin kunya ne ya buɗe ido ya ganta a haka, girmanta zubewa zai yi a idanunsa. Tana motsawa ya motsa, ya sake riƙe ta ya cigaba da baccinsa.

Ƙasa ƙasa ta ce, "Ikon Allah! An sangarta yaron nan da yawa, yanzu tsakani da Allah baccin ma sai ya riƙe babarsa yake yi? Ji yadda ya maƙale min kamar wata matarsa. Mtsw! Wannan matarsa zata yi kayan takaici, in irina ce bamu san lokacin da zamu gaggaura masa mari ba saboda takaici. Miji irin wannan sangartacce ko wahala, shi zai rarrashe ni ko ni zan rarrashesa? Ni zan yi shagwaɓa ko shi zai yi?” ta faɗa tana ɗan zamewa ta kwanta da baya amma bata yi flat ba dan yana jikinta, itama a haka bacci ya ɗauke ta bata sani ba.

Sai asuba Rehaan ya buÉ—e ido, har lokacin yana kwance a jikinta, dan ta saki jikinta gabaÉ—aya tunda itama ta yi bacci. Ya É—ago kai a hankali yana cize baki saboda ciwon da yake ji a cikinsa, duk a zatonta Mamy ce, ya kalle ta da niyar gyara mata kwanciya sai ya ga sam bata yi kama da Mamy ba.

Cikin ƙaramin hasken ɗakin yake kallonta yana so ya gano wacece wannan, gabaɗaya rigar jikinta ta tattare daga ƙasa ana ganin laps ɗinta, ya kalli samanta sai ya yi saurin ɗauke kansa, dan rigar ta same daga sama ana iya hango rabin ƙirjinta a waje, ya kalli fuskarta ya ga bacci take yi amma a takure, kanta yana gefe ga gashinta ya tarwatse a kan gadon.

"C wife!.”

Ta furta cike da mamakin abinda ya kawo ta É—akinsa har kan gadon, har ya kwanta tare da ita.

Ya ɗauke ido daga kallon ta, yana tuna yadda ya kwanta a jikinta kafin ya yi bacci. Ya sake kallota yana so ya gano abinda ya hanasa sakewa ya kwanta yadda yake so a ƙirjinta, shi daman ya ji banbanci sosai, ya saba jinsa comfort a jikin Mamy, amma a wannan lokacin sai ya ji wani yanayi daban.

Ya ɗauke idanunsa daga kanta, dan kallon kawai ta yana sakawa ya ji wani iri a jikinsa, espacially daga ƙirjinta da yake a bayyane daga sama, ba ya so ya gani ko kaɗan. Ya zura ƙafarsa ya sauka daga kan gadon, ya miƙe daƙyar yana cize baki saboda yadda yake ji kamar ana ƙona cikinsa, ya ya shiga bathroom.

A lokacin alarm ɗinta ya fara bugawa, ta buɗe ido  ta jawo wayar ta kashe. Sai ta firgita ta miƙe tunawa da inda ta kwana, ta kalli kanta ganin rigar jikinta gabaɗaya ta tattare, kuma in ban da pant babu abinda yake jikinta. Ta kalli ƙofar bathroom ɗin tana gano haske ta ƙasa alamun yana ciki, ta miƙe tsaye ta saka hijjab ɗinta ta fita daga ɗakin da hanzari..

Kamar wacce ta yi ƙaton laifi haka koma ɗakin jikinta ya yi sanyi sosai, ta yi alwala ta yi sallah tana zaune akan sallaya tana tuna yadda ya maƙalƙale mata a jiya. Gabaɗaya jikinta ƙhamshin turarensa yake yi, kamar ɗaukar turaren ta yi ta fesa a jikinta haka take jin ƙhamshin ya mamaye ta.

A lokacin wayar ta fara vibrating kamar jira ake ta idar da sallah, sai ta kalli wayar ta ga new number ce sai ta share, a ganinta waye zai kira ta da asuba.

Tana katsewa aka sake kira sai ta É—auka ta ji ance, "Islaha Mamy ce."

Islaha ta ce, "Mamy ina kwana."

"Lafiya kau, Rehaan ya yi bacci kuwa?."

"Ya yi bacci, yanzu haka ya ta shi yana sallah."

"Ma sha Allah! Na ji daÉ—in wannan labarin sosai, kin haÉ—a masa tea É—in?."

Islaha ta É—an harari wayar sannan ta ce, "sallah na yi, yanzu zan kai masa."

Mamy ta ce, "Thank you Islaha, in da wani abun ki kira ni." Bata jira me zata ce ba ta kashe.

"Ni fa dan kina yi min kirki kwana biyu ne ya saka na ce zan kula da ɗanki, amma gaskiya bana so a takura wallahi. Haba! Ya kwana yana maƙale min jiki kamar wata matarsa, kuma yanzu na haɗa masa tea?. Ni ba abinda ya kawo ni gidan nan kenan ba, ku nemi matar aure ta dinga yi masa ta samu lada, ni C wife ce” ta faɗa tana miƙewa ta fita daga ɗakin.

Rana ta farko da ta shiga kitchen ɗin gidan, ta kunna switch a take haske ya gauraye ko ina. Ta ga babban kitchen ne iya ganin ka, mai kyau wanda da kayan alatu kala-kala. Ta ƙarasa tana kallon stove ɗin, sai kuma ta yi tsaki ganin kettel a gefe, ta zuba ruwa ta kunna ta tsaya tana jira ya yi.
Chapter 63 · 0% Book details